Page 06
by @mrsjmoon
ZUCIYAR REEMA
©Mrsjmoon.
ADABI WRITER'S ASSOCIATION.
Page 06
Dangartakansu da juna.
Umarul Faruq (Abbie) da Halimatus Sadiya (Ummie) uwa d'aya uba d'aya suke. Fulanin Gombe ne a wani gari mai suna Kaltingo, su biyu mahaifansu suka haifa, mahaifinsu Alhaji Abdurrahman dan boko ne wanda ya sami aiki a garin Abuja ya zauna da iyalinsa lokacin Umar yana matakin primary, Halima kam ko nursery bata shiga saboda tazararsu da juna mai yawa ne. Sun taso da k'aunar juna na ban mamaki wanda hakan ya faranta ran mahaifansu.
Nana Asma'u (Mommy) aminiya ce ga Halima wanda suka had'u a makarantar secondary, amincinsu ya yi k'arko har ta zamo mata ga yayanta wanda a rana d'aya aka d'aura masu aure inda Ummie aka kaita Kaduna gidan mijinta Dr. Habib.
Abdul Basit, Sagir, Nafisat, Ahlan and Aslam, 'ya'yan su Abbie da Momy ne. Sanaaya da Reema 'ya'yan Ummie ce wanda mahaifinsu ya rasu tun Reema na ciki 'yar wata huɗu, dalilin zamansu kenan da su Abbie har izuwa yanzu, an aurar da Sanaaya kimanin shekara ɗaya da rabi wanda bata sami rabon haihuwa ba har izuwa yanzu sannan mijinta ba mazauni ba ne shi ne, yana fita waye gudanar da harkan kasuwancinsa shi yasa take yawan zuwa gida idan ya yi tafiya dan kad'aici na damunta.
Saif kuwa ɗan yayan Momy ce da babansa ya rasu yana ɗan shekaru uku zamowar itama su biyu mahaifansu suka haifa sai ta d'aukoshi ta haɗa da ƴaƴanta ta raina ba tare da tsangwama ba.
Rashin sake auren Ummie kuwa ya samo a saline daga irin ƙaunar da takeyiwa Marigayin mijinta wanda da Abbie ya matsa mata da zancen auren sai ta sanar masa sai ta aurad da su Reema jin haka ya gano ba auren zatayi ba shi kuma saboda bai son ɓacin ranta ya sa bai matsa mata da zancenba domin shi ne tamkar uwa da Ubanta tunda sun rasa iyayensu tun tana da cikin Sanaaya, sakamakon annoban amai da gudawa da ya kamasu a lokacin da sukaje mahaifarsu ziyara. A yanzu shekaru ashirin da huɗu da 'yan watanni kenan da rasuwar mijinta Dr. Habib Adam Jama'a. Sanadin gobara da ta kama motar dake ciki wanda Allah ne kad'ai masanin afkuwan lamarin. Cikin Reema yardan Allah ne ya sa ya zauna Amma tayi zuban jini wanda sai a lokacin aka gano tana da shiga ciki, Abbie ne ya d'auketa zuwa Babban asibiti da ke garin Abuja ya sa aka d'aure mahaifan tunda zuban jinin bai lalata cikin ba. Tunda wannan lokaci take zaune da su tare da yayanta cikin kwanciyar hankali.
Ita da Mommy suke gudanar da kasuwancinsu wanda Allah yayi masa albarka ta ko wani fanni nasara suke kan gani, yan bani na iya kam sunyi sun gaji saboda sun hana masu k'ofan shigo da gulma a tskaaninsu.
Abdul Basit, Likitan k'ashi ne kuma ɗan kasuwa amma yafi bawa kasuwancin muhimmanci, bai cika shiga Asabiti ba sai in an nemeshi ya yi aiki domin ya k'ware akan aikinsa, kawai ra'ayin zama a Asibiti ne kullum bai da shi, ya mallaki k'addarori masu yawa wanda idan bai zarta mahaifinsa dukiya ba to zasu zo kunnin doki, ya samu wannnan nasarar ne sakamakon aikin da ya yi a ƙasar Germany na wasu shekaru kafin ya dawo gida Nigeria cike da tarin nasarori.
