6- a Girl, a Woman
by @azizat
6
*..........Aaliyah.........*
A girl, A woman
Abubuwa dayawa sun faru a tsakanin shekaru uku da zuwan Hamma Sa'eed gidanmu. Hamma Sa'eed ya zamo tamkar wani ɓangare na jikina wanda idan babu shi ba zan rayu ba. A gidan mu na koma daga Aaliyan Jiji zuwa Aaliyan Sa'eed. Banida ɗanuwa ko ƙawa dana shaƙu da su sama da Hamma Sa'eed. Sanah da muke kusan kai ɗaya, ita ce kaɗai ƙawata ta kusa dani bayan Hamma.
Mu kan je ya koya mana karatu domin Allah ya bashi ƙwaƙwalwa, daga ƙauye ya zo amma ya ɗara mutane dayawa da su ka yi karatu a birni.
Watarana ina shekara goma muna ɗakin Hamma yana koya mana karatu, da ke ni da Sanah ajinmu ɗaya, duk da kuwa ta girmeni.
Abunda Hamma ke koya mana na riga na gane tuntuni shiyasa ya maida hankalinsa kan Sanah domin itama ta gane. Cewa yai na koma gefe na dinga practicing wasu lissafi da ya bani. Ina cikin yi na hangoshi da Sanah su na dariya. Hamma ya kan yi raha da barkwanci lokacin kowa mana karatu musamman darasi na Maths. A ƙarancin shekaruna sai na ji wani kishi ya mamaye ni, na ji ba abun da na ke ji sai haushin Sanah. Ji na ke za ta ƙwacemin Hamma Sa'eed ne.
Na taso da sauri na zo na ture Sanah.
Sanah ta kalleni "Aaliyah ba na son tsokala kinga muna karatu"
"Ki dena zuwa karatu wajen Hamma. Hamma na ne ni kaɗai" ban san maganar da na yi a ranan magana ce da ta ƙunshi abubuwa dayawa ba.
Ba ranan ne muka fara karatu a wajen Hamma tare ba, kusan shekara biyu kenan.
"Aaliyah ba yayar ki ba ce" Sa'eed ya ɗan daka mini tsawa.
"Ta tashi ta tafi, ba ta iya komai ba dama"
Sanah ta fusata fuuuu ta tashi ta fita.
Sai da na zauna ya kalleni ya ce "tunda kin koreta ke ma tafiya za ki yi angama karatun yau ɗin"
Na yi-na yi da shi amma ya ƙi kulani ya ce sai dai na je na bawa Sanah haƙuri, cikin fushi na kwashi littattafaina na tafi. Maimakon na tafi gida sai na wuce garden na je na zauna ina wasa.
Kusan awa ɗaya da rabi ina cikin wasa sai ga jini ya biyo ƙafata na tsorata da ganin jinin nan sai na fashe da kuka dan na ɗauka ciwo na ji a cinyata duk da kuwa ba wai ina jin zafi bane.
Ban je cikin gida ba domin na kai kuka na wa Amma ko wa Jiji wanda na san tabbas tana kitchen tana haɗa mana abincin dare, ban je wajen Sanah ba wanda ba mu jima da yin faɗa ba. Ban je wajen Hajia ba wanda ta ke so na, ta ke son surutu na. Sai na wuce wajen Hamma Sa'eed wanda na san ina fushi da shi amma kuma shi kaɗai zan nunawa ciwo na.
Hamma Sa'eed yana zaune yana karatun wani littafi na faɗo ɗakinsa. Ɗaki ne da kafin zuwan Hamma 'ya'yan Jiji ke kwana amma kuma tun zuwan sa ɗakin ya juye ya koma na shi yayinda Jiji da Baffa ke amfani da ɗaya ɗakin.
Ina kuka na fara ɗaga skirt ɗina ina nuna ma sa pant ɗina da ya jiƙe da jini. "Hamma jini, Hamma ciwo na ji"
A shekarunsa shabiyar ba zan ce ga takamaimai inda ya samu ilimi gameda jinin haila ba. Amma bayan ya duba sai ya gane ba ciwo bane.
