TSOHUWAR SOYAYYA

9- Love

by @azizat

9

*................Sa'eed..............*

 Love

Tafiya na ke akan titi amma ji na nake kamar a kan gajimare na ke tafiya. Farin cikin da ya mamayeni a wannan lokacin ba zai bayyanu ba. Ji na nake a sama, ban ƙi na dinga tiƙar rawa a wajen ba dan na nuna yadda na ke cikin tsananin farin ciki. Duk nisan gidan Aaliyah da Hostel ɗin mu ban gani ba, a haka na tafi a ƙafa, ina tafiya ina ji kamar kar wannan dare ya ƙare, wannan dare mai tarin albarka, wannan dare da na iya amayar da abinda na jima ina ƙunshe da shi a zuciyata.

Idan na tuna yadda idon ta ya bayyana shauƙi da farinciki lokacin da na bayyana ma ta sirrin zuciyata, sai na ga kamar na fi kowa sa'a a rayuwa...

Kamo hannunta na yi na kai dai-dai ƙirjina da ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi na ce

*"Kin ji yadda ƙirjina ke bugawa ko? Zuciyata ta jima tana bugawa domin ki Aaliyah. Ba zan taɓa gudun ki ba, har ƙarshen rayuwata haka zuciyata za ta cigaba da bugawa domin ki. I have always love you, and will always love you till my last breath on earth. Ke ce zuciyata Aaliyah, ke ce farin ciki na"*

Na tallafo fiskanta da ya riga ya jiƙe da hawaye na manna ma ta light kiss a bakin ta. Ta shige jikina tana kukan farin ciki, nima ɗin sai na ji hawaye na zubowa a idanuna. Ban son rabuwa da ita, ina son kasancewa da ita har washegari, har ma ƙarshen rayuwata amma....

"Are you crazy!" ihun wani mai mota ya dawo da ni daga duniyar tunani. Ashe na kai tsakiyar titi ban sani ba, na matsa da gudu ina bashi haƙuri. Idan ina tunanin Aaliyah mantawa na ke da komai...

.............................

Baccin daɗi na yi daren ranan, baccin da na jima ban yi irin sa ba. Na tashi da niyyar shimfiɗa sabon rayuwa, rayuwa mai daɗi tareda masoyiyata Aaliyah...

Shaƙuwa tsakanina da Aaliyah ba abinda ya ragu sai ma ƙaruwa da yai. Kullum muna maƙale da juna. Ko a makaranta ko a gida, ko kuma a shagon da na ke aiki. Ina haɗa coffee, tea, capuccino, frapuccino da sauran su a shagon. Tun shekarana na farko na fara aiki a wajen saboda samun kuɗin shiga da kuma 'yan chanjin da zan dinga turawa su Baffa Manu. Cikin ƙanƙanin lokaci na yi fice a shagon, ta kasance duk wanda ya zo za ka ga ni ya ke buƙatan na haɗa ma sa order ɗin sa, duk da kuwa ba koyaushe na ke aikin ba na kan yi da yamma ne ko dare idan ba ni da class.

Ranan ina tsaka da haɗa coffee wa wani customer sai ga Oga na ya zo.

"Seed" ya kira ni kamar yadda ya saba saboda bai iya kiran Sa'eed ba. Na juya ina kallon sa. Da mamakina sai ga Aaliyah a gefen sa tana murmushi tana sanye da T-shirt mai ɗauke da sunan shagon. Ya nuna min Aaliyah a matsayin sabuwar ma'aikaciya tareda cewa na koya ma ta aiki har ta iya. Na amsa da to ina aikawa Aaliyah kallon za ki gamu da ni...

Ƙarfe shaɗaya na dare na gama aiki na na ranan, na fito daga shagon ina yin biris da Aaliyah da ke ta kiran suna na.

"Hamma dan Allah ka jira ni, Hamma please ka rage sauri"

Ban kulata ba na cigaba da tafiya. Ganin idan na cigaba da tafiya a haka zan ma ta fintinkau ya sa ta kama gudu. Da ta isoni ta tsaya gaba na tana haki.

