NADIYA

Chapter 6

by @jeddahlawals

Ranar Litinin bata tashi da wuri ba, da tayi sallar Asubahi komawa tayi tayi kwanciyarta. Cikin ikon Allah kuma hayaniyar yara bata dameta ba don sai wajen karfe tara da rabi ta tashi. Maryam zata raka wajen registration din Jamb dalilin da yasa ta tashi da wuri kenan. Saboda daren jiya bata kwanta da wuri ba. Ta rasa dalilin da yasa yan kwanakin barci yake gagararta sosai musamman na dare. 


Maryam ta shiga dakin dai-dai lokacin da take kokarin nade kayan shimfidar tata. Tace, "yauwa Adda, kin tashi? Dama ke kadai nake jira saboda tun dazu na gama shirina."

Ta gyada kai, "ok! Bani mintuna talatin, yanzunnan zan shirya. Abba yana gida ko ya fita?"

Tace, "yana nan. Naji yana cewa Lantana yau sai bayan Azzuhur ma zai fita saboda yana da meeting da ko wani Sanata ne ko me?!"

Nadiya ta tabe baki. Ta hade kan kayan ta mikasu daki kafin ta shiga wanka.


Cikin mintuna talatin din da tace kuwa ta gama shirinta tsaf. Riga da siket ta sanya na wani leshi ruwan madara, bata daura dankwali ba sai gashin kanta data kame a cikin band babba, ta dora bakar hijabi wadda ta tsaya mata a gwiwa. Kamar kullum ba wata kwalliya tayi ba ta a zo a gani, amma tayi wani irin kyau mai daukar hankali. 


Suka fita tsakar gida inda ta samu Mama tana gyaran masara saboda ranar ita take da girki. Su Lantana kuwa da alama suna dakin Abba don bata ga giccinsu ba. 

Suka mata sallama akan zasu tafi. Dubu biyu ta kunto a habar zaninta ta ba Nadiya wai su kara kudin mota, tace, "a'ah wallahi Mama, ki bar kudinki saboda da isassun kudi a hannuna. Ki ajiye kayanki kinyi wata hidimar dasu."

Mama tace, "to Allah Yayi albarka Nadiya, Allah Ya amfana!" 

Tayi murmushi tace, "ameen ameen Mama! Mu ai addu'ar muke so!"


Sun samu Abba zaune akan kujera da takardar kilishi a gabanshi yana ta tauna, su kuma iyalan nashi suna gefe sun hade kawuna suna kus-kus. Salame sai kaiwa takardar naman hari take da idanu tana hadiyar yawu amma ya ki bata fuskar tagawa ma balle ta rokeshi.

Nadiya ta danne dariyar da take ciyota, da alama yau Abban cikin yan rowar yake. 


Ta durkusa ta gaisheshi ya amsa mata sama-sama. Da yake itama ranar izgilanci take ji, sai ta juya gefen su Salame su ma ta gaishesu, sai dai daga jin gaisuwar bata kai ciki ba, suma haka suka amsa mata kadaran-kadahan babu yabo babu fallasa. Ko a kwalar rigarta ita kam. 

Ta juya tana kallon Abban nasu, tace, "Abba zamu je ne wajen registration din jamb ta Maryam."


Jin haka sai yayi kicin-kicin da rai ya fara hura hanci kamar wanda aka aikawa da sakon mutuwa, "to! Sai kun dawo ko?"

Ta wani langwabar da kai gefe guda, "wai dama cewa nayi ka bamu kudin registration din ko? Dubu shida ne da dari uku, ga kuma kudin abin hawa..."


Kafin ma ta karasa ya katseta, "... ke dakata min don Allah da wannan lissafe-lissafen naki! Kudin kin bani ajiyarsu ne? Ko kuwa ni din asusunki ne da zaki dirar min da zancen kudi kai tsaye in dauka in bada! Ce miki aka yi sharo kudin nake yi a kasa ne ko kuwa shukasu nake yi?!"


Tace, "amma fa Abba tun wancan satin fa na fada maka haka kuma kai kace Allah Ya kaimu!"

