5- A Friend
by @azizat
5
*..............Aaliyah.............*
A friend
"Ai sunum?" na ce da shi lokacin da na matsa kusa da shi.
Kallona kawai ya ke ba tareda ya ce komai ba.
"Mi ye sunanka?" Na maimaita tambayar da Hausa
"Aaliyah, Aaliyah ki zo in ji Baba"
Muryan Sanah ya doki kunnena. Idan akwai wanda na fi so bayan Jiji to Baba na ne, duk da ba wai muna ganin shi kullum ba ne amma duk lokacin da ya ke nan to ina son kasancewa da shi. Haka na ruga da gudu ba tareda wannan ɗan fulanin ya gayamin sunan sa ba.
Lokacin da na shiga gida sai da kowa ya san da labarin ɓayawon radio. Jiji ma da ke goge-goge a kitchen sai da na bi ta na bata labari, ta yi ta dariya. Kamar yadda Baffa Manu ya ce mini ba ɓarawon radio ba ne haka ma Jiji ta ce min. Na ce "to waye shi? Miyasa ya shiga gidan ku?"
Buɗan bakin Jiji ta ce "Hamman ki ne ya zo Aaliyah"
Zamana da Jiji na koyi yaren fillanci duk da harshe na a lokacin ya fi ƙwarewa a Hausa da Kanuri harta yaren Amma na da ta ke min ba wani ji na ke ba kamar yadda na ke jin fillanci saboda sabo da Jiji. Ita Amma ma munfi yin Hausa da ita.
"Hamma na kuma?" na sake tambaya.
"Ko ba kya son shi?" Jiji ta tambayeni
Ba tareda na san cikakkiyar ma'anar kalmar so ba, ba tareda na san sarƙaƙiya da ke tattare da kalmar so ba na furta " Ina son shi Jiji"...
Da yamma da Jiji ta gama ayyukan ta ta ɗaukeni mu ka wuce gidan su. Anan na sa ke ganin yamutsatstsen yaron nan yana zaune a ƙofar gida yana kallon su John da Shina yaran dreban mu da gardener su na wasa.
Na zauna kusa da shi na ce " wai kai Hamma na ne?"
Bai min magana ba sai ma kallona da ya ke yi. Ganin kallon yai yawa ya sa na kai hannuna na tsokale ma sa ido, na tashi da gudu na shige gida ina dariya. Abinda na tsammanta shine ya biyoni ya dakeni kaman yadda yayuna Bukar da Aliyu su ke idan na tsokale su amma wannan yaron ba abinda yai, bai biyoni ba kuma bai min magana ba. Haka na dinga fitowa ina jan koɗaɗɗiyar rigarsa sai na shige gida da gudu amma ko ajikinsa. Ina cikin haka na ci tuntuɓe na faɗi ƙasa, baki na ya bugi sumunti sai jini. Nan take na fashe da kuka, a wannan lokaci ya taso da sauri ya ɗaga ni yana karkaɗe min jiki na yana faɗin "shannu, shannu ka ji" da gurɓacacciyar Hausar sa. Jin maganan sa a karo na farko ya sa na dena kuka na zuba ma sa ido saboda rashin maganar sa run farkon ganin shi ya sa na ɗauka ko baya magana ne.
Jin kuka na ya sa Jiji ta fito da sauri ta ɗaukeni ta shige da ni ciki tana mini sannu.
Tun daga wannan rana na samu sabon abokin wasa duk lokacin da na je gidan Jiji. Maimakon da da nake maƙalewa Jiji yanzu wajen Hamma na ke maƙalewa. Ba ya damuwa idan na tsokale shi haka nan ko sau goma zan ce ya goyeni ko ya min doki baya min mu su. Cikin ƙanƙanin lokaci sunan Jiji ya fara ɓacewa a bakina, yanzu taɗi na baya wuce Hamma na Hamma na.
Hamma bai cika magana ba amma duk lokacin da na takura shi akan ya bani labari sai yai ta bani labarin shanun su da labarin gona, ko ya bani labarin Rafin da su ke zuwa su yi wanka. Ina son labaran sa, ba na gajiya da su haka nan shi ma ba ya gajiya da maimaitamin labaran a duk lokacin da na buƙata.