"Hamma Dan Allah na ce fa, ka yi haƙuri ba zan sake ba"

Na tsaya da tafiya ina kallon ta ba tareda na ce komai ba.

"Hamma ina son kasancewa tareda kai shiyasa na nemi aiki a wajen. Please forgive me" ta ƙarasa maganan tana haɗa hannunta biyu.

Na sa hannu a haɓata kaman mai tunani na 'yan wasu daƙiƙu kafin na ce "zan yafe amma da sharaɗi"

"Mi ye sharaɗin?" Ta tambaya tana kallona

"Daga yau ba na so ki sake kirana da Hamma"

Ta ƙwalalo ido waje saboda ba tun yau ba na ce ta dena kirana da hakan amma ta ƙi, ta ce ba za ta iya denawa ba.

"Ni gaskiya ka chanja wani sharaɗin" ta faɗa da sakalci.

"Wannan ne kaɗai sharaɗin"

Ta fara buga ƙafa tana faɗin dole na chanja sharaɗi. Ni kuma na ce sam shi kaɗai ne sharaɗin. Da ta ga na doge dole ta haƙura ta faɗa.

Ta rufe idonta kafin ta furta sunan a hankali "Sa'eed"

Na ji abinda ta ce amma saboda yadda sunan yai daɗi a bakin ta ya sa na ce ma ta ni banji mi ta ce ba.

"Sa'eed" ta sake maimaitawa.

"Ni fa idan ba ki kalli ido na kin kira sunana ba ban san kina magana ba"

"Kayya! that's not fair Hamma"

"Shikenan barin tafi" na sa kai zan cigaba da tafiya ta yi saurin riƙe hannuna. Na juyo ina kallonta ina kuma jin yadda duk jijiyoyin jikina su ka amsa da riƙon da ta min.

*"Sa'eed"* wannan karon ido cikin ido ta kira suna na, wannan karan da wani salo me haɗe da yauƙi ta kira suna na, wannan karan na fi jin daɗin suna na fiye da kowanne lokaci...

So kenan, mai sa ka ji za ka iya yin komai domin masoyinka. Saɓanin ni da na ke aiki ake biyana Aaliyah na aiki ne dan kawai ta kasance tareda ni. Maƙudan kuɗi ta bawa mai shagon domin ya barta ta yi aiki sannan ya ƙara min albashi. Ban tashi sanin ƙarin albashi da na samu daga wajen Aaliyah ba ne sai da tafiya ta yi nisa...

Mun kusa yin hutun ƙarshen shekara, yayinda mafiya yawanci ɗalibai da ba 'yan ƙasan ba ke ta murnan za su je gida, ni baƙin cikin rabuwa da Aaliyah na ke ji. A wannan lokacin da ba karatu na ke samun daman yin ayyuka dayawa domin samun kuɗi shiyasa ban damu na nemi kuɗin jirgi na dawo gida hutu ba.

Kwana uku ya saura Aaliyah ta koma gida, mun fito daga wani cinema inda mu ka je mu ka yi kallo. Aaliyah ke sake roƙo na akan lallai na amince na koma Nigeria tareda ita za ta biya min kuɗin jirgi.

Na nuna ma ta ba zan koma Nigeria koma Nigeria ba sai na gama karatu na.

Hakan ya sa ta yi fushi ta fara tafiya ta bar ni tsaye a wajen.

"Aaliyah wait..wait please" na bi bayanta da sauri...

"Ni ka sake ni na tafi, dama ba ka damu da ni ba ai. Ka yi ta zamanka a nan har Mahdi ya zo..."

Ganin ta ƙi yin shiru ya sa na rufe bakinta da nawa. Wannan ne karo na farko da na kissing ɗin ta properly, our first deep french kiss.

