SADAKI

001

by @auntysis

SADAKI...!


AuntySis đź’ś


001.


A hankali take tafiya cikin Ayis shopping mall dake cikin garin Katsina.Tana tura cart tana jidar abubuwan da take buƙata tare da sakawa a cikin cart ɗin a yangance. Kyakkyawa ce ajin farko son kowa kin wanda ya rasa. sanye take da Egyptian Abaya maroon colour daya sha aiki da duwatsun dasu kansu abun kallo ne. Irin Abayas din nan ne na Maryam Egyptian Abaya mazauniya kasar Egypt. Kanta na yafe da veil din abayar wanda shima kalar shi maroon ne. Tsintsiyar hannunta na sanye da Apple smart watch,yatsun nan sunsha jan lalli gwanin ban sha'awa abunka da farar fata ga zoben gwal kantarere na ta walwali a yatsarta na tsakiya..

Kafarta kuwa sanye yake da black covershoe kirar kamfanin nan na Dior da suka yi fice wurin kera takalma da jakukkuna designers na yan gayu. Fuskarta babu wani kwalliya,powder ce da wet lips kawai tayi applying amma karkuso kuga irin kyawu da glow din da takeyi.


Cikin mintunan da basu haura talatin ba ta kammala shopping ɗinda take ta tura cart ɗin a yayinda ta nufi counter dan settling bills dinta. ATM taciro daga purse ta miƙa a cire kuɗin amma ga mamakinta aka dawo mata dashi.

"Hajiya an riga da an biya miki" 

Mamaki ya cikata

"An biya min kaman yaya?"

Ta san dai ita kadai tazo bata kuma ga fuskar data sani ba bare ta gane inda maganarshi ta dosa. The boy attending to her daga cikin masu aiki a counter na payment din a takaice yace 

"Eh" Muhibba da har lokacin fuskarta ke dauke da tsantsan mamaki tace 

"Waye shi?" Adan kafule nuna alamar ya gaji da kalolin tambayarta, Yaron yace

"Alhaji Mustapha Hashim Safana" dan gani yake tambayar ma ta rainin wayau ce saboda ana shi tunanin tare suka.zo da Muhibbar forming kawai take.

Shiru tayi tana nazari amma gaba daya bata tunanin tasan wani mai suna Alhaji Mustapha Hashim Safana bare ace har wani abun ya hadasu dazai sa ya biya mata kuÉ—in shopping amma ganin in tace zata tsaya neman enquiry wani bata lokacin ne gakuma mutane dake que a bayanta suna jira ta fito su shiga yasa

kawai ta dauki shopping bags É—inta guda biyu ta fi ce a mall din. Anma me? Sai ganin mutum tayi tsaye jikin mota yayi folding hannayenshi a kirji yana binta da idanu da alama dai ita yake jira and from a bit far kallo daya ta mai ta gane kyakyawa ne shekarunsa na haihuwa kuwa zasu kai irin 44 - 45 dinnan. Shi ba fari ba ba kuma baki ba,za dai a kimanta kalar fatarshi da "Wankan tarwada" round face gareshi,a pointed nose with a cute brown lips hakanan bashi da tsayi sosai amma kuma bazaka sa shi jerin guntaye ba. sanye yake da gray colour É—in shadda,gaban rigarsa ya ji aiki da dinkin zamani irin dinkunan da ake gani a Instagram ina na manyan Tailors irinsu Seyi Vodi a yayin da kanshi ke dauke da hular nan da suke kira da tangaran. Hannunshi na hagu na lankaye da agogo kirar kamfanin rolex a yayin da yatsarshi na tsakiya ke dauke da zoben azurfa mai kyauka,kafunshi sanye da male sandals na kamfanin Aldo dasuka yi matching da shaddar jikinshi. Duk son gayu da raina kalar mutum a gurin Muhibba wannan mutumin is an "A" for her. 

ga wani fitinannen ƙamshin Dior Sauvage dake tashi daga jikinshi, kada ku tambayeni yadda na san sunan turaren da ke jikinshi, Ya Muhammad na kawo ma Yaya Farouk tsarabar irinshi idan yayi tafiya ni kuma Allah ya jarrabeni da son kamshi, don duk ranar ba zan fita ba sai na sata na shafa a kayana.


Da kyar ta iya dauke idanunta daga gareshi gudun kada ya kamata tana mai kallon kurulla ta zubar da ajin da takeji dashi kafin ta nufi hanyar gate cikin sauri sauri, Kafin ta ankara ya sha gabanta and before she could even muster courage tayi mai magana ya bata hanya sai taji sanyayyar muryarshi ma'aɓociya sanyi da kamala yana mata sallama

"Yan mata Assalamu alaikum!"

