MAR'ATUSSALIHA BOOK 1

MAR'ATUSSALIHA BOOK 1

by @safhat

Pege 11


Hello , my name is isha'' duk maganar da take shi dai juneid idon sa na kan jari da be dago'' ya kalleta ba'' har sai da taga ji da magana ,azafafe ta fisge jaridar tace'' juneid'' magana fa nake maka'' kansa ya dago a hankula ya zuramata wadannan manyan idanuwan nasa mekama da na aljanu'' ya watsamata harara''jiki na rawa ta mika masa jari dar tace Am sorry '' banza ya mata bece komai ba ya karbi jaridar sa ya mike ya bar gurin'' bayansa tanufa da kallo'' tare da runtse idonta'' tace wow'' Juneid is very very beautiful'' atake a gurin ta hadiyi wani azababben yawu jikake kukukut'' ta sharce gurin da ya tsatstsafo mata tace Juneid sai na samu abin da nakeso '' kajira dawowata'' tana gama fadar haka ta bargurin...



Shiko juneid'' gurin Parking ya nufa'' zai shiga motarsa'' da sauri aka budemasa kofar tare dacewa'' ranka ya dade ''allah ya karamaka lafiya danisan kwana'' ameen kawai yace'' yashiga motar'' shima wan da ya bude din wata motar ya bude ya shiga'' sanna ragowar masu gadin juneid suma suka shiga tasu motar'' suka sakashi a tsakiya suka bar gurin'' tafiya sukeyi sosai'' ba su tsaya a ko ina ba'' sai bakin wani katafaren gida'' wan da Ni kaina nayi tunanin gabaki daya garin ne a gida Daya'' ashe gidan mutum dayane wato Juneid'' me gadine ya wangale musu get suka shiga'' masha ALLAH'' iya kacin gurin ajiye motocin ma abin kallone'' harabar gurin na dauke da fulawoyi masu kyau da daukar hankali'' musamman ma gefan da ruwa yake sama da kasa ''yana gudana a tsakiyar gurin'' bakaramin kyau yayiba ruwan na da launi kala biyu'' launin farko farine na biyu kuma blue'' dasauri daya daga cikin masu tsaronsa ''ya fito ya bude masa murfin motar ya fito'' yana tafiya kamar bazai yitaba sabo da tsananin isa da kasaita'' har ya isa bakin kofar falon'' gidan'' tun kan ya karasa kofar ta bude'' kofarma kadai abin kalloce''domin juyi takeyi tana haske tana walwali'' kamar dai wadda aka sa mata wayarin a ciki'' shiga yayi ''ya dan tsaya kadan ''sai ga wani basamu dan mutum nan ya karaso'' in da yake ya zame rigar dake sanye a jikinsa'' yana cire masa ya tsaya cak'' tare da cewa'' Barka da isowa yallabai'' daga kai kawai Juneid yayi ya huce'' wow masha Allah'' tarkashi idan kaji ana cewa aljannar duniya to ga ta a cikin gidan Juneid'' falon'' gidan na dauke da kujeru kala biyar'' na farko fararene inda suke a hannun yamma'' nabiyu kuma milik inda suke a arewa '' na uku kuma blue color ne suna a hannun gabas'' na hudu kuma Pink color ne suna a hannun kudu'' sai goldin me kelli da wasu fulawoyi a jikinta'' ita kuma tana a tsakiyar kujerun'' kunga idan aka lissafa kujeru 22 ne a tsakiyar falon'' gidan ahakama akwai fili'' sai wata plasma dake makale a jikin bangun dakin ''in daka san allon karatu haka ta kusan cinye bangon dakin'' daga gefan ta kuma flawar ce fara me ratsin ja a jikinta'' sai daya gefan kuma matattakala ce wadda zata kaika zuwa saman bene '' gidan yana da hawa 25 wan da kowanne daga cikin an kawatashi da duk wani dukiya na more rayuwa'' a gaskiya tsayawa fasalta muku yanayin gidannan'' sai muahekara muna yin abu Daya'' amma kowacce nabata dama ta fasalta shi a cikin idonta'' ta bani labari...


