Complete book
A Dalilin
'DA NAMIJI
1
NA
FAREEDA ABDALLAH
“A
yau ne Alqalin babban kotun da yake cikin garin Kaduna ya yanke wa wata mata mai suna Fatima Ibrahim hukuncin xaurin rai da rai a gidan yari, abisa laifin da ake tuhumarta da shi na halaka babban xan mijinta mai suna Nasir ta hanyar watsa mishi ruwan zafi duk jikin sa, wanda hakan ya yi sanadiyyar salvewar duk wata fata da take jikinshi. bai xau awa xaya ba a asibitin “BIBA HOSPITAL” ya ce, ga garin ku nan.
Mijin matar mai suna Alhaji Muhammad shi ya danqa matar ta shi a hannun hukumar ‘yan sanda kuma ya tsaya tsayin daka akan lallai sai da ya qatarwa xanshi mai rasuwa haqqin shi akan azzalumar matar ta shi, wacce ba ta da tsoron Allah ko kaxan azuciyarta inji mijin na ta. Ga dai yanda tattaunawar tamu ta kasance da shi.”
Gaba xaya ‘yan matan da suke zaune a tafkeken falon suka qara shiga nutsuwar su don jin yanda tattaunawar za ta kasan ce.
Fitowa ta kenan daga ban xaki xaure da towel a jikina, na rufa wani qaramin tawul xin akaina, fuska ba walwala na zauna a kan kushin mai zaman mutum uku, sannan na xauki “Remote” a gefena na qure Radion sosai tamkar zai fasa mana dodon kunne.
“Ya sunan Malamin?” Xan jaridar ya jefa wa mutumin da suka kira mijin matar da ake tuhuma tambayar.
“Sunana Alhaji Muhammad Yusuf.” Mutumin ya amsa da cikakkiyar muryar da ba ta nuna jimami ko kaxan.
“A yau ne aka kawo qarshen shari’ar nan da aka xauki tsawon watanni uku anayi tsakanin mai xakinka Malama Fatima da Marigayi xanka Nasir , mai zaka iya cewa akan hakan.”
“Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) da ya kawo qarshen wannan shari’ar, tabbas ina cikin farin ciki da godiya ga Allah domin an fitar wa da mai haqqi haqqinsa, mata irinsu Fatima waxanda basa tsoron Allah ko kaxan azuciyar su wannan ya ishe su darasi amma idan har sunada tunani, tun lokacin da marigayi Nasir Allah ya jiqan shi ya tabbatar min da Fatima ce ta aika ta mishi hakan kawai don ya ziyar ci gidan ta a matsayin shi na xan mijinta karo na uku tun bayan dawowar shi daga qasar Malesia karatu. lokacin da ya faxa min hakan bai fi saura minti ashirin Allah ya xauki rayuwarsa ba, kuma na xaukar mishi alqawarin ko da zanyi yawo tsirara sai na xaukar mishi fansa, don haka ayau ina mai farin ciki matuqa su kuma ma su irin halinta ina ma su fatan Allah ya shirye su idan kuma ba ma su shiryuwa ba ne Allah ka tarwatsa su aduk inda su ke a faxin duniya"
“To yanzu ya matsayin igiyar auran da yake tsakanin ku?” Xan jarida ya sa ke jefa mishi wannan tambayar.
“Tun ranar da abin ya faru na yanke igiyar aurena duka ukun da yake tsakanin mu, kuma na danqa mata takardar ta tun kafin a kawo qarshen wannan shari’ar.”
“Akwai zuri’a a tsakanin ku?”
“Babu yaro ko xaya a tsakanin mu shekarar mu biyu da aure amma ko vatan wata bata tava yi ba.”
“Ba ka tunanin wani irin kallo da iyayanta zasuyi maka?”
Dan jaridar ya sake tambayar shi.
Muryar shi a fusace ya amsa da cewa,
“Ita xin marainiya ce a hannun qanin Babanta na aureta, kuma tunda ya ji abin da ta aikata ya zare hannunshi daga kanta bayan ya yi mata Allah ya isa rainon da ya yi mata, kuma ko iyayanta su na da rai bazan damu da duk wani abu da ya za su ce ba, don kuwa Xa bai fi Xa ba.”
“To amma….."
“Dakata Malam!! tambayo yinnaka sun ishe ni haka, ina da abinyi”
ya katse dan jaridar ya na gwama numfashi ci ke da fusata.
“Qarshen tattaunawar da ta gudana tsakanin wakilin mu kenan da mijin mai laifin, wakili namu ya nemi tattaunawarsa da uwar marigayi amma hakan bai samu ba, kuma ya nemi tattaunawa da mai laifin itama ta qi ba mu haxin kai, kalma xaya kawai ta iya furtawa ga wakilin namu.
Cikin hawaye ta ke nanata kalmar.
“ADALILIN DA NAMIJI”
Daga nan ta varke da matsanancin kuka ya yin da ‘yan sanda sukai awon gaba da ita cikin motar shiga ba biya fi ta da Allah ya isa, nan muka kawo qarshen shirin na JAKAR MAGORI…."
“Xif na sanya hannu na kashe Redion hankali na atashe kyawawan idanuna sun rine zuwa jajaye saboda tsananin tashin hankali, Safa da Marwa na ke a tsakiyar falon ina doka hannu na dama cikin na hagu, tsawon minti goma na xauka ina hakan da ga bisani na zube akan kujerar da na fara zama tun bayan fitowa ta da ga wanka.
Hankalina ‘yan matan da su ke zaune tunda farko a falon yana kaina da alamun jira su ke in furta wani abu sannan su ma su samu bakin magana.
“Me maza su ke so su mai da mu a duniyar nan?” Na furta hakan murya ta a kausashe ina kallon ‘yan matan cikin falon xaya bayan xaya.
qarar shigowar Messages ba tare da qaqqautawa ba aduk wayoyi na guda uku da suke cikin xaki shiya katsemin maganganun da na fara yi
"Safiyya kwasomin wayoyina a xaki"
Na faxi haka ina kallon xaya da ga cikin ‘yan matan.
Daqiqa talatin tsakani ta fito riqe da wayoyina a hannunta, sai da ta xan rusuna sannan ta miqamin, duk saqonnin sun fito da ga guri xaya ne. number ce kuma babu suna, 7777 shi ne number da ya turo min saqon. Gyara zama na yi don kuwa saqon mai muhimmanci ne a gare mu, saqon daya daga cikin wayoyin na fara karantawa a fili don sauran ‘yan matan su ji meya qunsa.
“TARIHIN FATIMA IBRAHIM WACCE TA KASHE XAN MIJINTA NASIR” hakan aka rubuta da manyan baqi a farkon saqon, na xan tsagaita ina kallon fuskokinsu cikin nazari xaya bayan xaya, kowacce a zaqe take da son jin cigaban saqon, don haka na xora daga inda na tsaya.
“Marainiya ce gaba da baya, iyayanta Allah ya xauki rayuwar su tun tana ‘yar shekaru uku a duniya, hatsarin mota sukai a hanyar su ta dawowa da ga Abuja zuwa Kaduna marigayi Alhaji Ibrahim mahaifin Fatima shahararren mai arziqi ne. Fatima ita kaxai ce xiyar shi a duniya, mahaifiyar Fatima ‘yar Zindar ce a jamhuriyar Nijar, yawon kasuwanci ya kai mahaifinta can qasar har Allah ya haxa fuskokin su sannan ya sanya soyayya mai tsanani a tsakanin su har sukai aure, bayan kai ruwa ranar da akai da mahaifin Aisha (Kakannin Fatima na wajen Uwa) kan cewa ‘yarsu baza ta yi aure a wata qasa ba.
Lokacin da kakannin Fatima na wajen Uwa su ka samu labarin rasuwar ‘Yar su da mijinta sunyi kuka sosai, kuma sunzo har akai bakwai sun buqaci tafiya da Fatima amma Alhaji Musa qanin mahaifinta yace, sam! Hakan bazai tava yuwuwa ba.
