006
by @auntysis
SADAKI
AuntySis
006
Sanye na ke da bakar doguwar rigar Abaya na Maryam's Epytian Abaya.
Abayunta na da kyau sosai, the texture and uniqueness is out of this planet,
Na saka mayafin Abayan na yane kaina da shi sannan na yi kwalliya, as in make up sosai nayi wanda da ka kalleni zaka san lallai nayi kwalliya saboda yadda fuskata ke ta daukan ido.
Kafata sanye da flat din takalmi baki mara tudu, yau har wata yanga nake wajen tafiyata....
Ina fitowa na hango bakar Motarshi Benz, yana ciki bai fito ba sai da ya hango ni da sauri ya bude murfin mota ya fito shima.
Wow ya yi kyau sosai gaskiya Mustyna ya had'u shi din ta ko'ina ya cika ya had'a komai da ake bukata wajen Nagartaccen namiji mai nasaba.
Tun daga nesa ya kureni da ido ya na kallona cikin kayattacen murmishinshi da ya ke narkar min da zuciya.
Kafafuna ne naji suna hardewa saboda irin kallon da ya kureni da shi hakan yasa naji ina tafiya kamar zan fad'i da kyar na iya karisawa gabanshi.
Cikin jin kunyar kalar kallon da yake mun sauke kaina kasa nace mai"Barka da zuwa."
Sai da naji sautin murmishinshi kafin naji yace cikin tausasa murya.
"Ke za'a yi ma darka da fitowa sauraniyar mata"
Nima martanin murmishin na maida mai, ko magana na kasa yi kaina na kasa saboda yadda ya ke ta kallona.
Fararen kaya ya saka wata shadda mai kyau har da babban riga aikin jikin kayan baki ne sai ya sanya bakar dara as usual bakin takalmin Aldo ne a kafarshi na fata mai kyau.
Agogon hannunshi na fata ne baki shima mai kyau da tsari, kana kallonshi zaka ga yana screaming luxury, daga kasan ido na kare mai kallo ina murmushi a cikin raina. Lokaci daya da jin wani farin ciki na nafi kowacce mace sa'a a duniya na samun miji kamar Alhaji Mustapha Safana.
Shi ya katse min dan gajeren tunanin da na fada da cewa"Yan mata na kin yi kyau sosai kamar wata a cikin taurari."
Murmushi na saki kafin nace"Nagode kai ma ai ka yi kyau sosai."
Kai ya girgiza kafin yace"Haba ai kyau na wajenki sauraniyar mata, in kina waje ba'a iya maganar kowa a wajen."
Kunya ta kamani na saka tafukan hannayena na rufe fuskata ina sakin murmishin jin dad'i ji na ke yi kamar wacce ke yawo saman gajimaren soyayya saboda farin ciki.
Gaba daya ya susuce a kallona ya kasa sukuni idanuwansa na kaina kamar ya lasheni ya maidani ciki haka ya ke ji, sai faman lumshe ido ya ke yi ya na kallona cikin idanuwanshi masu kassara gangar jikina.
Lokaci d'aya da murmishinan nashi mai sakani kara matuwa akan soyayyarshi.
Kamshin turarenshi kad'ai da na ke shaka a cikin kofofin hancina wani irin mugun dadi nake ji saboda asalin kaunata da turaren.
Ina jin kaina kamar ba cikin duniyar da muke ciki ba.
Shiyasa har na manta da sakon Abba na shagala na sakankance gaban Musty ya na gayamin kalamai masu dad'i da sanyaya rai masu nuni da cewa duk duniya bayan ni babu wata mace a cikin zuciyarsa.
(Ko ina matarshi??? Oho! Ku tayani tambayar sarauniyar love don Allah)
Kamar an tunasar dani na tuna Umma tace na kaishi falon baki da sauri na kalleshi kasa kasa kafin nace"Au na manta muje falo sai ka jira Abba kafin ya fito."
Kai ya kad'a kafin yace"Daman ai izininki na ke jira sarauniyar zuciyata muje."
