NADIYA

Chapter 5

by @jeddahlawals

Kwanaki biyu da yin haka, amma har an gama gyaran dakin da amarya zata tare fenti kadai ya rage. A cikin satin kuma aka daura musu aure. Saboda daurewa karya wani gu, Abbansu har Kamu ya hadawa amaryar tashi. Can aka tsinto bidiyo din yadda ya dinga barin kudin liki a wajen kamun a wajen yan ba-ni-na-iya din yan unguwarsu.

Don kuwa har gida suka yi sallama suka kaiwa matan. Mama data gani baki ta tabe tace 'Allah Ya kyauta.' Nadiya ma haka. 


Don kuwa abin ya girmame mata. A ranar da safe ya gama tijara da ihun ba shi da kudin da zai biyawa yaran gidan na makarantar boko da islamiya. 'Amma da yake amarya ce, ita ai gata can yana mata barin kudi da na jiki a banza.'

Irin maganganun da taji su Lantana sun hade kawuna a kofar kicin suna ta furtawa kenan cike da bacin rai. Lokacin kuwa taje wucewa zata fita waje da safiyar Alhamis, tayi dan murmushi, tace, "a dai juri zuwa rafi, saboda watarana tulun zai fashe!"


Salame ta zaburo mata, "ke karamar yar iska! Allah dai Yasa ba dani kike ba don naji me kike cewa sarai!!"

Tayi banza ta kyaleta ta kara gaba abinta tana dariyar mugunta. 

Yadda taga maganar bikin ta gigitasu gabadaya abin dariya yake bata. Ko kuwa dai don Abban ya jima bai yi auren bane shi yasa suka fara mantawa har suka saki jiki suna tunanin ko shikenan? Ta tare abin hawa ta tafi wajen aikinta abinta.


A shago ta tarar da Aramide. Tayi mamakin hakan saboda ranar aiki ce, koda zata je bata cika zuwa da safe ba sai can yamma idan ta tashi daga aikin. Kuma mafi yawanci ta kan je ne kawai don ta karbi wasu abubuwan ko kuma kudi idan bata da su a hannu. 


Ta shiga dakin da take canji ta rataya Apron a saman doguwar rigar jikinta. 

Yadda taga dakin a hargitse ya tabbatar mata da cewa lallai Aramide anan ta kwana. Tayi tsaye cikin mamaki tana kallon Aramide din da tayi zaune akan arm chair, sai lokacin ta kula da yadda tayi wani jugum-jugum kamar wadda aka yiwa mutuwa. Gefen fuskarta daya yana can gefe guda ta ki yarda su hada ido da Nadiya. 


Ta taka ta matsa gabanta cikin nuna alamun damuwa, tace, "Ara, me yake damunki ne wai? Lafiya?"

Kai kawai ta iya girgiza mata bata ce komi ba. Ganin haka sai ta dafa kafadarta tare da juyota ta kalleta, ai bata san lokacin data ja da baya ba hannu dafe da kirji tana zare ido a kidime. Gefen fuskarta ya hau yayi wani irin kumburi, idonta a rufe yake ma ruf da kyar take iya daga shi. 

Tace, "innalillahi wa Inna ilaihi raji'un! Aramide me ya sameki ne haka? Waye yayi miki haka?"


Dama mai neman kuka ne aka jefeshi da dunkulen kashin awaki, tana jin haka sai kawai ta dargwaje da kuka. Tayi-tayi har ya isheta, Nadiya ta kasa ce mata komi sai ban baki da kokarin tausarta da kalamai masu dadi. Zuwa lokacin data gama kukan, fuskarta ta gama baci da hawaye da majina. Ta dauki tissue tana goge fuskarta tare da fyace majina. 

Cikin murya data gama dusashewa da kuka take cewa Nadiya, "wallahi na gaji da wannan cin kashin da ake yi min Nadiya, na gaji! It's either in kai mutum kara ko kuma in kai kararshi wajen iyayenshi!"


Nadiya sai tayi sakato! tana kallonta cike da daurewar kai, tace, "wa ke nan? Ba dai maigidanki ba ko?"

Ta jefa mata harara cike da kulewa, "idan ba shi ba ta ya kike tunanin zan bari wani gardin yayi min wannan danyen aiki?"

Ta daga kafada tana dan tabe baki, "na sani?!"


