10- Ahmad Wamako
by @azizat
10
Wayar Zaid da ke ringing ne ya katse shi daga karatun da ya ke yi. Ya ɗaga ido ya kalli Aaliyah da idon ta ya cicciko da hawaye.
"Mi ya same ki kike kuka?" Ya tambaya yana ƙura ma ta idanun sa.
Ta girgiza kai kawai tana matse hawaye da gefen gyalenta.
Cigaba da kiran da aka yi ne ya sa yai tsaki tareda jawo wayar da ke kan gado.
Kafin ya swiping ya ɗauka kiran ta ga sunan da ke jikin screen ɗin *Zahra* babu tantama ta san Zahra MCcollins ce ke kiran sa. Waye bai san Zaid Ahmad Wamako da Zahra MCcollins su na soyayya ba.
Zahran da ta ke da over 2million followers a instagram da twitter. Manyan mutane da 'ya'yan manya sun yi chaa a kanta amma ba wanda ta damu da shi kamar Zaid. Shekara ɗaya da ya wuce ta tabbatar da zargin da ake ma ta kan soyayyar su da Zaid ɗin, inda ta bi duk shafukan ta na sada zumunta ta posting hoton ta da Zaid da su ka yi a Dubai ta rubuta *my man* a ƙasan hoton. Ba dan rasuwan mahaifin Zaid ɗin bama ƙila da anyi auren Zaid da Zahra tuntuni...
Arnold MCcollins shine kakan Zahra ta wajen Uba. Baturen ƙasar Ingila ne wanda ya zo Nigeria lokacin turawan mulkin mallaka. Kusan shekaran sa shabakwai a Nigeria kafin Allah ya sa yana da rabon musulunci ya musulunta. Kasancewa matar sa Rebecca ta daɗe da mutuwa ya sa bayan musuluntar sa aka bashi mata a Niger state inda ya ke da zama.
Hadiza Mamman Kankana 'ya ce a gidan Alhaji Mamman Kankana ɗaya daga cikin masu kuɗi kuma jigajigan ƙasa 'yan asalin Minna.
Auren Abubakar Arnold MCcollins da Hadiza Mamman Kankana sun haifi yara biyu, mace da namiji. Muhammad da Aisha.
Shekaran su goma shabiyar da aure Abubakar ya rasu yana mai shekaru sittin da ɗaya.
Muhammad da Aisha ba ƙaramin gado su ka samu ba saboda dukiyar da wannan baturen ya mutu ya bar mu su.
Muhammad A.A MCcolllins fitaccen mutum ne a ƙasar Nigeria da ma duniya gaba ɗaya. Ya riƙe muƙamai da dama kafin ya koma aiki da United Nations. Matar sa ɗaya Hajiya Maryam Tambuwal wanda itama 'yar babban gida ce. Allah ya azurta su da yara uku.
Hanifa Mccollins ita ce 'yar fari, wacce ta ke auren ɗan sarkin Sokoto. Sai Anwar MCcollins wanda ke auren 'yar shugaban ƙasa. Sai autar su Zahra wanda ta ke cin karenta ba babbaka a ciki da wajen ƙasar.
A shekarunta ashirin da biyar ta na da kwalin degree uku a ɓangare daban-daban. Tana da Kamfani da ta buɗe shekaru uku da su ka wuce, Zahra MCcollins brand ce. Tana da kyau, kuɗi, asali da nagarta. Yarinya ce da ta ke da girman kai da jiji da kai, ba da kowa ta ke harka ba, iya matsayin ka iya kusancin ka da ita.
Za ta iya walaƙanta kowa indai ka shiga gabanta. Ta samu tayin soyayya da ga wajen 'ya'yan manya da dama, sai dai da mutum biyu ta taɓa soyayya ko kuma na ce ta amince da soyayyar su. Masoyinta na farko cousin ɗin ta ne Junaid, ɗa a wajen ƙanwar Baban ta wato Aisha MCcollins. Ba su jima tare ba su ka rabu dan yanzu haka shekarar sa uku da aure. Zahra na masifar son Zaid, duk girman kan ta ba ƙaramin walaƙanci ta sha a wajen Zaid ba kafin su ka zo su ka zama masoya...
Bayan ya gama wayar da Zahra ya kashe wayar gaba ɗaya ya ajiyeta gefe. Sannan ya juyo ya kalli Aaliyah da har lokacin tana ƙoƙarin goge hawaye ya ce " a ina ki ka samu diary ɗin Sa'eed?"
"Wamako mu cigaba da karatun za ka gane daga baya"
Kallon ta yai na ɗan wasu daƙiƙu kafin ya buɗe diary ɗin Mom ya cigaba da karatu.
*..........Aaliyah...........*
Ahmad Wamako
Tun daga ranan hankalina bai kwanta ba, amma Sa'eed bai wani nuna damuwa ba. Koyaushe ce mini ya ke na kwantar da hankalina na cigaba da addu'a komai zai zo da sauƙi. Sai da aka ɗau lokaci mai tsayi kafin na cire damuwa a raina na, koyaushe Sa'eed nuna min ya ke akwai nasara a tattare da soyayyar mu...
