IYALAINA

1

by @sadiyanasir


  Tunda suka fito daga cikin gidan babu wanda ya iya furta koda kalma daya wa ɗan uwansa sa, a haka har suka iso jikin motor, jiki a matukar sanyaye Alhaji Goni ya buɗe murfin Motor tare da Alama wa Jidde Akan ta shige. tamkar wacce Kwai ya fashe wa a ciki haka ta shige ciki, cikin yanayin damuwa ya shiga yaja Motar suka bar harabar gidan, ganin shurun yayi yawa A motor yasa Alhaji Goni kunna Karatun Qur'ani. Hakan ya cigaba da sharan gudu A hanya yana satar kallon Jidde.


Jidde kuwa karatun Qur'anin dake tashi A motor ya  fara ratsa zuciyar ta sannann ya sauƙar mata da nutsuwa. Hawaye masu zafi ne suke bin kuncinta alokaci guda suka wanke mata fuska, tuno irin zafafan Kamalan da Hajja ta yaɓa mata, duk Abinda take yi idanun Alhaji Goni yana kanta, a haka har suka ƙarasa gidan su dake Airport road.


 Hassan Mai gadi yana hango Motar Alhaji daga nesa yayi hanzari yazo ya buɗe Gate, kai tsaye suka danna hancin motar cikin gidan. parking-lot suka nufa anan ya ajiye motar da kanshi ya fito ya buɗe wa Jidde kofa ta fito, murmushin ƙarfin hali ta mishi suka sanya kai suka shiga Babban Palon gidan da yasha kayan Alatu na Alfarma.


Kokarin zama yayi A ɗaya daga cikin kujerun palon yaga Jidde tasa kai zata hau sama, da hanzari ya jawo hanunta ta faɗo ƙirjin sa, kallon ban fahimceka ba tayi mishi, kauda Kai gefe yayi ya kama hanunta suka dawo Kujera suka zauna, hanunsa na makale cikin nata ya fara magana da sassanyar murya "Da farko dai kiyi haƙuri kinji? Na sanki da haƙuri kuma ina alfahri da hakan, kuma insha Allah za kiga ribar hakurin, Umurnin da Hajiya tayi min A yau Jidde bawai yana nufin idan nayi wannan Auren na daina sonki bane, wallahi kinji rantsuwar Musulmai, babu wata mace da zan so A duniya sama dake, dalili kuwa! Kina Kaunata tsakani da Allah ne Jidde, ba wai don wani Abin duniya da nake da ita ba.


Ki sani Falmata da Mahaifiyarta ba tsakani da Allah suke so Ayi Auren nan ba, zan iya rantse miki don Abin hanuna yasa Gwaggo Hajara samun Hajja Akan zancen aure na da Falmata" Rufe mishi baki Jidde tayi "Ka daina furta irin waɗannan kalaman don girman Allah? Hajja da Gwaggo Hajara basu da banbanci a wajen ka, Uwa ɗaya Uba ɗaya ba wasa ba, idan hhhat kana tunanin saboda Kuɗi zata Aura maka Falmata to kayi kuskure, karka manta suna da wannan ƙudirin tun A baya, Allah kawai ya ƙaddara dole sai Falmata tayi Aure A wani gida tafito tunda Akwai rabo! Kafin ta zamo Matarka.


Don haka ka daina fadin wai sabida Abin duniya take son hada Auren ka da Falmata, Gwaggo Hajara tana da iko da komai daka mallaka A rayuwa, kuma A duniya babu Abinda za tace kayi mata kace Aa, kawai ka ɗauka Auren Falmata yana cikin ƙaddarar rayuwar ka, kuma karka ɗauka wai ina zubda kwallah sabida Hajja tace zaka Auri Falmata ne, Aa, kawai Abinda yake sakani baƙin ciki guda daya ne, rashin sanin takamammen Abinda nayi wa Hajja yasa kwata-kwata bata ƙaunata, iya kyautatawa irin ta Uwa wallahi ina yi wa Hajja kaima shaida ne, Amma Abin yaci tura,  duk da nasan Akwai sa hanun 'Yan-uwan ka A tsanar da Hajja tayi min, kuma tamkar Uwa daya Uba daya na ɗaukesu".