Sunyi rabuwar dutse da hannun riga wanda hakan ya yi matuqar tunzura su har suka sha alwashin yanda su ka rasa ‘yarsu Aisha mahaifiyar Fatima suka haqura itama Fatima sun haqura da ita har abada, indai ita jinin su ce zata neme su amma su kam baza su tava nemanta ba har gaban abada idan akwai.
Bayan komai ya lafa riqon ta ya koma hannun qanin mahaifinta ya zama mahaifin ta kuma mahaifin dukiyar ta. Babu wata rayuwa ta jin daxi da Fati za ta karar wanda tayi a gidan qanin mahaifin nata.
makarantar gwamnati ya sanya ta savanin ‘ya’yan shi da suke makarantar kuxi, duk waxanda ya kamata su tsawatar mishi ya gama siyesu daman kuma mahaifansu (Kakan nin Fatima na wajen Uba tun ta na ‘yar jaririya suka rasu) Da daxi ba daxi har ta kammala Secondary School inda ta fito da sakamako mai matuqar kyau, babban burinta ta ci gaba da karatu amma sam Alhaji Musa yaqi bata damar hakan, amma ‘ya’yan shi da mazan da matan duk babu wanda yake karatu a qasar nan.
Alhaji Muhammad aminin kawunta ne don duk wani qulle qulle na kawun nata Alhaji Muhammad ya sani, tun tana aji uku a Secondary School yake damunta da maganar soyayya, nauyin shi ta ke ji sosai dan ta xauke shiu tamkar qanin mahaifinta, batare da saurarar amincewa ko ra’ayinta ba. Alhaji Musa ya xaura mata aure da Alhaji Muhammad.
Hannu bibbyu tasa ta rungume shi duk da ba ta son shi ko kaxan, gidanta da ban da na uwar gidan shi kuma uwar yaranshi, ya na nuna mata kulawa dai – dai gwargwado saboda ya na sonta, kuma tana daga cikin jerin matan Allah ya kyautata surar jikin su, da na fuskar su.
qarin armashin kuma shi ne yarinya ce qarama dan ita sa’ar xan autan shi ce, ita da Hajiya Kumatu uwar gidan shi suna zaman amana dan kuwa ba ko da yaushe suke ganin juna ba.
Idan bada wani qwaqwqwaran dalili ba sukan dauki tsawon lokaci ba su haxu ba.
Ba su fara samun matsala ba sai da Xan Alhajin mai suna Nasir ya dawo gida daga inda ya ke karatu acan qasar Malesia, tunda suka je air port da niyyar xauko shi ita da Alhaji da Hajiya ta lura da irin kallon da yake binta da shi, Nasir bunsuru ne gurin bin mata tun kafin ya tafi karatu qasar Malesia da ya je can kuma sai idonshi ya qara buxewa duk yarinyar da ya qyalla ido a kanta sai ya bi duk hanyar da yasan zai samu biyan buqatar shi.
Tun yana can ya ji labarin Dadyn shi ya yi aure amma bai tava tunanin daqwalwa irin wannan ya aura ba, ganin farko da ya yi mata gabanshi ya yanke ya faxi daqyar yayi qarfin halin daidaita nutsuwarshi don karya bada kanshi a gaban iyayan shi.
Suna tafe a mota zuciyar shi tana saqa mishi hanyar da zai bi dan cimma mummunan manufarshi a kanta, a zuciyar ta take ta addu’a Allah ya daidaita zaman su dashi dan sam bata fahimci wane irin kallo yake yi mata ba, a zaton ta kallon tsana ne da tunani yana taya mahaifiyar shi kishi ne, a minti biyar ya mantar da ita wannan tunani ta hanyar fara janta da hira yana kiran ta “Aunty Fati” duk iyayan ransu cike yake da farin cikin dawowar xan nasu dan haka sam hankalin su ba shi a kan Fatima, idan ya tsomata a hirar shi a xarare ta ke amsawa muryarta a sanyaye.
Hakan ba qaramin burgeshi yake ba, shauqin sha’awarta yayi ta xibar shi, har su ka isa gida, ba ta bar babban gidanshi ba zuwa gidanta sai bayan magariba gab da isha’I da yake Alhajin a gidan yake da kwana sai ya haxa ta da Driver ya kai ta gida da sauri Nasir ya miqe ya na kallon iyayan shi fuska a sake ya ce, “Ba ri in raka aunty Fati gida sai mu dawo ta re da Drivern”
jikinta sanyi qalau ta ke kallon shi don rashin ga ne manufar wannan cusa kai da ya ke mata. Izinin tafiyar daya samu daga gurinsu ya hanata tankwavar da shisshigin shi , sai ta qara yi musu sallama ta nufi harabar gidan.
Dukkansu suna zaune a bayan motar ba mai cewa wani uffan, amma idon shi ya na kanta tamkar zai cinyeta xanye, ba qaramin takurata yayi da idanun shi ba don haka ta takure acan jikin motar, a zuciyarta ta ke addu’ar Allah yasa su isa gidanta lafiya ko zata samu sa’ida da ga mayataccen kallon da yake bin ta da shi.
Suna isa ta dakatar da Driven a qofar gida, ta valle murfin motar ta fita sannan ta leqa kanta ta saqon glashi ta ce, “Nasir Allah ya huta gajiyan tafiya mu kwana lafiya” ta qarasa da sauri ta ciro key a jaka ta na buxe get xin gidan ba taga fitowar shi daga mota ba balle lokacin da ya nufota kawai muryarshi ta ji a kusa da ita ya na faxin “Haba aunty na rowar ruwan gidan ki za ki yimin?”
a firgice ta sa ki key xin ya faxi qasa muryar ta na rawa ta ce, “Ba… ba… ba haka ba ne, na… naga su Alhaji suna can suna jiranka ne.” bai ce komai ba ya ya tsuguna ya xauki makullin ya buxe get xin ya shige ciki ya bar ta nan a tsaye. Ganin da ta yi ba sarki sai Allah ga idanun Driver tun xazu ya na kanta ya sa ta yi shahadar bin bayan shi, har ya samu nasarar buxe qofar falonta ya shige ciki don haka ta haxa da sassarfa zuwa cikin falon.
Yana kwance akan kujera mazaunin mutum uku idanun shi alumshe, jakarta ta aje akan kushin ta nufi kiching ta jero mishi lemuka da ruwa ma su matuqar sanyi a cikin faranti ta xora Cofi guda biyu ta kawo mishi.
A zaune ta tarar da shi hannun shi riqe da remot xin T.V ya na canza tashoshi, a gefe xaya ta aje ta xauko xan qaramin table ta xora sannan ta kalle shi ta saki fuskarta ta ce “Bisimillah.” Maqe ka faxar shi ya yi tamkar wani qaramin yaro sannan ya fara kashe ma ta ido irinna gogaggun ‘yan duniya. Muryar ta da mamaki ta ce
“Me ya sa? Bayan ruwa ka buqaci sha”
“Ni ba irin wannan ruwan nake so ba”
Ya faxa yana tura baki, ya fara kwarkwance mata tunanin ta don kuwa ya girme mata nesa ba ku sa ba, a qalla zai girmeta da shekaru goma sha huxu, wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi. Sam bata fahimci inda ya dosa ba don haka ta ce,
“dare yana qara yi fa kar su Hajiya su ji shirun ya yi yawa"
“Bikin Magaji ya na hana na Magajiya ne?" ya jefa mata tambayar yana qara qura mata ido. Kallo kawai ta bishi dashi ba tareda ta amsa mishi ba. Tashi ya yi ya matso dab da ita sannan ya ce,
“Gaskiya Fatima bazan voye miki ba sam baki dace da irin su Dady ba, da irin mu ki ka dace, kina da kyau matuqa, kina da dirin da duk wata qasaitacciyar mace za ta so ta mallaki irinshi, ganin farko da nai miki sha’awarki ta mamaye zuciya ta “Ina sonki” zanso ace kin rabu da mahaifina ki dawo gareni, idan kuma hakan bazai samu ba to gaskiya sai dai mu raba shi daidai da Daddy, don wallahi tunda na xora qwayar idanuna a kanki to tabbas sai na biya buqatata.
Gobe Daddy zai dawo gidan nan donhaka kwana biyu na baki ki yanke hukunci a ranar da Daddy ya koma gidan Momy zanzo danjin shawarar da kika yanke”
ba tare da ya qara kallota ya fice da ga falon.
Tofa! In ka ji qi gudu sa gudu ne bai zo ba, tsawon minti arba’in batasan a wace duniyar ta ke ciki ba dawowa hayyacinta ta yi ta ganta zaune dirshan a kan kafet xin da ya malale tsakiyar falon. A ranar idan ta ce tayi barci to tabbas ta yi qarya, duk qwarewar sarkin varayin gurin satar mutane a ranar bai yi nasarar satarta ba, daga qarshe ta xauro Alwala ta fara jera nafilfili tana kai kukanta da Ubangijin talikai.
Har Alhaji Muhammad ya bar gidan ta rasa mafitar da tafi dacewa a tsakanin zavin da Nasir ya bata, Alhajin da kanshi ya fahimci bata cikin walwala kuma ya tambaye ta amma ta kasa sanar dashi gaskiyar abinda yake damunta.
Tun qarfe shida da yamma ta kulle get xin gidan da qofar falonta, a tsammaninta ta kuvuta daga zuwan Nasir, don ko yazo zai koma tunda gidan yana rufe ne. fitowarta kenan daga wanka misalin qarfe takwas da rabi na dare, taji kamar hayaniyar T.V take jiyowa daga falonta, don haka ta xora hijabi akan towel xin da take xaure dashi ta fito zuwa falon. Yana hakimce akan kujeara yana karkaxa makullin motar mahaifinshi wanda ya ke haxe dana qofar get xin gidanta dana qofar falonta, hakan shi ya ba ta tabbacin inda ya samu makullin cak ta tsaya tana kallonshi ta kasa furta ko kalma xaya. “Babyna…” shiya katse mata tunanin da take yana mata kallon qurilla tamkar zai cinyeta.
“Me ya kawo ka gidannan?”
Ba tambayeshi fuskarta ba walwala ko kaxan, saida ya xan ja fasali kamar bazai yi magana ba sannnan ya ce,
"Amsar buqatata nazo ji”
“Ni ba irin ‘yan iskan matan daka saba hulxa da su bane, ka je can ka samu dai dai dakai ni matar mahaifinkace ko mun rabu dashi aure ya haramta a tsakaninmu kuma ba zan tava yin zina da aure na ba, don haka karka qara zuwa min da zancen banza.”
Ta fadi hakan muryanta cike da masifa, idanunta a kankance.
“Kin manta abinda na faxa miki rannan koh? To wallahi bazan tava haqura dake ba, ko da tsiya ko da arziqi sai na cimma burina a kanki kinsan irin azabtarwar da nayi a kwana biyun nan kuwa? To wallahi sai kin haxa jikinki da nawa a gobe goben nan.”
Ya fadi haka cikin nuna rashin damuwa da masifa da take mishi.
“Qarya kake Nasir Allah bazai tava barinka ka cimma qazantacciyar manufarka a kaina ba, kuma idan baka janye wannan maganar ba zan kira mahaifinka in sanar da shi duk abinda kace.”
“Wannan shine babban kuskuren da zaki tabka a rayuwar ki kin manta irin son da iyayena suke min ne? ko kin faxa musu wallahi bazasu tava yarda ba, a qarshe sai dai ma ki janyowa kanki wani bala’in don zan tabbatar musu da cewar tunda na dawo qasar nan kike bibiyata, don naqi amincewa buqatarki ne kikai niyyar shiga tsakanina dasu.”
Ya qara matsawa dab da ita, ita kuwa ta fara ja da baya har sai da ta qure da jikin bango yana kusantar ta. Hannu biyu yasa ya dafa bango ya tare ta a tsakiya, fuskarshi ya matsar dab da ta ta sannan yace, “Kinsan kuma tsab zasu yarda da abinda nace, don ana canza mata amma ba’a canza da, kiyi tunani ki samu nutsuwar yau gobe zan dawo in kashe qishirwata.”
Daga haka bai qara furta komai ba ya fice ya barta tsaye a gurin kamar mutum-mutumi.
yau kam kasa yin sallar ta yi kawai sai ta rushe da kuka mai tsananin qarfi tsawon awa biyu tana kuka wa wannan mummunan al'amari da ke tunkarar ta, daga qarshe sarkin varayi ya yi awon gaba da ita a tsakar falon.
Washe gari ba abinda ta iya hassalawa a gidan jikinta sanyi qalau tana kwance akan kujera tana jan carbi, lokaci zuwa lokaci gabanta yana faxuwa tanajan “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un” har Alhaji ya shigo ya dubata kamar yadda ya saba idan ba’a gidan ya kwana ba.
“Bana jin daxi ne” amsar da ta bashi kenan lokacin daya matsa da tambayar abinda ke damunta.
“Zan turo Nasir ya kaiki asibiti” ya faxi hakan yana ficewa da sassarfa don karya makara zuwa Office.
Ganin zaman bazayyi mata ba yasa ta miqe ta nufi banxaki da niyyar watsa ruwa ko zata ji qarfin jikinta. Heater bayinta ya lalace kuma ta manta ba sanar da Alhaji ba don haka ta ciko bokiti da ruwa ta jona a jikin soket abayan kujera a falon, tana zama Nasir ya shigo ba tare da sallama ba, kallonshi tayi sama da qasa yana sanye da qananan kaya jeans da T.shet.
“Oh My God! Babyna wai baki da lafiya inji Daddy?” ya faxi hakan yana kusantar ta nufinshi don jin yanayin jikinta.
“Dakata Nasir, karka kuskura ka matso kusa dani.” Ta yi mishi gargaxin hakan muryarta tangaran babu alamar rashin lafiya a tare da ita cak ya tsaya tamkar an riqe shi, shi bai qarasa kusa da ita ba kuma bai koma baya ba.
“Kina tunanin akwai abinda zai hanani biyan buqata ta dake a yanzu?”
“Qwarai kuwa” ta faxa muryarta babu alamun tsoro ko kaxan.
“Meye shi?” ya tambaya da tsananin mamaki a fuskarshi.
“Allah bazai baka nasara a kaina ba.”
Dariya ya qyalqyale da shi tamkar sabon hauka sannan ya qara kusantar ta da niyyar haxa jikinta da nashi ko ta halin qaqa.
“Dakata” ta sake bashi umarnin haka a karo na biyu lokacin baifi saura taku biyu ya isa gareta ba, bayyi niyyar tsayawa ba amma ga mamakinshi sai ya tsaya.
“Bani minti biyar inyi wanka…” ta faxa sannan ta rava ta gefenshi ta wuce zuwa bayan kujera inda ta jona heater.
“Fatima shure shure ba ya hana mutuwa duk abinda zakiyi yau sai na biya buqata ta a kanki, don haka jeki dawo ina jiranki” yana gama faxin haka ya zauna akan kujerar da ta tashi yana qyalqyala dariya.
Idanun shi kaxai ta kalla ya tabbatar mata da cewa tabbas yau da gaske yake don haka gara ta nemi mafitar qarshe tun kafin wankin hula ya kaita dare, ruwan yana tafarfasa don ya haura minti talatin da jonawa, tana xaukar ruwan a bayan kujerar da yake zaune ta xaga bokotin ta sheqa mishi tun daga tsakiyar kanshi ba tare da ya ankara ba.
Raxaxin da ya ji tun da ga tsakiya kanshi zuwa sassan jikinsa yasa ya qwallah gifitaccen qara saboda azaba, second goma tsakani ya sume akan kujerar sai a lokacin ta ji dana sani mai tsanani ya mamaye zuciyarta jikinta ba inda ba ya rawa saboda tsabar tsoro.
Tsawon minti biyar ta rasa waqar farawa sai kuka take tana safa da marwa a tsakiyar falon, daga qarshe ta yanke shawarar kiran number wayar Alhajin, kuka kawai take a wayar tana faxin Alhaji Nasir ne…..”
“Me ya faru da Nasir din…..?” Ya tambaye ta hankalinshi a tashe.
Ta kasa furta komai bayan sai kuka daga bisani ta jefar da wayar ta ruga cikin xaki ta kulle kanta.
Duk inda aka tava a jikinshi savewa yake yi, gaba xaya likitocin sun taru akanshi don qoqarin ceto rayuwarshi.
Alhaji Muhammad yana jikin qofar hankalinshi a matuqar tashe, Nasir kawai ya samu a sume akan kushin duk jikinshi a jiqe da ruwa ba Fatima a gidan ba alamar ta, sai da ya kama hannun Nasir yaga ya saluve fatarshi sannan hankalishi ya qara mummunan tashi da taimakon Allah dana Drivern da ya kawo shi daga Office suka kama Nasir duk jikinshi a qone zuwa asibiti tswon minti talatin kenan likitoci suna cikin xakin da aka kaishi amma har yanzu ba wanda ya fito.
“Kaine mahaifinshi ko?” wani siririn likita daya fito daga xakin ya katsewa Alhaji Muhammad tunanin da yake yi. “Qwarai kuwa" ya amsa yana gyaxa kai don qara tabbatar da abinda ya faxa.
“Biyoni ciki don tunda ya farfaxo yake roqon a kira mishi Daddy”
Duniya ba komai ba ce, duk wanda bai ji tsoron Allah ba ya shiga uku cikin lokacin da bai wuce awa xaya ba Ubangiji ya canzawa Nasir halittan jikinshi yana kwance tamkar gawa. Daqyar ya yi qarfin halin faxawa mahaifinshi cewa:-
"Fatima … Fati ce … tamin haka!!! Saboda… saboda …” Allah bai bashi ikon qara faxin koda kalma guda ba bayan haka Mala’ikan zare rai ya zare mishi ranshi.
Cikin kuka Daddy ya ke xaukarwa kanshi alqawarin ko zai yi yawo tsirara sayya xaukar mishi fansa, bai iya haqurin ankai Nasir ma kwancinsa na gaskiya ba sai da ya danqa Fatima a hannun ‘yan sanda. Bayan angama addu’ar bakwai aka turasu kotu, Alhaji Musa qanin mahaifinta ya bita har gidan Prison ya yi mata “Allah ya isa rainon da ya yi mata ya qi bata dama kokaxan tayi mishi bayanin yanda abin ya faru, kuma ya qara tabbatar mata da cewa bashi ba ita har abada.
A wannan ranar ne Fatima ta yanke qauna da rayuwar duniya, shi ya sa ko da aka shiga kotu bayan amsa laifinta babu wani qarin bayanin da ta yi har zuwa yau da aka yanke mata hukunci.
***
Na xago idanuna daga kan wayar ina kallon fuskokin ‘yan matan da dukkansu hawaye suke saboda tsananin tausayawa Fatima, Idanuna abushe suke qamas, babu ko alamar hawaye amma zuciyata suya kawai ta ke saboda tsananin takaicin halin maza da mugunta irin tasu.
“Wannan labarin ka xan kenan daga cikin rashin adalci irinna maza, kunga dai A DALILIN XA NAMIJI ta shiga cikin uqubar daya janyo za ta qare rayuwarta a gidan yari, shi yasa a kullum nake qara fada muku maza azzalumai ne! Tsakanin mu da maza ba sani ba sabo, duk wacce takeso rayuwarta yazo qarshe ta qulla dangantaka da Xa namiji, zamu gudanar da kyakykyawar rayuwa ba tare da Namiji ba, kuma ko a gurin Allah ba laifi bane.”
“Qwarai kuwa ‘yar uwa Aysha”
Dukkan su suka haxa baki gurin faxin haka cikin nuna gamsuwa da maganganu na.
Dayar wayar tawa na janyo na buxe saqon da aka turo min daga 7777.
“ZAKU KAI HARI GA GIDAN YARIN DA AKA AJIYE FATIMA”
Abinda aka rubuta kenan da manyan baqi a saman saqon, da qarfi na karanta don sauran ‘yan matan suji abinda ya qunsa.
"Gidan yari ne da ake ajiye mata a hanyar da mutane da suke bi idan zasu je Abuja daga Kaduna, akwai masu gadi da makami a hannunsu su biyu daga qofar get xin gidan yarin, katangar gidan yana da matuqar tsawo ya wuce ace za’a haura ko kuma a dira, koda da tsani ne za’a xauki tsawon lokaci don haka ta get xin zaku shiga bayan kun janye hankalin masu gadin ko da ta hanyar sumar dasu ne. Xakuna ne a jere sama da guda xari cikin gidan, ako wani xaki ana zuba mata su goma sha biyar duk da qanqantar xakin, akwai jami’an tsaro guda goma sha biyar daga gaban xakunan, duk wani shige da fice na masu laifin akan idonsu suke yi, babu wata hanya da zaku iya fitar da Fatima face sai kun fafata da jami’an tsaron, idan kukai amfani da hikima zaku ya xauke hankalinsu har ku cimma burinku. Xaki mai lamba 87 anan aka ajiye Fatima abayan rigar ta an rubuta lamba 268, da farko zata yi muku gardama kan cewa ba zata biyoku ba tunda ba ta san ku ba.
To dukkanku ku juya mata bayan rigar ku taga tambarinku, ku da ita daga yau ta zama ‘yar uwarku, duk matsalarku iri xaya ne A DALILIN XA NAMIJI kuka tsinci kanku a halin da kuke ciki.
zaku fita da misalin qarfe goma sha biyu da rabi na dare, ku lazimci karanta “HAZBUNALLAHU WA NI’AIMAL WAKEEL” don samun nasara kamar yanda ku ka saba."
Iyakar abinda na saqon ya qunsa kenan don haka ban tsaya vata lokaci ba na janyo dayar wayar na buxe saqon da aka turomin a cikinta daga Number 7777.
“GAREKI AYSHA AZZAHRA’U”
Ganin hakan da aka rubuta ya tabbatar min da saqon zuwa gareni ne kaxai banda ‘yan matan, don haka na fara karantawa a zuciyata, “Ki tashi da misalin qarfe sha biyu da kwata lokacin da ya rage minti goma sha biyar ku fita, ki xauro alwalarki sannan ki tada sallar nafila raka’a biyu ki karanta fatiha da ko wacce irin sura bayan kinyi sallama ki xaga hannun ki izuwa sama ki yi wannan addu’ar “Allahumma inni as’aluka bi anna lakal hamdu la’ilaha illa antal Hannanul Mannanul badi’us samawati wal aradi zuljalalu wal ikhram.” Sannan ki roqi Allah nasara a kan fitar da zakuyi sai ku kama hanya. Muna bayanku ni da ‘yar uwata, kuma mu na muku fatan NASARA"
qarshen saqon kenan don haka na ajiye wayar ina kallon sauran ‘yan uwana. “Da fatan dukkanku kun fahimci yanda fitar tamu zata kasance?”
“Qwarai kuwa" suka amsa gaba xaya.
“Ubangiji ya bamu sa’a.”
“Amin summa Amin" suka amsa gaba xaya cikin samun qwarin gwiwa.
“Barkan ku da yammaci… Jummala mai dafa mana abinci dattijuwa ‘yar shekara talatin da takwas ta faxi hakan bayan tayi sallama an amsa mata ta shigo cikin falon.
“Barkanmu dai Baba sannu da qoqari” muka amsa a tare fuskata xauke da murmushi, da sauri na qarasa gareta na xan durqusa na karbi kular hannunta na xora a kan Dining table.
“Sannu Aysha Allah ya miki albarka.”
“Amin summa Amin Baba” na amsa cikin jin daxi don ganinta nake tamkar mahaifiyata, kusa da ita na koma na tsugunna kusa da qafa funta murya a sanyaye nace,
"Baba yau muna da fita da daddare muna da buqatar addu’ar ki.”