Jin haka sai ta kara tunzurashi ma, ya fara sakar mata lissafin kudaden daya kashe a wannan satin wadanda rabinsu duk wajen amarya suka nufa, sai kuwa kudin fadar kishiya daya ba matan wanda dukansu dubu goma-goma ce ya basu. 

Ita dai tayi kasa da kai tana bashi hakuri. Daga karshe dai ya tashi ya shiga daki, ya dawo ya jefa mata yan dubu-dubu guda uku suka zube akan cinyarta, "gasu nan kuyi maneji da wannan. Idan kuma bai zasu isheku ba to ku bani kayana, tunda ba neman kai nake dasu ba!"


Ta tsincesu tas ta zuba a jaka tana mishi godiya. Ta yunkura zata tashi kuma sai ta koma ta zauna, ya daga kai yana kallonta warily don yasan maganar bata gama mutuwa ba. 

Murmushi ta dan yi, tace, "Abba nace wai ka dan bani kilishin mana in kore mugun yawu!"

Tsabar rasa abinda zai ce mata da yayi a lokacin, takardar naman ya cukuikuye gabadaya ya mika mata, duk da cewa saura yajin kilishin kawai da dan guntun nama, haka ta amsa tana zabga mishi godiya, ta fita tana dariyar mugunta a ciki ita kadai. 


Maryam ta girgiza kai tana kallonta, "wallahi wani lokacin ba ki da dama ko kadan Adda! Kin rabashi da nama kuma kin rabashi da yan canjinshi!"

Tayi dariya tace, "ke raba mugu da makami ibada fa! Idan ba ta haka ba ta yaya ma wai ake cin kudin Abba ne?!"

A haka kuma sai ta jinjina kai, "hakane kuma!"


Kai tsaye KASU suka wuce. Bayan an gama duk cike-ciken da za ayi, aka basu slip dinsu. Daga nan sai suka gangara unguwar Rimi gidan Yayansu Yaya Hannafi, mahaifiyarshi bata gidan kuma shima kusan sa'an su Anty Jamila ne. 

Matarshi tana da kirki Anty Aisha, yana da rufin asirinshi dai-dai gwargwardo. Yana aikine da wani kamfanin kera robobi da reshensu yake nan Kadunar. 

Anan suka yini a gidan. Da yake Nadiya ta iya jera lallen salatif, ta jerawa Anty Aisha shi kafa da hannu, Maryam kuma ta tayata tsifar kai. Da suka tashi tafiya ma da yamma ita ta hana tace dole su jira Magriba Nadiya ta sha ruwa tunda Azumi take yi, watakila kuma kafin nan Yayan nasu har ya dawo su samu su gaisa. 


Don haka suka shiga kicin har ita suka hada abincin dare. Ta samu kunun tsamiya ta dama, don ya zame mata ka'ida, matukar tana Azumi dolene ta dama kunu ko ta hada shayi. 

Suna cikin shan ruwan kuma sai ga Yaya Hannafi din ya dawo, yaransu uku, kuma dukansu sun tasa. Yanmata biyu suna boarding school sai karamin ne Ammar yake nan. 


Ya tsaya suka gaisa suka mishi sannu da zuwa. Hira suka dan yi dashi sama-sama kafin ya tashi ya shige dakinshi. Dama can dai shi ba mai yawan jan yan'uwanshi a jiki bane, tunda zumuncinma da ba don jajircewar matarshi ba to da ba lallai ayi shi ba. 

Da zasu tafi ya basu dubu biyu su yi kudin mota suka mishi godiya sosai kafin suka dauki hanya. 


Suna gab da karasawa gida taji wayarta tana vibrating a jaka. Duk a tsammaninta Mama ce take nemansu shi yasa bata daga wayar ba. 

Suna komawa gida kuma sallah suka yi, suka zauna cin abincin da Mama ta ajiye musu suna mata hirar Anty Aisha. 


Sai da tayi shirin kwanciya can wajen karfe goma da rabi sannan ta tuna wayarta dake cikin jaka. Ta bude ta ciro wayar tana so ta hau whatsapp ta tabo Aramide taji ya ake ciki. Sai lokacin taga missed call din da aka bar mata. 

