SADAKI

007

by @auntysis

SADAKI 


AuntySis


007


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yadda Ubangiji ya tsarama ko wane bawanshi,wasunmu cike su ke da buri mai yawan gaske da fata kamar yarda yake a nawa bangaren da bani da wani buri da fata a nan duniya ban da inga yau na zama matar Musty ni da shi mun zama miji da mata an daura mana aure na tare a gidanshi a matsayin matarshi, kalar dokin da nake da zumudi kan auren nan bama gaskia bane ba, ko zama kayi dani na lokaci kankani zaka gane yadda zuciya da ruhi na suke kaunar Musty...


Zuwa wannan lokacin a cikin dangin mu ba wanda baisan matsayin musty a wajena ba, ni kaina sai in zauna inta tunanin irin son da na ke yi ma Musty kamar wanda ya yi min asiri duk da na san ba asiri bane, tsabar iya soyayya ne da kula da mace da bukatunta, duk da ni din ba wai na taba soyayya da wani bane duk da yawan masoya na shiyasa da abun ya zo sai zurma jikin nawa yayi yawa.. 

Duk yadda nake rawar jikin nan idan na tuna cewa shima yana sona sosai, don tsananin son da ya ke min ya ninka wanda na ke yi mai sai naji hankalina ya kwanta duk da yana da iyali amma hakan bai hana shi nuna mun so dari bisa dari ba.....

Kaf a cikin abokan aikinshi da makusantanshi kalilan ne ba su sanni ba, duk tsananin Abba sai da ya hakura Musty ke kaini makaranta in yana free sannan yaje ya daukoni a motarshi da kanshi, kuma Abban ya amince ma hakan ne ganin Musty ya bada Sadaki na har an saka ranar aurenmu wanda lokaci kawai muke jira...

Tunda a cewarshi bai amince yana mijina wanda ya biya Sadakina ya kwanta a gida wani kato yana jan matarshi a bayan mota ba. In ya fad'i haka sai dai kawai inyi dariyar murna da farin ciki ina ji a jikina kamar na yi ma sauran mata zarra.


Da ya ke Alhaji mustapha yana aiki ne a CBN Katsina sannan yana kasuwanci dan kwangila ne sosai a garin katsina da wajenta shiyasa ya ke da kudi kuma ya ke kashe min su kamar bai san zafin su ba....

Idan nayi magana sai yace shi yanzu yana matsayin mijina ne, tunda ya riga ya biya Sadakina.

Mama ta yi ta fad'an kashemin kudin da ya ke yi ya yi yawa kada azo a samu matsala...Umma kan tareta da fadin ba komai ai yana sona ne shi yasa kuma ai an saka mana rana har Sadaki ma ya biya, daurin auren ne kawai ya rage, kuma da ashe babu zancen aure ne tsakaninsu sai abun ya zama damuwa, saboda kowa yasan mazan yanzu basu kashe ma mace kudi haka a banza babu zancen aure..

Abba kuma sai dai ya yi ta nanata min in kula da kaina sannan in kiyaye saboda duniyar dukkanta da mutanen cikinta sun zama abun tsoro sai da taka tsan tsan... 

Sauran yan'uwana ma haka ne tsakanina da su barin ma Ya Faruq da koda yaushe maganarshi irinta Abba ce ta in kula da kaina in sani daga gidan mutumci na fito...


Ko me yasa suke min irin wannan hanunka mai sandan?

Na taba tambayan Hafsat kai tsaye ta kalleni tace min"Saboda sun ga rawan kafan da kike yi a kansa ya yi yawa shiyasa."

 Da ta fad'i haka ban damu ba sai nayi mata murmishi kafin ince"In ma nayi mai rawan kafa ai ya isa ne, kuma kafin na fara yi mai rawan kafa shi ya fara rawan kafa a kaina."

A lokacin baki kawai Hafsat ta tabe bata kara magana ba.

Har a cikin raina bana jin dadin yadda wasu lokutan Hafsat sai ta rikice kuma ta nuna wani lokacin bata son tarayyata da Musty...da irin kawancen da babu fahimta ne tsab zance bakin ciki take mun, amma deep down nasan mun wuce wannan level din da Hafsat na tayi mun ko in mata jin zafi kan abun dunia, I just don't know her reason for not loving our relationship saboda it's not like her, ko kare na kawo Hafsat zata so shi ta kauna ce shi saboda ni ce mai karen amma tun abun na kona min rai ina nuna mata muna yin fad'a har nazo ma fita batunta saboda na taba gaya mata ikon Allah ne kawai zai rabani da Musty nah...