Tayi kwafa tare da yin tsaki, "ban taba fadawa kowa halin da nake ciki ba har iyayena kuwa. Amma yanzu tura ta kai bango, na gama gajiya. Nadiya mutum ya mayar da ni kamar jakka, abu da wanda ya kai da wanda bai kai ba kawai sai kiga mutum wai ya hau ni da bugu babu gaira babu dalili? Ina dannewa ne ina cijewa saboda bana so a ga kamar na cika korafi ne, kuma bani da isasshiyar shaida saboda sau tari yana yin bugun nashi ne a inda mutane ba zasu gani ba balle a zargeshi da wani abu. Amma wallahi yau ya tsokanowa kanshi! Ke wallahi kotu kawai zan maka dan iska fakat babu wani jan dogon zance!"


Nadiya dai ta baza kunne tana sauraronta, ranta rabi cike da tausayi rabi kuwa dariya ce take tuketa tana dannewa. 

Tace mata, "ba haka ya kamata ayi ba saboda komi na duniyar nan fa da kike gani dan hakuri ne. Idan kika kaishi kara yanzu saboda kina cikin fushi, kuma nan gaba kuka shirya to da wane ido zaki kalleshi da yan'uwanshi?"


Tace, "ai dama tsakanina dashi kotu zata shiga ba wani abu ba, don wallahi ba zan zauna ya nakastani a banza ba! Wai ma kinsan ko saboda me yayi min wannan mahangurbar?"

Nadiya ta girgiza kai.

Tace, "kawai saboda ya tambayeni ina links din hannun rigarshi nace ya duba cikin kayanshi. Kawai sai ji nayi ya kai min naushi a gefen ido! Ya kuma hau ni da jibga kamar wata jakar gidansu! Wai na raina mishi wayo saboda yana min magana ina maida mishi amsa gatsar babu ladabi! Nadiya mutum ga gori, ga shi da dan karen rashin mutunci. Duk wasu abokaina ya rabani da su saboda rashin mutuncin da yake musu idan sun zo inda nake. Yanzu abin ya tashi a kansu ya koma kan yan'uwana da dangina. Shikenan ranar nan har jaka yace min saboda na cinye malmalar amala hudu a gabanshi!..."


Nadiya kuwa me zata yi ba dariya ba. Ta dinga kyakyatawa har tana tuntsurawa. 

Aramide ta tsaya tana kallonta cike da takaici. Sai da taga bata da alamun dakatawa sannan ta dada mata duka a cinya, tace, "baki da kirki wallahi Nadiya. Wato ma maimakon ki tausaya min shine zaki sanyani a gaba kina min dariya ko?"


Ta kai hannu tana goge hawayen da suka cika mata ido saboda dariya. Tace, "abin naku ne ai gwanin ban dariya. Kinga nan gaba sai ki dinga ba mutane shawara, a dinga hurawa kafin a ciza!"

Sai tayi turus tana kallonta. Ta yada kai gefe guda, tace, "ashe maganar nan ba zata taba wucewa a wajenki ba?"


Nadiya tayi saurin girgiza kai, "a'ah wallahi, ke kin fi kowa sanin cewa tuni data gama wucewa a wajena, kawai dai wata magana da kika taba fada min ne na tuna shine ta bani dariya..."


Sun hadu da Aramide a ABU Zaria, Division of Agriculture (DAG) inda duk suke karantar Home Economics. Itama Aramide haifaffiyar Kaduna ce amma iyayenta dukansu yarbawa ne, aiki ne ya kaisu Kaduna. Idan kaji Hausa a wajenta kuwa yadda kasan jakar Kano. Tasu tazo daya sosai da Nadiya, suka kulla kawance sosai. 

A shekararsu ta karshe dai suka koma cikin ABU da zama sai suka hada suka kama gida off-campus. 


A shekarar ne Allah Ya hada Nadiya da wani saurayi AbdulGaniyyu, shima Yoruba ne amma mahaifiyarshi bahaushiya ce. Yana da iliminshi babu laifi kuma yana aiki a Kaduna a hukumar NNPC. Babban mutum ne ba laifi, don ya ba shekaru talatin baya amma bai taba aure ba. 

