FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuciya ce
Sample · 1
Tunda suka fito daga cikin gidan babu wanda ya iya furta koda kalma daya wa ɗan uwansa sa, a haka har suka iso jikin motor, jiki a matukar sanyaye Alhaji Goni ya buɗe murfin Motor tare da Alama wa Jidde Akan ta shige. tamkar wacce Kwai ya fashe wa a ciki haka ta shige ciki, cikin yanayin damuwa ya shiga yaja Motar suka bar harabar gidan, ganin shurun yayi yawa A motor yasa Alhaji Goni kunna Karatun Qur'ani. Hakan ya cigaba da sharan gudu A hanya yana satar kallon Jidde.Jidde kuwa karatun Qur'anin dake tashi A motor ya fara ratsa zuciyar ta sannann ya sauƙar mata da nutsuwa. Hawaye masu zafi ne suke bin kuncinta alokaci guda suka wanke mata fuska, tuno irin zafafan Kamalan da Hajja ta yaɓa mata, duk Abinda take yi idanun Alhaji Goni yana kanta, a haka har suka ƙarasa gidan su dake Airport road. Hassan Mai gadi yana hango Motar Alhaji daga nesa yayi hanzari yazo...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.