KORAMA

Day 6

by @kwalisa

KORAMA


FITA TA 6


Kalaman soyayya ba baqin abubuwa bane a zuciyar Fina, haka nan ba sabuwar shiga fagen soyayya bace. Kamar yadda samari da yawa sun sha zuwa suna neman soyayyarta daga baya su gudu su barta. Amman a wannan karon data tsinci kanta a duniyar son Dr Bala duk sai taji tana neman dawowa wata baquwar shiga soyayya.

Tabbas tana cikin duniyar qaunarsa, amman kuma akasin da aka samu ta yadda ya zo mata, to bata maraba da shi akwai abubuwa da dama yanzu data shiryawa kanta da kuma rayuwarta cikinsu kuwa har da burin ganin ta yi aure… tabbas lokaci ya yi daya kamata ace itama ta yi aure.

Daren jiya kusan raba dare tayi tana saqawa da kuma warwarewa na wannan cukurkuxaxen yanayin daya zo mata, qarshe ganin wanki hula zai kaita dare sai ta miqe ta xauro alwala ta dawo ta shimfixa sallaya ta shiga gabatar da nafila, ta jima a sujada tana neman agajin ubangiji akan wannan abun daya taso mata. Haka bayan ta idar ta jima hannunta a sama tana roqon Allah akan ya kawo mata agaji idan kuma Dr Bala ba zai zamar mata alheri ba to Allah ya kawo qarshen haxuwarsu.

Washe gari ta tashi zuciyarta fes, babu wata damuwa ko ta sisin kwabo. Sai tunanin Bili kawai data farka da shi, shima saboda wani mummunan mafarki da ta yi da ita, hakan ya saka tana tashi daga bacci bayan ta kammala duk wani abinda ya kamata sai ta shiga shiri domin zuwa gidanta. Bayan ta kammala ta leqa take faxawa Ummanta cewar zata gidan Bili. Ta mata fatan dawowa lafiya ta fito cike da qwarin jiki da jin sanyin zuciya.

Wani mai adaidaita ta tsare ta faxa masa wajen da zai kaita, bata jira taji nawa zata basa ba, ta hau shima bai tsaya ciniki ba, ya ja mashin suka yi gaba. Har suka je qofar gidan bata ce masa qala ba, shima bai ce mata uffan ba. Ta sauka ta xauko xari biyar ta basa ta yi gaba abinta.

Da sallama ta shiga aka amsa mata daga cikin falon ta qarasa shiga ta samu Inna marwa tana aikin goge-gogenta suka gaisa cike da kulawa da mutunta juna. “Inna ina mutuniyar?” Ta yi dariya “Tana cikin xaki yanzu ta fito daga wanka” Ta samu waje ta zauna tana murmushi.

Bata jima da zama ba Bili ta fito cikin wani tsadajen jan leshi da xinki ya kamata jikinta. Tana tafiya cikin taqama ta nufo wajen da Fina take fuskarta xauke da murmushi suka gaisa ta zauna kusa da ita “Qawata ta kaina” Ta ci gaba da magana “Yau da wurwuri hala kin kwana da tunanina” Ta yi dariya.

“Kamar kin sani kuwa” Ta xan yi shiru tana kallon farfajiyar falon.

“Wani abune yake mun barazana…” Ta ci gaba da bata labarin duk abinda ya faru tsakaninsu da Dr Bala har zuwa yadda suka rabu da shi a daren jiya.

Su duka biyun suka yi shiru ko wacce akwai abinda take tunani a cikin ranta game da wannan sarqaqiyar data taso musu.

“Yanzu mene abinyi?” Bili ta tambaya.

“Shi yasa ni ma na zo wajenki wata qila na samu wata shawara” Bili ta koma ta sake jingina da jikin kujera “Duk kaina ya kule, amman tabbas maza suna abinda suka ga dama, har yana iya kallon idonki yace miki shi yanzu bai shirya yin aure ba, amman kuma a shirye yake ya yi zina dake…” Ta furza da wata damuwa dake narke acan qasan zuciyarta “Gaskiya babu adalci a wannan lamarin nasa” ta ci gaba da jijiga qafarta.