Wata ranan Alhamis na dawo daga aji zan shiga gida sai na ji kamar ana kuka, na kasa kunne sosai sai na ji kaman daga ɓangaren Cassy maƙociyata ake kukan. Da farko na yi niyyar na share ta sai kuma na ga hakan bai dace ba, maimakon na shiga ɓangarena sai na je ɓangaren Cassy na fara buga ƙofar ta. Ba ta buɗe da wuri ba sai da na yi ta mata magiya kafin ta zo ta buɗe. Ganin yadda idon ta ya koma saboda kuka ya sa na shiga tambayarta miya faru. Da farko ma na ɗauka ko faɗa su ka yi da saurayin ta dan na san tana son Damien sosai. Sai da ta faɗa min asalin abinda ya faru sai jikina yai sanyi.
Saurayin ta Damien yai hatsari ya mutu. Abinda ya ƙara ɗaga ma ta hankali shi ne sati biyu da su ka wuce wata ƙawarta ta ma ta kwatancen wani mai duba. Out of curiosity sai ta je, da ta je mutumin ya gaya ma ta Damien zai mutu. Ta harzuƙa da wannan zance ta zage shi tatas, ta kirashi da maƙaryaci. Sai ga shi da safiya aka kirata akan Damien yai hatsari, bai jima da kawoshi asibitin ba ya mutu. Ba shiga rarrashin Cassy ina nuna ma ta lokacin Damien ne yai...
Bayan kwana huɗu da mutuwar Damien na je na samu Cassy akan ta kai ni wajen mai duban nan, ina so nima ya min duba. Da farko ta ƙi saboda tana tunanin kar na je a gaya min abinda zai ɗaga min hankali amma da na nuna ma ta koma minene zan jure ba zan tada hankali ba sai ta yarda...
Mutumin da mu ka je irin sufi ɗin nan ne, yana yin sa da kuma turancin sa ya daɗa tabbatar min da ba zai wuce ɗan ƙasar India ba ne.
Muna zuwa ya kalleni ya ce *Aashiƙan* yai murmushi wanda na rasa gane murmushin ko na minene. Tun kafin na ma sa bayanin mi ya kawo ni ya ce ya sani na zo ne akan maganar soyayya na gyaɗa ma sa kai ina sawa a raina wannan mutumin da gaske yana duba ɗin.
Na miƙa ma sa hannun dama na bayan ya buƙaci hakan. Ya sa yatsar sa yana bin zanen hannuna kafin ya ce *Makhtub* ya cigaba da cewa "ko sama da ƙasa za su haɗu sai kun yi aure" ya kalli ƙwayar idon na ya ce "sai dai za ku yi shekaru talatin kuna kewar junan ku" ba tareda na gama gane ma'anar maganar sa ba na ce "ka ce ni da Sa'eed za mu yi aure?"
Sai da yai dariya kafin ya ce "za ku yi aure"
Kalmar za mu yi aure kaɗai ya wadatar da ni duk wani bayani da ya ɗaura akai duk shirme ne a waje na.
Na ɗau maƙudan kuɗi na bashi sannan mu ka bar wajen sa zuciya ta cike da farin ciki.
Tundaga wannan rana na sawa kai na salama domin ance ni da Sa'eed za mu yi aure. Ko gayawa Sa'eed ban yi ba dan na san zai mun faɗa. Na riƙe abin a raina ni kaɗai...
Saboda ni Bayan Sa'eed ya kammala degree ɗin sa ya ɗora da masters domin mu samu mu gama makaranta tare. Wannan karan tun kafin ayi hutu na kira Baba na ce ba zan zo Nigeria ba saboda zan tsaya yin project ɗi na. Bai musa min ba ya amince kai tsaye. Da na kira Amma na gaya ma ta sai ta dinga mun faɗa domin ta san saboda Sa'eed ne na ƙi dawowa gida. Ni dai ban damu ba tunda Baba ya amince...
Kwamci tashi har Allah ya kawo mu ƙarshen karatuna inda ni Aaliyah Badamasi Bulama na kammala degree ɗina yayinda shi kuma masoyina Sa'eed Aliyu Modibbo ya kammala masters na shi.
Mun sa dogon buri a zukatan mu. Da mun dawo Nigeria kafin mu tafi bautar ƙasa zan sanar da Baba maganar Sa'eed saboda muna gamawa sai a mana aure. Kasancewa an tabbatar min ni da Sa'eed za mu yi aure sai ban sa a raina za a samu matsala ba musamman idan na tuna cewa Baba yana so na ba zai min auren dole ba sai dai...
........................
Cikin ikon Allah ba mu jima da dawowa ba aka tura Sa'eed bautar ƙasa chan Minna. Ni kuma Borno, ban ji daɗi ba dan ina so mu tafi bautar ƙasa tare. Na je na samu Baba a falon sa da letter ɗin da niyyar ya min hanya a maida ni Minna sai na tarar da wani zance marar daɗin ji.