“Allah ya baku sa’a Allah ya kareku daga dukkanin abun qi, mutum da aljan.”
“Amin summa Amin”
wannan karon dukkanmu muka amsa.”
Idona ne ya faxa akan agogo qarfe bakwai da kwata na dare, “Subahannalahi” na furta don ganin har lokacin sallar Magariba ya wuce bamu gabatar ba ga Isha’i ta kusanto,
"ya kamata mu gaggauta mu gabatar da sallah kafin mu faxa fushin Allah.”
“Baba barin shiga ciki inyi sallah”
na faxi hakan ina kallonta ba tare da na saurari amsarta ba na wuce da sassarfa zuwa cikin xakina.
“A fito lafiya Aysha.”
Na jiyo muryarta ta na faxin haka.
Babban teburin cin abinci ne wanda yake zagaye da qana nan kujeru har guda ishirin manyan kulolin abinci ne har guda uku akai, gefe guda kuwa da qananan farantai guda goma sha biyu. Cokula da abin xiban abinci suma jeri a wani xan qaramin kwando, lemuka kala daban daban da Kofuna da ruwan gora ajiye a gefe daya.
muna zaune akan Dining xin mu takwas har da Baba mai dafa abinci. Bisimillah na fara yi sannan na sanya hannuna na buxe kulolin abincin, qamshin da ya bugi hancinmu nace, “Waw! Yau wani abin daxin aka shirya mana Baba?”
Tana dariya ta ce,
“Ya dai idon naki Aysha? Sa mai ganin da kyau kiga me yake badadeki da qamshi?”
Fried rice ne a babban kulan wanda ya sha kayan haxi kuma ya yi kyan dafuwa sai zabga qamshi yake, a kula ta biyu kuma farfesun kayan ciki ne shima sai tashin qamshi Citta da Curry da Thyme yake yi, a kula ta uku kuma farfesun kan rago ne shima sai fidda nashi kalar qamshin yake.
Murmushi na qawata fuskata dashi na ce, “Ubangiji Allah ka qarawa Baba lafiya mu ci gaba da sharvan lagwadan girke girke.” Dukkan su suka qyalqyale da dariya sannan suka amsa da amin.
“Indai har da gaske abincin ya qayatar da ke ina qaunar ganin duk abinda na dafa ki zuba a flet kin cinye…”
Baba ce ta faxi hakan tana kallona ido cikin ido don ta ji me zance, dariya nayi cikin salon basarwa sannan na xauki flet na zuba kayan ciki kaxan na ce,
“Kin san yau munada fita Baba bai kamata in cika cikina in kasa hassala komai ba.”
“Yan mata bisimillah ko wacce ta zuba abinda take bukata"
ina gama faxin haka nai bisimillah na fara cin abinda na zuba.
Murmushi kawai Baba tayi sannan ta zuba abinci ta fara ci, tsawon awa guda muna kan Dining xin duk da na gama cin kayan cikin tuni, bisa ga al’adata bana tashi akan Dining in bar ‘yan uwana, ko na gama nakan zauna inci gaba da danne dannen wayata har sai dukkan su sun gama sannan mu tashi gaba xaya.
Safiyya da Rahma ne suka fara tattara kwanukan da mukai amfani da su zuwa kiching sannan suka goge gurin.
muna zaune a tsakar falo dukkanmu Baba ce kawai akan kushin bisa ga al’adarmu idan akwai fitar da zamuyi a ranar ko T.V bama kunnawa. Yau ma hakan ta kasance, muna riqe da casbaha a hannayen mu muna jan “HASBUNALLAHU WANI’IMAL WAKIL” har lokacin da agogo ya buga qarfe goma sha biyu na dare.
“Qarfe goma sha biyu da rabi zamu fita, ya kamata mu je mu shirya.”
Ina gama faxin haka na shige cikin xakina, suma duk suka nufi xakunan su don shiryawa.
Wanka na fara yi wanda ya xaukeni tsawon minti goma sannan na xauro alwala sha biyu da kwata daidai na tada kabbara sallah. Tsawon minti goma ina roqon Allah nasara akan ceto rayuwar baiwar Allah Fatima da zamuje, saura minti biyar na fara saka kayana. Wando ne na jeans mai xauke da manyan aljihu har guda shida, abaya akwai biyu ta gaba gurin cinyoyina akwai guda biyu, gefe da gefe akwai guda biyu, ‘yar qaramar T.shit na xauko na sanya bayan na tamke kirjina a cikin brezian da ya yi matuqar kamani, powder kawai na shafa a fuskata na sanya man baki sannan na kama suman kaina na nannaxe shi na xaure da rebom. Drower gefen gadona na buxe sai ga bundigogi kala-kala a ciki.
Qanana na xauka guda huxu na saka biyu a aljihun wandona na baya, na saka biyu a aljihun gefe da gefe. Wata riga mai kama da leda dake ajiye akan gadona na xauka na wareta na sanya, rigar tana da xan tsawo don ta rufe quguna dana adana makamai na. a bayan rigar rubutu ne qanana anyisu da Golden Color idan ba kusa dakai na matsa ba bazaka iya gane abinda aka rubuta ba.
Hula ta na xauka asaman akwati na sanya a kaina, sai na xauki wani baqin gilashi na aje a gefena, takalmi na xauka na zura a qafafuna na xaure igiyar tamau yadda duk rintsi bazai tava kwancewa ba, gilashin na riqe a hannuna na fito da sauri zuwa falo idona kan agogo qarfe goma sha biyu da rabi da minti xaya.
“MATAN FAMA kenan”
Nai musu kirarin da ya sanya su sakin murmushi dukkan su suna sanye da riga da wando, da takalmi shigen na qafa ta kala ne kawai ya bambanta sun xora rigar mai kaman ta leda a jikinsu irin nawa, amma savanin nawa da akai rubutu da ruwan gwal su nasu farin rubutu aka yi, suna sanye da gilashi baqi wanda ya kusa mamaye rabin fuskarsu.
Baba ta na zaune kan kushin jikinta sanye da babban hijabi, hannunta riqe da casbaha da alamu sallah ta idar.
“Baba za mu tafi.”
Na faxi hakan bayan na durqusa a gabanta. “Allah ya bada sa’a Ubangiji yasa ku dace da abinda zaku fita nema.”
“Amin summa Amin” muka amsa gaba xaya cikin qwarin gwiwa.
Babbar mota ce Jeep kirar sienna, duk sanda zamu yi irin wannan fitar na gaba xayan mu a ita muke fita. Sadiya, Nafisa Siyamah su suka zauna a kujerar baya na motar, Suhaila Rahma su suka zauna a kujerar tsakiya na motar, Safiyya ta zauna a mazaunin Driver ni kuma na zauna a gefenta sai da ta karanto addu’ar hawa abin hawa sannan tayi bisimillah ta tada motar.
Baba ce ta buxe mana get xin gidan muna ficewa ta maida get xin ta rufe ta kulle.
Tafiyar minti ashirin ta kawo mu hanyar da zamu sauka daga kan babban titin zuwa Prison xin, tun daga can nesa nai mata umarni ta yi Parking xin motar a gurin, muna fita ta kulle motar muka fara tafiya a qafa, hasken tocilan da muke hangowa acan nesa damu shi ya ba mu tabbacin masu gadin gidan ne su ke aikinsu.
Tsayawa na yi cak! Suma sauran ‘yan uwana sai suka tsaya a guri xaya, haxa kawunan mu mu ka yi nayi musu raxar abinda za mu yi sannan na xauki hanya na shige cikin daji da Tochlight a hannuna.
Su kuma suka fara sanxa suna qara kusantar gidan.
Gudu nake yi iya kacin qarfina ina taka busassun ganyayyaki da takalman qafata, idan da idan da sabo na rigada na saba da keta daji komai tsawon dare haka babu tsoro ko kaxan a tare dani, sai da nayi gudu mai yawa na zagaya gidan yarin ta can baya sannan na ciro bindiga ta na harba sama ta bada qara “Dam!” minti biyu tsakani na sake danna kunamar bindigar zuwa sararin samaniya. Harbin da nai na farko shi ya fara janye hankalin masu gadin suka fara waige waige suna qara dallara hasken tocilar su da gyara riqon bindiga qirar Single barrack xin da take hannun su.
