SADAKI

004

by @auntysis

SADAKI...!


AuntySis💜


004





"Ni kuma bai yi min ba duk nacin shi har yanzu bai sami karɓuwa a zuciyata ba.

Da wannan zance mu koma class around five o'clock muka fito daga lectures, direba ya zo ya daukeni, a kasalance na shiga É—akina abu na farko da na fara yi shine wanka, na shirya cikin cotton gown mai gajeren hannu, na fito zuwa parlor kaitsaye na wuce kitchen, mama na tarar a ciki tare da mai aikinta Larai tana tayata aiki da yake yau Mama ce ke da girki with respect na gaida Mama da Larai duk suka mun sannu da dawowa, na zari plate na É—iba abinci na fi ce zuwa parlor na zauna akan two seater ina ci,ina kammala cin abincin na kai plate kitchen na wuce É—akina ina shiga na ji ringing É—in wayata da sauri na isa wurin wayar, sunan mayataccen nawa na gani sai da gabana ya faÉ—in kaman ba zan yi picking ba sai na dauka so nake naji yanzu kuma me zai ce dani. Cikin taushin muryarta na yi mishi sallama.

"Assalamu alaikum! Ma'abociya kyau da cikakkiyar sura. Ina fatar kin dawo gida cikin koshin lafiya?" 

"Lafiya ƙalau.

"ma-sha-ALLAH! Idan ban takura ki ba mai kyau gani a ƙofar gidanku ki fito mu gaisa idanuwana sun kasa haƙura da rashin ganin kyakkyawar fuskarki.

Sai na ja wani gwaron numfashi tare da saukewa "Gani nan zuwa.

Na faɗa tare da sauke wayar daga kunnena ina mai tu'ajjabin faruncinsa, sai da na ɗan gyara fuskata ta hanyar shafa powder na ɗan fesa turare mai saukin ƙamshin, sai kawai na zura ɗaya daga cikin long hijab ɗina, na fita na leka kitchen tare da faɗawa Mama na yi bako Mama ta dawo da ganinta akan fuskata "Wai ni Muhibba har samari nawa za ki tsaya dasu? Kuma har yau kin kasa fito da ɗaya kwakkwara a cikinsu ga Muhammad nan har yau kin kasa amincewa dashi idan na yi miki maganarsa ki dinga yi min nuku-nuku idan ba kyasonshi babu dole ki fito ki faɗa mashi ya haƙura mana amman wannan jan rai da kike mai ya yi yawa.

 "Ni gaskiya Mama ba son yaya Muhammad ne bana yi ba kawai dai ba zan iya da wannan miskilanci nashi ba gashi da masifaffen kishi.

"To ai shikenan sai ki faÉ—a mai ba tsuke ba ki yi za ki yi ba ki yi shiru ba.

Juyawa na yi ina faɗin "Sai na dawo Mama. Na buɗe ƙaramar ƙofa wadda ke haɗe da gate ɗin gidan na leka na hango mota sai dai ba wacce ya dauko ni da ita jiya ba wannan ta fi wancan kyau da tsada nesa ba kusa ba. Cikin tako ɗaɗɗaya na isa gun motar ya yi saurin balle murfi ya fito tare da jinginar da bayanshi a jikin motar, yana sakar min da murmushi ba ƙaramin kyau ya yi min a idanuna ba yana sanye ne cikin tsadaddiyar brown shadda, wacce ta ƙara ƙawata fatar jikinshi kanshi ba hula sumar kan tasha gyara baƙa sidik da ita irin ta fulani asali ƙamshin turarenshi ya baibaye kofofin hancina. Cikin sanyi murya na yi mai sallama tare da gaishe shi ya amsa min da sakakkiyar fuska gashi sai murmushi yake zubawa.

"Zuciyata ta hanani na zauna lafiya ke kadai take son gani a koda yaushe Muhibba.

Murmushi nayi tare da sadda kaina ƙasa ina wasa da gefen hijab ɗina, bugun zuciyata ya tsananta wani kalan bugawa da take yi da karfi wadda na rasa gane dalilin bugawarta.

