Chapter 3
Tana zuwa motar saura mutum biyu ta cika da yake golf ce. Don haka ta zauna jiran cikon mutum daya.
Sai lokacin ta ciro wayarta a jaka ta kira Mama wadda ta daga nan take.
Tace mata, "Mama a mana addu'a, gani nan a hanyar Kano!"
Mama tace, "Kano kuma da wannan yammacin Nadiya? Anya? Ga dare yayi kuma ga yanayin hanya da wannan rashin tsaro da muke fama?"
Tayi dan murmushi, "babu abinda zai faru in shaa Allah Mama. Ni dai kawai kiyi mun addu'a!"
Mama tace, "to Allah Ya kiyaye hanya Nadiya, Allah Ya saukeku lafiya. Kin fadawa Abbanku dai ko?"
Nan da nan sai fara'ar fuskarta ta dauke. Tace, "in kira shi in ce mishi me? Na tabbata dai babu wani fatan alkhairi da zai mun, kila ma sai dai ya min fatan inyi hatsari a hanya in mutu tunda dama ba yau ya saba hakan ba!"
Mama tace, "duk da haka, mahaifinki ne ai. Kuma idan kinyi hakan hakkinshi kika fitar. Ki daure ki kirashi din!"
Tayi dan jim, kafin ta gyada kai kamar Maman tana gabanta, tace, "to shikenan, zan kira shi din in shaa Allah."
Mama tace, "yauwa Nadiya haka ake so. Ki gaishe da Jamilar idan kin je."
Tace, "zata ji in shaa Allah."
Nan suka yi sallama.
Lambar Anty Jamila ta kira, sai dai har tayi ringing sau biyu ta gama ba a daga ba. Sai ta kira lambar diyarta Rabi'ah.
Tana shiga ta daga kamar wadda take jira. Ta fara magana cike da azarbabi, "Mommy Nadiya ina yini?"
Tayi yar dariya, "kai Rabi'ah, Allah Ya shiryeki wallahi. Ina sallamar to?"
Sai itama tayi yar dariya cike da alamun jin kunya, tace, "Assalamu alaikum wa rahmatullah"
Ta amsa, "wa alaikumussalam wa rahmatullah. Ina Mommynki ne, ina ta kiran wayar tata amma bata dagawa?"
Tace, "aikuwa yanzu babu jimawa suka fita ita da Daddy. Ina tunanin ko wayar tana jaka ne ko kuma ta barta a gida."
Tace, "ok, to idan ta dawo da wuri ki fada mata ina kan hanya. Don kada ta tarar da missed call ta kira kuma yanayin network bata sameni ba."
Rabi'ah tayi tsallen murna ta dire, "da gaske? Allah kiyaye Mommy sai kin iso! Ki kawo min tsaraba fa!!"
Yadda taji tana murna da dokin zuwanta sai taji itama murnar ta kamata, tace, "to shikenan Rabi'ah, zan kawo miki in shaa Allahu!"
Suna gama wayar aka samu fasinja. Nan da nan aka rufe mota direba ya dauki hanyar fita daga Kaduna.
Sai da suka fita a tashar sannan ta lalubo lambar Abbansu ta tura mishi sakon ita dai ta tafi Kano gidan Anty Jamila. Sai dai har suka fita daga Kaduna suka dauki hanyar Zariya bata ga ya maida mata da amsar sakon ba. Don haka ta kada kanta gefe guda ta jinginar da gilashi tana kallon gari.
Karfe takwas da rabi suna cikin Kano, amma bata karasa gidan Anty Jamila dake can cikin Nasarawa GRA ba sai wajen karfe goma saboda yanayin abin hawa.
Mai napep ya tsaya a gaban tangamemen gate din gidan nasu. Bakin gate ne mai gida-gida sai wasu adon furanni da aka yi a jiki masu kalar zaiba. Kai daga gani ba sai ka tsaya tambaya ba kasan cewa ya ci kudi ba kadan ba.
Ta sallami mai abin hawar kafin ta karasa jikin gate ta kwankwasa, mai gadi ya leka yana tambayar waye? Daya ganta sai ya koma ya bude mata yana mai yi mata sannu da zuwa. Ta amsa mishi a matukar gajiye.
Motocin data gani a cikin gareji ya tabbatar mata da cewa su Antyn sun dawo. Ta raba ta gefen garejin ta bi ta gefen madaidaicin lambu da kuma wajen shan iska na gidan, ta shiga falon farko na gidan.