Ina gaba ya na bi na a baya duk kunya ya kamani saboda ina jin kallon da yake mun a cikin jikina.
Har cikin falon na kaishi ya samu saman daya daga cikin kujerun falon ya zauna.
Ni kuma na koma cikin gida na shiga kitchen na had'o mai ruwa da lemu na kai mai.
Na durkusa a gabanshi na zuba mai ruwa tunda shi kadai yace zai sha.
Na bashi ya karb'a ya na kallona lokaci d'aya ya na fad'in "godiya na ke yi sarauniyar mata."
Ina murmishi na mike na fita ya bini da kallon so da kauna.
Ina fitowa falo naji muryan Abba ai da gudu na shige dakina na rufo ina jin gabana na fad'i.
Kan gado na fad'a ina sauke numfashi sai gani ina addu'an a raina Allah yasa Abba ya yaba da Musty kamar yadda nima na yaba domin wlh in har Abba bai karb'esa ba to yadda na ke jin kaina bansan kuma wani hali zan shiga ba.
Zaman ne ya isheni da Zullumi tare da fargaba sai na kira Hafsat sai da ta gama ringing ta kusa katsewa sannan ta daga kiran nawa muryanta a cunkushe.
Cikin fargaba nace"Besty ina jin tsoro.".
Barci Hafsat ta ke yi amma sai da ta wartseke cikin mamaki tace"Tsoron me kuma besty?
Cikin tararradi nace"Mustyna ya zo gida suna can falo suna ganawa da Abba."
Hafsat ta bude idanuwanta sosai kamar Muhibba na ganinta kafin tace"Waye kuma Mustynki?
Cikin sauri nace"Alhaji Mustapha Safana mana."
Kai Hafsat ta jinjina kafin tace"Oh ai bansan lokacin da ya koma naki ba shiyasa, ke kam tsoron me ki ke ji? Tambayoyi ne Abba zai yi mai in ya aminta da shi ba shikenan ba."
Cikin tsoro nace"duk da haka ni dai ina jin tsoro."
Cikin takaici daga can bangaran Hafsah tace"Wai tsoron me ki ke ji?
Da sauri nace"Kada Abba ya ki aminta da Musty, wlh in har haka ta faru na shiga uku besty ina zan saka kaina."
A cikin ran Hafsat kuma salati ta ke yi, tausayin kawarta ya kamata yadda taga ta yi nisa bata ji bata gani.
Sanin da ta yi ko ta gayamata gaskiya bazata ji ba tunda soyayyarshi ta gama rufe mata jinta da ganinta.
Sai kawai ta kama lallashina ta na nuna min na kwantar da hankalina ba bu abunda zai faru sai alkhairi.
Mun rabu da juna akan yadda suka yi da Abba zan kirata na gaya mata.
Bayan mun gama waya da Hafsat kuma sai na kasa samun natsuwa kwata kwata.
Na kasa zaune na kasa tsaye, daga karshe sai gani a falo ina shawagi.
Umma na cikin daki Mama ce ta fito ta ganni sai da naji kunya.
Itama kallon mamaki ta yi min kafin tace"Muhibba yaushe kika zama mara kunya akan namiji kin fara ma Abbanki labe?
Ina jin haka sai na kwashi sauri zuwa dakina lokaci d'aya ina fad'in'"Laaa Wlh Mama kitchen na shiga na sha ruwa."
Da ga haka na shige ciki da sauri na rufo kofa Mama ta bini da kallon mamaki da tsoro.
Aranta tana tunanin anya haka Mutumin nan ya zo ma Muhibba bata ji bata gani a kanshi wanda ko wata ba su yi da had'uwa ba ya fara sauya mata dabi'unta.
Girgiza kai ta yi, daman kitchen zata shiga kuma har ga Allah ita Muhammad ta yi ma Muhibba sha'awa saurayi ba mai mata da yara ba.
Amma tunda Abba da Umma sun ce abunda ta ke so shi zaa bata sai ta kama bakinta ta bi Muhibba da fatan alkhairi....