Abinda ya fara ce min shine "ki dena kuka, ba ciwo bane"
"To minene?" Na tambaya cike da wasu tambayoyin a cikin ƙwaƙwalwata.
"Bari mu je wajen Jiji"
Akwai wani mayafi da ya ke rufuwa da shi sai ya ɗauko ya ɗaura mini ya ce muje wajen Jiji.
"Idan na yi tafiya jinina zai ƙare Hamma"
Bai ce komai ba sai ya tsugunna, ni kuwa na hau bayanshi.
Ta ƙofar kitchen mu ka shiga inda mu ka tarar da Jiji tana yin farfesun kaza.
Yana direni Jiji ta haushi da faɗa " Lamiɗo ba na hanaka goyon Aaliyah ba, kai ba ka jin magana ko"
Bai ce komai ba saboda shi dama ba mai yawan magana bane balle kuma duk lokacin da babba ke magana to za ka ga Hamma Sa'eed ya yi shiru idon sa a ƙasa.
"Jiji jini a jikina, ki zo ki min wanka"
"Jini kuma?"
A wannan shekaru babu irin gurɓacewar zamani inda ake yawan faɗe musamman har acikin yara saffa. Jiji ba ta kawo wannan a ranta ba sai dai ta tsammanta ciwo na ji.
Ta kama hannuna mu ka bar kitchen ɗin.
A wannan rana Jiji ta zaunar da ni tamin bayani gameda jinin haila cikin ɗan iliminta na gargajiyanci. Ni dai a lokacin ko kashi goma ban ɗauka ba cikin kashi ɗari na abubuwan da ta faɗa min. Sai ma ƙara dulmiyar dani da ta yi musamman yadda ta yi ta jajanta min wai na girma, ta dinga karanto min farillai da mustahabban mu'amala da Hamma Sa'eed wanda jinsu kawai na ke amma yadda su ke shiga haka su ke fita ta ɗaya kunne na.
Abu da mai surutu babu wanda bai san labarin jini na ba, sati uku kenan Baba ba ya gida ranan da ya dawo tare su ka dawo da abokinshi Alhaji Wamako wanda ya zamo tamkar Baba na, duk lokacin da ya zo gidan mu sai ya taho min da tsaraba, sannan ko da su na meeting ne to Baban Lagos kaman yadda na ke kiranshi zai ɗaukeni a cinyar sa ko kuma ya barni na yi ta wasa a wajen.
"Baban Lagos na fara jini" abinda na faɗa kenan lokacin da ya ɗaukeni bayan na ma sa oyoyo.
Baba na da shi Alhaji Wamakon su ka tsaya kallon-kallo
Baba ya ce "Aaliyah shekarun ki nawa?"
Na ɗan ɓata fuska na ce " Baba har ka manta. Ba na yi birthday ba ranan"
Na ɗan ɗaga murya na ce " I am 10yrs 7months now"
Haka na zauna na basu labarin jinina tirtiryan tun daga faɗan mu da Sanah har zuwa yadda na ga jinin.
Alhaji Wamako ya ce " Masha Allah, ashe ɗiyata ta zama budurwa, sai a fara haɗa kayan gado kawai"
Baba ya ce "wannan ɗin. Allah ya kaimu lokacin"
Alhaji Wamako ya ce " 'yata ai sai ɗana, wagga kyau da kwanya ai sai gidana"
A wannan lokacin ya min tambayan da na yi dana sanin ba da amsarta.
"Za ki auri ɗana ko Aaliyah?"
Ta ya zai min wannan tambaya a wannan lokaci, ta ya zai sa na yankewa kaina hukunci bisa abin da ban da ilimi a kai.
Na gyaɗa kaina alamar e ba tare da na san me tambayar ke nufi ba.
Abinda ban sani ba shine wannan amsa tun daga wannan lokaci ta ɗaureni gaba ɗaya ta hanani sakat ta hani samun abinda zuciyata ke so...