Ta kwanta a ƙirjina tana murmushi. Na sa hannu a aljihu na ciro zoben da na jima ina tara kuɗi domin na siye shi, zoben zallan azurfa ne mai kyau. Na kamo hannunta na sa zoben a yatsar ta tareda kissing ɗin hannun ina faɗin *"ke ce zuciya ta Aaliyah, idan na rasa ki na rasa zuciya ta gaba ɗaya. A duk inda ki ke, a kowani lokaci, a kowani hali, duk min rintsi ina son ki Aaliyah, har ƙarshen rayuwata, har ƙarshen numfashina a doron ƙasa. I will forever love you Aaliyah"*

*...........Aaliyah............*

Fear

Ina son Sa'eed sosai, kowacce rana kamar ƙara dasa min son shi a ke a zuciya ta. Sa'eed mutum ne mai karamci, tsaftacecciyar soyayya ya ke gwada min wanda ta ke babu ƙarya a cikin ta. Idan ka cire riƙe hannu ko runguma sau uku Sa'eed ya taɓa kissing ɗi na. Wani lokaci na kan nuna ma sa alamun ba matsala idan ma mun aikata abin da ya fi kiss amma sai ya dinga janye jiki da ni. Akwai lokacin da na fito fili na faɗa ma sa ni da shi ɗaya ne kuma zan mallaka ma sa kai na ba tareda wani tsoro ko fargaba ba. Yai murmushi kawai ya ce "Aaliyah ba jikin ki na ke so ba, haka nan akwai lokacin da za mu kasance tare har abada, ki yi haƙuri kafin nan"...

Saura kwana ɗaya na tafi gida muna zaune da Sa'eed a gida na aka fara ƙwanƙwasa ƙofa. Muna zaune a kujera mu na shan tea ɗin da ya haɗa min wanda har yau na ka sa iya haɗawa kamar yadda ya ke haɗawa. Tunanina pizza da mu ka order ne aka kawo ma na, dan haka na tashi da sauri na je na buɗe ƙofa. Ido na zaro ganin Amma na tsaye.

Na faɗa jikin ta ina murna...

Shigowar da ta yi ta ga Sa'eed ya sa ta haɗe rai tana yiwa Sa'eed kallon tuhuma. Da ƙyar ta amsa gaisuwar da Sa'eed ɗin ya ma ta. Shima ɗin sai na ga tsoro ya bayyana a fiskar sa.

Suna gama gaisawa ya ce zai tafi, na nemi ya tsaya a kawo mana pizzar amma ya ce yana sauri ya tuna zai je ya amso saƙo.

Sa'eed na tafiya Amma ta kalle ni cike da masifa ta ce " mi ya ke yi a nan?"

"Amma ya zo tayani hira mana tunda ba makaranta" na faɗa ba tareda wani fargaba ba.

"Na shiga uku, Aaliyah ba dai anan ya ke kwana ba?"

Duk yadda na faɗawa Amma Sa'eed ba ya kwana a gidana haka nan bai taɓa kwana a gida na ba bata yarda ba sai da ta dudduba gidan ta ga babu kayansa ciki.

"Amma wai miye haka ne? Sa'eed ɗan uwana ne, ko da ya kwana anan mi ye a ciki?"

Amma ta fara min faɗa, ta inda ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba. Tun ban maida abin komai ba har tsoro ya fara shiga na saboda maganganun da ta ke faɗa. Ba abinda ya fi ɗaga min hankali irin abinda ta ce wai idan ma soyayya mu ke to mu dena dan ba inda zai kai mu.

"Amma miye ne idan mun yi soyayyar? Sa'eed mutumin kirki ne"

"Tsakanin ki da Sa'eed babu soyayya Aaliyah, idan kuma ki ka fara za ki sha baƙar wahala ne dan ba inda zai kai ku. Ki kama kan ki Aaliyah ko kuma na sa Baban ki ya chanja miki makaranta"...

Har mu ka koma gida Nigeria ban ga Sa'eed ba gashi Amma ba ta bari na fita a gidan ba. Dama ta je ganin yayanta da ba lafiya ne ta biyo min akan mu wuce Nigeria tare tunda nima chan na nufa...

Tundaga wannan lokaci na ji tsoro ya shiga rai na. Ina tsoron ka da kashedin Amma ya tabbata, ina tsoron kar wata rana a raba ni da Sa'eed...