Ni kuma ko da na koma dakin sai na kasa zaune na kasa tsaye na rasa abunda ke yi min dadi.
Abun da ya banu tsoro har an kira sallar magariba.
Sai na dauki waya kamar na kira Musty sai na kasa, sai naga kamar na zake da yawa akan lamarinshi...
Kasa tashi na yi zuwa sallah har aka idar a wasu masallatan sai da naji kamar maganar Umma kuma ta na tahowa zuwa cikin dakina.
Ai da gudu na fad'a tiolet dai dai shigowar Umma dakin.
Ina jinta tana kira sai na bude famfo taji karan saukan ruwa.
Sai ta daga murya ta na fad'in"Au kina toilet ne, to in kin fito kije falo wajen bakon ki, yanzu suka dawo masallaci tare da Abban ki."
Daga haka ta fice ina jin haka da karan fitan ta sai da na yi tsalle a bayi ni kadai cikin farin ciki.
Hakan kenan ya bani tabbacin Abba ya yi na'am da zabina.
Allah na tuba ko sallar ma faka faka na yi ta, ina sallamewa na kara gyara fuskata na fesa turare na kara gyara Rolling din mayafin da ke kaina na fice.
In da Allah ya taimake ni Mama bata falon Sai Umma ita tace na shiga Kitchen akwai abinci ta had'amin na kai ma bako na.
Farin ciki ya kamani na rungumeta ina fadin"Sai Umma ta."
Dafani ta yi kafin tace"Allah ya tabbatar da Alkhairi, Abban ki yace shima ya yaba da zabin naki daga gani surukin namu ya ci jarabawarshi."
Da wannan farin cikin na shiga falon dauke da faranti a hannuna shake da kololin abinci shi ya taso da kanshi ya karbeni yana fad'in"Bai dace da Sauraniyar mata kamar ki ta na daukan kayan nauyi haka ba."
Kunya ta kamani sai na sakar mai, duk soyayyar da ke damuna amma sai naji na kasa sakewa a gabanshi.
Nesa da shi na zauna tun bayan da yace sai anjuma zai ci wani abu yanzu cikinshi ya cika yaci abinci kafin ya fiti gida ga farin cikin yadda Abba ya tarbeshi kadai ya isa ya cika mai ciki ko dai bai ci komai ba....
Kai tsaye na kalleshi ina fadin"Ko Madam ta dawo ne?
Yana yi min wani kallo yace"Ta dawo shekaranjiya ita da yara, amma ta min laminnin yin dinner a wajenki bakomai."
Cikin mamaki nace"Au ta sanni ne?
Yana yar dariya yace"Kina mamaki ne? Ai daga kan iyayena zuwa makusantana a yanzu dai ba wanda baisan da labarin ki ba My Love, ni fa ba da wasa na ke yi ba, mun yi mgana da Abba kuma bisa alamu ya aminta dani yace na bashi lokaci ya yi magana da yan'uwanshi da yayyenki, da zarar ya amince dani zan turo magabatana ayi magana Muhibba ina kaunarki bani da wani buri illah naga na mallake ki, Madam kuma da kike magana ita na fara samu da maganar ta kuma bani goyon baya tace kuma na gaya miki ta na miki kyakyawan maraba Sauraniyar mata."
Ya karisa fad'a ya na kasheni da Murmishinshi da ya kara sumar dani.
Sai naji kaina ya fashe ashe haka na ke da matsayi ban sani ba?
Irin wannan soyayyar ko a novel dinsu Maamuh Geee Su Rano Su Sadnaf albarka don ta ci uban ta Toyin din Fa'iza da oga Dr. Bobby kai Bulkachuwa ma albarka Ballatana a irin fina finan India na soyayya da basu da aiki sai koyar da munafunci da mugun abu.
Bansan na shagala ba sai da muka ji an fara kiran sallar isha'i sannan yace min zai tafi, da kyar yaci rabin tuwo guda d'aya wanda Mama tayi miyar Agusi.