Inna marwa ta gama aikinta, ta dawo falo tana gyara wasu kaya dake kan table ta juyo tana kallon fuskar Bili a hankali tace mata “Irin waxannan shexanun mazan maganinsu ake yi” Su duka suka zuba mata idanu cike da mamaki suna kallonta.

“Magani kuma Inna marwa? Ta ya ya za ayi maganinsu?” Ta bar gyara kayan tace musu. 

“Irin waxannan shaixanun mazan ma su lalata rayuwar yara mata, ana musu maganin kafi ne, sannan a turke su waxanan abubuwan idan aka musu to ba za su qara kallon wata mace idan ba matarsu ba hakanan kuma ba za su sake iskanci da wata mace idan ba matarsu ba” Su duka biyu suka zuba mata idanu cike da mamaki.

“Wannan aikin ai yanzu samun wanda zai yi tsakani da Allah to sai an sha wahala, saboda duka mallaman gaskiyar sun qare sai ‘yan damfara” Inna marwa ta yi murmushi ta dauke wani kofi dake saman table a hankali tace musu “Nasan halin ko wacce a cikin ku, nasan kamun kanki Fina tabbas ba za ki cutar da shi ba idan kika samu aka miki wannan aikin, don haka idan har kina son shi da gaske to ni zan miki wannan aikin”.

“Ke kuma Inna marwa?” Da mamaki Bili ta tambaya.

Inna marwa ta yi murmushi tana kallonsu “magani ne a gonar yaro amman bai san da shi ba” Ta xan matso kusa da su kaxan “Akwai mutane da yawa da sun san za su sameni anan to za ku sha mamaki yadda za su zo nema na. Da yawansu manya ‘yan siyasa ne, da yawansu manya ne a cikin qasar nan, amman ni bana son irin wannan mu’amala nafi son na baiwa wanda yake cikin buqata taimako kamar yadda zan taimake ki Fina insha Allahu”

Cike da jin daxi Fina ta riqa mata godiya “Ki bani awa xaya zan je na dawo” Bata jira taji abinda zata ce mata ba ta fita daga cikin falon ta kai kofin kicin sannan ta musu sallama ta fita, su duka suka zauna cike da mamaki suna kallonta.

“Za ka zauna da mutum tsayin lokaci amman baka san baiwar da Allah ya yi masa ba” Bili ta faxa cike da mamaki.

“Irin su kuma gadon bayar da magani suka yi, wasu kuma aljanunsu ne ke taimakawa mutane” Fina ta faxa cike da zumuxi.

Haka suka ci gaba da tattauna matsalolinsu har suka gangaro kan matsalar dake damun Bili “Mai zai hana mu faxa mata wata qila kema ta taimaka miki” Fina ta faxa mata.

“Kamar kinsa abinda nake saqawa a cikin raina kenan, amman kuma naga kamar ya samu sauqi saboda daren jiya na ji gabansa a miqe sanda ya dawo haka kuma, sanda na farka na samu kaina a wani yanayi na daban” Fina ta tsareta da idanu.

“Wani irin kika farka kika ganki a cikin yanayi” Ta tsareta da idanu.

‘Ni nasan bacci mai nauyi ya xauke ni, amman da safe na farka naga duk jikina ya baci da maniyi, alamun ya ji daxinsa” Fina ta yi shiru kamar tana tunani.

“Kuma ke kin samu gamsuwa?” Ta jinjina kanta kaxan “A lokacin dana farka sam na ji bana sha’awa amman sanda na fito daga wanka duk sai naji komai ya dawo mun saboda” Suka yi shiru su duka.

“Akwai lauje a cikin naxi tabbas” Fina ta tabbatar sannan ta ci gaba da magana “Ke ina ganin Allah ne ya kawo miki xauki har gidanki, don haka kar ki yi qasa a gwiwa wajen sanar da Inna marwa matsalarki” Ta gamsu da shawarar Fina.



Awa xaya na cika suka ji sallama Inna marwa a qofar falon, ta shiga tana murmushi su duka suka zuba mata idanu suna kallonta ta qarasa gabansu ta zauna yadda tana kallonsu, ta xauko wasu qulukan magani guda uku ta baiwa Fina .