"Muhibba ko ke san cewa kowacce rana kyawunki daÉ—uwa yake a cikin idanuwana?" Tabbas ba zan dakata da bege haÉ—e da kwaÉ—ayin mallakar kyakkyawar mace mai cike da haiba da zati uwa uba wadda aka gina rayuwarta cikin ilmin da tarbiyar musulunci, zuciyata ba zata huta ba har sai goben da bata da gobe. Muhibba na kai kololuwa a sonki bani da buri a yanzu da ya wuce na kasance miji a gareki na kawo kudin aure da kayan aurena har sadakin aurena a gidanku. Dan Allah ki karÉ“i tayin soyayyata ki so ni koda rabin kwatakwacin son da nake miki ne.

Shiru na yi na kasa furta uffan ga baki É—aya ya kashe min jiki da daddaÉ—an kalamanshi masu dadi da sanyayya zuciya.

"Mai kyau ba ki ce komai ba wannan shiru naki yana azabtar da ruhi da gangar jikina. Wallahi a shirye naki na zama bawanki sai yadda kika so za ki sarrafa ni, idan kuma so kike yi na zube a gabanki na saka miki kuka tare da roƙar soyayyarki shi ma a shirye nake, ni dai burina kada ki ce min a'ah!

Yadda ya karashe magana muryarsa tana rawa kaman zai rushe da kuka koma waye kai dole ya ba ka tausayi, ballantana ni da nake mace, kowa yasan zuciyar mace yadda take da rauni nan take ya karya min zuciya, na tsinci kaina da ja dogon numfashi tare da saukewa "Gaskiya ba zan boye maka ba Yallaɓai idan na ce ba zan karɓi soyayyarka ba tamkar na yaudari kaina ne fatana ka riƙe min amana domin akwai waɗanda ke sona daga cikinsu har da cousin ɗina sai dai duk a cikinsu ba wanda na ba wa damar da nake ji zuciyata za ta ba ka.

"Al-hamdullilah! Na yi matukar farin ciki da jin fitar waɗannan daddaɗan kalamai daga bakinki mai kyau ni kuma na daukar miki alƙawari zan riƙe soyayyarki gam-gam riko bana wasa ba zan rirrita ki na shayar dake ɗanɗano daga cikin zaki da gardin da soyayya take dashi, ba za ki taba danasani ware min fili a zuciyarki ba.

Daga nan muka ci gaba da fira dukka maganganunshi masu dadi ne da tsayawa a zuciya, don Alh Mustapha ya kware da iya tsara kalaman SOYAYYA.

Duk da can kasan zuciyata ina so na tambaye shi ko yana da iyali sai kuma naga rashin kyatuwar hakan, shine ya dace ya faɗamin watakila ya bari ne sai ya gama samun karɓuwa a wajena.

Washegari ina tashi daga bacci na ci karo da text message É—inshi guda biyu hausa da turanci sa'ili da nake karanta sakon nashi bansan lokaci da fuskata ta cika da murmushi ba.

Mornings are beautiful, but they are especially satisfying when I get to wake up beside you and that sweet smile of yours. It's the best way to start the day. l love you beautiful.

Na hausa kuma sai ya ce "Sonki a cikin zuciyata tamkar numfashi ne da yake fita daga hancina wanda tsayar dashi daidai yake da mutuwata, idan haka ne tayaya kike iya gani Mustapha zai cire sonki daga zuciyarsa?" Ina sonki ma'abociya kyawu da kyakkyawar surar jiki. Barka da safiya.

Cike da wani kalan farin ciki na shiga bathroom na yi wanka na fito na shirya na wuce school, muna fitowa first lectures sai ga kiranshi ya shigo wayata cikin zumudi na yi picking ga wani kyayataccen murmushi akan fuskata.