Jikinta ne ya dauki wani irin sanyi ganin sunan mai kiran. Madam Zarah! 


Mahaifiya ce, amma tafi jinta a matsayin wata dangi ta nesa, wadda babu sanayya da kusanci a tsakaninsu ko na azo a gani. 

Kiran wayarta ba wai yana nufin tana so taji muryarta ko ta tanbayi ya take bane, tana da tabbacin ko dai wani abu ne ya taso a cikin dangi, ko kuma tana bukatar tayi mata wani abu ne. Tana da tabbacin hakan. 


Canki-canka take yi, akan ta mayar mata da kiran ko kuwa. Laifine dai ta riga da tayi shi. Don kuwa idan akwai abin da Madam Zarah ta tsana, bai wuce ta kira wayar mutum ya ki dagawa ba. 

A matsayinta na mace mai influence a cikin Kasarnan, gani take yi ba karamin nasara bane a gareka idan ta dauki wayarta ta kira ka ba, a ganinta ka ciri tuta sosai. Bata duba da cewa 'ya'ya da iyaye da yan'uwa bai kamata su shiga cikin wannan tsarin ba. 


Ganin tunane-tunane ba inda zai kaita yasa ta mayar mata da kiran. Amma har ta katse ba a daga ba. Dama tayi tunanin haka. 

Ta daga kafada ta gyara kwanciyarta abinta ta fara addu'ar barci. 


Washegari kuma tunda safe sai ga kiran nata. Ta gyara zama akan abin sallar da take kai zaune ta daga baki dauke da sallama, kafin gaisuwa ta biyo baya, "Assalamu alaikum. Mommy barka da safiya, kun tashi lafiya?"

Daga can bangaren aka amsa mata a gaggauce, babu ya kike babu ya kwana biyu, kawai kai tsaye zuwa dalilin da yasa ta kirata. 


Tace, "Nadiya kin tuna Hadiza yar wajen Kawu Kabir ko?"

Tace, "ehh, na tuna ta."

Duk kuwa da cewa ba tunata tayi din ba. Dangin Mamanta ba wani sani ta musu na azo a gani ba sai na kusa dasu sosai. 


Tace, "satin wannan da zai kama za a fara bikinta a can Maiduguri. Don haka ki shirya kije sai mu hadu da ke a can. Zan turo miki Invitation card, at least kije a day before a fara events saboda a fara dake. Kin gane?"

Tace, "ehh... Amma Mommy....!"


"...Ba ki da kudin zuwa ne?" Ta katseta da wannan tambayar. 

Tace, "a'ah, dama..."

Nan ma bata bari ta karasa maganar ba tace, "yauwa, to sai na turo miki da katin. Sofia tace a gaida ki!"

Ta katse wayar ba tare data bari Nadiya ta kara cewa wani abu ba. Tayi zaune da waya a hannunta tana kallo kamar wata sakara. 

Shikenan duk wani tsari da tayi na hutun da zata yi an wargaza mata shi cikin dan kankanin lokaci. 


Ita fa ba zuwa bikin bane yafi damunta, shiga cikin dangin Madam Zarah ne bata so. Ba a cikinsu ta tashi ba, shi yasa bata saba dasu ba. Akwai wadanda suke magana dasu suna gaisawa ta waya, amma suma yan'uwan Madam dinne na kurkusa wadanda yawanci daga 'ya'yan yayunta, sai ko na kannen mahaifanta dai. Amma sauran ba saninsu tayi ba, suma kuma basu santa ba. 

Tana so ta sansu din, amma ta yaya? Da yawa wasu daga cikinsu kallon hadarin kaji suke mata idan taje wajensu, ta rasa dalili. Ko gani suke yi bara da roko zata je wajensu? 


Dangin Mahaifiyarta mutanene da suka hada masu arziki da kuma masu rufin asiri. Suna zaunene a garin Maiduguri. 

Mahaifiyarta rabi shuwa ce rabi bare-bari, iyayenta suna da rufin asirinsu dai-dai wa dai-da. 