Har hutu na ya ƙare ban ji daɗin hutun ba saboda kewar Sa'eed da na ke yi. Sai da na koma Cambridge na samu nitsuwa. Kwanaki kaɗan da komawata na fara ganin chanji tattare da Sa'eed kamar ƙoƙarin ja baya ya ke da ni, gashi ya daina zuwa gidana. Da na tuhumeshi sai ya ce karatu ne ya ke riƙe shi wanda na san ba haka ba ne. A hankali na gane Amma ce ta gargaɗe shi a kai na. Ranan na ma sa kuka sosai na kuma nuna ma sa soyayyar sa ƙarya ne indai zai ji tsoron Amma. Abin ya ma sa ciwo, hakan ya sa ya dena baya-baya da ni ya kuma nuna mini duk rintsi muna tare. Muka cigaba da soyayyar mu kawai mu ka manta da komai...

A shekara na biyu da na zo gida hutu na tuhumi Amma akan dalilin son rabani da Sa'eed da ta ke yi. Ranan ne na ji tsanar gidan mu, na ji a raina ina ma ni ba 'ya ce a gidan Alhaji Badamasi Bulama ba, na ji inama ni 'yar wata maigadi ne ko dreba. Amma ƙiri-ƙiri ta faɗa mini babu aure tsakanina da Sa'eed idan ma zan bar shirmen da na ke yi to na bari. Domin makaranta kawai ake jira na ƙare amin aure domin an min miji.

Ban san ya na ƙare satuttukan da na yi a Nigeria ba domin na kasance tamkar mara lafiya ba na fita ko'ina kuma ba na shiga cikin 'yan gidan mu. Jiji ma dana samu da maganar sai ta tabbatar min da maganar Amma, 'Yar mai kuɗi sai ɗan mai kuɗi...

Ranan da na koma makaranta ina zuwa gida na kira Sa'eed akan ya zo ina neman sa. Tun a Nigeria na riga na yanke wa kai na shawara kuma ko sama da ƙasa za su haɗu ba zan fasa abinda na yi niyya ba...

Yana zuwa na rungumeshi saboda ba ƙaramin missing ɗin sa na yi ba.

"Sa'eed ka min ciki" abinda na faɗa ma sa kenan kuma har zuciya ta abinda na ke so kenan.

Ya janye ni a jikin sa yana faɗin "ciki kuma? Why? Miya kawo wannan maganar?"

"Amma ta ce ba za mu yi aure ba, Jiji ta ce ba za mu yi aure ba. Sun ce wai ba mu dace ba. Sa'eed idan na rasa ka mutuwa zan yi. Dan Allah ka sadu da ni na samu ciki ko za su bari mu yi aure"

"Kwantar da hankalin ki Aaliyah, da sauran lokaci har yanzu saura miki shekara biyu ki ƙare ƙaratun ki. Kafin nan za su amince mana"

Wannan karan cikin kuka na ce " ba za su taɓa amincewa ba Sa'eed. Amma ta ce ina gama karatu za su min aure, wai anriga an min miji"

Na fara ƙoƙarin cire kayan jikina.

"Aaliyah stop this nonsense, ki bar cire kayan nan"

Ban saurareshi ba na yi tsirara gaban sa.

Ya daka min tsawa akan na maida kaya na. Amma ba abinda na yi sai ma na fara ƙoƙarin cire ma sa belt ɗin wandon sa.

"Ba ka sha'awata ne, kai ba namiji ba ne, ka yi duk abinda ka ga dama dani ni Aaliyah ta ka ce"

"Stop Aaliyah" ya faɗa yana tureni amma ban daddara ba na sake matsowa kusa da shi zan cire ma sa riga.

Saukar mari na ji a fiskata wanda ya sa na tsaya da abinda na ke shirin yi.

"Ke mahaukaciya ce Aaliyah, i said akwai lokaci. Ba zan taɓa ɓata miki rayuwa saboda wani dalili marar kan gado ba. Yes I love you amma ba irin wannan soyayyar na ke miki ba, what i feel for you is beyond this"

Har ya je ya ɗauko bargo ya zo ya rufa min ina tsaye ina zubda hawaye.

"Ki je ki sa kayan Ki" ya faɗa a hankali...