Babban falone sosai. An sanya kujeru manya-manya na leather sai babban center table, rabin bangon dakin wata katuwar plasma ce yayinda rabin kuma show glass ce mai girma da fadi da aka zuba abubuwan ado na tangaran da gilashi a ciki. Dim lights masu kyau suna ta sheki a ciki suna kara kawatata. Falon an fi amfani dashi saboda manyan bakin Daddy, amma su ma mutan gidan su kan fita su sha iska a wasu lokutan.
Tana bin wata kofa sai gata a tsakar gidan. Dakuna ne a jejjere daga kowacce kusurwa, Yayinda sauran tsakiyar gidan kuma aka shuka wata bishiya babba wadda ta bude daga sama ta saki rassai duk sai ta lullube gidan. All in all dai, gidan Anty Jamila gida ne wanda tsarinshi yayi matukar burge Nadiya. Domin gidane da daga gani kwalwa da dukiya suka jajirce wajen ganin an samar dashi. Kuma yanayin tsarin yana nuna rayuwa ta wayewa da kuma sanin darajar kai, ba irin ta gidansu ba.
Bangaren yaran gidan daban yake, duk da cewa dai a waje daya suke, amma kuma kowa bangarenshi daban yake.
Kana shiga daga bangarenka na dama, nan ne dakin yara mata yake. Idan kuma ka mike straight, nan zai kaika turakar mai gidan. Bangaren hagu kuma wanda ya dan shiga ciki nan ne bangaren maza.
Kai tsaye dakinsu Rabi'ah ta wuce. Tayi knocking kafin ta tura kofar dakin ta shiga. Dakin nasu yana da fadi matuka. Gadaje uku ne a dakin, guda biyu wadanda suka kasance bunk, a hade, suna daga jikin bangon kofar dakin, sai dayan kuma daya kasance single a daya bangon. Daya bangon kuma gabadayanshi wardrobe ce ta jikin bango, sai daya gefen da aka zuba desks na karatu, kowanne makale da laptop dinshi da sauran essentials, sai kuma karamar tv da aka manna. A tsakiyar dakin kuma an shimfida kafet mai taushi an zuba tuntu da wasu abin zama da hutawa masu kyau.
Rabi'ar tana zaune akan desk dinta tana rubuce-rubuce lokacin data shiga. Tana daga kai ta ganta, tayi tsalle ta wancakalar da abubuwan hannunta ta nufeta a sukwane tana ihun murna. Murmushi tayi itama ta rungumeta, nan suka hau juyi a tsakiyar dakin har dai suka dangane da gado suka zube a kai.
Sai data gama murnar tata sannan ta saketa, ta zauna a gefen gadon tana kallonta, "wai! Gaskiya sannunki da zuwa Anty, ya hanya?"
Tace, "hanya Alhamdulillahi, gamu mun iso ai!"
Rabi'ah tace, "sannu da hanya to. Mommy tace idan kin iso a miki sannu da zuwa zaku hadu da safe saboda tuni suka shige turaka ita da Daddy!"
Dan murmushi ta saki a tausashe, sanin halin Anty Jamilar sarai da yadda bata hada harkokin mijinta da komi yasa bata ji komi ba, sai kai data daga, tace, "to Allah Ya kaimu goben lafiya. A gajiye nake ai dama, ruwa kawai zan watsa in kwanta."
Tace, "to ki shiga kiyi, ga kayan barci da Mommy ta shigo miki dasu."
Tayi godiya tare da amsar kayan ta fita daga dakin ta fada toilet da yake fuskantar dakin. Shower stall ta shiga ta saki ruwa mai dumi a jikinta sosai, ta jima a ciki kafin ta fita tana jin yadda jikinta ya fara saki, gajiyar itama ta fara barinta.
Ta tsaya gaban karamar mirror dake makale a bandakin tana goge jikinta da tawul. Data gama ta dauki spray na CC mai sanyin kamshi ta fesa a jikinta kafin ta fasa ledar kayan ta sanya, dogayen riguna ne guda biyu na barci a ciki. Dayar bata da tsayi sosai da kadan ta sauka gwiwarta, kuma hannunta siriri ne haka kuma bata da nauyi. Dayar kuwa doguwa ce har kasa kuma tana da dan kauri haka hannunta dogo ne, tana da madauri a jiki kamar bath robe. Ganin su kadai ne a dakin kuma yanayine na zafi, sai bata dora ta saman ba, ta barta.