Tom bayan juneid ya hau matattakalar tsayawa yayi kawai akai'' sai gashi a saman benen'' kai jama,a iya tsaruwar falonnan tafi takasa tsaruwa''karasa wa yayi ciki da sauri'' wani mutum mesanye da jan kaya ya karaso'' ya zare masa wani don dake cikin jikinsa ''yabarsa daga shi sai turoza'' na maza'' daga nan kuma ya daukeshi be tsaya ko inaba sai bathroom'' yana ajiyesa ya fito ya jamasa kofar ya tsaya'' sai da yayi kusan minti 40 kafin juneid ya danna wata kararrawa ta sanarwa'' dasauri wannan mutumin ya juya'' ya dakko juneid daga bathroom'' ya lullube sa da wani milik din tawul ''sannan ya daukeshi'' betsaya a ko ina ba sai bedroom'' yana zuwa ya dora shi a kan kujerar dake gaban mudubi'' sannan ya fita''yana fita'' sai wani ma ya shigo shikuma bakin kayane a jikinsa'' dasallama dauke a bakinsa yashigo'' yace Allah ya kara lafiya yallabai'' sannan ya kama gashin kan juneid''ya shiga busar masa dashi'' sannan ya debi mayuka iri daban daban ya shaida masa akalla ''da nan kuma yadakko wata na ura'' ya dora masa a kansa ''bayan minti 3ya ciremasa ''saiga kanya koma kamar namace'' sai shainin yake'' manjiki ya dakko ya shafamasa a jikinsa'' bayan ya gama ne ya dauki juneid'' ya dorasa a kangado ya jamasa bargo'' sannan ya tsaya a bakin kofa'' kamar wani sakago yana jira yayi bacci ya tashi ya saka masa kaya''


TURkASHI'' tashin hankali wan da ba,a samashi rana''anyako juneid zaiso Anisa''馃 wanga mutum akwai iyayi da girman kai aradu.



'' SALIHA''


Tun da gari yafara duhu saliha tabi ta daga hankalinta ''tana ta kuka'' dontasan wallahi me rabata da Habib sai Allah ''ya zatai tun da kaddarar tace auren Habib'' bayan sallar magariba motoci kusan guda 34su kayi parking a bakin layinsu'' saliha'' suna jiran afito da amarya'' ita ko saliha tana zaune a gaban mahaifiyarsu''tana yimata nasiha akan zamanta kewar aure'' bayan angama yiwa saliha nasihane'' aka fito da ita tana kuka'' Hafsah da Safiyya na rike da hannunta'' har suka sata a mota'' ragowar mutanen gidan da makota suma suka shiga motocin aka tafi kai amarya'' gaba daya ragowar motocin gidan amarya suka huce'' Amma banda motar amarya da aka wuce da amarya gidan su Habib'' suna isa aka bude get'' sanan aka fito da amarya '' zuwa ciki'' afalo'' suka samu su Hajiya fateema da ''yan,uwan ta dana abba'' suna ta shewa'' karasawa akai da saliha gaban momy da Abba'' sukayi mata nasiha me ratsa jiki'' daga nan kuma Abba yayi musu addu'ar Allah ya basu zaman lafiya, sanan aka fito da amarya'' aka kaita gidanta da ke can cikingari'' , babu laifi gida yayi kyau ya tsaru'' babu abin da zamu ce sai dai addu,ar Allah ya san ya alkairi'' bayan anje an ajiye amarya a kangadonta'' ango ya shigo da shi da munir '' daga nan kuma kowa ya watse hatta munir bayan ya bawa Habib shawara akan ya sassauta wa saliha'' muguntar da ya shirya mata''ya tafi''



Gida dai yazana daga saliha'' sai Habib kadai a gidan'' tana zaune a tsakiyar gado fuskarta a rufe'' Habib ya funcike mayafin yace'' to uban mene kike kunshe a mayafi'' kamar wata ta allah'' Ni dai kinsan babu abin da zanyi da kazamin jikinnan naki'' wallah saina koya miki hankali '' kinga wancan dakin dana ce ayimin domin na yi kiwon kaji aciki'' to wallahi ke zan yi kiwo aciki don kece kazartawa'' karuwa kawai'' yayi tsaki ya futa.....



TURkASHI'' Habib waikai zuciyar mece dakai.