SADAKI

009

by @auntysis

SADAKI


AuntySis


009




Lokacin da Alhaji Mustapha yace gashi a haraban gidanmu ji nayi kamar zuciya ta zata fito waje saboda fargaba da tunanin da na kwana yi na mai yasa ya yi mun haka?

Jikina na rawa fuskata duk ta kumbura na rarumi gyalena na saka na fita duk kiran da Hafsat take faman yi min na inzo in gyara fuskata ban tsaya sauraranta ba babban burina kawai in ganni gabanshi ko Allah zai sa inji miye dalilinshi don in samu natsuwa, don idan nace jia na runtsa cikin jin dadi wallahi nayi karya...shi kanshi baccin a wahale na dinga yinshi guntu guntu mai cike da rashin dadi da fargaba....

Ina ga Hafsat din ce ta tsaya a falo tana yi ma su Umma bayanin Alhaji Mustapha ne yazo shine na fita da sauri.

Nan Aunty Hadiza tace Hafsat tabi bayana domin taji meke faruwa.

Haka ko akayi ina fita sai gata ta biyo ni da sauri.

Ni ko ganin gabana ba na yi sosai, Na dai san na hango Musty a jikin motarshi saboda damuwa ban tsaya ma duba kayan da ke jikinsa ba.....

Ina karisawa gabanshi naci burki ina mai kura mai ido shima ni ya ke kallo cikin wani yanayi kafin yace"My Love kuka kika yi ne?

Naga fuskarki ta kumbura ne? Takaici ne ya hanani magana saboda nasan ina bude baki zan iya sakin masa kukan da na keta rikewa a cikin zuciyata tun tashina yau....

Karisowan Hafsat ne ya ceceni cikin yar damuwa tace"kai kuma haka ake yi ehe? Kasan da labarin daga biki baka fadamana ba sai da muka ji mgana kamar daga sama sannan ta na ta kiran wayarka tun jiya a kashe shi ya daga mata hankali kaga idanuwanta sun kumbura tunda kuka ta kwana ta na yi.."Hafsat ta karisa fada a kufule...

Cikin irin kallonshi ya ke kallona sannan cikin karyewan sauti yace"Afuwan Sarauniyata nasan daman kina cikin damuwa shiyasa yau ina dawowa garin nazo, jiya kaduna na shiga kan matsalan wata kwangila ne sannan wayata ta fadi ta dauke shiyasa kika ji ni shuru amma don Allah ki yi hakuri Saurainiyata ba nufina na bata miki rai ba, balle har na saka ki kuka."

Hafsat ta sauke ajiyar zuciya ta na kallona kafin tace"To kin ji wayarshi ce ta fadi ta dauke hankalinki sai ya kwanta haka nan, kinbi duk kin damu kamar wadda akace ma Alhaji Mustaphan ya mutu." Wani irin kallo ya bi Hafsat dashi wanda shi kadai ya san ma'anarshi...

Ni dai maida kaina nayi ina jin yar natsuwa na shigata, sai da na samu yar salama amma har lokacin na kasa magana.

Hafsat ce ta kalleshi lokaci daya ta na fadin"Sai muka ji an daga biki kuma? Gashi mun gama duka shiri har kati mun raba sannan baki na nesa nesa ma sun fara isowa."

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Ba a son raina ba ne Hafsat bani da mafita ne abubuwan ne suka zo min lokaci daya suka ruguza tsarina."

Hafsat tace"Subhanallah me ya faru ne?

Cikin bayyanna Jimaminshi ya kalleni kafin yace"Maganar bata tsayuwa ba ce, shiyasa ma ki ka ga nazo saboda nasan na barku cikin zullumi."

Jin haka yasa nace mu karisa falon bakin Abba na waje.

Muna gaba yana bin mu a baya nan na barshi shi da Hafsat na koma cikin gida na dauko mai ruwa...amma duk da naji abunda ya fada ma Hafsat na kasa samun natsuwa saboda duk wanda ya kalleni da kyau a lokacin yasan cewa bani cikin walwalata...