Tana komawa daki ta tarar har Rabi'ah ta baza mata kayan abinci duk da dai marassa nauyi ne. Dambun cous-cous ne da yaji hadin kayan lambu sai kuma yankakkun kayan marmari da madarar hollandia yoghurt ta strawberry. Ta zauna tana ci suna taba hira da Rabi'ah, gajiyar tafiya yasa ta kasa cin abincin da kyau sai fruits din data sha sosai, ta kuma sha yoghurt din. Data gama sai ta rufe komi, Rabi'ah ta wuce ta kai kayan kicin ita kuma sai ta koma bayi ta wanke bakinta ta dawo daki ta kwanta. Rabi'ah tana sama ita kuma tana na kasa, ta kira Mama ta shaida mata sun sauka lafiya, ta hadata dasu Maryam suka mata sannu da hanya kafin su yi sallama.
Daga nan ta yada kai akan filo babu jimawa barci yayi awon gaba da ita. Ba ita ta farka ba sai da alarm ya tashesu sallar Asubahi. Bayan sun yi sallar, suka yi azkar, sake komawa suka yi suka kwanta abinsu.
Karfe tara da rabi ta farka. Jikinta ya saki sosai, babu kuma gajiya a tattare da ita sai rashin karfin jiki da kasala.
Ta sauka daga kan gadon ta fita tare da shiga toilet, baki ta wanke kawai. Ta bi dogon corridor din gidan ta shiga kicin. Ko'ina na gidan a gyare yake tas-tas, babu hayaniya wadda ta sanya mata natsuwa. Tana son rashin hayaniya da tsafta ita kam.
Yunwa take ji sosai, kuma ita ta tasheta. Ta fara bude-buden fridge da cupboards tana neman wani abu da zata fara dashi kafin ta yi abin kari, saboda tasan mutanen gidan zasu iya kaiwa sha daya ma basu tashi ba. Tasan kuma abu mai dan nauyi zasu bukata.
Freezer ta bude ta ciro kaza guda, ta fara wanketa ta dora akan wuta bayan ta yanka wadatacciyar albasa ta zuba kayan kamshi.
Sai ta dama quicker oats ta hada ta sha kafin kazar ta gama dahuwa.
Ta fara fito da abubuwan da zata bukata tana warewa. Kafin kace me, ta hargitsa gidan da tattausan kamshin girki mai dadi.
Dage-dagen kaza tayi da kayan lambu, sai ta soya kwai, ta yi toasting din biredi, sai shayi mai kamshi data hada. Ta riga ta gama sanin tsarin gidan, don haka tana gamawa ta samu flask da warmers ta zubawa Anty Jamila nata da na mai gidan, ta debar musu ita da Rabi'ah, sauran kuma ta ajiyesu a wani mazubin na daban. Duk mai so daga cikin mazan gidan wadanda kannen maigidan ne dake karatu a BUK, sai yazo ya dauka duk da cewa bata ji motsin kowa ba yau.
Tana cikin wanke-wanke Anty Jamila ta shiga kicin din. Doguwar macece mai dan jiki, baka ce amma kuma kalar fatarta mai kyau ce da sheki saboda tana bata kulawar data dace. Saye take da doguwar rigar barci cotton, sai ta dora hijabi karama a sama wadda ta tsaya mata a kugu, kafarta saye da takalmin silifas mai taushi.
Nadiya ta juya tana kallonta lokacin data shiga kicin din, fuskarta dauke da murmushi. Durkusawa tayi tana gaidata, Anty Jamila ta jata jikinta tana dariya, "ai tunda naji gida ya karade da kamshi nace lallai Nadiya ta dira gidana!"
Dariya ta sake a tausashe, tace, "haba dai Anty! Ke ma fa bangaren girkinnan ba daga nan ba. Ni ai nawa sharar fage ne!"
Anty Jamila tace, "ba wani nan. Ke kanki ai kin san kafin a kamo kafarki a bangaren girki, za a jima gaskiya!"
Murmushi ta sake yi tana girgiza kai kawai.
Tray din data shirya musu kaya da maigidanta ta nuna mata, tace, "ga abin karinku na hada muku, Rabi'ah bata tashi ba shi yasa bata kai muku ba!"
Saboda ita bata shiga bangaren Maigidan. Bakin iyakarta dashi idan sun hadu a falo ta gaisheshi, ko kuma tayi dakonshi da safe idan tana kicin tana aikin girki.
