TSOHUWAR SOYAYYA

7- Feelings

by @azizat

7

*...........Sa'eed.........*

Feelings

Shekaru bakwai kenan da zuwa na Maiduguri. Wannan gari mai Albarka ya zame mun tamkar asalina. Ina jin daɗin garin, ina kuma son garin sosai. A shekaru bakwai ɗin nan sau uku na je ƙauyen mu, na farko lokacin da Inna ta ta rasu shekara ɗaya bayan na zo Maiduguri mu ka je ta'aziya tareda Jijiɗo. Na biyu mu ka je da Baffa Manu lokacin da mahaifiyar sa ta rasu, sai na uku wanda ya zamo min wani tarihi mai muhimmanci a rayuwa ta.

Ina shekara shatakwas, lokacin ina aji biyar a sakandare mijin babbar 'yar Jijiɗo ya rasu, lokacin ana hutu sai ya zama na tare mu ka tafi.

Ban sanar da Aaliyah ba saboda sun tafi Lagos bikin wata cousin ɗin su.

Su na dawowa daga tafiyar su, ko cikin gida ba ta shiga ba ta yiwo wajen mu da gudu. Kwana biyar kenan ba sa gida.

Da ta zo ta samu ɓangaren mu a garƙame da kwaɗo. Ta shiga wajen su Mama John ta tambayi ina mu ka je. Mama John ta ce mun tafi ƙauye an ma na rasuwa.

Daga wajen ta fara kuka ta shige gida da kuka. Kai tsaye ta je ta fara haɗa kayanta, da ta gama ta fito da jaka ta samu Amma a ɗaki tana baccin huce gajiya.

Yadda ta ke ƙwala sunan ta ya sa tun kafin ta shigo ɗakin Amma ta farka.

" Aaliyah ki na so na zane ki ko? Yaushe mu ka dawo za ki fara damuna da shirmen ki"

Cikin kuka ta ce "Amma wai Hamma da Jiji sun tafi ƙauye, zan bi su"

Takaici ya sa Amma ta ce " Allah ya kiyaye"

Aaliyah ta fito da jaka ta nufi gate. Ma su gadi sun tafi Sallah, Ɗaya Maigadin da baya sallah kuwa ya kwanta a kan benchi yana hutawa bacci ya tafi da shi. Ta je ta buɗe ƙaramar ƙofa ta fita.

Taxi ɗin da ta tsare tace da shi ƙauyen Durum zai kai ta. Ganin kayan jikin ta ya san 'yar gidan manya ce. Ƙarancin shekarunta da rashin wayo da ya bayyana a fuskar ta ya sa ya gane ƙila guduwa za ta yi. Ya ce ta shigo.

Su na tafiya ya fara ma ta tambayoyi akan mi za ta je yi a Durum, shi da ko sunan ƙauyen ma bai taɓa ji ba sai lokacin.

"Zan je ganin Hamma da Jiji ne"

"Ayya 'yan mata, Ashe ki na son Hamma da Jijin na kin nan sosai. Amma ban ga kin ɗauka mu su tsaraba ba, na ga kamar jakar kaya ne a hannun ki"

Aaliyah ta dafe kai "oops ai na manta. Mu koma gida sai na ɗauko mu su tsaraban Lagos"

Dama abinda mai taxi ɗin ke so kenan.

Lokacin da ta ce gidan Alhaji Badamasi Bulama zai kai ta sai da yai mamaki.

A ƙofar gate ɗin gidan ya tsaya ta fita da gudu ta fara buga gate ɗin. Mr Francis ya leƙo ta ɗan ƙaramar ƙofa da akayi ajikin gate ɗin sai ya ga Aaliyah. Da sauri ya buɗe ma ta ƙaramar ƙofa ta shigo, yana ma ta magana ma ita kan ko ajikin ta tsarabar Hamma da Jiji ne a gaban ta.

Lokacin da ta fita daga taxi yai dai-dai da karyowar kwanar motar Alhaji Badamasi. Tsayawa su ka yi dreban sa ya fita ya je ya kirawo mai taxi ɗin. Mai taxi ya zo jikin window jikin sa na rawa duk da kuwa shi niyyar sa da Aaliyah ta shiga sai ya miƙawa ma su gadi jakarta ya kuma gaya mu su abin da ta ke niyyar yi. Sai dai abinka da ma su kuɗi yanzu sai a fassaraka da wani manufar.