“Kamar ta bayan gidan nan akai harbin nan ko? daya daga cikin masu gadin ya tambayi 'yan uwansa, Bai samu sararin a je numfashin maganar shi ba balle har dayan ya ba shi amsa suka qara ji yo wani qarar harbin, ba su qara tankawa junansu ba suka rabu zuwa inda suke da tabbacin harbin ya fito, daya ya bi hanyar dama, dayan kuma yabi hanyar hagu, da sauri na ajr tocilan hannuna a jikin wani dan itaciya yana haska gidan yarin yanda duk wanda ya biyo ta bayan gidan zai iya hango hasken. Daya ne ya fara qarasowa kafin ya ankara na lallaba ta bayan shi na buga masa kan bindiga a kunnenshi, shu…. Ya tafi zuwa qasa idanunshi suna rufewa suna budewa saboda azaba.
Kafin ya dawo hayyacinshi na shaqa mishi wata farar hoda wanda na karba a hannun Sadiya, daga can nesa na ji alamar tahowar daya mai gadin don haka na sulale na kwanta a cikin ganyayyaki.
Idanunshi da tocilan hannunshi can nesa suke haskawa don bayyi tsammanin wani zai kwanta a gurin ba, qafata na sanya na tade shi ya hantsila can gefe bindigar hannunshi ma tayi can gefe daya, kafin yayi yunqurin tashi na sanya qafata na buga mishi naushi a ciki, runtse ido yayi saboda tsananin zafi kafin ya bude na shaqa mishi hodar hannuna.
Tocilan na dauka na haska fuskar mai gadin da ya fara isowa gurin barci yake hankali kwance, amma wanda bai sani ba sai ya yi tsammanin mutuwa ya yi, ban saurari dayan ba don nasan shima yanzu barcin zai dauke shi, na qara matsawa jikin gidan yarin kadan, harbi na fara sakewa ina bada tazarar minti biyu tsakani sai da nai harbi hudu, qarar harbe-harben shi ya gigita hankalin jami’an tsaron da suke cikin gidan don sun tabbatar ba lafiya ba, duk tsammaninsu ya tafi kan cewa ‘yan fashi ne suka biyo wani da yake neman tserewa har kusa da gidan yarin, don hakan ya sha faruwa basau daya ba ba sau biyu ba.
Jin da sukayi harbin yakika qarewa ya sa suka fito da gudu dukkansu don ganin me yake faruwa. Su Rahma suma suna kwance a cikin ganyayyaki kamar yadda muka tsara, kafin jami’an tsaron su ankara aka ringa zarge qafafunsu da igiya ba tare da suna ganin masu musu wannan daurin talalar ba.
Sun samu nasarar zarge qafafun mutum tara, yayin da mutum shidda suka ankara da abinda yake faruwa.
Kin qarasawa gurin suka yi don gudun afkawa tarkon da sauran ‘yan’uwansu suka afka, Daga nesa suke haska gurin da tocilan hannunsu amma ba su ga komai ba sai ‘yan uwansu a kwance. Ga makamansu duk sun faxa gefe guda, a tsorace suka cigaba da haskawa suna harbe-harbe a iska.
Ta jikin katangar nake leqan abinda yake faruwa, ganin suna bata mana lokaci yasa na yi bismillah na saita qafafun mutum biyu daga cikinsu na harbe su a qafa da bindigogin da sike riqe a hannuna dama da hagu.
Nayi nasarar samun su, hakan ne ya ankarar da sauran mutum hudun daga inda harbin ya fito, wani ragon azanci da suka yi sai dukkansu suka biyo bangaren katangar da nake cikin sanda suna haska tocila, su Rahma ne suka miqe da hanzari suka dauki bindigogin ‘yansandan da suke kwance suna kici-kicin kwance qafafunsu suka harbi ‘yan sandan a qafafunsu ba tare da sun ankara ba.
Da sauri duk muka bi su muka shaqa musu hodar da take hannun Sadiya minti biyu tsakani nannauyan barci ya yi awon gaba da su. Mu kuma muka shiga cikin gidan hankali kwance. Don muna da tabbacin ba za su farka ba sai sun xauki tsawon awa goma sha biyu suna barci.
Mabudi ne da yake bude kowane irin kwado mukayi amfani dashi gurin bude dakin da take ciki, don haka ba mu sha wahalar bude dakin ba, suna tsaye cirko-cirko tamkar kajin da suke fada Sun tsaya maida numfashi.
Ganin shigowarmu ya sa suka nufo mu suna zazzaro ido. Kallon sakan biyar ya ratsa tsakaninmu, da alamun mamakin yadda muka shigo cikin gidan har muka bude dakin da suke ciki, ba tare da mun fuskanci matsala daga masu gadin gidan ba suke yi,mu kuma kallonsu muke don tanrance wace ce Fatima a cikinsu? Can kusurwar dakin na hangi wata ta takura kanta a tsakanin cinyoyinta.
Da hanzari na nufi gurinta don jikina na ba ni tabbacin ita ce Fatima. Hannu na sa na dafa kafadarta bayan na durqusa kusa da ita.
Da sauri ta dago kanta a dan firgice take kallo na sannan ta maida dubanta zuwa ga su Safiyya.
“Wace ce ke? Ku su waye?" Ta tambayi hakan bakinta na rasa, idanunta a warwaje, wadanda suka kumbura kuma suka rine zuwa jajaye, saboda tsabar kuka.
“Mu ‘yan’uwanki ne, kuma mun zo mu tafi da ke ne.” Na fada mata hakan da tattausar murya don in kwantar mata da hankali.
Kallo ta bi ni da shi na rashin yarda da abinda na fada. Dagabisani kuma ta ce “Ban san ku ba, don haka ba zan taba bin ku ba. ku bar ni kawai. Haka Allah ya qaddara zan qarasa rayuwata a gidan yari…”
tana gama fadinn haka ta fashe da kuka, sannan ta qara maida kanta tsakanin cinyoyinta, kamar yadda muka tarar da ita da farko.
Muna da tabbacin za mu fuskanci tirjiya daga gare ta, don haka ranmu bai vaci ba ko kadan. Da yatsu biyu na kira su Rahma zuwa gare mu, sannan na qara dafa kafadarta a karo na biyu. Hawaye ne wasu na korar wasu tamkar ruwa suke bin kyakkyawar fuskarta. Ban ba ta damar fadin komai ba nace, “Ga wannan tocilan ki haska bayan rigarmu ki ga me aka rubuta.” Na miqa mata tocilan hannuna, sannan duk muka jujjuya bayan rigarmu zuwa gare ta.
Tsawon minti uku kafin na jiyo muryarta na faxin, “na amince zan bi ku.”
Da matuqar murna na rungume ta, sannan na kama hannunta duk muka nufi hanyar ficewa daga dakin.
“Ku taimaka don Allah ku fitar da mu gaba daya.”
Muka jiyo muryar wasu daga cikin fursunonin suna fadin haka.
“Kofa a bude take ga duk wanda ya yi niyyar fita, amma mu dai ga wacce muka zo dauka nan.” Ina gama fadin haka muka fice da sauri don ganin lokaci yana dad'a qurewa.
Karfe uku da minti biyu muka isa gida, Sadiya ce ta dauki dan muqullin qofar get din a cikin mota ta bude mana aka shiga da motar. Baba tana zaune a falo kamar yadda ta saba idan muka fita komai tsawon dare bata kwanciya barci sai ta ga dawowarmu, Yau ma hakan ce ta kasance. Tana zaune da casbaha a hannunta tana lazumi muka shiga cikin falon.
Fatima ta nufa kai tsaye bayan ta amsa sallamarmu, da fara’arta ta tarbe ta sannan ta yi mana barka da zuwa.