A cikin yan dakinsu akwai masu kudi sosai, su dai sune suka kasance masu rufin asiri. Watakila ko shine dalilin da yasa ma iyayenta suka yarda ta auri Babansu Nadiya din. Ko kuwa kaddara ce da tsananin rabo? Allah kadai Ya sani. 

Tana da masaniyar a danginsu idan kaga wani ya auri bare wanda ba Kanuri ko Shuwa ba, to kudi yake dasu ba kanana ba. Saboda su sun fi yin auren gida ya-su ya-su kawai. Idan kuma sun fita to dukiya suka gani. 


Shi yasa fa ita sam tsarin mutanen bai mata ba ko kadan. Shi yasa bata cika shige musu ba take baya-baya dasu. 


Ta san dai cewa shi Alhaji Kabir mai aurar da diyar tashi, kawun mahaifiyarta ne. Dan wa da dan kani suke da kakarta, Dada Iyani, wadda itace Mahaifiyar Madam Zarah da sauran yayunta biyu, Hauwau da kuma Yasir. Wadanda dukansu suna zaunene a can Maiduguri din banda Madam Zarah, wadda take zaune a Jos. 


Ajiyar numfashi ta ajiye mai nauyi, rufe wayar tayi tare da tashi ta nade abin sallar. Ta tashi taje ta gaishe da Abbansu, ta koma daki suka gaisa da Mama. Kafin ta fita tsakar gida ta fara shara. 

Mama ta fito ita kuma ta shiga kicin ta fara kokarin hada abin kari. 


Kosai suka yi shirin yi da koko. Da yake waken an gyara shi tun jiya, sai aka ba almajiri ya tafi markade. 

Kafin ya dawo Nadiya ta gama hada kan tsakar gidan, Mama kuma har ta dama koko. Ta shiga kicin din ta zauna tana tayata suyar kosan suna hiransu kamar dai wasu manyan abokai. 


Yaran gidan da suka fara fitowa don shirin tafiya makaranta, nan da nan suka kara wartsakewa. Murna kamar su yi me, don kuwa su ranar take sallah a wajensu. 


Kowa idan ya zo zai amshi abin karinshi, sai Mama ta kulla mishi wani a cikin leda wanda zai tafi makaranta dashi. Abu ne da bai cika faruwa a gidan ba sai a dai-daikun ranaku wadanda suka zama na girkinta kawai. Don shi dai Abbansu baya bada kudin kashewa ko cin abinci a makaranta. Wanda Mahaifiyarshi taga zata iya sai ta bashi, amma ba dai shi ba. Su kuwa da mugunta ta cikawa ciki da shegen mako, babu mai iya wannan aikin. Shi yasa ma yaran duk basu cika mayar da hankali kan zuwa makarantar ba. 

Lokaci zuwa lokaci dai Nadiya ta kan basu na kashewa a hanya, amma itama ba kullum ba. 


Su Salame suka fito daga dakinsu suka je kofar dakin Abba suka coge suna ta harare-harare da yada maganganu. Nadiya dai kai kawai take girgizawa cikin tu'ajjibin wadannan mutane. Daga tashi tun da farar safiya kawai ku dinga neman mutane da fada? Ina dalili. 


Da suka kai kwanukansu Mama ta zuba musu nasu, sai da suka kara kokarin tada rigima. Wai su ala dole ta zuba musu kadan, me zasu yi dashi? 

Mama ta nuna musu nata itama wanda bai ma kai nasu ba, tace, "ni kunga ma wanda na tashi dashi. Idan kuma kuna ganin ba zaku amsa ba sai ku dawo dashi ai, dama nema muke yi."


Lantana taja wani dogon tsaki ta juya ta shige dakin Abba tana maganganu kasa-kasa, Salame ta bi bayanta itama. 

Nadiya ta bisu da kallo kawai, kafin ta jinjina kai tana mai furta 'Allah kyauta!' a cikin ranta. 


Bayan Aminatu ta tafi makaranta, ita da Maryam suka zauna suka yi wanke-wanke suka gyara madafin, sannan suka je suma suka karya.