Bayan yai wa Alhaji Badamasi bayani Alhaji ya fito da kuɗi ya bashi sannan ya ce dreban sa ya ɗauko jakar Aaliyah...

Aaliyah tana chan tana haɗa tsaraba ba ta san mi ake ciki ba sai da ta fito falon su ta ga Alhaji zaune ga jakarta a falon.

"Kiramin Amman ki"

"Baba zan je wajen Hamma da.."

"Je ki kiramin ita na ce" ya daka ma ta tsawa.

Ta juya da gudu ta tafi. Lokacin da Amma ta fito faɗa ya fara ma ta akan tana ina Aaliyah ta haɗa kaya har ta fita daga gidan nan wai za ta je ƙauye ba ta sani ba.

"Alhaji na ɗauka shirme ta ke yi ai"

"Shirme? Idan da wani abu ya sameta nan za ki gane shirme. Ba na son irin wannan sakacin Mariya. Aaliyah ta fara girma ki sa ido akan ta" daga haka ya fita, haƙurin da Amma ke ba shi ma bai saurara ba.

Wannan ranan Aaliyah har mari sai da ta sha a wajen Amma.

Aaliyah ta ƙauracewa cin abinci, ranan farko Amma ba ta damu ba ta ce idan yunwa ya cita za ta nemi abinci da kan ta. Rana na biyu da yamma mai'aiki ta samu Amma da cewa har yanzu Aaliyah ba ta ci abinci ba kuma ta ki buɗe ƙofa.

"Yarinyar nan ba za ta kashe ni ba, ni kam ko Jijiɗo mayya ce wannan abu da mi yai kama"

Extra key ta nemo ta buɗe ƙofar ɗakin Aaliyah, anan ta ga Aaliyah na kwance zazzaɓi ya rufeta. Ranan Aaliyah sai kwanan asibiti.

Amma ta yi faɗan har ta gaji amma Aaliyah ta ƙi cin abinci, sai da aka kira Alhaji Badamasi wanda ba ya gari ma lokacin. Aka bawa Aaliyah wayar tarho su ka yi magana da Baban na ta, ya ma ta alkawari da ta ci abinci ta warke za a kaita wajen Jiji.

Hakan kuwa aka yi. Duk da Alhaji yana da 'ya'ya mata amma Aaliyah yarinya ce mai shiga rai, ta kasance 'yar gaban goshin Baban ta.

Kwana uku da murmurewan ta Alhaji ya sa aka tsara ma ta tafiyar. Dreba aka sa ya kawo su Bauchi zuwa Toro zuwa ƙauyen mu Durum. Ita da Sanah, saboda itama ta ce za ta je.

Ina zaune kan wani dutse kusa da rafi ina karatu kamar daga sama na fara jiyo muryan Aaliyah "Hamma Sa'eed, Hamma Sa'eed"

Na ɗan girgiza kai na, dan a ganina kunnena ke min ƙarya. Ta ya zan ji muryan Aaliyah a nan, bayan Aaliyah ta min nisa.

Sai dai wannan kira sai ƙara kusantoni ya ke. Na ɗaga ido sai na hango Aaliyah tana gudu, hular ta a hannu tana sanye da doguwar riga irin ta turawa wanda aka fi kira da 'yar kanti a lokacin, rigan ya tsaya iya silangarin ƙafarta. Iska na kaɗa dogon gashin ta tana dariya. Na tsaya kawai ina kallon ta, sai ya zama kaman ranan ne na fara ganin ta lokacin tana shekara bakwai, sai dai yanzu wannan yarinya ta zama budurwa she's now 13. Ban motsa a wajen ba ban kuma ɗauke ido na akan ta ba har ta iso.

"Hamma ta ya ka hau dutsen nan? ya yi tsayi dayawa" ta faɗa tana haki.

"Tsaya barin hauro da ke" na faɗa ina mamakin ganin ta.

Ina saukowa daga dutsen domin na hauro da ita kawai sai ta faɗa jiki na. A da duk lokacin da ta rungumeni ba na jin komai ko dan akwai ƙarancin shekaru ne, ko dan kuma da ɗin bana jin abinda na ke ji gameda Aaliyah yanzu.

"Hamma i miss you, shi ne ka tafi ka bar ni ko" ta faɗa tana ƙara shigewa jikina.

