8- Confessions
by @azizat
8
*.............Aaliyah.............*
Confession
Lokacin da Hamma Sa'eed ya tafi Cambridge, sai ya zamo kamar ya tafi da rabin jiki na ne sauran rabin kuma yana Maiduguri. Duk su Jiji sun ɗauka rashin ganin Hamma zai sa na dena damuwa da shi amma abin bai zamo haka ba. Kullum na dawo daga makaranta ɗakin sa na ke tarewa wani lokaci na yi ta kuka, wani lokaci na zauna na wuni ina kallon hotunan sa. Abin ta kai har kwana na ke a ɗakin sa duk da kuwa Jiji ta hana ni amma na ƙi ji. Itakam Amma ta yi faɗan har ta gaji ta sallama ni.
Lokacin da Yaya na Bukar ya tafi Oxford karatu mu kan yi waya da shi lokaci zuwa lokaci, amma Hamma tun ina irga kwanaki har na fara irga watanni ƙarshen shekara na baza ido ko zan ga Hamma kamar yadda Ya Bukar kai zuwa duk ƙarshen shekara amma ba Hamma ba dalilin sa.
Safiyar wata Lahdi ina karatu a ɗakin Hamma, Jiji ta shigo da murnan ta. Ta miƙamin wani envelope mai ɗan girma ta ce yanzu Baffa Manu ya kawo, an aiko daga post office wai na karanta mu su daga Sa'eed ne. Ai da sauri na farke envelope ɗin na fiddo da abinda ke ciki. Akwai wani envelope madaidaici wanda ke ɗauke da sunana a jiki.
Ban san lokacin da na kissing envelope ɗin ba ina shaƙar ƙanshin jiki. A gurguje na karanta ma ta abinda ya rubuto mu su. Gaisuwa ne da kuma bayanin yadda za su rinƙa amsan kuɗin da zai dinga turowa. Ina gama karanta ma ta na yi waje da gudu. Ban tsaya sauraron wasu tambayoyin ta ba balle na amsa su. Ina zuwa na faɗa kan gado na ina maida numfashi. Finally Hamma Sa'eed ya turomin saƙo. Kenan bai manta da ni ba, kamar yadda ni ma kullum ya ke rai na. Sai da na samu na nitsu sannan na buɗe envelope ɗin na fiddo da takardu goma shabiyu da ke ciki. Na fara karantawa ɗaya bayan ɗaya saboda ya sa number a jiki. Taƙaitattun bayanai ne akan yadda shekara ɗayan nan ta kasance ma sa a Cambridge ba tareda ni ko su Jiji ba. Duk inda ya rubuta *i miss you Aaliyah* sai na bi wajen da kiss. Haka na sa letters ɗin nan a gaba ina karantasu ina sake maimaitawa...
Shekara na biyu ya zo min da sauƙi saboda mun yi musayar letters har sau shida. A wannan shekara na yi jarrabawar Waec ina aji biyar. Babban abinda ya fi sa ni farin ciki da kammala jarrabawar nan bai fi tunanin tafiya Cambridge da zan yi ba. Ina tunanin zan kasance tareda Hamma na.
Sanah Oxford ta zaɓa ni kuma na zaɓi Cambridge duk da ma dai Baba ya so mu tafi waje ɗaya tunda tare mu ka taso amma kowa da ra'ayin sa. Ita Sanah tuntuni Oxford ta ke son zuwa ni kuma tun lokacin da Hamma ya samu scholarship a Cambridge na sa wa raina Cambridge zan je.
Abu ne na 'ya'yan ma su kuɗi. Ko ina za ka je indai ana zuwa to ba matsala ba ce a wajen ma su arziƙi. Baba ya sa aka fara ma na shirye-shiryen tafiya. Ni excitement ɗi na ba na makarantar da zan je bane sai dan ganin Hamma da zan yi after 2yrs da ba ma tare.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka sama mana admission aka arranging ma na komai hatta wajen da zan zauna an shirya komai. Ranan tafiya ta zo, Baba da kan sa ya raka ni airport abunka da shalele, da ke ba tare za mu tafi da Sanah ba ita sai nan da sati uku.
Ban sha wahalar komai ba saboda an riga an shirya wanda zai ɗauke ni tundaga airport ya kaini gidan da zauna. Gidan flat ne ɗaki ɗaya da falo sai kitchen. Ba abinda ke raina illa na ga Hamma, ko ya ya ƙara girma yanzu oho.
Mun riga mun tsara inda za mu haɗu a cikin makaranta idan na zo. Ba tareda hutawa ba na ce da wanda ya kawoni gida akan ya kaini makaranta. Baturen Mr Wallace ya nuna na huta yau gobe sai muje ya nuna min yadda zan ƙarasa registration. Na mai fau-fau akan dole sai mun je makarantar. Ba mu su ya amince, tunda kuɗi aka biya shi ya kula da ni...
