MAR'ATUSSALIHA BOOK 1

MAR'ATUSSALIHA BOOK 1

by @safhat

Pege 13



INDIA


Uhm'' bro Meyasa kake son batafin raine?" Yaya juneid''abin da yasa ban fada maka bikinba '' Ni ba auren dindindin nayiba'' ba sonta'' nakeba'' kawai dai na auretane don na koya mata hankali'' kai ma kasani yaya atsarin rayuwata banason yarinyar talakawa'' sabo da ba,afiya samun masu tarbiyya ba''stop Habib banason hauka'' ban maka dole saika auri ''yar talaka ba ,amma Ni nasan yaran talakawa sunfi ''yayan masu ku蓷i nutsuwa da hankali da tarbiyya'' Habib shawara da zan baka amatsayina na yayanka kada ka yar da ka watsar da damar ka'' dama sodaya take zuwa ma mutum a rayuwa'' inason ka rike matarka da kyau domin ina maka zaton ka auro saliha ce'' hmm yaya ay sunantama saliha amma batada tarbiyya katuwace fa'' what karuwa taya kasan haka waya fadamaka?" Yaya abokinane kuma yace 茩aruwar sa ce ''hmm Habib idan kanason cire zargi a kan matarka sai ka kwanta da ita '' ananne zaka tabbatar gaskiya ya fadamaka ko karya''allah ya kiyaye na kwanta da karuwa har abada wallahi'' okay yayi maka kyau'' Ni kagama matar auren tagari nake so amma nakasa samu'' sabo da kowacce yarin ya idan zata soni'' akwai abin da take nema a gurina''kuma Ni nafison ''yar talaka'' banason ''yar masu kudi'' sannan haryau ban ga macen da ta burgeni har naji zan iya furta mata ina sontaba'' ban ganta ba''nafison nafurta inason mace'' badai ita tafurta ba '' uhmm idan na shigo kasar zan zo na ga kanwata'' yaya kama dai na cewa kanwarka''kabari zan dai auro maka kanwa amma ba wannan rasa kunyar ba.. hhh bye sai anjima ya kashe wayar tare da lunshe kwawan idanuwansa..



IN THE MORNING


Washe gari da sassafe Habib ya mike, yanufi dakin saliha, akwance ya sameta'' sai baccinta take baiwar Allah cikin kwanciyar hankali, jijjiga kai yayi kawai ya juya kicin ya debo ruwa me sanyi'' yafito dakin ya koma ''yana zuwa ya sheka mata a jikinta'' agigice ta mike tare da furta innalillahi wainnailaihirraju un'' Habib tagani a tsaye dauke da cofin ruwa fuskar nan a hade kamar daren mutuwa'' yace'' ke daman hutu kika zo yi'' maza tashi muje''yafada tare da dakamata tsawa yana nunamata hanyar futa'' tashi tai Yan tafe tana binsa a baya har suka isa harabar gidan'' inda datti da kasa ya dankare a wajen alamar gurin yana bukatar gyra'' tsintsiya ya nunamata ta dakko'' daganan kuma ya janyo kujera ya zauna '' ya fara danna wayar sa yace'' kafin nagama abin da nake yi ''na dago naga tsakar gidanan tass'' babu duk dattinnan'' babu musu saliha ta dauki tsintsiya tasoma shara, har ta kusa gamawa sai sukaji'' sallamar su hafsa'' tsabar murna da farinciki'' saliha ta tafi da gudu ta rungume su tana murmushi'' Hafsat ce ta kalleta'' tace kay meye haka kuma amarya da ayki aykinma sharar harabar gida'' ina masu aykin'' saliha ta bude baki kenan. Zatai magana ''sai Habib ya karaso'' gurin yace'' wallahi kinganta ko da rigima na fadamata ta bari masu ayki zasu gyra amma taki''wai tafiso ta samu ladan '' ko ba haka bane Honey '' eh ehy hakane Hafsat kinsan dai malam Abubakar yace '' komai mudingayi da kanmu sai munfi samun lada tafada tana sosa kai ko ba haka bane abban hanif'' jijjiga kai kawai Habib yayi ya watsa mata harara ta gefan ido'' sanan ya huce'' ciki'' suma hucewa sukai dakin saliha'' Suna shiga dakin saliha'' tace umman hafsa'' ina kwana'' lafiya klau ''yar arbarkq'' kinga dama hafsace ta dameni'' wai sana zo naga yanayin zamanku da Habib '' karya dinga cutar dake'' sai kuma kukazo muka tarar da ku alhamdulillah'' hmm Hafsat tayi kwafa azuciyar ta tace ''bakin mugu ba ay Ni nasan me hali bazai fasa halinsa ba''shiyasa ta wanan sharar da sanyin safiyar nan sabi da bakar mugunta irintashi'' afili kuma tace amaryr Habib'' mata daya kuma gimbiya a gidan Habib'' ah dole kuyi kirari'' daman ansamu gidan hutu anbar zaman gidan langalanga'' ay dole adinga zuwa akai akai cewar Adama '' ta fada tare da rike kugu


Daman ay nasani'' babu shinka fa ko''kullum sai tuwo allallabo za,a cinye kayan yaro ko'' hhhhhh Ni banma ga amaryar ba '' ta fada tana kallo saliha'' ko dai wanan yarinyar ce me kama da ''yayan aljanu'' ah dole ya ki ''yar uwarsa , tun da naga tana da kyau'' amma kuma Anisa tafiki ki dangi da asali'' afusace Habib ya fito ya daka mata tsawa yace'' mami'' ya isa haka idan kina yimin abu ina jurewa'' to bazn lamunci ki dinga ciwa matata mutunci ba''dan Allah zaki iya tafiya ''' what habib ni kake kora'' lallai ba bu laifinka''aykin asirine ''ay daman duk dan talaka ya gaji asiri ''ga uwarka nan ma ta asirce mana dan,uwa'' Adama kifita'' nace wallahi summa tallahi kika kara minti 蓷aya anan saina karya ki''mahaifiyar tawa zaki ciwa mutunci a gabana '' futa nace''yafada yana huci kamar wani zaki''sumsum Adama ta fita daga dakin jikinta na rawa dan ta tsorata da ganin yadda Habib ya fusata'' tan futa ya kalli umman su hafsah ya basu hakuri sanan ya koma cikin dakinsa'' saliha kam'' duk da tasan bason ta yakeba amma taji dadi yadda ya nuna kishin ta a gaban adama''