Baba shi ya sa aka posting nawa Maiduguri saboda yana so na zauna kusa da gida.
"Baba na yi karatu a ƙasar waje ma balle kuma bautar ƙasa a chan wani state, za ku iya ganina duk lokacin da ku ke so fa" na faɗa da sigar sakalci.
"Aaliyah ki zauna a gida, ba na son ƙananun maganganu da na ke ji ana faɗa a kan ki"
"Baba wani magana kenan?" Na faɗa cike da tsoron tambayar da na yi da kuma amsar da zan iya samu.
"Aaliyah ba na son kusancin ki da Sa'eed. Dan kun yi makaranta ɗaya ba yana nufin ɗaya ku ke ba. Ki riƙe matsayin ki shima ya riƙe na sa"
Baki na rawa na ce " Baba ina son Sa'eed"
Bai yi mamakin kalamai na ba dan ya san da hakan tuntuni.
"Ko ma mi ki ke ji game da shi ki yakice shi. Na riga na miki miji"
Na fashe da kuka ina bashi haƙuri amma ko saurarata bai yi ba ƙarshe ma ya tashi ya bar min falon...
Kalmar an min miji yana da girma a wajena, hakan na nuna ba ni da 'yan ci kwata-kwata. Ya kuma nuna cewa banida ikon zaɓar mijin da na ke so sai dai a zaɓa min.
Sa'eed yana Minna bai san miya ke faruwa ba ni kuma ina Maiduguri ina fama da ƙunci. Wasa-wasa fa Baba ya ɗauke min wuta, yai biris da lamarina ya nuna matuƙar na cigaba da maganar Sa'eed a gidan nan zai aurar da ni tun ma kafin na gama bautar ƙasa na. Babu wanda ya damu da halin da na ke ciki, kowa nuna min ya ke bamu da ce da Sa'eed ba. Harta Jiji abinda ta ke nanata min kullum kenan. Sanah ce kaɗai ta yarda da soyayyata ta kuma supporting ɗi na...
Na turawa Sa'eed wasiƙa akan halin da na ke ciki amma har yau bai tura mini amsa ba. Ina kwance a ɗakina ina duba tsoffin wasiƙun Sa'eed Amma ta shigo ɗakina.
Na ɗaga ido na kalleta na kau da kai. Ta ajiye min wassu kaya a gabana ta ce, "ki sa wannan anjima za ki yi baƙo"
"Ba zan sa ba" na faɗa kai tsaye.
Amma ta min kallon banza ta ce " idan kin isa ki ƙi sa kayan nan mu gani. Ni da ke a gidan nan"
Yadda ta ajiye kayan nan haka ta dawo ta same su bayan awa ɗaya da rabi.
Faɗa ta shiga min sosai wanda ni kam ko ajiki na.
"Ki tashi ki sa kayan nan Aaliyah ko na sassaɓa mi ki"
Na kalli cikin idon ta na ce ba zan sa ba, idan za ta kashe ni to ta kashe ni amma ba zan sa ba.
Ina ganin yadda ɓacin rai ya mamaye fiskarta lokaci guda amma ni ko a jikina.
Ba ta ce ƙala ba ta fita daga ɗakin.
Minti takwas bayan fitar ta sai ga Baba ya shigo ɗakin ran sa a ɓace. Na ɗan tsorata da ganin sa amma na dake.
"Ɗan gidan Alhaji Wamako ya zo ganin ki ki shirya ki je ki same shi a falon baƙi"
Sai da ya juya zai tafi ya ce " umurni ba shawara ba Aaliyah" ya faɗa kafin ya sa kai ya fita...
Ina kuka ina saka kayan, ina kuma zagin Alhaji Wamako a zuciyata domin duk ƙauna da so daya nuna min tun ina yarinya ashe akwai abinda ya ƙimtsa min ne na baƙin ciki.
Kayan kawai na sa ko kwalliya ban yi ba na wuce sashen Baba.
Yana zaune a falo lokacin da na shigo, an cika gaban sa da tarkacen ciye-ciye da shaye-shaye. Shiga ta alfarma yai, shigan 'yan ma su ji da naira. Ba wannan ne karo na farko dana fara ganin sa ba, na taɓa ganin sa a Sokoto shekaru biyar da su ka wuce lokacin da mu ka je bikin ƙanwar sa.
Ahmad Ibrahim Wamako kenan, babban ɗa a wajen Alhaji Ibrahim Wamako. Kamar yadda mahaifina ke ji da arziƙi da dukiya haka Alhaji Wamako ke ji da kuɗi da dukiya, sunan sa ya shahara a Nigeria da Africa baki ɗaya.
Ban ko zauna ba na kalleshi na ce " kar ka bawa kan ka wahala Malam. Ina da wanda na ke so kuma shi zan aura. Ka nemi wata matar a gaba"
Sai dana gama maganar sannan ya ɗago ido ya kalleni ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya.