3
by @sadiyanasir
"Huhmm tabdijam, Sannu Jidde Ashe irin zaman da kike kenan da zuri'ar Mijinki? Lallai sannu da kokari? babu wanda zai ce irin rayuwar da kikeyi cikin su kenan, kin yi kokari, ko ince kina da hakuri, nasan ina da hakuri Amma Jidde duk hakurina kin fini, idan nice ba zan bari 'Yan-uwan sa su addabeni kamar yanda Uwarsa ta addabeni ba, domin bana daukar Raini agun wanda na fisa. Ni lokacin da Hamza zai min kishiya a wajensa na samu matsala, gaba daya juyamin baya yayi, duk farin cikin da yake bani janye sa yayi, idan kinga dariyar sa agidan nan to zancen Auren sa suke da Yaran sa, gaba daya rayuwa tamin zafi, haka nake zama naci kuka kamar Raina zai fita, kuma nima irin taki nayi, domin kasa fada nayi ma kowa nawa irin zaman da muke tsakanina da Hamza, haka na danne cikin zuciya ta har Akayi Auren. Huhmm A wannan lokacin naga rayuwa Jidde, tamkar Yar Aiki haka Hamza yaso mai dani a gidan nan, bani da anfani sai in dafa Suci da Amarya, ko dakina baya zuwa ko ranar kwana nane, kafin kice meye Yarinya ta soma rainani sabida Abinda taga Hamza yake min, wannan kam nace ba zan dauka ba, Miji ya zama dole nayi hakuri dashi Amma banda Kishiya. Watarana data cikani da Habaici A harabar gida haka na fito mu kayi sosai da ita, Mutumin ki yana dawowa dauki Amarya yace naje gidan mu saiya nemeni. To a wannan lokacin gidan mu suka san miye Hamza yake min, shiyasa Umma tace nayi zamata babu wanda zai nemeshi tunda giyar aure ke dawainiya dashi, in Takaice miki sai da Hamza ya shafe wata biyu mai kyau kafin Mahaifiyarsa tazo gidan mu, itama Rai A bace domin bata San Hamza yace nabar gida ba, sai da ta kwabe musu da Amarya Abin harya kaisu ga dambe shine ya tuna ina da Anfani yaje ya fada mata, haka tarinka bada hakurin wa iyayena Akan na koma gidan Hamza, su kuma su kace ikon komawa na wajena,
Matarnan haka ta rinka lallabina tana min magiya na koma sabida Yarana, domin wahala suke sha waje Badi'a. haka dai 'Yan-uwana su kace yazo da kanshi ya nemi biko, da daddare kuwa yazo kamar munafuki, haka ya rinka zuba min dadin baki, dake Iyayena mutanen Arzikine kwana biyu da zuwansa suka tusa keyata na koma gidansa. ina komawa kuma na fada masa muddin Matar sa ta sakemin rashin kunya zan dauki fansa kamar yanda nayi A baya, haka muka cigaba da zama har Amaryan ta dawo, tsakanina da ita idanu, Rainin data soma yimin yaja baya, haka idan rikicin su ta hadasu zata zageshi Uwa ta uba, ni dai tawa idanu, A haka har ta samu ciki. Kawayenta suka zugata Akan ta zubar, to fa A wannan karon Abban su bai dauki iskanci ba, rikici har wajen Iyaye, daga karshe da aka rasa mafita ya sake ta, haka mika dawo tsakanina dashi kamar bai min Abinda yamim a baya ba, tsakanina dashi ganin girma da Arziki. Jidde? na baki wannan labari ne sabida ki gane ribar hakuri, Mijinki yana sonki baki da wata matsala dashi, shawarar da zan baki itace, kicigaba da hakuri Akan Uwar Mijinki domin itama Mahaifiyarki ce, kuma hakuri da Iyaye ya zama dole, idan har Hajja ta saka Alhaji Goni kara Aure domin ta musguna miki ne Akwana a tashi za kiga Abinda zai faru dasu, ke dai kawai koda wasa kada ki dauki raini Agun kishiya, domin bata da hurumin daza kiyi mata biyayya dole, Mijinki da Mahaifiyarsa sune miki dole ki hakura dasu. Dafa kafadarta Jidde Saratu tayi, nasan Akwai zafi idan Miji zai kara Aure domin naji zafin, ki daure wa zuciyarki ko da wasa kada ya gane hankalinki ya tashi Akan Auren sa, musamman 'Yan-uwansa da suka nuna basu kaunarki, hakan ba karamin tsoratasu zaiyi ba. Sannan idan Alkairine shigowarta gidanki Allah yahada kanku, idan kuma Babu Alkairi Allah ya wargaza komai kamar yanda ya kori Badi'a A gidan nan". Murmushi Jidde tayi.