Kaman yadda na haddace sunan Hamma Sa'eed haka na haddace sunan address ɗin garden ɗin da za mu haɗu. Ba tareda ɓata lokaci ba Mr Wallace ya kaini wajen. Dai-dai wajen fountain ɗin da ya ce zai zauna ya jira ni dai-dai nan na tsaya amma banga Hamma ba. Na tsaya a wajen ina irga saukar numfashina, wanda ke sauka da sunan Hamma Sa'eed. Ban fi minti goma da zuwa ba amma gani na ke kamar na fi awa ɗaya. Tun ina sa ran zan ganshi har na fara jin ko dai ya manta ne, ko dai baya son ganina ne ko dai... hawaye su ka fara sauko wa daga ido na. Ina zaune sanyin ruwan da ke ɓulɓula daga fountain ɗin yana ratsa ni amma ni zafi na ke ji.
Daga ta baya na aka sa hannu aka rufe min ido, na sa hannu na taɓa hannun da ya rufe min ido, nan ta ke farin ciki ya mamaye ni. Shekara biyu amma ban manta yadda ɗumin hannunsa ya ke ba.
"Hamma" na faɗa ina ƙoƙarin cire hannunshi da ga fiska ta.
"Miye na kukan kuma?, kwata-kwata minti shabiyar ki ka yi a nan har kin gaji da jira"
Na juyo da sauri and there he is. Hamma Sa'eed ɗina, sai dai wannan ya ƙara ƙiba ya kuma ajiye gemu. Murmushin sa mai rikitata tunani na shi ne shimfiɗe a fiskar sa.
Kallon sa na ke yi ido cikin ido duk da yanzu ina jin wani abu na tasowa daga chan ƙasan zuciyata lokacin da na ke kallon sa. Ban sani ba ko tunda ɗin akwai wannan abun ko kuma yanzu ne da na girma na ke jin wannan abin ko kuma saboda munyi shekara biyu da wata huɗu ba tareda mun ga juna ba ne.
A hankali na tashi ina cigaba da kallon sa, gani na yi ya ƙara min tsayi, sai na ganni 'yar guntuwa a kusa da shi duk da kuwa a cikin shekaru biyun nan nima na ƙara tsayi. Hannu na sa na shafa fiskar sa ina ƙara tabbatarwa kai na finally Hamma ne a gaba na. Har lokacin bai dena murmushi ba. A hankali na shiga jikin sa ina dariya. Shima ya sa hannu ya ƙara jawoni jikinsa sosai ya ɗan ranƙwafo kan sa ya ce " finally"
Mun jima a haka har ban san adadin lokacin da mu ka tsaya a wajen a haka ba, har cikin raina so na ke mu cigaba da kasancewa haka. Lokacin da za mu bar wajen bayan Mr Wallace ya zo akan yana so ya maidani gida cewa na yi dole Hamma ya goyeni ya kai ni wajen da aka yi parking motar.
"Aaliyah yanzu kin girma fa"
Na tuɓure na ce ban san wannan ba ni dai dole ya goye ni. Ban san miyasa Hamma ba ya son musu ba, ko dan tun asalin sa ba wai yawar magana ba. Haka a wajen nan ya tsugunna ni kuma na hau bayan sa, abin ya burge Mr Wallace har ya sa ya je ya karɓo wani camera a wajen wa su masoya da su ke ɗaukan hoto a gefen mu. Ya ɗauke mu hoto ina bayan Hamma yana dariya ina dariya.
Wajen da aka ajiye motar ba ƙaramin nisa ne da shi ba amma haka Hamma ya jure ya kaini har wajen. Abinka da ƙasar waje ba wanda ya damu balle a tsaya a muku magana. Kallon mun burge sosai ma ake ma na...
Ba zan iya tuna rana ɗaya da ba mu haɗu da Hamma ba tun daga wannan rana duk da kuwa abin da mu ke karanta ba ɗaya ba ne, kuma wajajen ɗaukan karatun mu ba sa kusa. Idan ba mu haɗu a makaranta ba to dole zai zo gidana, duk yadda na dameshi akan ya tattaro ya dawo gidana sai ya ce min a'a tun ina fushi akan haka har na dena.
Wata rana maƙociyata Cassandra wadda ake kira da Cassy ta gayyaceni birthday party ɗin saurayin ta. Da ke bayan Hamma, Cassy ita ce wadda na shaƙu da ita tun zuwana Cambridge.
Na bar wa Hamma saƙo akan idan ya zo na fita tareda Cassy da ke ya san inda na ke ajiye ma sa key.
Ƙarfe bakwai na yamma mu ka fita daga gida amma kafin mu isa wajen da ake party ɗin ma sai tara saura domin chan bayan gari ne wajen ruwa.
Mata da Maza ne a wajen kowa da shigarsa na wajen beach. Mata da bikini Maza da gajerun wanduna. Dayawa mu baƙaƙen fata idan munje ƙasar waje mu ka ga ana abu to fa ba ma so a barmu a baya, ba ma so a mana kallon mu 'yan ƙauye ne. Haka ta ke tun 80's haka ta ke kuma har yau.