Yaya Hauwa'u ce ta tareni tana tambayata me yace mana?

Muryata a dakushe nace bai mana bayani ba tukunnah.

Sai da ya sha ruwa ya natsa sannan ya kalleni cikin muryansa mai dadi ya kira sunana na amsa.

Ina kallonshi cikin kwantar da kai yace"Ki yi min afuwa nasan na bata abunda muka shirya sai dai ku sani muna namu ne Allah na nashi, kuma nashi tsarin shine daidai, ban taba tunanin ba za'a yi bikin mu a lokacin da na tsara ba, sai gashi komai ya rushe."

Kai na gyad'a kafin nace"me ya faru ne?

Cikin Jinjina kai yace'"Abubuwa da dama sun faru ciki har da rashin kudi daga bangarena, kwangilolina duk ba su fito ba, sannan na kwashe sauran kudaden hannuna gabadaya duk nayi hidima da shi, na dauka aikin gidan nan zan karisa shi kafin Bikin nan amma My Love wlh duk dubaruna sun kare sai na zauna na yi tunanin gwara a daga bikin nan zuwa gaba lokacin abubuwa sun warware min yadda komai zai tafi cikin kyakyawan tsarin da muka tsara Sarauniyata."

Ni dai na kasa magana saboda wani irin mugun tausayinshi na ke ji, ya yi kashe kashe kudi ashe shi ba shi da wani kudi a hannunshi.

Hafsah kuma fadi ta ke yi me yasa sai na zauna a wannan gidan? Ya kama min haya mana kafin ya karisa gidan.

Cikin Yanayin maganarshi yace"Na so na yi hakan sai kuma nayi tunanin in dai na kama mata haya ban kyauta mata ba tunda ga tsarin mu, gwara na bari sai na kamallah ginin gaba daya ni ba ma wannan ba, duka kudaden hannuna duk sun kare wanda ma zamuyi hidimar da muka tsara babu su shiyasa ma na karfafa zencen daga bikin, su kawu ma sun kawo maganar haya na dakatar da su ni kadai nasan halin da na ke ciki sai Madam tunda ita tasan komai nawa sai yanzu ku da na ke yi ma bayanin tunda ya kamata kusan abunda ke faruwa." Gaskia Hafsat idan na kama ma kawarki haya ban mata adalci ba saboda ba haka tsarinmu da ra'ayinmu yake ba...Amma dai ki sani duk inda zan nemo kudi zan nemo su don ayi hidimar nan yadda aka tsara...ki dauka lokacin ne kawai baiyi ba, kin san shi aure, haihuwa da mutuwa duk na Allah ne, kuma "kunn faa ya kuun ne" da Allah SWT yace su zamo, zasu zamo ba tare da bata lokaci ba..ina da yakinin daga auren nan alkhairi ne a garemu baki daya...


Ajiyar zuciya na sauke cikin wani yanayi kafin nace"Akwai kudaden da ka turamin ban yi amfani da shi ba, sai na tura maka ko?

Da sauri yace"A'a ai wannan naki ne, kada ki damu My Love abubuwa zasu warware ni dai fatana kada ki damu muna nan tare kuma zamu yi aurenmu da yardan Allah."

Hafsat tace Allah yasa... sun cigaba da tattaunawa kafin ta yi mana Sallama ta koma cikin gida bayan yace in ta shiga ta yi ma su Umma bayani.

Tana ko komawa ta zauna a falo ta kwashe yadda suka yi da Alhaji Mustapha ta fad'a musu.

Umma tace"Allah yasa haka shi ya fi zama alheri."

Aka amsa da Amin..Yaya Hauwa'u kuma fadi ta ke yi", Ni fa har yanzu dalilinsa bai gamsheni ba, bai zama dalilin mai karfin da za'a daga wannan auran ba"

Umma ta harareta kafin tace"Kada Allah yasa ki gani, in bazaki ce Allah yasa hakan ya zama alkhairi ba ki yi shiru da bakin ki kawai."