"Bakomai Saratu naji Abinda ki kace kuma insha Allah zan cigaba da hakurin kamar yanda kikace, nagode sosai da shawara".
"Bakomai, ki sake Jan Mijinki a jiki fiye da yanda kike jansa A yanzu, zan kuma baki wasu sirrika irin tamu ta Mata kije ki jarraba, yanzu kishiya za'ayi miki dole sai da gyara" Dariya sukayi gaba daya. Haka Saratu ta cigaba da bata satar amsa na zamantakewar rayuwa musamman zama da kishiya, tare da hadata da kayan mata masu kyau da inganci. Sai wajen Azahar kafin ta kira Driver idan ya dauko su Sabriya ya biyo ya dauketa.
30minute a tsakani sai gashi sun iso da Yaran, Sabriya da Amman ne suka shigo suna kiran Mummy tasu, haka Saratu ta hadasu da kayan makulashe ta rakosu har jikin motor, sosai Jidde ta sake yi Mata godiya bisa shawarwari data bata kafin suka nufi gida. Da isarsu kaya kawai ta canza ta nufi kitchen ta fara kiciniyar hada Tuwo Miyar Kukar da Alhaji Goni yace yana so yaci. Yaran kuwa haka Saddiqa ta hada musu Abinci A dinning suka ci. sai wajen karfe Hudu kafin ta kamala komai, dakinta ta dawo ta fada toilet ta sake wanka, dake tana period kaya kawai tasa ta fito, dakin su Sabriya ta nufa, ganin bata gansu ba yasa ta tuna Ashe Akwai islamiya ,shiyasa ta dawo Palo ta zauna ta cigaba zancen zuci.
Alhaji Goni kuwa Ana kiran Sallah Azahar yabar company domin Hajja ta kirasa idan ya samu lokaci yazo, shiyasa yana Sallah kai tsaye gidan su ya nufa, zaune ya sameta Kubra tayi mata romon kifi tana sha. Cike da ladabi ya nemi waje ya zauna ya gaisheta, sai da kammala shan romonta kafin ta dubesa "Ya Aikin dai?"
"Da godiya Hajja".
"Masha Allah, dama nace ka zone akan zancen Falmata, jiya Hajara tazo munyi Magana, so nake tsakanin Yau da gobe ka dauki kudi ka kai wa Falmata Matsayin Sadaki nida asona ma da sisin gwal naso kabiya sadakin tunda Allah ya hore maka, ka haɗa duka da kuɗin turare dana Shiga kasuwar uwa kabata. Sauran abubuwanda yakaamta kuma Kamar kayan toshi Kayan lefe saika bar kuɗi anan ƙannenka su saya kamar abubuwan al'ada idan yaso saina kira gwaggonku da kanta tazo ta amsa tunda Abin na gida ne kuma mun yanke shawara nanda sati biyu za'ayi Auren". Saida ta dasa maganar sannan tasake faɗin.
"Yawwa ka haɗa gabaki ɗaya da kuɗin flour na kayan cin-cin" saurana abubuwanda take buƙata kuma saika tambayeta ta faɗa maka. Tunda kasam ba lallai ta iya sanarda kai idan baka tambaya ba."