Yana da yawan hidima sosai, ga kyauta. Don kuwa kullum tafe yake da abubuwa iri-iri, kayan makulashe da tande-tande, kayan kawa da ado, har waya yaso ya canza mata a lokacin amma ta ki saboda ita har ga Allah bata da kudirin aurenshi saboda sam-sam bata jin auren nashi a cikin ranta ko kadan. 


Bata san ya aka yi ba, ko cikakken watanni hudu basu yi da haduwa ba don har ya fara zancen idan suka je gida hutu wannan karon zai tura gidansu a tambayi aurenta. Kawai sai taga mutum ya janye mata rana daya. Sai ga Aramide ta fara fantamawa iyaka son ranta, tayi sabon saurayin dake mata hidima yana mata kashe-kashen kudi. Tun tana jin wai-wai a gari har dai ta gansu da idanunta, ya dai tabbata lallai Aramide ta mata snatching din saurayi. Tace umma ta gaida aysha don kuwa dama bata cikin yan kayan. Ta zuba mata ido tayi ta boye-boyenta, daga baya dai da kanta taje tana mata kame-kamen zance, wai wallahi kai tsaye gidansu ya aika yace yana sonta kuma iyayenta suka amsa da sun yarda shi yasa ita kuma bata zauna yin musu da su ba saboda ba zata iya bijire musu ba duk da tasan cewa hakan bai dace ba. 


Nadiya dariya tayi sosai a lokacin, tace mata kada ta damu don kuwa ita har ga Allah abin bai dameta ba don dama bata sa a ka ba. Ta kuma yi musu fatan alkhairi, tace in dai namiji ne taje gashi ga ta nan. 

Daga haka basu kara tada maganar ba. Suna gama makaranta kuma aka daura musu aure. Nadiya tayi musu kara sosai wajen halartar bikin da hidimtawa sosai a matsayinta na babbar kawa. Shima kuma AbdulGaniyyu din har aka yi aka gama bai taba nuna mata wani abu ba ko a fuska, don haka itama bata taba nuna mishi wani abun ba.


Biki aka yi gagarumi, irin nairar da aka barar abin sai ya baka mamaki. Amarya ta tare a gidanta dake Korau road, ita dai Nadiya tun washegari da suka koma suka kammala gyara mata gida, bata kara waiwayarsu ba. 


Tare suka shiga camp da Aramide, da Allah Yasa itama tayi marriage certificate sai aka barta anan Kaduna. 

Bayan sunyi service dinsu, Aramide din ta bata shawarar mai zai hana su kama hayar wajen da zasu bude shago na kayan ciye-ciye? Tunda ita Aramide din ta samu aiki a kamfanin Indomie, sai ya zamana Nadiya din tana kula musu da wajen? Aka yi haka kuwa, cikin dan kankanin lokaci an samu waje an gyara shi, aka bude wajen inda kwastomomi suka fara tururuwa. Jajircewar Nadiya da sadaukarwarta ya kai wajen matsayin da yake dashi a halin yanzu, don kuwa ita kanta Aramide din ta san da hakan. 

Daga farko ita Aramide din cewa tayi mijinta ne yayi mata kyautar kudade masu yawa shi yasa ta yanke shawarar ta bude wajen. Sai da tafiya tayi tafiya daga baya dai Nadiya ta fahimci kwata-kwata zancen ba haka yake ba. Iyayen Aramide din su suka bata kudin wanda ya kasance na sadakinta ne da kuma wasu kudade da iyayen suka saba ba 'ya'yansu mata idan sun yi aure domin su ja jari. 


Ita dai Nadiya hakan bai dameta ba, tunda ko babu komi tana jifar tsuntsu biyu ne da dutse daya. 

Na farko tana gudanar da abinda tafi so a duniya, wato girke-girke, na biyu kuma ana biyanta da kudaden dake daukar nauyin dawainiyarta. Don haka bata da wata damuwa sam. 


Ta muskuta ta gyara zama tana fuskantar Ara dake shan shayi da cupcakes a lokacin. Tace, "me zai hana ku zauna ke da shi kuyi magana ta fahimta? Idan yaso sai ku ajiye ground rules (dokoki) da watakila zasu iya taimaka muku wajen rage yawan dukan. Saboda gaskiya baya da dadi ko kadan."


Ta girgiza kai, "kina tunanin bamu yi hakan bane tun farko? Lokacin farko dana tunkareshi ma da wannan maganar ai wani dukan ma na janyowa kaina. Wallahi wani mari daya falla min sai da naga taurari suna min yawo a idanuna!"