“Wannan turare za ki riqa yi da shi na kwana bakwai, wannan wanka har tsawon kwana bakwai, sai kuma wannan na qarshen kawai a ruwa za ki zuba ki riqa bismillah duk lokacin da za ki sha. Tabbas za ki sha mamaki insha Allahu, amman ina qara nanata miki duk sanda kika masa cin mutunci domin taqamarki kina da wannan laqanin to komai zai lalace” Ta amsa tana mata godiya.

“Mene abin sadaka?” Fina ta tambaya.

Inna marwa ta yi murmushi, “Idan aiki ya yi kyau to ki riqa yiwa iyayena add’ar neman gafarar Allah, amman bama aiki domin a bamu kuxi” Tana murmushi ta miqe tsaye a lokacin Bili ta yi magana.

“Ina ni ma akwai tawa matsalar…” Kafin ta qarasa magana ta koma ta zauna tana murmushi “Nasan duk matsalar ki Bili, kawai ba ki kawo kanki bane shi yasa ni ma na qyale ki”.

“Kin sani Inna marwa?” Da mamaki Bili ta tambaya.

Ta gyaxa mata kai “Qwarai ba matsalar rashin kusantarki da mijinki baya yi bace, tsawon lokaci gabansa baya tashi, yana ta miki qarya kala-kala don nuna miki cewar zai samu lafiya, harma jiya daya dawo ya yi amfani da gindi roba ya nuna miki cewar ya samu sauqi…”

Cikin ruxani Bili da Fina suka tambaya a tare “Gindin roba?” Inna marwa ta yi murmushi kafin tae musu “shakka-babu”.

“Ta yaya haka ta faru?”

“Idan ya dawo ya shiga wanka ki duba lokon gado za ki ga abinda nake faxa miki. Sai kin tabbatar da abinda na faxa sannan mu yi zama na musamman dake domin matsalar taku ta girma, amma babu abinda ba zai gagara ba da izinin Allah” Qirjin Bili ya ci gaba da bugawa.

Inna marwa ta miqe “Zan tafi ni sai zuwa goben” Suka yi sallama.

Ba wata doguwar hira su Fina suka yi sa, saboda damuwa ta dawowa Bili sabuwa saboda tabbas ta fahimci yaudararta Oga Abdul daren jiya ya yi ya bata maganin bacci, idan hakane kuwa tabbas akwai wani voyayen abinda yake faruwa wanda yana da kyau ta gano ko mene.

Har qofar gida ta rako Fina suka yi sallama, ta koma cikin gida ta zauna, zuciyarta tana saqe-saqe.


Da dare Oga Abdul ya dawo kamar yadda ta saba, ta nuna masa babu wata damuwa haka nan ba wata matsala. Ta faxa jikinsa cike da nuna kulawa suka xan yi kiss xin juna sai taji abu yana zungurinta ta qara shiga jikinsa cike da ba shi kulawa. Ta kai hannu zata tava cikin azama ya janye jikinsa yana murmushi.

“Nasan an haxa mun ruwan wanka” Ta gyaxa kai “Eh ya kamata ka shiga ka yi wanka, ko na zo na yi maka?” Ya girgiza mata kai “Na hutar dake my wife kawai ki haxa mun abinci da lemo mai sanyi wanda za mu sha” Ta jijiga kai “An gama Oga” Ta bar jikinsa ta shiga kicin shi kuma ya shiga xaki ‘yan mintina ya fito ya xaura tawul ya shiga banxaki, ganin haka ta yi wuf! Ta shiga xaki ta soma dube-dube can bayan gado ta leqa taga abu ta jawo shi, cike da mamaki tsoro ta zuba masa idanu.

Tabbas ya cita da buguzum, kamar yadda Inna marwa ta kira abun da bura roba to hakane, sak kamar burar mutum ta gaske, idan ka xaurata sai ta miqe qyam… ta rasa me za ta yi tsakanin kuka da dariya.

Amman ta yi imani wannan karon maza sun faxi babu nauyi.