Duk da ƙarancin shekaruna a wannan lokacin bai jima ba na fahimci Hamma ba ya zuwa makaranta. Duk da kuwa ya ce min a chan ƙauyen su yana zuwa makaranta idan hantsi yai kuma ya wuce kiwo.
Nan na fara takura Jiji akan a saka Hamma a makarantar mu. Jiji ta kan ce mini za a sashi amma sai maganarta ya zama ƙanzon kurege.
Sai na koma damun Amma na. Hmm ita kan rana na biyu da na kawo maganar da faɗa ta ce min na samu Baba na ba ta son shirme. Haka na fita da gudu ina kuka na wuce sashen Baba amma bayanan, na yi ta zaman jiran shi ƙarshe anan falon sa bacci ya ɗaukeni. Cikin bacci Baba ya shigo falon ya ɗaukeni zai maidani wajen Amma na ya ji na ce "Baba a sa Hamma na a makaranta"
Sai da ya kai ni ya ke tambayar Amma na waye Hamma dan shi ya manta wa na ke kira da Hamma.
"Ɗan ƙanin mijin Jijiɗo ne da ya ke zama a wajen su"
Ta bashi labarin yadda muka yi kafin na je falon sa. Ya ce zai wa Manu maigadi magana akan ya sa Hamma a makaranta.
Sai dai abu da ɗan kasuwa zuwa wayewar gari har ya manta wani maganan Hamma.
Ni kam maganan na rai na da shi na kwana da shi na tashi. Da safe ma sai da na yiwa Amma magana, ta ce min Baba na ya ce za a sa shi, nan ta ke na fara murna. Sai dai kwana biyu shiru ba maganan makaranta...
Da gudu na faɗo falon Baba inda ya ke ƙarɓan baƙin sa ma su mahimmanci.
"Baba ba a sa Hamma a makaranta ba" abinda na faɗi kenan lokacin da na ƙaraso wajen sa ba tareda na yi la'akari da baƙin da ke wajen ba.
"Je ki Aaliyah za a sashi"
"In in" na girgiza kai tareda fara bubbuga ƙafa ina cewa.
"Ai haka Amma ta ce, amma ba ka sa shi ba"
"Aaliyah!" Ya daka min tsawa nan ni kuma na ɓarke da kuka.
"Zo nan 'ya ta" ɗaya daga cikin baƙin ya faɗi.
Na kalleshi sosai, ban taɓa ganin sa ba amma kuma murmushin da ke fiskar sa ya sa na ji zuciyana ta yadda da shi. Na yi saurin ƙarasawa wajensa ina goge hawaye ina shan majina.
Ya ɗaukeni ya ɗaura ni akan cinyar sa ya ce " wa ki ke so a sa a makaranta"
Na ce "Hamma"
"Waye Hamma?"
"Hamma ɗan gidan Jiji mana"
"Alhaji Wamako ka ƙyale wannan mai surutun, rigimarta ya fi ƙarfin ta"
Baba ya faɗi.
Shi kam sai murmushi ya ke yi yana faɗin " 'yata ba ta da rigima, ka bari na ji damuwarta"
Ya kalleni ya ce " yanzu mi za ayi miki"
"A sa shi a makaranta"
Ya shafa kaina ya ce " gobe-gobe za a sashi a makaranta"
"Idan ba a sashi ba fa?" Na tambaya cike da damuwa
"Ni da kai na zan zo na kai shi"...
Daga wannan rana kuka na ya ƙare aka saka Hamma a makaranta sai dai ba makarantar mu ba, sannan ba da mu ya ke zuwa ba, mu ana kai mu a mota shi yana tafiya a ƙafa. Wannan ma na yi ƙorafi akan dole sai ana kai shi tareda mu. Sai dai ban san ya aka yi ba tunda Hamma ya ce shi ba ya son shiga mota sai na dena ƙorafi.