Itama daga baya gajia da ta ga da gaske dai nayi nisa sai ta kama kanta sai dai tayi ta min nacin in rage rawan kafa a kan namiji kada watarana na ciji yatsa, ko kuma nayi nadama....

Da karfin gwiwata na kan ce mata"In sha Allahu tsakanina da Musty ba bu nadama har Abada."

Tunda na lura da mugun bakinta a kaina na daina gayamata wasu labaran da ya danganceni ni da Mustyna.

Itama bata damunta kanta da sai taji wani abu, saboda shi ya kan zo daukata ma bata jira muna tashi karatu take tafiyarta gida duk don kada ta shiga motarshi,shi kanshi har ya fahimci lallai bestyna har yanzu dai bata yinshi....


Ranar muna mota bayan yazo ya daukeni zai maidani gida.

Ya juyo yana min kallon nan nashi mai rikitani, nan da nan na dadirce ina yar murya kafin nace"Me ya faru musty na?

He gave me his killer smile kafin yace"ina tunanin irin son da nake yi miki, amma kuma har yanzu kawarki bata sona da ke, bansan me ta ke tunani a kaina ba ko ta na tunanin ban dace da ke ba ne My Love?

Ya karishe fad'a cikin raunin murya da sauri na tareshi da cewa"Ba haka ba ne, ita Hafsat fa haka yanayinta ya ke bata cika sakin jiki da mutane sosai ba, in zaka kula ni kadai ce kawar Hafsat duk fad'in makarantar nan."

Nayi ta kokarin na gyara Hafsat wajen Musty saboda kada ya ga kamar bata son shi dani, shi kuma da ya fahimci haka sai kawai ya yi dariya kafin ya kad'a kai yana fad'in"Shi kenan tunda kin ce haka, ni daman babban burina a yanzu ke ce, ki so ni ki kula dani ki maidani dan gata tunda kuma kina sona shikenan bani da damuwa."

Da haka muka bar maganar Hafsat muka kama wata hirar da ta shafemu wanda ya shafi maganar auran mu.

Tunda yanzu bamu da buri sai na ganin wannan ranar da zata zo da Tarihi mai yawan gaske...


Anty Aseeya ta dawo daga makaranta kuma sun hadu da Musty na itama sai da ta ce min"Ke kam muhibba wannan Mutumin bai yi miki girma ba, gwara Muhammad yaro ne matashi zaku ci kuruciyarku tare amma ga matashi me zaki yi kuma da wani mai mata da yara."

Tura mata baki nayi kafin nace"Ni fa shi na ke so Muhammad din da kuke ganin mu bai taba burgeni ba."

Mama na wajen tace"Kyaleta Aseeya Muhibba tayi nisa bata jin kira in dai kan wannan mutumin ne, mu yi mata fatan alkhairi da fatan zaman lafiya a tsakaninsu ni farin cikina daya mutumin da kin ganshi kin ga kamala da dattako kuma yana sonta ina ma Muhibba fatan samun kyakkyawan rayuwa tare da shi.".kuma babban abunda ke kara kwantar mun da hankali da ba muhalli daya zai hadasu ba, don Muhibba da sauranta akan zaman aure, gani take kamar yadda suke waje haka auren yake, amma kuma ba hakan bane, sai ta shiga duk zata gane abubuwan da muke nuna mata, marriage isn't bed of roses, hakuri shine ginshikin zaman aure...

Farin ciki ya cikani Mama ta sauko for the first time in history ta yabi Mustyna itama ma A. Aseeya sai bata kara jan maganar ba sai ta bi maganar Mama da Amin kawai.

Kafin komawarta makaranta itama sai da ta sare har ce min tayi"Gaskiya Muhibba ki rika tausayama bawan Allah nan jibesa kamar ya haukace a kanki ya zama kamar wani bita zaizai."

Kaina naji yayi girma sosai na ji farin ciki ya cikani, sai faman murmishi na ke yi saboda jin dadi.

Ni kaina nasan Musty na sona kowa kuma yasan baya had'ani da kowa ina da matsayi mai girma a cikin Rayuwarshi....


Bikinmu ya rage sauran wattani biyu maganar auran Ya Faruq ta taso itama sai dai Abba yaso ya hadamu rana daya amma daga gidansu yarinyar suka ce su basu shirya ba.

Sai nan da wattani biyar, da ya ke yarinyar iyayenta masu karamin karfi ne anan cikin garin katsina.

Abba kuma bai matsa ba yace Allah ya kaimu, kowa ai da lokacinshi...