Jin haka yasa sai bata kara magana ba ita kanta Hafsat jikinta bai bata ba, tafi jin tausayin kawarta sama da kowa saboda wannan so na masifa da ta dauka ta dora ma mutumin da ita dai a zucci take ganin kamar akwai wata boyayyiyar rashin gaskia tattare da shi...


Ni ko a can falo Musty ya rika lallashina kukan da na ke ta rikewa na saki ina fadin"Naji tsoro ba na so na rasaka ne"

Cikin dadin maganarshi yace"waya ce miki zaki rasani? Har abada ina tare da ke Sarauniyar zuciyata" don't you know you are one of the best thing that ever happened to my life, I can't live without you Hibbatah...just know that you built a kingdom in my heart and you rule it...I wl 4eva love and cherish you queen of my heart..

Da irin kalamanshi ya samu ya lallasheni har na saki jikina muna ta hira da zai tafi yace na yi mai iso cikin gida zai shiga ya gaida su Umma.

Haka ko akayi na shiga na gaya musu suka kimtsa har falo ya shiga ya durkusa a kasa ya gaishe su.

Na nuna masa Yaya Hauwa'u da Yaya Hadeeza suma ya gaishe su cikin Ladabi.

Kamar yadda ya yi mana bayani suma haka ya yi musu.

Umma tace"Gaskiya ne, Komai lokaci ne kila lokacin ne bai yi ba shiyasa aka daga bikin muna fatan Allah yasa haka shi yafi zama alheri."

Mama da su Yaya Hauwa'u suka amsa da Ameen Ameen.

Da zai tafi Yaya Hadeeza tace bai tsaya yaga kaya ba.

Yace kaya nawa ne in dai na gani sun yi min shima sun yi masa saboda zabina shine nasa zabin....

Kayan da bai gani ba kenan har na rakasa wajen mota.

Muka yi sallama yace ya kai gyaran wayansa in an gyara zai kirani.

Ya tafi ina daga masa hannu nima yana dagamin zuciyata fesss tunda naji bayani daga bakin da bazai min karya ba.

Tun kuma daga lokacin na saki raina na cigaba da harkokina sam daga bikin bai dameni ba.

Hafsat sai yamma ta tafi, ita na barin da kiran mutane ta na gaya musu an daga bikin sai nan da wattani hudu.

Bansan a ina Muhammad yaji an daga biki ba kila daga gidan su ne aka gaya mai.

Tunda Mahaifiyarshi abokan wasa suke da su Abba.

Yana ta kirana ban dauka ba sai gashi ya Turomin wani banzan sako...


""Har yanzu kina da sauran dama Muhibba, ya kamata ki farka ki san cewa ni kadai ne mai sonki tsakani da Allah ko yanzu kika amince za'a iya daura mana aure gobe." The love I have for you bama gaskia bane ba, duk wani bugu da zuciyata zatayi dake takeyinta Hibbah....Don Allah ki taimaka mun, ina jin kamar zan mutu idan na rasaki""


Karamin tsaki naja na goge sakon tare da lambarshi gaba daya na kuma yi blocking dinshi domin bani da lokacinshi..Safwan tuni ya daina kirana ina ga shi ya dade da daukan dangana ne sai anace sarkin naci..


Tunda dangi suka samu labarin daga bikina magana ke yawo kananu har ana fadin daman auren kudi zan yi gashi nan ai ya fara raina mana hankali bashi da gaskiya dan yaudara ne, maganganu dai suna ta zuwa ni dai na toshe kunnuwana su Yaya Hauwa'u tunda ba maganar biki sun tattarra sun koma in da suka fi wayau....

Abba shima ya yi bakam duk wanda ya taresa da wata mgana sai yace Allah bai yi za'a yi a lokacin ba.

Umma ma haka take fadi Mama ce wani lokacin ta juye ta yi ta fad'a ta na jin kunyar yadda aka kunyata Abba shi kuma ya gayamata kada ta damu ba kan Muhibba aka fara daga biki ba, ballatana kuma ya zama abun magana.