Ni na rakashi har bakin mota ya dauki katuwar leda cike da kaya ya bani tare da kud'i da nace bazan Karb'a ba sai ya marairace yana fadin"Haba Sauraniyar zuciyata, kiris fa ya rage ki zama matata, sadaki kawai ya rage na kiya ki zama tawa gwara ma tun yanzu ki shirya komai na dawaniyarki ya dawo kaina abunda kike so da ma wanda baki so ni Mustapha na yi miki alkwarin sai in da karfina ya kare."
Dole na karb'a ina masa godiya yace baya so ya shiga Motarshi yana daga min hannu ina daga mai har ya bar haraban gidanmu....
Ina shiga gida Dldakin Umma na wuce na nuna mata kayan da kudi.
Kai tsaye tace na kai ma Abba yana falonshi daman kuma yace in bakon ya tafi ya na nema na.
Mama ce ke tare da Abba a falonshi yana ma shirin tafiya masallaci ne sanda na shigo.
Ganin haka yasa yace nima na yi sallar kafin ya dawo.
Anan falon na bar kayan kudin kuma na bama mama itama sai da ta jinjina.
Cikin fad'a tace meyasa na karb'a?
Ni kuma cikin Shagwaba nace"Mama sai da nace baxan karb'a ba ya matsamin fa"
Mama ta tabe baki kafin tace"Bari Abban ku na ku ya dawo mu ji abunda zai ce."
Da haka na wuce dakina nima na yi alwala na yi sallah.
Hafsat na kira jikina na rawa na bata labari sai ba ta dauki wayata ba.
Umma ce naji ta na kwalamin kira sai na fito da Sauri.
Kai tsaye tace Abba ya dawo yana son mgana dani.
Ban ji wani tsoro ba, saboda na gama samun tabbacin amincewar Abba.
Da Hijabin da na yi sallah na shiga falon Umma da Mama duk suna zaune gefe da gefenshi.
Shi kuma yana tsakiyarsu ya na kallon labarai.
Ina shigowa ya bani Umarnin na rage karan TV, jiki na rawa na dauki remot na rage na koma gefen mama na zauna a kasa kaina na kasa.
Abba ya dago ya na kallona kafin ya kira sunana cikin kaushin murya alamun ba wasa.
Na amsa nima cikin natsuwata kafin naji yace"Naga kudi da kaya iyayenki sun nuna min shi ya baki?
Kai Tsaye nace"Eh Abba."
Sai Abba ya jinjina kai kafin yace"Da kyau, bazan ce kada ki amshi komai daga hannunshi ba, amma ya dakata da baki kyatttuka haka sai nayi magana da yan'uwana tare da yayyenki zamu yi bincike tunda yace da gaske ya ke yi, in har na sameshi a yadda na yi tsammani zan bashi damar turo magabatanshi kamar yadda ya bukata, kina ganin hakan ba matsala kina son shi?
Kaina na kasa na kasa magana Abba ya kara maimaita tambayarshi nan ma ma yi shuru ina murmishi.
Umma tace"Abban su shirun mace fa Eh dinta ne."
Abba ya jinjina kai kafin yace"Shikenan ta shi kije, ki yi ta addu'a sannan ki kula fa In har mun gama magana da su an kuma bincika zamu ba shi damar da ya nema in sha Allahu.'
Kaina na kasa na mike ina fadin"In sha Allahu Abba nagode."
Sum sum na fice kaina a kasa suka bini da kallo.
Mama ta yi tsaki kafin tace"Ni har ga Allah hankalina ya fi kwanciya da Muhammad"
Abba ya yi murmushi kafin yace"Ta ga Muhammad din amma ta kawo wannan din Asma'u hakan kad'ai zai baki tabbacin shi ta ke so, ni kuma ba auran dole a gidana abunda mutum ke so shi zan tayashi so, kema kuma ina baki shawaran ki bar maganar Muhammad don Allah"
Umma tace"Nima shi nagani Abban su, yarinya tace ga wanda ta ke so ba shikenan ba shi Muhammad din sai ya yi hakuri tunda daman bata bashi wata dama ba, ballatana yace an yi mai ba dai dai ba."