*..............Sa'eed...........*
The rich girl versus the poor boy
Ban san ya aka yi ba shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanina da Aaliyah sai dai al'amari na Allah rubutacce ne kuma tsararre. Tun ba na iya ma ta magana sosai har na fara yi, tun ban fahimtar ta sosai har na fara yi. Duk da shekaru biyar cur da na ba ta rata, hakan bai hana mun zama tamkar abokai ba. Aaliyah to koremin zaman kaɗaici da rashin sabo da na ke yi farkon zuwa na. Mu kan ci abin ci tare mu yi wasa tare sannan mu yi karatu tare. Yayinda sauran yara tsarana su ke ball a ƙofar gida ni ina chan garden ina yiwa Aaliyah do ki ko goyo.
Dalilin Aaliyah aka sani makaranta. Ita ta dinga kuka tana birgima har sai da aka sani a makaranta.
Wata rana ina zaune ina yin Homework (aikin gida) sai ga Aaliyah da kaya a hannunta. Tana zuwa ta watsa min ta ce "gashi Hamma, kai ma ka sa kaya ma su kyau"
Na tsorata matuƙa da wannan kaya saboda irin kayan da su Aliyu ke sawa kenan. Na ce "Aaliyah wa ya baki kayan nan"
Sai ta fashe da dariya tana yi tana rufe baki.
Na ce " ta Aliyu ce ko?" Saboda Aliyu shi ne tsarana ko da na girmeshi ba zai fi da shekara ɗaya ba.
Maimakon ta ɗau kayan sai ta koma da gudu tana faɗin " barin je na ɗauko ma wasu"
Kafin na ma ta magana ta yi nisa. Na ɗau kayan na shiga na nunawa Jijiɗo, ai kuwa ta tisani a gaba muka wuce sashen Hajia.
Jijiɗo ta nunawa Hajia kaya tana ba da haƙuri. Hajia ta ce ba komai mu tafi da kayan wanda riga biyu ne da wando ɗaya.
Ana haka sai ga Aliyu ya shigo ɗauke da Aaliyah, ya direta gaban Hajia.
"Mama idan na daki Aaliyah ki ce na cika mugunta. To ga ta nan na kama ta tana ɗauka min kaya wai za ta kai wa Sa'eed"
"Ni a Hamma zan kaiwa"
Ta katse shi da ƙarfi.
Hajia ta ce " yanzu dai ka yi haƙuri, ka ga Aaliyah yarinya ce"
Ta ɗauki Aaliyah ta ce " 'yar fara ba a ɗaukan abin mutane sai an tambaye su kin ji"
"Mama ai shine ya ce wai a John zai ba wa kaya, wai ba zai ba wa Hamma ba"
Hajia ta ce maza ya je ya ɗauko kayan sa da su ka tsufa ya kawomin.
Aliyu ya fita yana ƙunƙuni.
A ranan saboda Aaliyah sai da na samu kaya kala takwas da takalma biyu. A wajen Aliyu tsofaffin kaya ne amma a wajena kaya ne ma su kyau, domin kaya ne na yayi. Tun daga ranan maimakon su John da ake bawa tsofaffin kayan Aliyu sai ya zama ni ake bawa waɗannan kaya...
Cikin shekaru biyu na gama primary saboda aji huɗu aka sakani lokacin, saboda na iya karatu da rubutu. A makarantar mu ta ƙauye ina aji shida na taho Maiduguri sai dai gwaji da su ka min lokacin da za a sa ni a makarantar ya sa dole su ka maida ni aji huɗu.
A shekaru na goma shahuɗu na fara aji ɗaya a sakandare yayinda su Aliyu da su John sa'annina suka min fintinkau.
Cikin shekaru biyu na gane banbanci tsakanin ni da Aaliyah. Aaliyah 'ya ce a gidan Bulama sunan da ke sa a kalleka da daraja a kuma mutuntaka. Ni Sa'eed kuma ɗan Baffa Manu maigadi ne. Wannan banbanci da kuma ƙara girma da na yi ya sa na ke ƙoƙarin ja baya da Aaliyah, sai dai a wajen Aaliyah ba ta bani daman yin hakan ba saboda tana ƙara girma da wayo tana ƙara shaƙuwa da kusanci da ni.
Jijiɗo da Baffa na koyaushe suna ƙara nusar da ni akan Aaliyah musamman da ya ke ni na fita wayo sai dai abinda ba su sani ba shine Aaliyah ta jima da zama jinin jiki na. Aaliyah ta jima da mamaye ruhina.