Ajiyar zuciya ya sauke mai sanyi a cikin dodon kunnena, wadda ta sakani lumshe idanuwa na tasa na kusa rasa balance dina.. Sallama yayi mun da muryarshi mai saukin amo wadda ako da yaushe take nuna tsantsar zati da haibar da Allah ya halicce shi da ita, bai bari na amsa ba ya fara kirarin nashi kamar yarda ya saba "The absolute love of my life, my one and only swt hrt,the queen of my hrt,my love from another star,the real definition of beauty with brain...da fatan sarauniyar zuciyata wadda ta mamaye duk wani jini da tsokar jikina da salon soyayyarta da kaunarta ta tashi lafiya"

Saboda tsabar yadda kalamanshi suka daki zuciyata su ka kuma samu nasara yin rassa a cikin gangan jikina, sanadin haka yasa naji kafafuwana sun kasa daukata ina neman zubewa kasa sai da Hafsat da ke gefena ta rikeni da kyau ganin na yi lum da ido ina neman fad'i.

Cikin kasa kasa da murya tace"Besty ki yi hankali zaki fad'i fa?

Ko jinta ba na yi na riga na yi nisa ni kaina bazan iya tantance a wata duniya na ke ba, abu daya na sani Alhaji Mustspha ya had'u sannan ya kai makura a had'uwa..ga love iya love, pure love mara algus a ciki.

Jin yadda na yi shiru na kasa magana ne yasa ya cigaba da fad'in"Bazan takurama sauraniyar mata da sai ta yi magana da ni ba, numfashin ki kada'i da naji ya tabbatarmin da kina cikin koshin lafiya kuma ni daman zaman ki cikin koshin lafiya shine zai saka nima na yini cikin koshin lafiya da salama, ki huta lafiya sauraniyar mata."

Ni kaina bansan lokacin da na saki wani kayattacen murmushi ba

Hannuna na kwace daga cikin na Hafsah da sauri sauri na samu wajen zama na zauna saboda inna cigaba da tsayuwa, kalaman da ke bakin Alhaji Mustapha tsab za su saka na yi fad'uwan tumaki a tsakiyar makaranta a kuma bainar nasi.

Hafsat cike da mamaki bakinta bude' ta bi ni da kallo har ta kariso kusa dani dai dai lokacin da Alhaji Mustpaha ke fad"in"Amma kafin na bar sauraniyar mata ta huta, ina so ta kara sanin ina sonta sannan duk duniya ba ki da wani Masoyi kamata I love u Muhibba Allah ya aura min ke domin in hakan ta kasance na zama mai sa'a a cikin maza."

Yadda Hafsat ta tsareni da ido ne yasa na kara sakin murmushi kafin a hankali nace"Ina cikin makaranta zan kira ka in na koma gida."

Shima murmushin ya yi min a nashi bangaren kafin yace"Yadda kika ce haka za'a yi sauraniyar mata, ina jiran ki a koda yaushe."

Daga haka ya yanke kiran amma ni na kasa sauke wayar daga kunnuwana..

Tsabar yadda kalamanshi suka yi sanadiyar kassara duka gabobin rayuwata gaba daya a cikin yan satikan da muka had'u da Alhaji mustapha ya yi sanadiyar mamaye duka zuciyata ban sani ba.

Ina zaune rike da waya ina faman murmushi, murmushin farin ciki da annushuwan da ban taba tunanin wani namiji zai iya jefani cikin tsananin farin cikin da na tsinci kaina a ciki ba yanzu.

Hafsat ce ta zauna a gefe na. Lokaci d'aya na sauke hannuna da wayar, kallo tayi ta na fad'in"Besty wai meke damun ki ne? Kin fara ba ni tsoro kamar mai aljanu"

Lumshe ido na yi kafin na kwantar da kaina saman kafad'an Hafsat na yi shuru a cikin duniyar da na ke ciki ba na jin kowa sai kalaman amon zakin muryan Alhaji Mustapha.

Hafsat cikin takaici ta kalleni kafin tace"Besty mai ke faruwa? Waye ya kira ki?

Ajiyar zuciya na sauke kafin nace"Alhaji Mustapha ne Besty shine ya kirani."

Cikin karin mamaki Hafsat tace"Au shine duk naga kin wani sukurkuce kamar wata mara lafiya.?sai murmushi kike kamar bugun iska lokacin iska...

Murmushi na sakar mata ina mai dago kaina muna kallon juna.

Cikin kwantar da murya nace"Besty gayen nan ya had'u wlh, maganar gaskiya na kamu da soyayyarshi batare da na sani ba."