Cikin nata sanyayyar muryar tamayar mashi da "Waalaikumus salam" fuska dauke da murmushi haka nan cikin raha yace "Sorry nayi miki bankan bankan a hanya koo?" Shiru tayi batace dashi komai ba. Ya cigaba da fadin "The moment i saw you going into that shopping mall i couldn't help run down here in jira ki. Bazan boye miki ba. Idan ban takura ki ba kuma ko zaki taimaka min da digits dinki muyi magana daga baya in fada miki sirrikan dake zuciyata kar in tsaidaki. I don't know if you're in a hurry"


Har ga Allah bata son bashi duk da mutumin yayi kama da spec dinta but looking at the way he's persistent tasan ko tace bazata ba shi ba aikin banza ne saboda fahimtar da tayi wannan mutumin ko na ce ba zan bashi ba zai kyaleni ba, na amince da hakan kuma sai magiyar shiga mota ya ajeni gida tunda yaga ba da mota na zo ba, gwada mai nayi a'a gaskia saboda ni dai ban sanshi ba ga kuma yadda mutanen zamani suka koma abun sai addua. Ganin idan ba shiga motarshi nayi ba ba zai kyaleni ba dole na juya hakan yasa ya yi sauri jera wa dani muna tafiya side by side har muka isa wajen da ya yi parking motarshi kirar Mercedes Benz GLS 2023 baĆ™a wulik da ita sai da ya fara karÉ“a shopping bags É—ina ya saka a backseat kana ya buÉ—e min front seat na zauna ya maida murfin ya rufe, ya zagaya ya zauna mazaunin direba ya ja mota ya halba kan titi, sai da muka yi tafiya mai nisa kafin ya yi gyaran murya ya ce

"Sunana Alhaji Mustapha Hashim Safana ko zan iya sanin sunanki.

Kamar ba zan yi magana ba can kuma na ce 

"Sunana Muhibba Hamza Akilu Malumfashi.

"ma-sha-ALLAH! Daman ke 'yar wajen Alh Hamza Akilu Malumfashi ce? 

"Uhm! Kasan shi kenan?".

"Haba! Ke kuwa waye zai ce a garin Katsina baisan mahaifinki ba.

ĆŠan murmushi na yi sai kawai ya cigaba da faÉ—in


"Muhibba tun lokaci da idanuwana suka yi tozali dake a cikin Ayis shopping mall na nemi natsuwata na rasa ga baki ɗaya kin yi awon gaba da zuciyata, a lokaci guda soyayyarki ta sarƙe min ciki da wajen zuciya. samun ki a rayuwa ta babban nasara ce a gareni, natsuwarki na cikin abunda ya ja hankalina a gareki haka ma kanmu kanki, Muhibba ki kalli kanki da kyau duk wani kyau da ýa mace ke bukata Allah ya halittaki da shi, da za ki iya tsayawa a gaban mirror na dan wani gajeren lokaci da za ki iya ganin irin tsarin halittar da ubangiji yayi miki, da kin gane cewa ke ta daban ce a cikin yammata haďaďďu. Kyawun ki ya sha bambam da na sauran matan duniya sai kuma ya zama mai ķayatarwa da ya hadu da natsuwa da kamun kai.

Na sha jin maza na kodani sosai, hatta da kawayena tun muna secondary school suna yawan yaba kyawuna da kyakkyawar surar da Allah yayi mun haka yan jami'armu amma yau da naji bakin Alhaji Mustapha sai naji wani irin nauyi da kaina ya yi min saboda tun da nake ban taÉ“a haÉ—uwa da namijin da naji tasirin yabon shi a kaina ba sai shi,sosai zuciya ke jin dadin hakan ta yadda naji farin ciki na sauka a cikin zuciyata har wani langwaÉ“ar da kai nake yi tare da lumshe manyan idanuwana.