Cassy ta dinga damuna a kan ni ma na cire kayan jikina, dan idan na fito a haka za a dinga min dariya. Da farko ban yadda ba amma daga baya na amince na cire doguwar rigan da na sa wanda itama doguwar rigan dama guntuwa ce, to wa ya damu, fashion ɗin lokacin kenan.
Na ajiye kayan a motar Cassy na fito daga mota ina ɗan ɗari-ɗari saboda ban taɓa fita haka ba, daga ni sai bra da pant kamar sauran matan wajen. Ba ma maganar ɗankwali dan tun asalina ba na son sawa sai kuma ya haɗe da zuwa turai na ma watsar da batun rufe gashi, yana ɗaya daga cikin abinda ya ke sa Hamma ke min faɗa a mafi yawancin lokuta.
Na ƙarasa wajen party ɗin da ƙyar. Ana ta rawa amma ni na kasa yi, Cassy ta miƙomin wani abu a kofi na girgiza kai na ƙi na karɓa. Ban ankara ba wani bature ya kama ni ta baya yana rawa yana shafa jiki na. Ina ƙoƙarin ture shi amma shi ina bai ma jin mai na ke faɗa saboda kiɗa da ke tashi. Hankalina ya tashi saboda duk da ba wannan karan ne na fara zuwa party ba amma ban taɓa zuwa irin wannan partyn ba.
Da ƙyar na ƙwaci kai na a wajen baturen na koma gefe na takure ina danasanin biyo Cassy da na yi.
Hamma ya je gidana ya tarar da saƙon da na bar mi shi, kasancewa ba na ɓoyewa Hamma komai hakan ya sa na rubuta ma sa address ɗin inda za a yi party ɗin incase zai zo. Tunda ya ga address ɗin hankalin sa ya tashi ya nemi wani abokin sa mai mota ya aro mota ya taho.
Zuwa na yi dan na gayawa Cassy akan zan tafi gida sai wani Matt wanda mu ke aji ɗaya ya ganni, ya kamo hannuna yana cewa mu yi rawa. "Plz Matt leave me" na faɗa ina ƙoƙarin cire hannuna daga cikin na shi. Ban san daga ina ya fito ba sai saukan mari da na gani a fiskar Matt. Matt ya riƙe ƙuncinsa yana kallon Hamma da ke tsaye fiskarsa kamar garwashin wuta.
Hamma ya cire jacket da ke jikinsa ya matso ya samun wanda tsabar tsoro na ka sa cewa komai. Ya ja hannuna mu ka bar wajen.
Har ya kai ni gida bai yi min magana ba, lokacin da ya buɗe min ƙofa kasa shiga na yi na tsaya bakina na rawa na ce "Hamma"
"Kar ki ƙara kiran suna na. Party girl ko"
Ya rufe ƙofar ya juya ya tafi. Ranan haka na kwana da zazzaɓi, ina sauraren Hamma ko zai zo ya duba ni amma bai zo ba. Idan na kira shi ba ya ɗauka.
Lokaci guda Hamma ya ƙaurace min. Duk inda mu ke haɗuwa da Hamma ya dena zuwa, har ajin su na je amma ya shareni. Cikin kwana uku na shiga tashin hankali da ban taɓa shiga ba a lokacin.
Ba abinda ke damuna irin Hamma ya gujeni, Hamma na ya guje ni.
A kwana na biyar sai da aka kwantar da ni a asibiti, ina nan ma duk halin da na ke ciki babban burina shine na ga Hamma, amma bai zo ba sai washegari.
Ina kwance ya shigo lokacin ina ƙara tambayar Cassy ko ta sanar da Hamma cewa banda lafiya. Ina ganin sa na yi yunƙurin tashi duk da ruwan da aka ɗaura min.
"Hamma i'm sorry, wallahi ba zan kuma ba, dan Allah kar ka gujeni" na fara faɗa ina kuka tun ma kafin ya ce wani abu.
Hannuna ya kamo ya ce "ba komai, get well soon"
Kwana ɗaya na ƙara a asibitin su ka sallameni. Tare mu ka dawo da Hamma gida, ya shiga kitchen ɗina ya min lafiyayyen girki, duk da bana jin daɗin baki na amma haka na daure na ci sosai. Sai chan dare tukunna ya tashi zai tafi.
"Hamma ka kwana anan" girgiza kai kawai yai ya nufi ƙofa.
" ki sha maganin ki akan lokaci zan zo gobe da rana"
Daga inda na ke zaune gani na ke idan ya tafi ba zai kuma dawowa ba.
"Hamma"
Ya juyo ya kalle ni. Na tashi na ƙaraso wajen da ya ke tsaye. Idon sa na kalla na furta abinda ya jima ya na damuna, wanda ban gane ba sai a 'yan kwanakin nan da Hamma yai fushi da ni.
"I love you Hamma Sa'eed, I love you so much. Dan Allah kar ka kujeni, ina son ka da dukkan bugun zuciyata, Ina son ka da kowanne fitar numfashina, ina son ka da duk wani jijiyar jikina. Ina son ka..."
Yatsunsa biyu ya sa ya toshe bakina ya ce "shhhhhhhh"...