Saif Lowyer ne wanda ke aiki a high court, Shima yana da rufin asiri daidai misali, Sagir kuwa aiki ya ke a Company nin su Reema a matsayin babban ma'aikaci, Sanaaya kam bata da ra'ayin yin aiki, ta ce komi ta nema ta samu dan haka bautar aure zatayi tare da bawa yayanta lokacinta, Reema da Nafi ne ke shirin soma aiki a Kamfanin da Sagir ya ke. Inda Reema ke burin amsar mikamin C E O dama Aminin Abdul Basit ne ke rik'e da shi, abinda Sagir ke k'ulafucin ya amsa da jimawa amma Abdul Basit ya hana.
Wannan shi ne dangartakan jama'an gidan a tak'aice.
***
Hannun Reema bai daina zub da jini ba duk kuwa dubarar da tayi masa akan ya tsaya, lamarin har ya soma bata tsoro sai ta sakko k'asa ba kowa a Falon ta fice zuwa sashin Abdul Basit ta buɗe da key d'in da ya bata ta shiga ta d'auko first-aid box ta zauna tayi dressing wurin tana runtse ido, ta ɓalli maganin rage zugi ta sha ta fito idanunta jajur ta nufi garden ta kwanta a ciyawa, sam bata tsoron wani k'waro mai cutarwa ya silalo ya cijeta. Har saida aka kira sallar Azuhur sannan ta bar wurin zuwa ciki. Momy ta samu a Falon sai ta saita kanta daga damuwa zuwa walwala amma duk da haka bata tsira da tuhumar momy ba domin tana sunkuyawa dan gaisheta ta hana mata yin hakan ta hanyar d'ago fuskanta tana cewa "Me ke damunki?"
"Babu komi."
"Amma idanunki suka sanja launi."
"Abu ne ya faɗamin cikinsu, kuma kinsan ba lafiya ne da su ba."
Shiru ta yi tana nazarinta zuwa can ta shafi fuskanta ta ce "Sannu Daughter, Allah ya ƙara tsarewa."
"Amin, Nagode Momy."
"Tafi kiyi sallah ki zo ki tayani kwance Jaka."
Ta motsa kai tare da mik'ewa ta haye sama, Momy ta raka bayanta da kallo tana doka murmushi.
"Sagir ya yi dacen mata mai tarin nagarta ta ko wani fanni, Allah ya ja da raina naga d'iyoyinku."
"Amin ya Rabbil Alamin."
Ummie ta ambata cike da farin ciki sadda ta iso ta zauna a kujerar sa ke kallon Mommy.
"Ummien Reema ina ganin tunda mundawo me zai hana a tsaida lokacin bakin kawai ayi a wuce wurin?"
"Nazarina kenan har ina cewa a saka sati biyu ko uku masu zuwa tunda yau Juma'a ya zamo saura kwanaki goma shabiyar kenan ko Ashirin da biyu."
"Wannan nazarin ya yi sai nace Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya, anjima zan sanar da Abdul Basit ya sanya a buga Invitation kafin lokaci ya k'ure."
Abbie ya amshe sadda ya fito zai tafi masallaci.
"Au Yaya ina yarona ya tafi har yanzu banji motsinsa ba?"
"Ya yi muku laifi amma na hannun damansa zata labarta muku, na wuce masjid daga can zan lek'a Alhaji Abdul Shakur baiji dad'i ba kuma idan kun huce gajiya sai kuyi haranar duba shi."
"Allah ya bashi lafiya."
Suka ambata a tare, ya amsa da Amin ya fice da hanzari.
"Ummien yara Yaron nan nada hankali kuwa?"
.
"Wakenan?"
"Ɗan ki Abdul mana."
"To me ya yi kuma?"
"Tafiya inda ya so ba tare da jiran dawowarmu ba saboda gashi ishash-she."
"Relax Momyn Nafi, kinfi kowa sanin waye Abdul Basit akan aiki da hankalin da Allah ya hore masa, na tabbata babban Uziri ne ya taso masa har ya tafi ba tare da jiran dawowar namu ba."
"Uhm ai dama baya laifi a wurinki mantawa nayi."
"Ba haka bane gaskiya ne dai ba kyason ji."
"To naji yanzu shi kenan?"
"Da saura, sai kiyi masa fatan alkhairi gami da dawowa cikin k'oshin lafiya."
"To Allah ya bashi nasara akan abinda ya je nema gami da dawo mana da shi cikin kwanciyar hankali."
"Amin ya Rabbil Alamin."
Muryan Reema ya ratso kunnuwansu, Suka zuba mata ido ta sakko ta zauna gefen Ummie tare da dafa guiwarta tana mai cewa "Ya ce a baku hak'uri ya san bai kyauta."