Abba dai na zaune kanzil bai ce ba sai ma Remot da ya dauka ya kara karan TV ya cigaba da kallon labarai...
Ya bar Mama da Umma na tafka Muhawara yasan halinsu shiyasa ya yi kamar baya falon ya maida hankalinshi wajen kallon Labarai.
Ni kuma ranar kasa barci na yi saboda farin ciki.
Da ban samu Hafsat a waya ba sako na tura mata na gaya mata Abba ya amince da Alhaji Mustapha.
Shi kuma da ya kirani tsab na fayyaace mai yadda muka yi da Abba cikin jin dadi yace"Alhamdulillah in sha Allahu ina ji a jikina kin kusa zama mallakina Sarauniyata."
Saboda Madam na nan ta bakinshi shiyasa bamu tsawaita magana ba muka yi sallama.
Da asuba kuma wayar Hafsat ta tasheni ta na tambayata an ce ya turo ne? Sai na zauna na yi mata bayanin abunda Abba yace.
Cikin basarwa tace"Allah yasa alkhairi."
Daga haka ta katse wayarta ni kuma bata gabana ta yi ta adawarta ni dai naji na gani ba bu wanda ya isa ya sauyamin ra'ayina.
A ranar Abba yaje can gidansu ya yi maganar, sauran kuma ya kirasu a waya sun dai tsara yadda binciken na su zai kasance.
Su yaya Faruq kuma A daran Abba ya tarasu shi da Yaya Ibrahim da Yaya Abubakar.
Sauran duk ba a garin katsina suke zaune da iyalansu ba.
Ya khalid yana Ibadan ya na Masters dinsa, sai Yaya Aseeya ta na Abu zariya ta na karatu amma ta na shekarar karshe.
Amatu da Isma'il an yi hutun makaranta suna gidan Anty Hassana tare da su Azeeza saboda jikokinta sun zo mata hutu suna can tare da su.
Abba ya yi musu bayanin komai suma suka ce xa su bincika.
Yaya Ibrahim shima ya kawo maganar Muhammad, Abba yace mganarshi ta kare tunda ga abunda na ke so.
Daman tuni na daina daukan wayarshi shi da Safwan.
Magana ce ta yad'u a dangi Muhammad ya samu labari Safwa ma kuma shima yaji labarin na ba ma wani dama har an fara magana.
Sun yi ta kirana ban dauka ba sun turomin sakonni ban bude ba na goge sannan na yi blocking din su.
Bani da lokacinsu ni yanzu lokacina da tunanina na kan Mustyna wanda ya ke bani dukkan wani soyayya da gata.
Sauran yan'uwana mata sun yi ta kirana suna min dan bikin me zai kai ni auran mai mata, ga samari zarata na sona, ni kuma nace eh din naji na gani Umma ke karemin tace a barni da zabina.
Ko sati biyu ba'a yi Abba ya kirani yace na gayama Alhaji mustapha ya turo waliyanshi, ranar kamar an sakani a cikin Aljannah haka nake ji
Shi kuma Musty da na gaya mai sai da ya yi sujud shukur washegari ya zo gida yana gayamin magabatanshi suna nan zuwa cikin satin nan.
A ranar kuma ya matsamin sai da ya shiga cikin gida ya gaida su Umma.
Sai ga mama itama ta fara yabawa da zabina tace yana da natsuwa da hankali ta na fatan na samu kwanciyar hankali tare da shi.
A weekend din magabatanshi suka zo daga can Safana sun zo da komai na kayan saka rana har da *SADAKI*.
Da Farko gidansu Abba sun zata za'ayi neman izini ne sai suka ga su da mai gaba daya suka zo.