Hafsat ta yi shiru ta ma kasa magana a cikin ranta ta na tunanin da mai wannan mutumin ya zo? Ko kuma da wasu irin kalamai ya shawo kan Muhibba cikin kankani lokaci?

Ban bari ta gama wani dogon tunani ba nace mata"Besty ni fa daman yau na ke shirin gaya miki, na yanke shawaran zan bama Alhaji Mustapha dama ya turo gida kawai tunda raina ya aminta da shi"

Cikin zaro ido Hafsah tace"dama? Wani irin dama kuma? Kar dai ki ce min shi ki ke so ki aura?

Cikin kayattacen murmushi nace"In sha Allahu Besty ina sa ran haka"

Sai kawai Hafsat ta fara tafa hannu lokaci d'aya ta na irin salatin na tsoho yaga bala'ee tana fad'in"Haba Besty mai ya shiga kan ki? Wannan tsohon zaki ce zaki aura? Duk cikin samarinki ki kasa zab'an daya daga cikin Safwan ko Muhammad sai ki kare ma wani tsoho mai ya'ya da mata?

Kamar saukar aradu haka naji kalaman Hafsat sai naji kawai suna sukar zuciyata, cikin mamakinta na kalleta kafin nace"Daman zuciya ai tana aminta da abunda ta ke so ne, Safwan d'in da kike magana bai min ba, ba na jinsa a cikin raina. Haka shima Muhammad din ban tab'a son shi ba, Alhaji Mustapha da kike kushewa shine ya shiga raina kuma ya yi daidai da rayuwata."

Hafsat ta wani yi murmushin haushi kafin tace"Besty tsoho ne fa? Shekararshi arba'in da doriya fa kika ce?

Cikin gajiya da maganganun Hafsat na ki kiri kir ga Abunda na ke so nace"To ko shi muhammad din da kike so na aura shekaran shi nawa? Shi kanshi Safwan din Yana da shekaru dukkansu da kad'an za su girme ma Alhaji Mustapha."

Hafsat ta yi wani dariyan rainin hankali kafin tace"Ke ma kinsan karya ki ke yi ki had'a wannan tsohon da su Safwan haba ai kalan zaren ba kalan yadin ba ne, Besty in har kina jin shawarata kuma kin dauke ni da mutumci to kada ki ba ma wannan mutumin dama a cikin jikina naji kamar bai dace da ke ba, ki zabi Safwan ko Muhammad,they are d best for u Besty akan wannan dattijon mutumin da baki san matansa nawa da manyan ya'yan da ya tara ba"

Kafin ta dire na tareta da sauri cikin fusata nace"Besty shawara ki ke bani ko Umarni?

Kai tsaye Hafsah tace"Ni ban isa na baki umarni ba, sai dai shawaran in kin ga zaki iya dauka fine in kuma bata yi miki wannan ya rage naki."

Cikin fusata na mike lokaci d'aya ina rataya jakata nace"To tunda shawara ce ki rike kayanki kila nan gaba zata yi miki amfania, amma ni ina so ki sani na tsaida magana abunda zuciyata ke so shi zan bata."

Ko tsayawa sauraranta ban yi ba na wuce abuna daman an fara kokarin shiga lectures na gaba.

Raina sai faman zafi ya ke yi jin irin aibata Alhaji Mustapha da Besty ta gama yi, ni kuma ina jin zuciyata bazata iya daukan a tozarta mutum mai mutunci irinshi ba.

Gadadaya ranar ban kara bari mun had'u da Hafsat ba, itama kamar ta zuciya da muka gama karatun ranar dagani har ita ba wanda ya nemi wani.

Direbana na zuwa na shige mota muka dawo gida....


A raina ina jin cewa in har Besty bazata daina aibata Alhaji mustapha a gabana ba, to kila bazamu kara daidaita da ita ba.

Yadda ma na ke ji a raina zan iya sabawa da duk wanda ya hanani kusanci da abunda na ke so ciki ko har da ýan'uwana.

Duk da nasan duk abunda na ke shima shi suke so..

Har na koma gida raina a bace ya ke, sai da Umma ta gane yanayina.