Al'amari na gidajen ma su kuɗi sai addu'a. Na fara al'ada da ƙarancin shekaru amma ba ni da wani ilimi mai inganci akan sa. Amma ta was busy da harkokin kasuwancinta, ta sadaukar da ragamar tarbiyata wajen Jiji, Jiji tana iya ƙoƙarinta a kaina amma ita kuma ba ta da wani ilimi mai zurfi, yawanci bayanan ta sunfi kama da gargajiyanci. Hajia na ta shirye-shiryen bikin 'yarta Falmata. Aje nan aje chan duk dan ana so ayi bikin da duniya za ta shaida.
Baba harkokinsa ba sa bari ma ya zauna a gida na cikakken sati biyu ba tareda ya yi tafiya ba. Mukan je makarantar Allo daga baya ni da Sanah mu ka watsar. Aka ɗauka mana malami yana zuwa yana koya ma na karatu. Kuɗin gidan mu ya sa malamin ba ya iya aiwatar da abinda ya kamata. Ba zai iya ma na tsawa ko ya bulale mu ba, mun iya ba mu iyaba a haka dai ake ta tafiyar, wata rana ma ya zo mu ƙi fita.
Hamma ya na koyamin ƙur'ani wasu lokutan saboda tun kafin ya zo yai sauka ta tartil hakanan tun farkon zuwan sa Baffa Manu ya kaishi wata makaranta yana hadda yana karatu.
Na tafka ƙwaɓa dayawa farkon balaga ta. Musamman saboda ƙarancin shekaruna da kuma rashin fahimtar abin. Babban ƙwaɓar da na fara tafkawa shi ne sallah cikin jini. Jiji ta ce min ba'a sallah idan ana al'ada amma ni kam ina yi wani lokaci ma sai na tada sallar sai in tuna maganar Jiji amma sai na dake na ce ai Hamma ya ce ba kyau a bar sallah.
A wata na uku da fara jini na, wata rana ina ɗakin Hamma muna karatu, saboda ko da baya koyamin karatun makaranta haka za ka ga mun samu littafin labarai na turanci muna karantawa. Sai aka kira Sallah, akwai masallaci a ƙofar gidan mu dan haka sai Hamma ya fita, idan akwai babban abinda zan shaidi Hamma da shi a iya tarihin rayuwar mu tare to sallah ne. Yayyena su Bukar da Aliyu ba su damu da sallah ba a wannan shekaru na ƙuruciyar su, banda kiɗa da kallo da zuwa party ba abin da su ka fi bawa amanna.
Bayan Hamma ya tafi na cigaba da karanta labarin saboda na ji daɗin sa, chan na tuna idan Hamma ya dawo ya tadda ban yi sallah ba zai min faɗa. Sai na tashi na je banɗakin su na yi alwala duk da kuwa na san ina cikin jini. Na zo na tada sallah, ina raka'an ƙarshe Hamma ya shigo.
"Aaliyah sallar mi ki ke yi?"
Na yi gyaran murya.
"Ki katse sallan nan"
Ban katse ba sai dai na yi dungure-dungure na ƙarasa a gurguje. Dama sallar ta wa ya aka ƙare dan ma Hamma na ƙoƙarin gyara mini.
"Waya ce mi ki ana Sallah idan ana al'ada?"
"Ba ka ce min wanda baya sallah ɗan wuta ba ne"
Sai da ya sa na zauna kusa da shi sannan ya fara min bayani bayanin da ya shigeni farat ɗaya saboda Hamma na ne ke min su. Tambayoyi kam ya sha su wassu ya amsa wassu ya ce bai sani ba amma zai tambaya.
Tambaya ta ƙarshe da na ma sa shi ne " Hamma wai inji Jiji idan ka taɓani zan yi ciki, da gaske ne?"...
Sai da na shekara ɗaya da fara al'ada kafin Sanah ta fara. Da ke tun lokacin dana fara ana cewa na girma sai abin ya shige ni, sai na dinga tsokalarta ai na rigata girma. Wata rana da na isheta sai ta ce "ai nono na sun fi na ki"
Ranan na wuni gaban madubi ina duba kai na ina ganin 'yan ƙananun nono na wanda na san tabbas ba su kai na Sanah girma ba.