A cikin ransa yana mamakin iron yanda Hajja ke ɗaukin abin amma ba abun mamaki bane idan akayi la'akari da ko abaya taso wannan haɗin. Afili kuma Alhaji Goni yace.
"Shikenan Hajja insha Allah gobe da Yamma zanje. Nan kuma saiki faɗamin kamar nawa ake buƙata saina tura ta account ɗin kubura"
"Yauwa toh zamu zauna da ita mu lisaffa duk abinda yakama zan sanar maka Allah yayi albarka"
"Ameen" ya amsa. Hiran rayuwa suka cigaba dayi da Hajja har Aka kira La'asar, A gidan yayi alola yayi mata sallama ya fito zuwa Masallaci, yana idar da Sallah kuwa gidansa ya nufa kai tsaye.
Jidde kuwa tunani mai zurfi ta fada, shiyasa bata San Alhaji Goni ya shigo Palon ba, saida taji hanun sa A jikinta ta firgita, durkusawa yayi A gabanta
"Haba Jidde meyasa baza kibar zuciyarki ta huta Akan Auren nan ba? Sau nawa zan fada miki Goni naki ne?" Dan Murmushi tayi
"Niba damuwa nake Akan Auren ba, kawai tunanin gida nakeyi" Murmushi yayi
"To shine baza kicemin za kije gida ba?"
"Dama wai..
"Ya isa, tunda kince kina so kije Umra saina biya miki kudin kujera ta garin ku, kinga sai kiyi tafiya daya, yanzu idan ki kace za kije gida Hajja za tace sabida zanyi aure ne, Amma idan kinyi tafiya daya shikenan". Dago ido Jidde tayi ta dubesa.
"Kenan Ansa bikin?"
"Eh to Hajja tace nanda sati biyu, kinga banda wannan Asabar da zaizo wata kenan, yanzu daga gidan nake, tace zuwa gobe naje na kai wa Falmata kudin Aure". Ajiyar Zuciya Jidde ta sauke.
"Allah ya nuna mana da Rai da lafiya, ya kamata ka karasa daki ka watsa Ruwan sai kaci tuwon"
"Yauwa matar so nagode". Mikewa yayi zuwa daki ita kuma ta nufi Kitchen, haka ta hada mishi komai a dinning zuciyar ta nayi mata kuna, yana fitowa tare suka zauna A dinning din ya sata cin Tuwon dole, shiyasa ta danci Kadan domin dama yunwar takeji damuwace ta hanata ci.
Washe gari kuwa da Yamma bayan Alhaji Goni ya dawo daga Office wanka kawai ya sakeyi ya fito zuwa gidan Gwaggo Hajara, A kofar gidan yayi parking ya fito da kafa zuwa cikin gidan, yana knocking mai gadi yazo ya bude ya durkusa ya mike gaisuwa, kudi Alhaji Goni ya Ciro ya damka mishi, tuni ya shiga kirari yasa kai zuwa cikin gidan isar da sakon zuwan Alhaji Goni. Kafin ya karasa cikin Palon Gwaggo Hajara ta hada masa kayan Motsa baki, da Azama tayi dakin Falmata da take zaune tana gyara kanta.
"Ke hanzarta ki kimtsa ga Goni ya iso, dama munyi waya da Hajja Tine tace mu tsumayesa zuwa dare".
Dafa Kirji Falmata tayi.
"To Mama gani fitowa" Da sauri Gwaggo Hajara ta fito Palo, zaune ta samesa yana latsa waya, yana ganin fitowarta ya durkusa.
"Gwaggo barka da Yamma?" Baki A Washe tace.
"Barka Dan Albarka Ashe kana tafe?" Murmushi yayi "Na sameku lafiya?"
"Alhmdullah ya mutan gidan ina kawata da Mai gidan?"
