MAR'ATUSSALIHA
by @safhat
pege 9
Lokacin da sanar War daurin hauren tazo kunnen saliha'' sai da ta gigice'' dajin sunan habib ''hakama Hafsah wadda tasan komai a tsakaninsu'' innalillahi wainnailaihirraju un'' Hafsah nashiga uku'' Habib ne ,nasan ya aureni ne domin ya wulakanta rayuwata innalillahi wainnailaihirraju un... Tana tsaka da yin salatin nan sai ga baffan ta yashigo'' yana zuwa yace'' Saliha ,tace na'am baffa'' maza kije mijinki yana son magana dake'' jikin Saliha na rawa zuciyar ta na dukan uku'uku ta mike jiki babu kwari'' tafuta kofar gida'' tana fita sukayi idon hudu'' dashi ya sakar mata wani mayau darin murmushi wan da ita kanta batasan me murmushi yake nufiba'' ahaka dai ta daure ta kara sa inda yake''ta tsuguna zata gaisheshi yayi saurin dakatar da ita yace'' au ashe daman kina da tarbiyya'' ay nazata iya masu tarbiyya ne suke iya gaishe da wan da kashin kare ya fisu daraja'' walhi sai na koya miki tarbiyyar da kika yi missing dinta a baya, sai na nuna miki Ni Habib dan duniya ne nafiki duniyan ci'' kuma daga rana irin tayau kifara irga'' ranakun mutuwar ki'' Ni bani zankasheki ba amma wahala zata kasheki'' yana gama fadar haka yayi tsaki ya ce karuwa kawai me bin mata'' daganan kuma yasa hannu a aljihu ya debo bandir din kudi ya mika mata ''dakamar bazata karba ba '' sai tajuya taka duk idon mutane akansu yake'' hakan yasata sa hannu ta amsa'' ta juya zata tafi'' yace kuma ki shirya anjima za,a zo adaukar mini ke amarsuna ,yayi murmushi ya kashe mata ido daya ya bargurin''....
Tsayawa tai tabi bayansa da kallo''tana nazarin abin da Habib zai iya aikata mata'' tabbas tun yanzu tafara gasgata maganar Safiyya''datace in dai rashin mutuncine zata samu ubanta ''ay ko gashi tasamu tunkan taje ko ina.
Gajiya tai datsaiwa a gurin don idan tacigaba da tsayuwa hawaye zai iya zubomata abin da yafi sauki ta koma gida tanemi shawarar hafsa''
Shiga tai gidan'' ta samu hafsa'' a zaune ta yi tagumi''karasawa tayi ta kamo hannunta suka fito waje'' tafiya suka shigayi har sai da suka isa wani lungu inda babu kowa sannan saliha tace'' Hafsah nashiga uku'' bana fadamiki ba''Habib bazai aureni ba sai da wata munifar'' dan Allah ki bani shawara'' yazanyi ne'' hafsa'' kodai na gudune?" Me ki gudu idan kika gudu ina zaki'' haba saliha kidai sake tunani'' uhm,to ya kikeso nayi dan Allah Hafsah ki taimaka kifadamin yazanyi'' idan kuma bazaki iya taimakona ba gwara na gudo'' don wallahi Habib bazai barni ba kasheni kawai zai'' hmm saliha ,naam hafsa'' tayi magana cikin kaguwa'' inason ki saurareni kiji mezan fada miki'' wannan fa abu da kika ga ya faru ''daman can Allah ya tsara haka saita faru arayuwarki ''allah ya tsara dole sai kin zama matar Habib ''karki wani saka damuwa a zuciyarki kawata'' inason ki dake kamar yadda nasanki baki da tsoro to inason idan Habib ''ya cemiki (A)kicemasa (Z)don billahillaxi da alamun Habib akwai abin da yatama''kada kiji wani tsoro'' wuya bata kisa'' ko da kin mutu'' a dakin mujinki kika mutu ba adakin wani katon ba''yanzu idan kikace zaki gudu'' bafata nake miki'' ba ,ki hadu da wasu mugayen suyimiki fayde ko su illata ki'' inga ya sun cuceki'' to ko kinga da wannan gwra zaman gidan Habib'' ko banza zakici ki sha'' kimore'' habama sai na koyamiki abin da zakiyi sai kace ba kike islamiyya ba ''kinga mukoma gida kada azo ana nemanki'' .uhm saliha tayi ajiyar zuciya ta goge hawayen ta'' suka koma gida,...
*Anisa Anisa, meyasameki haka'' fadamin kukan mekikeyi'' yanaganki da jakar kaya niki__niki kodai fateeman ce ta koroni?" Anisa a guje tasaki jakar ta fada kan kirjin Hajiya Adama ta rungumeta'' tasaki kuka me sauti''zuciyarta na tukuki'' hankalin adamane ya tashi sosai'' tarasama mezatai'' bakinta har rawa yake daker ta iya buda baki tace'' wai Anisa lafiya me akai miki'' kifadamin kinkasa magana'' ko wani abunne ya samu Habib''...?
Mami'' sun cuceni'' sai da suka bari nayi nisa akan soyayyar shi'' Meyasa za,ayimin haka ''mami menarasa na ''ya mace''mene bani dashi?" Dallah Malama ki fahimtar dani meyake faruwa ban gane ba'' suwaye'' suka cuceki'' zaki fadamin ko saina ci ubanki a gidannan'' mami yau aka daura auren yaya Habib da wata, what ''hajiya Adama ta zazzaro ido tace'' kan kutumar uban can'' ammafa za a maimaita yakin Badar '' me aurefa wai dagaske kike ko dai fada kikayi Anisa ,anya kuwa kinji daidai'' za,ayi auren Habib dinne bansani ba''wallahi Allah mami da gaske nake miki'' tarkashi ayko yau '' za ayi yakin duniya a gidan Alhassan'' Ni za aywa tijara '' Ni Adama '' toni ba,a taboni bama hawa nake ballantana an tabani'' jar uba'' Anisa'' huce'' muje gidan wallahi basu isa su wulakanta min zuri aba'' nafisu dabbanta wallahi marabar mu da tinkiya wajan hauka'' Ni mutumce'' ita dabba, mota suka shiga ''suka figa'' har cikin gidan su Habib'' ko motar bata tsaya ta gama parking ba ''tafigi hannun Anisa tayi cikin gidan tana kwallawa Fateema'' kira'' kina ina bakar munafuka'' Fateema'' kufito ayita ta kare'' don wallahi yau ''mutuncin ma bansan shiba'' Fateema''munafuka ki fito ko na shigo ciki na koya miki hankali...