FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuci... Kuma Mai harka buga littafi.
Sample · Day 6
KORAMAFITA TA 6Kalaman soyayya ba baqin abubuwa bane a zuciyar Fina, haka nan ba sabuwar shiga fagen soyayya bace. Kamar yadda samari da yawa sun sha zuwa suna neman soyayyarta daga baya su gudu su barta. Amman a wannan karon data tsinci kanta a duniyar son Dr Bala duk sai taji tana neman dawowa wata baquwar shiga soyayya.Tabbas tana cikin duniyar qaunarsa, amman kuma akasin da aka samu ta yadda ya zo mata, to bata maraba da shi akwai abubuwa da dama yanzu data shiryawa kanta da kuma rayuwarta cikinsu kuwa har da burin ganin ta yi aure… tabbas lokaci ya yi daya kamata ace itama ta yi aure.Daren jiya kusan raba dare tayi tana saqawa da kuma warwarewa na wannan cukurkuxaxen yanayin daya zo mata, qarshe ganin wanki hula zai kaita dare sai ta miqe ta xauro alwala ta dawo ta shimfixa sallaya ta shiga gabatar da nafila, ta jima a sujada tana neman agajin ubangiji akan wannan abun daya taso mat...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.