Ko Yaya Al'amin da ya zo garin da zafinshi Abba ya taka masa burki shi da Yaya Ibrahim ya nuna musu miye a ciki? Ko daga bikin laifi ne ai ba laifi ba ne su yi fatan Allah ya sa hakan da akayi ya zama alkhairi shine fa suka kwantar da hankalinsu.

Yaya Faruq kuma ganin ni ban damu ba sai shima ya saki amma yana yawan gayamin Alhaji Mustpha ya yi musu wasa da tunani ni dai ba na magana sai murmishi tunda ina son shi bazan so a fadi wani aibunshi ba.


Wajen Sati biyu da daga bikin nan sai kuma maganar ta yi sanyi, ni ma na cigaba da harkokin gabana na koma makaranta na cigaba da karatuna, gefe daya Musty na kara kasheni da zazzafar soyayyarshi, a kaina ji yake kamar zai yi hauka ko nace kamar an kara masa soyayyata wani lokacin har cewa na ke ya kamata ya rage son da ya ke yi min saboda gaba, ya kan ce min ba shi ke da ikon sarrafa zuciyarshi ba da yana da iko da ita bai yarda ya saka kowa a ciki ba sai ni kadai.

Na kan yi dariya in yace min haka duk da deep down na san yana da mata harda yaya, so dole ko yaya ne yana son matarshi ko da kuwa auren dole aka masu tunda gashi harda zuria, amma dai abunda ya dameni ni shine kalar son da yake nuna min...duk da bashi da kudi abubuwa sun kulle masa bai bar yi min hidima ba.

Mama ta yi ta fadan ya cika almubazzaranci da wannan kashe kashen da kudin hidimar auran ya tara.


Ni dai ba na magana saboda Mama ta fara jin auran ya fita kanta kada na yi mgana na kara bata lamarin.

Yanzu bikin Yaya Faruq ne ke karatowa kuma shine a gabanmu muna ta faman shiri ankunan da muka yi na bikina sai akace a yi amfani da su a wajen bikin Yaya Faruq daga baya ni sai aka fito da wani in lokacin ya zo.

Haka ko akayi amma Yaya Faruq yace baya son bidia da kyar ya amince zai yi mana Dinner bayan an daura aure daddare mu kuma muka shirya Sister's Day anan gidan Abba.

Duk wani kudi da zan bukata Musty ke bani in ta mamakin yace ba shi da kudi na hidimar bikinmu, to a ina ya ke samun kudin da ya ke kashemin.

Na taba tambayarshi sai ya yi dariya kafin yace"Ko ba ni da kudi hidimarki ai dole na ce Sarauniyata Na biya Sadakin ki, ni mijinki ne a yanzu tunda waliyanki sun shaida ni ma nawa sun zama shaida kinga kina matsayin matata "

Ba na mamaki in naji Musty yace shi Mijina ne tunda ya fadamin haka tun lokacin da Sadakinshi ke gidammu.

Nima ban damu ba har a raina ina girmamashi ina mai kallon Mijin da zan aura tunda dai an gama komai shafa fatiha kawai ya rage, sadakin kanshi gaban shaidu ne da waliyaina da waliyanshi kamar yarda yake yawan gaya mun,tunda kuma wani abu na batanci bai taba giftawa tsakaninmu ba tun bayan rikemin hannun da ya taba yi kwanaki....

Ana shagalin bikin Yaya Faruq gidanmu ya cika da mutane duka iyalan su Yaya Al'ameen sun zo garin saboda wannan sha'anin. Ranar da aka daura aure akayi dinner na gayyaci Mustyna domin bani da wanda ya fishi a wannan lokacin.

Sai a lokacin muka had'u da Muhammad tunda Yaya Faruq abokinshi ne.

Bai min mgana ba, nima sai na yi kamar ban ganshi ba, Safwan dai ban ganshi ba kila bai samu zuwa ba ne, ban kuma damu ba tunda baya gabana.