A lokacin ji na yi na shiga wani hali na daban, wani yanayi wanda ke da wuyar fassarawa. Ban san ya akayi kalmomin su ka fito a baki na ba " I miss you more Aaliyah"

Mu ka zauna a saman dutse tana bani labarin yadda akayi har aka bari ta zo. Tana cikin labari na karɓi hular hannunta na sa ma ta aka na ce "Aaliyah ba na hana ki barin gashi a buɗe ba"

Ta turo baki " Hamma ni kam"

Mu ka zauna a saman dutse kusan awa ɗaya da 'yan kai muna hira. Da magriba ta gabato mu ka koma gida.

Sati ɗaya Aaliyah ta yi a ƙauyen mu. Kullum mu na fita na nuna ma ta yadda ƙauyen mu ya ke, mu je gona, mu je kiwo tare, mu je rafi. Aaliyah was so excited and fascinated with my village, ni kuma na fi kowa farin ciki da zuwan ta.

Da su ka yi sati dreba ya dawo ɗaukan su saboda makaranta da za a koma. Mu ma albarkacin Aaliyah mu ka shiga mota aka tafi da mu.

Wannan rikici da Aaliyah ta yi kafin a barta ta zo ƙauyen mu shi ya jawo Jiji ta fara ja baya da Aaliyah hakanan ni ma ta min faɗa akan na rage mu'amala da Aaliyah saboda yanzu ba yarinya ba ce.

Sai dai Aaliyah idan tana son abu ba mai hanata. Duk wani hannunka mai sanda da Jiji ko ni ke ma ta kamar ba ta san ma munayi ba, sai ma ƙara shige ma na da fa ke yi.

Ni kam na shiga wani hali domin kuwa zuciyata ta na jin wassu sabbin shauƙi gameda Aaliyah, zuciya ta tana raya min wani al'amari mai daɗi gameda Aaliyah wannan al'amari da ya ke da kamar wuya. Amma ko da mafarkine to zan so na cigaba da yin wannan mafarki har ƙarshen rayuwa ta...

Kasancewa jarrabawata ta yi kyau sai aka awarding nawa scholarship karatu a Cambridge da ke ƙasar England.

Har falon Baba Aaliyah ta raka ni na nuna ma sa admission ɗin. Ya ji daɗi kuma ya sa min albarka. A wajen Aaliyah ta ce "Baba ni ma Cambridge za ka kai ni ko?"

Baba ya ce "duk inda ki ke so 'ya ta"...

A hankali ina ta shirye-shiryen tafiya har ya zama rana ta zo, gobe da safe zan tafi.

Kullum sai Aaliyah ta min ƙorafin zan tafi na barta ita ba ta so na tafi, wai na bari itama ta ƙare sakandare sai mu tafi tare. Ni kam kawai dariya na ke yi dan nima ba ta san ya na ke ji gameda rabuwa da za mu yi ba.

Da yamma ta zo muka wuni a ɗakina da maghriba ta wuce cikin gida. Ban ɗauka za ta dawo ba shiya sa nima ban dawo daga masallaci da wuri ba. Wajen ƙarfe goma na shigo ɗakina sai na tarar da Aaliyah tana zaune tana jirana.

"Aaliyah dare ya yi, mi ki ka dawo yi?"

"Anan zan kwana" abinda ta faɗa kenan kai tsaye.

Na sani ta kan yi baccin rana a ɗakina, hakanan lokacin ba ta kai haka ba bacci kan ɗauketa a ɗakina da dare in ɗauketa in mai da ta gida ko Jijiɗo ta maidata. Amma yanzu Aaliyah budurwace she's 14.

Duk yadda na yi da ita ta tafi ta ƙi. I have no choice haka mu ka kwanta tare a gado ɗaya tun ina tunane-tunane har bacci mai daɗi ya tafi dani. The best sleep i ever had.

Washe gari Jiji ta ga Aaliyah ta fito daga ɗakina, Nan ta fara faɗa. Ba dan tafiya zan yi ba da ban san irin masifar da Jijiɗo za ta min ba.

Dreban gidan, Aaliyah ta sa ya kaini airport wanda tun cikin motan Aaliyah ke hawaye har muka isa. Nima daurewa kawai na yi amma ina jin yadda ta ke ji a ranta, ina jin ma fiyeda yadda ta ke ji....