Jawo ta jikinsa yayi "Nagode miki Maman Abie, ki kara haƙuri kamar yanda kike A yanzu, watarana Sai labari, babu Abinda zai tabbata A doron kasa sai sarautar Allah, tunda Mijin ki yana sonki Magana ta ƙare Jidde, duk tsanarsu dake duk cikin su babu wacce za tace wa Hajja na rabu dake ta sauraresu, sabida tsakanin mu babu haka, kuma Falmata da kike ikirarin wai Gwaggo Hajara ba sabida Abin hanuna take son na aureta ba to abin ba haka bane.


Ai kafin Falmata tayi auren farko Hajja taso wannan haɗin, Amma Gwaggo da Falmatan su kayi karan tsaye akan Maganar Akwai wanda zai aureta a lokacin, kuma yana gane rayuwa, haka Hajja ta hakura da zancen, shiyasa yanzu Auren ta yana ƙarewa tun kafin ta gama Idda Gwaggo ta fara samun Hajja da Maganar, sabida sun san ina matukar jin Maganar Hajja, babu wata buƙata da zata zomin da ita nace Aa, da wannan sukayi Anfani, amma wallahi bani son Falmata, Amma kiyi hakuri Jidde.


Zan kuma sake fada miki babu wata Macen da zan so A duniya sama dake Jidde" Murmushi tayi ta kwantar da Kanta A kafadarsa "Allah ya bamu tare ya hada kanmu da Falmata ka samu farin ciki Alhaji".


"Ameen Jidde na. haka ya cigaba da kalallameta da kalamai masu sanyata zuciya, A haka har akayi kiran Sallar Azahar, ya kamata na fita Akwai Aiken da zai iso gareni daga Lagos Anjima, so ya kamata Ace ina kusa" Daga kanta tayi daga kafadar sa "Allah ya rufa Asiri barin tashi in duba ko Saddiqa ta kammala lunch?" Mikewa yayi tare da fadin "Aa babu Abinda zan iya kaiwa bakina saina dawo kawai"


Itama mikewa tayi ta rakosa har jikin Motor, sai da taga ƙulewarsa kafin ta koma ciki, ɗakinta ta haura direct ta shiga toilet ta ɗauro Alola, tana shirin fara Sallah Sabriya da Aman suka shigo da gudu, Aman ne ya faɗa jikinta "Mummy na dawo?" Shafa kansa tayi "Barka da hanya Aman" Turo baki Sabriya tayi "Mummy yunwa?"


"To ki kama hanun kaninki kuje ki sauya masa kaya sai ku karasa wajen Saddiqa ta baku Abinci?"


"To Mummy suka Amnata da sauri suka fice, mikewa tayi ta gabatar da Sallah Azahar, tana idarwa ta nufi dinning, domin tasan Iyalanta suna wajen, haka ta karasa ta zauna suka cigaba da hira suna cin Abinci duk da Abincin baya mata daɗi sabida damuwar da take ciki.


Bangaren Hajja kuwa Alhaji Goni yana barin gidan tasa Auta kubra kira mata wayar Gwaggo Hajara, tana ɗauka Hajja tace "Hajara idan kin samu lokaci kizo mu tsara yanda Abin zai kasance, yanzu barin Yaron nan A wajena, munyi magana yace bakomai duk lokacin da muka tsara hakan ta mishi" Wani irin guɗa Gwaggo Hajara tayi "Kai Amma wannan Abu yamin dadi, insha Allah da Yamma zan shigo" Cike da farin ciki Hajja tace "To sai kinzo".


Gwaggo Hajara tana kashe wayar tayi dakin da Falmata take, tana hakimce A gefen gado tana zuba Bala'i ma wata Kawarta da Akace mata tana zuwa sauran gidajen kawayen su tana cewa Auren ta ya kare A wtsp Gwaggo Hajara ta shigo, yanda taga Mahaifiyar ta fuskarta ya nuna tsananin farin ciki yasa ta Ajiye wayar ta dubeta "Hajja Mama Albishir na miye akayi miki haka?"