Tunda bikin ya karato sai shirye shiryen mu ya karu hatta gidan da zan zauna Musty ya zo ya nuna min zanen gidan da tsarin da na ke so har an fara gina min wani irin kayattacen gida mai kyau da tsari.

Maganar kayan lefe kuma yace na yi list din duk abubuwan da na ke so zai bani kudi na had'a lefena da kaina dai dai ra'ayina da muradina.

Jikina na rawa na samu Umma na fad'a mata ita kuma tace na nemi Hafsat mu yi lissafin komai da komai sai na yi ma ko Aunty Hadiza magana.

Haka ko akayi na shirya naje gidan su Hafsat na sameta muka tattauna.

Da ita muka zauna muka Rubuta duk abunda na ke so tunda Musty yace kada na damu daga Naira d'aya har Naira miliyan hamsin zai iya kashemin saboda na yi ma sauran mata zarra.

Sai bayan mun gama rubuta abubuwan da na ke so ne na kira Aunty Hadiza muka yi magana sai tace shi kenan daman ai kasuwanta ne had'amin kayan lefe bazai gagara ba.

Duka duka abubuwan da na rubuta ina so ko miliyan biyar ba su kai ba amma Mustyna yana gani sai yace min wai kayan sun yi masa kadan Miliyan goma ya turamin yace in bai isa ba zai karamin.

Da ina masa korafin kudin sun yi yawa a karon farko naga bacin ranshi cikin kaushin murya ya kalleni kafin yace"Ba su yi yawa ba Muhibba, ko kin manta ke ce sarauniyar da ke mulkin zuciyata, wlh tallahi zan iya baki dukkan abunda na mallaka saboda farin cikin ki, in kina nuna min haka sai naga kamar baki sona son nawa a iya fatar baki ne"

Bakina da Muryata na rawa nace"Wlh ina son ka Mustyna"

Na karishe fad'a kamar zan saka masa kuka zuciyata ta gama narkewa acikin Soyayyarshi.

A karon farko tun had'uwarmu ya dago ya na kallona a cikin fararen kwayan idanuwanshi cikin wata irin murya yace"Ai baki taba nuna min haka ba, yar karamar kyauta in na yi miki sai ki rika nuna kamar ina miki wahala ko kin mata ke matatace? Sadakin ki na wajen Waliyan ki kowa ma ya shaida haka."

Kaina na kasa na gyad'a masa kai kafin nace"Ka yi hakuri bazan sake ba."

Ban tsammanci haka ba sai ji kawai nayi ya kamo hannuna na dama ya kai saitin bakinsa ya sumbuta cikin wata irin murya yace"Ya wuce, soyayyarki ta yi min nisa a cikin raina har ta kai ba na iya sarrafa kaina in ina kusa da ke"

Ya fad'a Lokaci daya yana kara damke hannuna cikin hannunshi, ban saba ba sai jikina ya fara rawa shi kuma ya wani lumshe ido kamar mai barci ya fara min tafiyar tsutsa a cikin tafin hannuwana.Da sauri na fara kokarin zare hannuna, kokarin da nake yasa ya dawo hayyacinshi da sauri ya sakeni bai bari mun had'a ido ba yace"Am sorry bansan na rike ki ba wlh."

Nima ina cikin wani yanayi da yasa da sauri nace"Nagode sosai sai da Safe."

Daman da daddare ne yazo ganina, da Sauri na bude mota na fito ina rawan jiki tare da na zuciya, kasa tafiya nayi sai da na samu wajen flowers na dan zauna kan kujerar rubber kafin in samu gudun da zuciyata ke yi ya daidaita, this is the first time having a contact with non muharram shiyasa naji abun wani iri, duk da min tashi gidan boko da gayu, amma muna da tarbiya daidai gwargwado da kiyaye dokokin ubangijin rahma..shima haka yaja motarshi ya fice daga haraban gidammu.

Ranar duk zumudi na sai ya ragu haka kurum naji jikina yana yin sanyi ina ganin kamar na tabka wani mugun abu mai cike da manyan manyan zunubbai....

Wata zuciyar tace min to miye? Domin ya rike hannunki kawai ai bai taba ba, kuma ya baki hakuri kasa ma natsuwa ya yi bayan ya koma gida sai da ya turomin apology texts barkatai...

Hakan yasa na yarda da cewa ba cikin son rai ya yi ba kuma ba da niyya ba ne.

Sai na yi masa uzuri na manta komai, washegari da safe na samu Abba a falonshi tare da Umma da Mama, bayan na gaishesu, na sadda kaina kasa nayi shiru har sai da Umma tace in fadi abunda ya kawoni suma magana suke da Abban, da kyar nayi masu maganar kudin da ya turamin na lefe...Abba ne ya fara saka albarka sannan Umma da Mama suka ce Allah ya yi albarka suma....