“Abinci kike buqata, ko wanka za ki fara yi ko sallah?” Duk na jera mata wadannan tambayoyin ina kallon ta cikin kulawa.
“Wanka da sallah.” Ta amsa muryarta a sanyaye.
“Rahma a kai ta dakina a ba ta duk abin da za ta buqata.” Na fadi haka bayan na zube a kujera ina lumshe idanu.
Suna wucewa na kalli Baba, “Baba a jera mata abinci a dinning in ya so kowa sai ya je ya kwanta.”
“An gama Ranki ya dade.” Ta fad'a da tsokana don ta san na tsani wannan sunan.
Murmushi na yi ina kara gyara kwanciya a kan kujera mazaunin mutum uku.
“Sannu da aiki ranki ya dad'e, mu kwana lafiya.” Na fad'a wa Baba hakan bayan na lura ta gama jera ma Fati duk abinda za ta buqata.
“Kin rama kenan?” ta fad'a tana dariya.
Shiru na yi mata ina motsa baki. Ganin haka yasa sum-sum-sum ta wuce zuwa dakinta. Sauran ‘yanmatan ma duk sallama suka yi min. ina amsa musu da kai suka wuce dakinansu.
Tsawon minti talatin da biyar ta dauka kafin ta fito zuwa falon tana sanye da jallabiya baqa wacce ta yi matuqar dacewa da farar fatarta.
“Kin fito? Barka da fitowa…” na fadi hakan idanuna a rufe. Ban bari tace komai ba na ci gaba da cewa, “Ga abinci can a kan dinning, idan akwai abinda kike buqata ki yi magana.” Na fadi ina mata ishara da inda dinning table din yake.
Tun fitowarta ta lura da idanuna a rufe suke, a zatonta barci na ke yi, jin na yi magana ya bata tabbacin idanuna biyu. Isharar da na yi mata ina daga kwance ya daure mata kai, sai ta ja ta tsaya ba tare da ta yi gaba ko baya ba.
Tsawon minti biyu tana kallo na, ba tare da ta furta komai ba.
“Ki je ki ci abinci mana, dare yana qara yi fa. Idan kuma kin qoshi mu je mu kwanta.” Na fadi duk da haka idanuna suna rufe.
Qafafunta har hardewa suke gurin zuwa dining din, don al’amarin ya fara ba ta tsoro. Tsattsakar abincin ta yi ta sha lemo kadan, daga inda take zaune ta furta a ciki. “Na qoshi.” Wanda tana da tabbacin ban ji abinda ta ce ba.
“Toh, mu je dakin da kika yi wanka mu kwanta.” Na fada ba tare da na tashi ko na bude idanuna ba.
“Na shiga uku ni Fatima!” ta fada a zuciyarta, kuma a tsorace, Allah yasa dai ba gidan Aljanu na Kawo kaina ba"
Murmushi nayi, don ganin tana neman sa wa zuciyarta kokwanto a kanmu, yasa nace, "Ba gidan aljanu bane, mutane ne 'yan uwanki"
Tsananin tsoro ne ya sake cika mata ciki, hannu biyu tasa ta dafe kirjinta,
“Taya aka yi kika san abinda na fada a zuciyata?”
Wannan karon sai da na qyalqyale da dariya mai isa ta, sannan na ce “Sanin abinda yake zciyar wani sai Ubangijin da ya halicce mu Fatima, kar ki gurbata imaninki mana.” Na fada mata hakan, amma har lokacin ban bude idona ba.
Kallo na take ta rasa abinda za ta furta saboda rudanin da na jefa ta a ciki. Ta buxe baki kenan za ta sake magana na dora dan yatsa manuniya a baki na ce “Shiiii….!!! Kar ki tsananta magana Fatima, ina miki rantsuwa da Alllah mu ba masu cutarwa ba ne gareki, saboda haka ki kwantar da hankalinki karki tsananta magana kan duk wani abinda zaki gani a tare dani. Ki tashi ki shiga ciki ki kwanta nima yanzu zan shigo.”
Ina gama fadin haka na juya mata baya idanuna a rufe. Tana son ta qara magana amma bakinta ya kasa furta komai, tamkar an daure mata bakin don haka ta lallaba ta miqe zuwa dakin da ta yi wanka wanda tun farko ta ji na fadi mallakina ne.
Minti goma tsakani na bi bayanta, jikina ya bani idonta biyu don haka ban kalli inda ta ke kwance ba, bandaki na shiga na dauro alwala, ina fitowa na dauki doguwar riga ta akan daddumar sallah na koma ban dakin na sanya.
duk abinda nake idanunta na kaina har na ta da sallar nafila lokacin agogo ya buga qarfe hudu da rabi na dare, Ina zaune ina lazimi da casbaha a hannuna har aka kira sallar asubah, tashin Fatima na yi a lokacin har barci mai nauyi ya dauke ta.
Ban tashi daga kan daddumar ba sai qarfe bakwai na safe, “Kin ta shi lafiya?” Na fadi hakan ina kallon ta bayan na fara gajiya da kallon da take bi na da shi tunda ta idar da sallar asubahi. A zatona barci za ta koma amma sia na ga ta ci gaba da zama a gefen gado.
Gyada kai kawai nayi, sannan na janyo wata ‘yar qaramar akwati a qarqashin gadon, budewa na yi cikin nutsuwa na fara ciro wasu qananan kwalabe a ciki.
“Idan kwai abinda kike buqata kina iya tambayar duk wanda kika gani cikin gidan nan. Zan yi barci… idan za ki yi kallo ki fita falo.” Na fadi haka ina kallon Fatima ido cikin ido.
Kai kawai ta daga a maimakon buda baki, ta ba ni amsa. Ban damu ba na bude kwalba daya daga cikin kwalaban na shanye ruwan ciki, Sai da nasha kwalabe uku, sannan na dauko wata qwaya na sanya a bakina na taune na hadiye ba tare da na kora ruwa ba.
Kadan kadan idanuna suka lumshewa suna budewa nan da nan na fara ganin komai hurhudu, Don haka na gyara kwanciya a kan gadon na juya wa kwalaben da na gama amfani da su baya.
“Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un!” abinda farima ta furta kenan hankalinta a tashe, tana kallon na yi daidai ina barci a kan gadon. Sadaf-sadaf ta tashi daga inda take zaune har zuwa gurin kwalaben.
Benelyn, Totalyn, sunayen da aka rubuta a jikin kwalaben kenan. A hankali ta janyo akwation ta bude, Abubuwan da suke ciki suka yi matuqar tayar mata da hankali. Kayan maye ne wadanda ba ta san iyakarsu ba a ciki, Qwayar da ta ga na tauna ba tare da ruwa ba, qwayar roci ne. jikinta a sanyaye ta rufe akwatin ta mayar inda ta dauko.
Kallo na take tsawon daqiqun da ba ta san iyakarsu ba, Fatima ta raya a ranta, kyakkyawa ce ni ta gaban kwatance, ta lura ba na jerin baqaqen mata, amma kuma ni ba fara ba ce. Kuma na fi kalar chakulet haske. Wani irin haske fatata take dauke da shi mai matuqar daukar hankali.
Ba ni a cikin jerin mata masu qiba, amma ni ba siririya ba ce, dukiyar fulanin da suke tsaye kyam kuma cikakku a qirjina shi ne abinda yake kara fisgar hankalin maza da mata a fuk lokacin da na fita sanye da qanana kaya (English wears). Cikina a dame yake tamkar ba na cin abinci.
Ina da yalwataccen qugu mai firgita hankalin duk wani lafiyayyen namiji. Gaba daya a jikina babu wani abu na kushe, sai dai ga hasidin iza hasadin. Dara-daran idanuna wadanda har ‘yan uwana mata daukar hankalinsu suke, ga wani irin lumshewa da suke a duk bayan second hudu, wanda wasu suke tsammanin gayu ne irin nawa, amma haka Allah ya halicce ni.