"Suna lafiya"
"To Madallah barin shiga Falmatan tana zuwa"
"To Gwaggo". Tana shiga dakin Falmatan ta nufa, A jikin madubi ta sameta tana kara gyara fuskarta "Ki hanzarta mana Falmata?" Mayafi ta dauka ta fito. Tunda ta doshi Palon ta sauya tafiya, tamkar wata hawainiya haka take rawa da jiki, kujeran dake zaune Akai ta zauna nesa dashi Kadan.
"Barka da zuwa Yaya?" Ta ambata da sassanyar murya irinta shagwaba. idon sa na jikin waya yace "Barka Falmata ya kike?"
"Lafiya Yaya"
"Masha Allah, Ajiye wayar yayi ya dubeta, sai A lokacin yaga kwalliyar da tayi, Dan Murmushi yayi domin Falmata Akwai iya gaye, babu wanda zai kalleta yace ta haifi yara Uku. Gyara zama yayi! nazo muyi Maganar Sadaki da wasu kudi da zaki bukata na hidima, Hajja tace nanda sati biyu za'ayi Auren Saiki faɗamin kamar nawa kike buƙata"cike da shagwaba tace.
"Yaya ka bayar da duk Abinda kaga yayi maka, nida kai Ai babu wani tsayawa lissafi" Ya jijjiga kai sannan yace.
"Dake kinsan wasu al'adun naku na mata ku kaɗai kuka sansu ni banda kuɗin uwa dana sadaki sai kuɗin cin-cin da Hajja ta sanar dani yanzu su kaɗai nasani ko su kennan?" dasauri ta girgiza kai. Yace.
"Toh kingani gara dai ki faɗa kar nabada bai kai yanda kike buƙata ba" Tayi murmushi sannan tafara faɗin.
"Uhmm dama dai kuɗin Lalle dana kayan lallae dana turare sai gyran jiki. kuɗin kitso. Kuɗin anko na ƙawaye da nawa sai entertaiment na ƙawaye Sai kuma lefe da zamu Shiga kasuwa mu haɗa inaga su kenan" Tunda tafara lissafi Alhaji goni yake murmushi yana kallonta aransa yana tunanin wacce tace yabada koma menene shida ita babu tsayawa lissafi itake masa wannan lissafi hadda wani entertaiment na ƙawaye da anko na ƙawaye kodai ta manta ita bazawarace? Afili kuma yace.
"Hajja tace zasu haɗa lefe ita dasu kubura sai acireshi a lissafi" ko kaɗan bataji daɗin maganar ba saida fuskarta ta nuna dakyar ta iya shanye bacin ranta sannan tace.
"Hakan yayi"
"Shikenan bani Account number dinki zan saka miki 300k Sadaki 100k gyaran jiki. 100k abawa goggo, 100k gyaran jiki da kitso. na ƙawaye ma haka 100k sai zan saka na cin-cin da turare. sauran kiyi Anfani dashi"
"Masha Allah Yaya nagode" Mikewa tayi ta zuba mishi lemun da Gwaggo ta kawo ta mika masa, Kadan yasha ya mike da niyyar tafiya.
"Nizan koma idan Akwai wani Abu ki karbi Number ta wajen Gwaggo, kuma kice mata zan wuce?"
"Da wuri haka Yaya?"
"Akwai Inda zanje daga nan" Ya fada A takaice. To tace tayi daki sai rangwadi take da jiki kamar zata narke. Gwaggo tana fitowa yayi mata sallama yadan ajiye Mata na kashewa, sosai tayi godiya tasa mishi albarka ya tafi.
Suna jin tashin Motarsa Falmata tayi tsalle "Mama Allah Yaya Goni dama can yana sona, kinga yanda yake rawar jiki?" Shewa Gwaggo Hajara tayi "Ai Falmata kina da Kyau dole duk wanda ya ganki ya soki, yanzu nawa ya bayar?"
"Ya karɓi account zai turamin amma da alamu zai turo dayawa"
"Yauwa to zaki cire 200k zan turaki Maradi wajen Kawata ta gyaramin ke tsaf, domin so nake idan kinje wannan gida sai Mutuwa, A mai dake tamkar budurwa....