" Baiyi laifin komi ba Reema, Allah ya taimakeshi akan abinda ya tafi nema."
"Amin Ummiena."
Ita dai Momy murmusawa take tayi tana motsa kai cike da jin daɗin ƙaunar da suke nunawa jininta.
"Kinyi sallah kuwa Daughter."
"Ina hutu ne."
"Ok to taho muje mu kwance Jakan ki zaɓa abinda kike so ki darje kada Hajiya Ummie ta rigani baki "
Mik'ewa tayi tana kallon Ummie wacce ke latsa waya tana murmushi.
"Ki zaɓa dana Masoyinki."
Sagir ya ambata hannayensa hard'e a k'irji na jifanta da kallon zaki sani amma ga masu kallonsa ba abinda suka hasko sai zallar ƙauna.
"Ummiena yaronki baida kunya ki yi masa nasiha ya daina rashin ta ido a gaban manya."
"Yo ai layi ɗaya kuke a soma yi miki faɗan kafin a zo kanshi."
"Yawwa sanar mata dai Special Aunty."
Tura baki tayi, Momy ta ja hannunta suka haye sama inda ɗayan bedroom d'inta ya ke tana yi mata magana a hankali tana gyaɗa kai cikin fitar siririn dariya, daf da zasu k'ule ta waigo suka haɗa ido da Sagir ta watsa mara harara tare da motsa baki kalman Mugu ya fito daga saman lips d'inta, motsa kai ya yi na cije gefen baki zuciyarsa na sake yi masu zafi, ji yake tamkar yanzu ne ta zabga masa marin da ya ɗauke masa ji na wucin gadi.
***
Rayuwarsu ya cigaba da tafiya cikin salon da suka barwa zukatansu sani domin tunda suka fahimci Saif ya maida hankali kan takonsu sai suka iya takon fiye dana baya, sannan duk yarda Sagir ya ci alwashin kama Reema dan ya hukuntata akan marin da tayi masa abin ya ci tura domin Momy da Ummie suna tsakani dan ako da yaushe tana tare da su hatta kwana ta dainayi a d'akinta ta dawo d'akin Ummie inda take aiki yi masu gyaran jiki ita da Nafi saboda an tsaida ayi bikin nasu tare da juna kamar yarda masoyan suka nuna. A haka kwanakin bikin ke gabatowa hankalin Reema na sake tashi wanda hakan ya kasa b'oyuwa a jiki da fuskanta har saida Ummie ta tsareta da tambayar me ke damunta amma ba ta sami gamsas-shiyar amsa ba, a kan dole ta rabu da ita ta maida hankali wurin yi masu addu'ar samun zaman lafiya tare da zuri'a d'ayyiba sai dai lamarin damuwar da 'yar nata ke ciki na damun ruhinta kuma tana mamakin abinda Reema ta b'oye a zuciyarta har takasa sanar da ita. Ganin itama damuwa zai hanata sukuni sai ta mai da shi gafe amma ta dage akan kome ke damun 'yarta Allah ya kawo mata mafita.
***
Kwanaki uku ya rage d'aurin aure dan haka a ranar gidan ya soma amsar baƙi daga dangin su Abbie, Momy da dangin mahaifin su Reema duk da bawani alaƙa mai ƙarfi ke tsakaninsu ba dan sun nuna amsar dukiyar ƴaƴan ɗan uwansu dan su juya masu Ummie ta hana inda ta nuna itama zata iya juyawa sai suka ɗauki gaba da ita tare da yanke alaƙa da su amma a gefen Ummie bata rikesu da komi ba dan tana tura su Reema zumunci da su inda sukeyin kwanaki biyu zuwa uku su dawo duk da ba wani kulawa suke samu ba sai wurin mutun ɗaya wacce take k'anwar mahaifiyar Abbansu.
Shi yasa zuwansu da yawa ya bawa Ummie mamaki bata ƙara shiga mamaki ba sai da suka sanar mata da Yayan mahaifin su Reema na nan tafe wato Alhaji Bashar domin ya ce shi zai bada aurenta, sai kawai ta barsu tare da su Sanaaya ta haye sama dak'in Reema ta kulle ta fashe da kuka wanda kuka ne na farin ciki saboda a bikin Sanaaya ba wanda ya zo cikin iyayensu maza ko matanma k'anwar kakannsu ce Hajiya Mairo da babban 'yarta Hajiya Asiya suka zo tare sa abin arzikinsu.