Anty tace, "da kyau Nadiyata! Wallahi kamar kin san ina kewar girkinki dama. Bari idan Daddy ya fita, zamu shiga kasuwa anjima muyi siyayyar spices don gashin kazar nan da kike mana da kuma local mac-D dinki nake son ci."
Tayi murmushi tana gyada kai, "to shikenan Anty, Allah Ya kaimu!"
Anty ta dauki farantin ta fita, ita kuma ta cigaba da aikinta.
Data gama ta dauki nasu abincin ta kai daki. Sai lokacin Rabi'ah ta tashi, ta shiga bayi. Kafin ta fito har Nadiya ta gyara dakin, ta hada musu shayi. Suka zauna suna kari. Mama ta kira suka gaisa, ta hadata dasu Rabi'ah suka gaisa, kafin hira ta kacame musu ita da su Maryam. Nan ta barsu suna ta yi, ta kwashe kayan abincin nasu ta kai kicin.
Dakin ta koma ta fara tsifar kanta saboda ya fara datti, a gida kuma bata cika samun lokacin yin tsifar ba. Tana jin sanda Rabi'ah ta kashe wayar tazo tana tayata itama. Tana son irin gashin Nadiya wanda ya kasance baki, sassalaka kuma mai tsayi sosai. Ba kamar irin nata ba wanda yake mai tauri sosai duk da cewa itama ba laifi tana da tsayin gashin da kuma baki.
Bayan nan dakin Anty Jamila suka je suka gyara mata, daga nan suka shiga dakin mazan gidan don su gyara. 'Ya'yan Anty Jamila hudu, danta na farko Auwal da suke cewa Yaya, shekarunshi sha bakwai, yana Sudan wajen Yayan Babansu, sai Rabi'ah yar kimanin shekaru sha biyar, sai mai bi mata Abubakar Sadeeq shekarunshi goma, dai autanta Haroun, suna ce mishi Haneep, shekarunshi biyar.
Da yake tana da abokiyar zama, wani lokacin yaran su kan je gidanta suyi weekend ko hutu, ko kuma ita nata yaran guda uku su zo nan gidan nata. Da alama wannan satin suna can.
Da rana ta mulmula musu tuwon semovita da miyar yauki, suka ci suka yi nak kafin Anty ta daukesu a motarta suka fita. Shagon saloon dinta dake nan cikin Nasarawa gra din suka fara tsayawa, aka wankewa Nadiya kai aka kuma yi mata kalba saboda ta fi sonta akan kitso. Daga nan suka shiga kasuwa ta taya Antyn hado kayan kamshi na abinci saboda a cewar Antyn ta ma fi son hadin spices din Nadiya akan ta siya na kanti.
Sai yamma likis suka koma gida.
Da dare tayi musu gashin nama mai ruwa, ta hada musu da taliyar indomie noodles wadda tayi steaming dinta sai ta soyata a cikin kwai sama-sama bayan ta wadatata da kayan lambu da taruhu daya sa tayi dan yaji-yaji.
Bayan sun gama cin abincin sun jima suna hira a falon Anty. Sai wajen karfe goma saura kafin suka yi mata sai da safe. A dakin ma koda suka gama shirin barci, wata sabuwar hirar suka dasa. Bata ma san lokacin da barci ya kwasheta ba sai can wajen karfe hudu ta farka. Da taga alamun barcin ba daukarta zai yi ba, sai kawai tayi alwala ta fara nafila.
Da aka yi Asubahi ta tashi Rabi'ah itama tayi, sannan ta sake komawa barci.
Ranar ita da Rabi'ah suka hada abin kari. Lokaci yana ta karatowa, don a yadda ta saba, ana yin Azuhur take yin haramar tafiya gida yadda zata isa da wuri. Ji ta dinga yi dama kada ta koma. Idan ta tuno irin tsarabe-tsaraben dake jiranta sai taji inama... inama. Inama ba zata koma wannan gidan ba.
Da zata tafi Anty ta hadata da tsaraba mai yawa. Ta dauki dubu goma ta bata tayi kudin mota, dubu goma ta kaiwa Mama, dubu ashirin kuma ta kaiwa Abbansu. Ta mata godiya sosai da sosai.
Har tasha suka kaita ita da Rabi'ah. Sai da suka tabbatar ta samu mota kafin suka yi sallama da ita cike da shauki. Babu jimawa mota ta tashi suka dauki hanya.