A makaranta muka had'u da Hafsat na gayamata abunda ya turamin kai ta girgiza kafin tace"Tabdijam ita kam wannan matar tasa tana ganin rawan jiki, gaskiya ta na da hakuri har naji ina so na ganta"

Cikin yar Dariya nace"Ina ruwana da ita sau daya ya taba hadamu a waya muka gaisa muna dai magana da su Aslam wani lokacin."

A ran Hafsat ta kuduri niyyar sai ta binciko wacece matar Alhaji Mustpha saboda ta wanke wani zargin da ta ke yi a kanshi..

Bansan yadda akayi kudin da Alhaji Mustpha ya turamin na lefe ya shiga kunnuwan dangi b, ni dai naji ana ta zuzuta abun ana fadin kamar za'a saida ni wai yana Kashemin kudi har da masu fad'in daman saboda kudi na ki dan'uwana, sun manta mahaifina na da kudi, haka cikin yayyaina, shi ma kuma Muhammad din ai ba daga baya ba tunda licensed bureau de changer ne, yana samun kudi sosai kuma ya mallaki manyan kudi, saboda yanzu dai a kasar nan suna cikin mutane da ke daria koda yaushe musamman yadda Dollar dasu pound stallion ke tashin gauron zabbi...ni dai na toshe kunnuwana saboda ba sa gabana. Anty Hadiza na tura ma duka kudin tace za'a yi kaya irin wanda ya ke so Tunda ya saki kudade.


Tun kuma daga ranar bai kara gigin taba ko da mayafin jikina ba, kuma sai da ya jima yana bani hakuri har na gaji da ban hakurinshi nace mai komai ya wuce nasan ba da niyya ya yi ba sannan ya bar jin kamar bai kyauta ba.

Tunda bani da wata kawa da ta wuce Hafsat dole ita na nema muka zauna da shi domin tsarin Shagulgulan Biki.

Da yaso a yi biki na nunawa a garin Katsina Abba ya hana Dinner kadai za'a yi sai Walima da Sister's Day da Bridal Shower sanin bani da wasu kawaye yasa muka sauya.

Sanda bikin ya rage saura sati hud'u har kudin gyaran jiki ya turamin, da kudin kayan da zan yi fitar biki da su.

Har mamakin irin kudin da ya ke kashemin na ke yi, amma kuma in nayi mgana sai ya nuna yaji haushi yana tutiyar ni matarsa ce zai iya bani duk abunda ya mallaka.


Hafsat kuma saboda nacinta sai da taje ta samo har Hoton matan sa da sunanta da labarinta.

Sunanta Hajiya Jamila, ba wata babba bace shekarunta na haihuwa basu wuce 35yrs fara ce doguwa ta na dan jiki kuma tana da kyanta daidai misali.

Amma kibar ne bata yi mata fasali ba.

Hafsat tace an gayamata yar kankia ce amma a katsina ta girma wajen kawunta.

A yadda aka fad'a mata a baya siririya ce yanzu ne jin dadi da kudi suka maidata haka dalilinta Musty ya kai duka iyayenta makka ita kanta taje aikin hajji sau 3, sannan Umra bata san iyaka ba....

Kuma yar kasuwa ce sosai ta na harka da kudad'e kuma a yadda ta samu labari matar bata da matsala tana da Kirki da kyakyawan mu'amala kuma mijinta baya mata mugunta mutum ne mai kyautatama iyalansa da ya'yansa.

Wannan labarin ya sakani farin cikin da baya misaltuwa, saboda ko babu komai hankalina ya kara kwanciya kuma na kara gane mutum ne wanda yake kyautata ma iyalanshi yana kashe masu kudi yadda ya kamata...hakan yasa na kara jin wutar son shi da son kasancewa mallakinshi..

 Hafsat kuma na turketa sai da ta gayamin dalilinta na binciko iyalan Mustynah.......



Duk wani abunda zanyi talla a cikin littafina na taba siye ne ko na taba amfani da shi...all what am saying is the truth and nothing but the truth...meaning that its tested and trusted by me.


*Online wholesale market* group ne na Jack of all trade master of none, tana saida komai ranging from kayan kitchen, kayan sawa, kayan decor and other stuffs...kamar yarda kuka ji sunan, tana saida kayanta ne a kudin wholesale, ma'ana kudin sari koda kuwa guda daya zaka siya...sai an gwada akan san na kwarai. Join her group and thank me later.


***


***