Dole suka ba su magana anan take aka saka rana wattani uku, suka kuma ce za su biya *SADAKI* Dubu dari biyar Amma dai dubu dari biyu gidan su Abba suka karba sai 100k kudin na gani ina so sai kayan saka rana kwalayen cingam da alawa, goro,dabino drinks kamar za'a bude karamin shago.
Ni daman ya fad'amin zuwan gaba daya magabatanshi za su yi, amma ban taba tunanin saka ranar zai zama kusa haka ba.
Farin cikin da na ke ciki baya misaltuwa, Yaya Faruq na ta yi min tsiya na bari ayi auran mu rana daya mana.
Ina tura baki nace kai da ko budurwa baka dashi ni kuma ina da mijina a hannuna bazan jiraka ba.
An rababba kayan saka rana, kowa yasan an sakamin rana da muradin raina.
Ni da kaina na shirya naje gidansu Hafsat na kai mata nata mintin saka ranar daga nan ta saduda ta daina adawa da Mustyna kamar yadda na ke kiranshi...
Tunda aka saka mana rana sai muka kara shakuwa, Mustyna sai yafi sona kamar ya lashe ni, kulawa ba wacce baya bani, shi ya ke kai ni makaranta in yana gari in kuma baya nan sai direba yaje ya daukoni.
A zuwa Lokacin a cikin yan'uwana kalilan ne ba su san shi ba, kuma kowa ya ganshi sai ya yaba da zabina....
Mun taba gaisawa da Madam dinshi sau daya.
Yaran kuma kananan guda biyu Islam da Aslam ya kawo min su, sun yi min yini na fita mukaje shopping na yi musu siyayya.
Har Hafsat sai da tace ta yarda Alhaji Mustapha na sona.
Ta kuma amince bani da masoyi kamarshi.. Muhammad ya dawo garin afujajan har kuka ya tasani yana yi min ni ko nace sai dai ya yi hakuri na samu miji daidai dani.
Mustyna ba shi da wani buri illah na mallakata koda yaushe kalamansa kenan.
"Sarauniyar ta, matata yan Matata, kin zama mallaki na yanzu tunda akwai Sadakina a hannuna magabatanki."
In ya yi min dawainiya nace ya yi yawa sai ya hade rai yace"Kul kada na kara jin haka, kada ki manta ni Mijin ki ne yanzu tunda na biya *SADAKI* kuma shaidu sun shaida hakan, wasu malaman ma sun hallatamin ke sauraniyata."
In ya fad'i haka sai naji kaina ya kara girma, abu daya ke kara burgeni da shi Ibadarshi tare da sanin ya kamatanshi.
Sannan uwa uba tunda na ke da Musty ko hannuna bai tab'a kwatanta fara rikewa ba, ko kusa dani bai tab'a zama ba.
In na yi wani tunani sai inga to ai yana da matarshi har da ya'ya kenan na yi sa'a ne samun namiji nagari a cikin dubu da sai an tona...
Tuni na zama yar gata, wacce na ke jin kaina a sama saboda ina ganin na yi ma sauran mata zarra.
Abokanshi kuwa duk na san su yana kawomin su, suna gaisheni Yaya Faruq kuma sun saba har lambar juna garesu Yaya Ibrahim ma haka..koda yaushe suna fad'in Muhibba ta yi dacen miji babban mutum mai hankali, dattako da kamala.
Da Anty Hadiza ta zo garin yazo gaisheta itama sai da tace gaskiya Muhi kin tako sa'a irin wannan mai zafin haka..
Ni ko sai dariya ina jin farin ciki ya cika raina. Hafsat kuma na yi kokarin Muhammad ya je wajenta su daidaita yaki amincewa itama haka.
Sai na had'ata da Safwa shima tace bata son wulakanci ai ba kwantai ta yi ba.
Shima kuma sai ya nuna tunda har naki shi to ya hakura, ni kuma ba na so na yi aure na bar Hafsat na fi son itama ta yi auranta ta samu dakin kanta kamar yadda nima na ke fatan samun nawa.
(Hajia Muhibba kenan,uwarda ta haifi titinic kaka ga Romeo da Julliet, mu je zuwa)