Na dai sha magana da kallo ne a sha'anin kuma saboda haka na jere ni da Musty har cikin Hall sai kallo ya koma kanmu shima manyan kaya ya saka farare kamar wani ango.

Nima na sha ankon dinner dina wani leshi ne, mai kalan deep blue na yi kyau sosai tunda an yi min makeup.

Har wajen su Yaya Faruq na kaishi ya gaisa da shi tare da Amarya su Yaya Ibrahim ba su zo ba, daman kuma yaje daurin auren sun ganshi har sun gaisa...


In da Hafsat ke zaune muka je muka zauna muna ta hira har Yaya Aseeya tazo ta yi masa sannu da zuwa suka gaisa.

An ta shagalin biki, an kira ango da Amarya su fito fili mu kuma muka fita yi musu likin kudi Alhaji Mustapha ya cika min Jakata da kudi haka na ke ta barin yan dubu dubu ashe ban sani ba har da daloli ya sakamin sai gani kawai akayi ina likawa ni ban lura ba suna cikin kudi ne.

Sai waje ya dau ihu mai kid'a kuma ya kama sunana da Hafsat ta gaya mai fadi ya ke ga Hajiya Muhibba Sauraniyar zuciyar Alhaji Mustapha Safana an gaisheki.

Kunya ta kamani da wani irin soyayyar Musty a cikin zuciyata ina ta lalubanshi a hall din amma ban ganshi ba.

Ban ko gama likin ba na mika ma Yaya Aseeya Jakar na fito sai na ci karo da Muhammad ya sha gabana.

Na hade rai na raba ta gefensa zan wuce cikin Rad'a naji yana fadin"Ashe dai da gaske ne auran kudi Muhibba zata yi ana ta gayamin ban yarda ba sai yanzu da naga wanda zaki aura da kuma abunda kika yi yanzu a filin rawan nan."

Kallonshi nayi cikin mamaki shi kuma sai kawai ya shige cikin filin yana yi ma Yaya Faruq manni shima wai dollar ya ke likawa abunka da bureau de changer...



Tsaki naja na koma filin na karbi wayata hannun Hafsat na kira Musty ina tambayan yana ina?

Muryansa a shake ya amsa min yana parking space a cikin mota....

Ina kashe wayata na kama hanya zan fita daga wajen naji mai kida na yi ma Muhammad waka da kirari Muhammadu bawan Allah mai babban suna ga kudi ga dala ga kyau ga samartaka ni ban tsaya sauraranshi ba na fita da sauri saboda naji kamar muryan Mustyna ba yadda na saba jinta ba.

Ina fita na hangi motarsa sai dai motar tayi duhu ba haske....

Ina zuwa na kwankwansa glass din sai ya budemin na shiga na zauna ina fadin"Me ya faru naga ka fito kuma?

Ta hasken wajen ne da ke shigowa motar na ke hango fuskarsa.

Ya sauke kanshi saman kujeran da ya ke kamar akwai gajiya a jikinshi.

Cikin muryarshi da tayi kasa sosai yace"Na gaji ne, ina son naje gida na huta ne sauraniyata."

Cikin mamaki nace"To ba sai ka gayamin ba ai bazan hanaka zuwa gida ba, ka je kawai ka samu huta Madam sai ta kular min da kai kafin in zo."

Murmishi ya yi kafin yace"Madam bata nan taje Kankia suma suna da sha'ani gidan ba kowa sai ni kadai ina jin kadaici ne gwara na zauna dake ko na koma gida ni kadai zan zauna."

Ya karishe fad'a cikin yar shagwaba wadda take rikitani take gigita tunani na, duk yadda ake fadin shagwaba bata ma maza kyau, gaskia banda Mustynah don idan yana shagwaba ma dole ya tafi da imaninka....

Nima sai na narke masa kafin nace"To ka tashi mu koma cikin Hall din mana."

Sai kawai naga ya yamutsa fuska kafin yace"Bana jin dadin jikina mu zauna a mota kawai.".....