Nadiya ta jinjina kai cike da jimami, tace, "gaskiya dai yakamata ku canza taku, saboda hakan ba zai haifar muku da da mai ido ba. Nan gaba idan kuka fara tara iyali fa kuma mai zai faru? It's either ya dinga hadawa har diyan yana jibga, ko kuma su yaran suna ganin abinda ke faruwa su fara raina shi da tuhumarshi. Kinga hakan duk ba abu bane mai dadi gaskiya."


Tace, "nima hakan nayi tunani shi yasa kawai zan wuce wajen iyayenshi in fada musu abinda yake faruwa, watakila su zasu iya bullowa lamarin da mafita. Don kuwa kin san idan naje na fadawa iyayena abinda ke faruwa ba zasu taba tsayawa su kwatar min yancina ba kila ma sai dai su hada da min Allah kara. Don tun lokacin da yaje neman aurena sai da suka bani shawarar kada in aureshi don sun riga da sun yi min miji, amma na kafe akan sai shi. Yafi dai kawai inje in samu iyayen nashi."

Nan ma Nadiya dariya ta so ta saki jin yadda kalamanta suka saba da cewar data yi iyayenta suka matsa akan sai ta aureshi.


Iyayen AbdulGaniyyu mutanen Benue ne. Shi ya tashine a hannun kawunshi dake zaune a Kaduna wanda Allah Ya yiwa rasuwa jim kadan bayan AbdulGaniyyu din ya tafi jami'a. Shi kuma sai yaci gaba da zama anan har Allah Ya taimakeshi ya samu aiki. 


Nadiya tace, "to Allah dai Ya. kyauta! Yaushe zaki tafi?"

Tace, "ai a yau ba sai gobe ba zan dauki hanya in Allah Ya yarda. Ni zan koma gidan wannan mutumin ya sabautani? So nake karshen satin nan a rufe shagon ma, ku tafi hutu ko da na sati biyu ne tunda dama bamu yi na shekara ba har yanzu. Nima hutun zan nema, saboda so nake idan naje in dan jima a can, wallahi garin ya fita a kaina gabadaya!"


Nadiya ta dan jinjina kai, "to shikenan, sai ayi hakan babu damuwa. Muma mun samu mu huta kafin ki dawo din. Dama na tara barci da gajiya sosai kwanakinnan."


Fita tayi suka cigaba da gudanar da ayyukansu kamar kullum. Bayan abubuwan sun lafa, suka fara shirye-shiryen rufe shagon da shawarwarin yadda hakan zai kasance. Sun saba yin hakan dama a duk karshen shekara, to kuma wannan shekarar data wuce ayyukan suka cunkushe musu basu yi hutun ba gashi har sun ci kwata. Nan da wata daya cikakke ma Azumi suke tunkara. 


Saboda shirye-shiryen ranar bata koma gida da wuri ba sai wajen karfe tara na dare. Tayi sallama tana jan kafa saboda tsananin gajiya. Abbansu yana tsakar gida, matan sun zagayeshi zaune akan tabarma. Ko kwanukan abinci da aka kai mishi ba a kwashe ba. Ana ta hirar da bata da kai balle kafafu. Da alama ma su biyu kadai ke hirar, don shi hankalinshi yana kan wayarshi yana ta latsawa. A ranta tace 'har an gama fadan da fushin sake auren kenan?'


Ta durkusa a gefensu tana mishi sannu da gida, ya daga kai yana kallonta, "ke kuma fa daga ina da wannan daren? Wai ba na hanaku kai dare a waje ba?"


Tace, "wallahi ayyuka ne suka tsaremu a shagon saboda muna shirye-shiryen tafiya hutun shekara ne."

Yace, "to, to, na gane. Ai nayi zaton yawon banza kika tsaya. Ni dai kullum ina fada muku, a dinga kiyaye yin dare a waje. Saboda mutane basu cika ganin mutuncin mace mai yawace-yawace da kai dare a waje ba."

Ta gyada kai, "hakane Abba. In Allah Ya yarda zan kiyaye!"

Ta tashi ta tafi daki. 


Ta tarar su Maryam har sun mata shimfida. Don haka tana gama shirin barci kwanciyarta tayi.