Alh Mustapha Safana ya ci gaba da faÉ—in

"Muhibba yana iya kasancewa ni ba irin namijin da kike so bane saboda age dina, amma ina tabbatar miki da cewa zan iya bada rayuwa ta dan farin cikin ki matukar hakan zai sa kisan matsayin ki a zuciya ta. Ba da wasa na zo gare ki ba Muhibba da aure nake sonki dashi ki bani dama na na turo magabata na su kawo gaisuwa da *sadaki* a gidanku domin hankalina ya kwanta in tabbata ke din tawa ce, don wallahi yadda Allah ya jarrabeni da sonki na farat daya, yadda nake ji sonki da kaunarki yana huda kasusuwan jikina idan har ban same ki a matsayin matata ba, zan iya shiga wani hali....Muhibba I never believed in love at first sight sai da na ganki, am not a love guru, but I will love you with all my hrt and soul...I will be your servant, I will build our kingdom but you will rule it Muhibba, plsss accept me and love me, you don't have to love me the way I love you, just accept me. Ya karisa faÄŹa muryarshi a karye kamar zaiyi kuka.....


Idan na ce daku kalamanshi ba su kanainaye min zuciya ba na yi ƙarya saboda a lokaci ɗaya na ji ya haura wani matsayi a cikin zuciyata amma gudun kada na yi saurin bada kai yaga kamar banida class sai na ce.....

"Gaskiya ban shirya wa aure nan kusa ba hasalima ina gabar karatu koda zan yi aure ba a nan kusa ba". 

Kyakkyawan murmushi ya sakar min wanda sautinsa ya fita hakan ya ƙara masa kyau a idanuna, cikin kwarewa da iya tsara kalami yake faɗin


"Karatunki wannan ba matsala bane nasan darajar ilmin saboda haka ba zan hana ki karatunki ba, na yi miki alƙawari zan tsaya miki har sai kin ce karatu ya isheki.....

Duk ta hanyar da na billo masa sai ya kawo min hujjarsa ya kafa dole na ce ya bani lokaci zan yi nazari da tunani har muka iso a kofar gidanmu yana ƙara jaddada min yadda ya kamu da kaunata. Kafin mu rabu na bashi number wayana na dauki shopping bags ɗina na shiga gida..

Ina jin ko kofar gidanmu bai bari ba sai ga text ya turo mun saboda ina kokarin tura kofar palon Umma naji karar shigowar text a wayata, ina shiga na aje kayan kan dining table na bude jakata na fiddo wayar, text na gani da sabuwar number an yi rubutu kamar haka ""hello my one and only swt pie, ki huta lafiya gimbiyar mata, get some rest, I wl call you later, I love you""....

Murmushi ne ya subuce mun bayan na gama karantawa sai na maida wayar jaka na aje ba tare da na bashi amsa ba..

Haka mukayi ta musayar texts da chats duk da ba kasafai muke waya ba, har mamakin yadda yake samun free time na lokacina nakeyi saboda nasan babban ma'aikaci ne...

Haka lokaci ya shuda har soyayyarshi mai karfin gaske tayi min shigar ba zata, ta samu matsugunni a zuciyata saboda Alhaji Mustapha ba green flag bane ba, green environment ne gaba daya...

Ban Ć™ara gasgata soyayyar Mustapha ta min shigar kutse ba sai da dare sa'ili da na zo kwanciya bacci na nemi bacci sama da Ć™asa na rasa Idanuna su nsoye babu abunda ke mun yawo sai irin kalaman da yake auna min na soyayya sai in dade ina faman juye juye akan gado da na rufe idanuna da zimmar na yi bacci ko ta Ć™arfin tsiya ne sai kawai hoton kyakkyawar fuskarsa ya dinga gilma min...

Haka wata rana ya kirani bayan sallar Isha'ee muka sha hirarmu ta soyayya daga baya mukayi video call, sai da nazo kwanciya duk wasu al-adu da nake na kwanciya na gama na shafa addu'o'ina na kwanta ina kulle ido sai hoton kyakkyawar fuskarshi mai cike da dinbin fara'a da haiba ta fara mun gizo, baki ɗaya daren ranar ban runtse ba sosai, sai mafalke mafalke nake da shi. Sai kusan asuba na sami bacci gashi ranar ina da lecture ɗin safe sai misali ƙarfe 7:44am na farka shima da taimakon alert ɗin da na saka a wayana ƙararsa ya dame ni dole na tashi adaddafe nayi wanka ina ɗaure da brown towel yayin da hannuna yake rike da hand towel ina goge raguwar ruwan wanka dake jikina. Long hijab na sa nayi sallah tare da Istigifari na rashin yin ta cikin lokaci. A gaggauce na shirya.

Ina fitowa daga É—akina na wuce bedroom É—in Umma dake upstairs na yi mata sallama ta tambaye ni na yi breakfast? Na amsa mata da cewa nayi latti amma idan na isa school zan yi a cafeteria, ina fitowa na tarar da Idi direba yana jirana a compound na shiga mota ya ja muka tafi......