Zama tayi A gefenta "Yanzu mu Kayi waya da Hajja tine Akan maganarku da goni? Tace ya Amince bakomai idan mun tsayar da lokaci kawai Ayi mishi Magana" Tsalle Falmata tayi "Wannan wane irin labari haka? Meye za'a jira Mama? Ai kawai a tsayar da lokaci nan da sati biyu haka, so nake don Uban Surajo da sauran masu tsinemin A gari har suna cewa Aga Wanda zai Aure ni sabida halina sai su nutse cikin ƙasa, kinsan miye Mama? Har Event sai nayi sabida na basu haushi".


"Haba dai Falmata Yaranki Uku wani Event kuma? Kefa Yanzu Uwace?"


"He he he Mamana kenan, da kinsan yanda gari ya Amasa Akan maganar barina gidan Surajo da kin goyi bayana, Yanzu haka Uwar wata nakeci kika shigo, sai zagawa takeyi tana fada musu Surajo ya sakeni sabida na ishesa da Bala'i"


"Uhumm idan banda Abinki meye na wani kiran ta A waya? Ba gashi Allah ya kashe ya baki ba? Idan kudi Surajo yake jin yana dashi, Ai a yanzu kafar Goni bai kai ba, sannan Ai ba Surajo bane yace baya son Aure kece ki kace ba kiyi, to meye A ciki da har wani zaki tada jijiyar wuya?".


"Mama basu da Mutunci ne, gwara na wanke su tsaf"


"Shikenan naji ni barin samu na kimtsa na jira lokaci, daga gidan Yaya na kai tsaye gidan Baffanki zan wuce na sanar mishi zaki karbi Sadaki"


"Sai Mamana" Falmata ta Ambata gamida rungumeta, Mikewa Gwaggo Hajara tayi ta fice daga dakin zuciyar ta fal farin ciki, haka Falmata ya sake kunna Data ta cigaba da zazzaga ruwan Bala'i daga inda ta tsaya.


Karfe hudu na Yamma kuwa A gidan Marigayi Alhaji Bukar tayi wa Gwaggo Hajara, tana shiga Kai tsaye dakin Matar Yayan nata ta nufa wato Hajja Tine, suna zaune da Kubra tana gyara mata Kumba tayi Sallama, fuska wasai suka amsa gaba daya "Hajara har kin iso?"


"Dolena Hajja Tine, Ai ba'a bori da sanyin jiki" waje ta nema ta zauna Kubra ta dago idanu ta dubeta "Gwaggo mun yini lafiya?"


"Kalau Yar Albarka ya karatun?"


"Alhmdullah"


"To masha Allah"


"Auta?"


"Na'am Hajja ?" Ta amsa tacigaba da Abinda take yi "Sake Ƙafar idan mun gama Maganar sai mu ƙarasa".


"To Hajja" Ta mike tabar dakin, Kallon Hajja Tine Hajara tayi "Ban dauka Abin zaizo da sauki haka ba, duba da wancan lokacin da Yaron nan ya nuna yana Son Falmata Amma ta dage sai Surajo, gashi Dan iskan yaro yazo ya watsa mana Kasa a idanu" Murmushi Hajja tine tayi "Allah ne baiyi ba Hajara, ki duba rabon dake tsakanin Falmata da Surajo? Ai kinga ko muna so ko bamu so dole sai Anyi wannan zama".


"Hakane to Aina zancen zata kwana?"


"Yauwa kinga Falmata ta gama Idda, ba kuma Yara bane bare A wani tsaya Fahimta juna, Sannan Yaron nan yana da komai a gidan sa, bare Ace za'a tsaya yin furniture's, ba wani shagalin biki bakomai, nanda Sati biyu Ayi Aure"


"Alhmdullah kamar kin shiga zuciyata Hajja Tine, wallahi nima sati biyu nace A zuciya ta, Allah ya nuna mana"


"Ameen da zaran ya sake shigowa zan turasa wajen Falmata ya kai mata sadakin ta".


"Shikenan hakan yayi Allah ya tabbatar mana da Alkairi"


"Ameen" Bata wani dauki lokaci A gidan ba tayi gidan Baffan su Falmata wato Habu, bata samesa A gida ba sai Matan sa, shiyasa tabasu Sallahu idan ya dawo Ace tana jiransa A gida akwai magana mai mahimmaci da za suyi.........


.