"Ya Allah kasa sanadin k'ulla dank'on zumuncinsu da ababen adonsu ne ya zo."
Ta ambata tana mai jin natsuwa a ruhinta wanda ta ke hango lokacin yin aurenta ya zo ko ta samu damar komawa ga mahaccinta cikin cikar sutura.
Reema ce ta banko k'ofar idanunta cike da hawaye mai nuni da tarin damuwar da take ciki, ta faɗa saman gado ta fashe da kuka mai sauti tana cewa "Ya zanyi da raina ni Khareematu?."
Sai ta ƙara sautin kukanta wanda ke fita daga tsokar naman zuciyarta. Ta jima tanayi sannan tayi shiru tana jan ajiyar zuciya, ta dafe kanta da ke ciwo, tana jin tamkar ta dauki wuk'a ta je ta sokawa Sagir ya mutu a fasa auren baki ɗaya.
Ummie da ke zaune saman sallaya ta zabga tagumi tana nazarin firucinta ganin zata wahalar da kanta wurin samo fashin baƙinsa sai ta mik'e ta dawo gefen gadon ta kai hannu saman goshin Reema, ta ko zabura tana salati ganin Ummie ce sai ta saki murmushi cikin ƙoƙarin kauda damuwan da take ciki, ta riƙe hannun tana cewa "Ummiena dama kina cikin dak'in shalelenki?"
"Kada ki wahalar da kanki Reema, maza sanar da ni damuwarki domin baki da wacce ta fini duniya da lahira in aka cire 'yar uwarki Sanaaya."
Shiru tayi tana nazarin me zatace domin ba zata iya sanar da ita karatun ruhinta ba akan jinin ɗan uwanta mafi soyuwa gareta.
"Ina sauraren ki Khareematu?"
"Ummie kema kuka kikayi kenan?"
"Eh amma nawa na farin ciki ne saɓanin naki da ke nuni da kina cikin k'unci."
"Ba haka bane Ummie kawai damuwata yarda zan daina ganinki kullum ga shi ban saba zama ni kaɗai ba idan Yaya ya tafi Office, shi ne fa ya kaini ga ambaton kalamin da ya zanyi da rayuwata."
Tsira mata ido Ummie tayi tana wasi-wasin aminta da zancenta sai dai tunowa da tayi Reema batayi mata ƙarya saita murmusa wanda ganin hakan yasa Reeman sakin b'oyayyiyar a jiyar zuciya tare da fad'awa jikin Ummie ta sake fashewa da kuka.
"Is ok Khareematu, aure wani yanki ne na bautar Allah Subbahanahu wa Ta'alah dake sada dubban mata zuwa gidan Aljannah dan haka ki daina damuwa kowa da haka ya fara har yaji zaman gidan miji ya fi masa zaman ko wani gida daɗi sannan ki ɗauka tamkar nunatare da juna ne dan ko bamuga idanun juna ba zamu riƙa gaisawa a waya balle na tabbata kika cewa Yaron kirki Sagir kina son zuwa garemu zai kawo ki ko ya baki dama ki zo da kanki haka maganar zaman kaɗaici ai ba mai yawa zakiyi ba tunda da Sagir ya gama hutun da ya ɗauka kema zaki soma fita aiki kuna dawowa tare kinga wannan ma ba abin tada hankali ba ne, dan Allah ki cire damuwarnan da kike ciki wanda ke sanyaki rama, kalleki kigani fa duk kinyi k'ashin wuya, baha Aminiyar Ummiena, ki kwantar da hankalinki ki dawo 'yar dumama- duma ɗin ki ko nima nawa hankalin ya kwanta na daina ramewa sanadin ganin naki."
Takai ƙarshen maganar cikin rarrashi cike da raha. Murmusawa Reema tayi tare da sake lafewa ta amsa da "To Ummie na daina d'aga hankalina amma dai ina buƙatar addu'arki."
"Wannan kingama samunsa Shalele."
Gyaɗa kai tayi tare da tashi zaune ta riƙe hannayen Ummie gam tana mai cewa "Ummiena a ko wani hali kika riskeni dan Allah kada ki juyamin baya, na rok'eki wannan alfarman kuma kiyimin alk'awarin fahimtana gami da bani kwarin guiwa ko da kowa zai juyamin baya to ki zamo ke ɗin kina tare da ni ruwa da iska."