Sai kuma da ta tambayeni, nace mata ba komai kaina ke ciwo tun a makaranta.

Sannu ta yi min kafin tace inje in yi wanka in sha ko tea ne sai in sha magani in kwanta in huta ta na jin gajiya ce.

Shawaranta na bi na shiga dakina na yi wanka na sauya kaya zuwa saukakku na zaman gida.

Kitchen na shiga na had'a tea kad'an na koma daki, ina sha ina tunanin kalaman Hafsat.

Sai ma in da ta kira Alhaji Mustapha da tsoho, wani mugun takaici ne ke kamani.

Karamin tsaki na ja kafin nace a fili"ina ga bata gan shi ba ne, zan so kuma ta ganshi nasan zata ga abunda na ke gayamata game da shi gaskiya ne."

Bayan na gama sha na maida mug din kitchen saboda yanayi na ko wajen Mama ban leka ba na koma daki na kwanta.

Na dauki wayata na rika karanta sakonnin Alhaji mustpha ina jin dadi da sanyi a cikin zuciyata da gangar jikina.

Sai na yi kamar na kirashi sai kuma na ji na kasa, ba na so yaga zakewata da yawa ne.

Cikin wannan yanayin barci ya kwasheni daman ina hutun sallah sai gabda mangariba na tashi shima Umma ce ta shigo ta na tashina wai na tashi ba'a son barci da mangariba.

Dole na mike na shiga toilet na gyara jikina ina fitowa naga wayata ta yi haske.

Har ina sauri wajen zuwa, na dauka don na san wanda na wuni da tunaninshi ne ya turomin sako wato Alhaji Mustapha Safana.

Da rawan jiki da na zuciya na hada wajen bude sakonshi.


_Sauraniyar mata ina fatan kin koma gida lafiya? Ki sani ina nan ina zaman jiran kiran ki, ba na so na kara kiran ki kiga kamar na dame ki, ni kuma a halin da na ke ciki na fad'a wani mummunn yanayi da muryan ki kad'ai ne zai iya fitar dani a cikin halin da na shiga._


Sai da na zauna saboda yadda na kara jin kalamanshi sun zauna a cikin raina ina ta murmushi ina kara maimaita sakon a cikin raina sai ga wani ya sake shigowa.


_Kin bani izini na sake kiran ki domin na samu waraka daga cutar da ta kamani?_


Cikin sauri na tura masa "Eh! Ina jiran ka"

Daga haka na koma na hard'e ina sakin murmushi ko minti daya ba'a cika ba sai ga kiranshi.

Har zan dauka sai wata zuciyar tace"Haba Muhi ki fara da jan aji mana."

Sai na dakata sai da ta kusa yankewa sannan na daga cikin kasa kasa da murya na yi mai sallama.

Ina jin sauke ajiyar zuciyarshi cikin samun salama yace"Da ace baki bani izinin jin muryan ki a wannan daren ba,da kila kafin safe ki samu labarin wani mummunan abu ya samu Alhaji Mustpaha."

Da sauri nace"Allah ma ya tsare, babu abunda zai same ka in sha Allahu"

Cikin saukewan numfashi yace"Kin tabbata? 

Cikin murmushi da soyayya nace"Na baka wannan tabbacin in dai kana tare da ni bazaka kara shiga damuwa saboda rashin jin muryata ba."

Cikin zumud'i yace"Hakan ya na nufin na samu karb'uwa wajen Saurauniyar mata?

Sai na kasa magana sai dai murmushi.

Ina jinshi ya kece da yar dariya kafin ya fara fad'in"Alhamdulillah Alhamdulillah Allah na gode maka"

Sai kawai naji shuru da alamun ya sauke wayar ina ta hello hello sai naji shuru, hakan yasa na katse wayar da mamakin abunda ya faru.

Sai zuwa can ya sake kirana ina dauka yace"Ki yi min afuwa Sauraniyar mata na kasa sarrafa farin cikina sai da na duka na yi ma Ubangiji sujudar godiya da kuma addu'an Allah ya aura min ke cikin gaggawa na kosa na ga an gama magana na kawo SADAKI gidan ku kin zama tawa gaba daya".......