A fuskata za ka gane ni din qaramar yarinya ce, a tunanin Fatima idan na yi wuta in kai shekaru sha bakwai. Ba ta tunanin zan dara haka ko kadan. A dan fahimtar da ta yi mana duk sauran ‘yan matan gidan sun girme ni.
"Idan akwai kuskure a hasashena ai zan tabbatar tunda ina gidan.”
Ta fadi hakan a zuciyarta. A dan fahimtar da a yi min daga daren jiya zuwa safiyar yau ni yarinya ce mai tsananin ibada, don ta lura tun daren jiya ban bar kan darduma ba saida na je jikin gadon na tashe ta ta yi sallar asubahi. Ina tashin ta kan dardumar na koma. Sannan na dauki tsawon awa daya da rabi ina karatun Alqur’ani mai girma bayan na idar da sallar asubahi.
Abinda ya daure mata kai a game da ni shi ne abinda ya faru tsakanina da ita a daren jiya, da kuma rayuwar shan kayan mayen da na daukar wa kaina ina ‘yar qaramar yarinya. Babbar matsalar shi ne, na yi mata kashedi a kan duk abinda za ta gani a tare da ni.
“Amma… a juri zuwa rafi…”
Tana fadin haka ta janyo bargo ta lulluba min, cikin tausayi da qauna ta da take ji a zuciyarta. Karatun Alqur’ani ta jiyo yana tashi cikin tattausan sautin muryar “Ahmad Sulaiman” a falo, don haka ta nufi can.
Duk su shidan da bata san sunayensu ba in banda “Rahma” da taji na kira sunanta jiya, sai kuma “Baba” da na ba ta umarnin ta shirya mata abinci a jiya, suna zazzaune a kan kujeru daban-daban.
Har qasa ta tsuguna ta gaida Baba, ta amsa mata da fara’a har tana tsokanar ta; “Ya kuwanan baqunta?”
Murmushi kawai ta yi sannan ta yi jam’in gaida su gaba daya.
“Akwai abinda kike buqata ne?” Safiyya ta tambaye ta tana kallon ta cikin kulawa.
“Alhamdulillahi, ba na buqatar komai, na gode.” Ta mai da mata da amsar hakan bayan ta fadada fuskarta da murmushi.
Qarfe ara da rabi Baba ta gama hada kayan karin kumallo a kan dinning table, suna zazzaune akan qananan kujeru zagaye da babban teburin da aka shirya kayan abinci. Kowa a cikinsu qoqarin hada kumallonshi yake yi, sabanin ita da ta zabga tagumi hannu bibbiyu.
Abinda ya kara bata mamaki har ya sanya ta tagumi shi ne ganin dukkaninsu babu wanda ya damu ya duba yadda na tashi. Kuma ko ita da muka kwana muka tashi daki daya ba su tambaye ta ya nake ba, qoqarin cika cikinsu kawai suke yi bayan kuma a yadda ta lura nice shigaba a cikinsu.
“Ya dai Fatima? Ko kina buqata wani abin karyawar ne daban?” Baba ce ta yi mata wanan tamvayar da damuwa a fuskarta, ganin kowa yana cin abinci amma ban da ita.
“A’a, ..yanzu zan hada nawa” Ta amsa tana qoqarin bude gwangwanin madara da cokalin hannunta.
***
Sanye nake da singlieti fara wacce ta yi matuqar dacewa da fatar jikina, wando na sanya three-quarter amma yana da fadi bai kama min jiki ba, duk wani lungu da saqo na jikina fidda kalar qamshi daban yake yi don haka zai yi wuya mutum ya iya tantance wane irin turare na fesa.
Qarfe sha daya da minti arba’in da biyar agogon falon ya nuna min. tsawon awa hudu ina barci, Minti arba’in da biyar kuma na dauka gurin wanka da shiryawa, Ganin fitowata falon ya sa dukkansu gyara zama suna min barka da fitowa.
Gaban Baba na wuce na tsuguna har kasa na gaisheta sannan na nemi gurin zama.
Hada baki suka yi gurin gaishe ni, na amsa da murmushin da bai cika yankewa a fuskata ba. “Ya dai Fatima? Ina fatan baki takura ba?” na tambayeta bayan na lura da kallon da take ta bina dashi tun bayan fitowa ta.
“Kin tashi lafiya?” abin da ta tambayeni kenan, ta share waccen tambayar da na yi mata.
“Alhamdulillah.” Na amsa mata ina dan dariya don in kara kwantar da hankalinta.
“Sadiya taimaka ki hada min ruwan lipton. Rahama bani remot din T.V pls.”
Da sauri suka miqe don cika umarnin da na basu duk da na yi umarnin ne cikin salon roqo.
“Zamu fita yammacin yau don samawa Fatima duk abinda zata buqata, so kowa ya kasance cikin shiri zuwa qarfe biyar na yamma. Fatima ki yi lis din duk abinda kike buqata.”
“Toh! Na gode, qwarai.” Ta amsa min.
"GA CIKAKKUN LABARAN DUNIYA..
A jiya da daddare ne wasu ‘yan bindiga mata da ba a san ko su waye ba suka kai hari wa gidan yarin da yake hanyar Kaduna zuwa Abuja, Sun yi amfani da bindiga gurin harbin qafafun mutum shida daga cikin jami’an tsaron da suke gidan, sannan suka zarge qafafun mutum tara daga cikin jami’an tsaron, mutum biyu kuma a can bayan gidan aka gansu kwance suna sharar barci sakamakon hoda mai sanya nannauyar barci da ‘yan matan sukayi amfani dashi.
Sunbi jami'an tsaron gaba daya sun shaka musu hodar, hakan yasa har yanzu da suke kwance a kan gadon asibiti na SALAMAT ba su san inda kansu yake ba.
‘Yan bindigan dai ko da suka sami nasarar shiga gidan basu dauki kowa ba sai wannan mai laifin Fatima Ibrahim wacce aka kaita gidan a yammacin jiya, sun yi amfani da dan mabudi mai lalata ko wani irin kwado ne gurin bude qofar dakin da fursunan take, kuma sunyi umarni ga duk matan dakin su kama gabansu idan suna buqata.
Wata mata mai suna Hajara Musa daga cikin fursunonin da suka fice daga dakin amma ba ta yi nisa ba ta suma a hanya ita ce ta bayyana hakan bayan farfadwarta, ga yanda ta bayyanawa wakilanmu faruwar al’amarin.
(Take aka dallaro hoton fursunan a fuskar talabijin)
Dan jaridan ne ya fara tambayarta da cewa,
“Ya sunan malamar?”
“Hajara Musa.” Da alamun galabaita a muryarta, fuskarta da jikinta ma sun nuna gajiyawa.
“Ya aka yi wannan al’amarin ya faru tunda kina cikin fursunonin da komai ya faru a gabansu?”
“Muna cikin barci muka fara jiyo harbin bindiga daga can bayan gida, daga bisani kuma muka ji shiru, minti goma tsakani muka ci gaba da jin harbe-harben ba qaqqautawa, sai kuma can muka ji ana bude kwadon qofar dakin mu, tsananin tsaro yasa duk muka miqe tsaye, fursunar da aka kawo ta jiya ne kawai ba ta miqe ba, tana zaune tana kuka, wasu ‘yan mata muka gani sanye da riga da wando, sun rufe fuskarsu da manyan tabarau, kai tsaye gurin wacce take kukan suka nufa, sun dan yi maganganu a tsakaninsu daga bisani suka kama hannun junansu suka fice da ita.”
“Kun ji maganganun da suka yi da ita?”
“A’a, qasa-qasa suke magana.”
“Yanzu idan kika ga ‘yan bindigan za ki shaidasu?”
“A’a, lokacin a rude muke, ba zan iya gane fuskar ko daya daga cikinsu ba.”
“Su nawa ne ‘yan matan?”
“Ban yi tunanin qirga yawansu ba, amma a hasashe na za su kai su goma.”
“Me yasa duk sauran ‘yan dakinku suka gudu, kema kin yi niyyar guduwa Allah ne bai baki sa’a ba.”
Duqar da kanta ta yi na wasu ‘yan sakanni sannan ta dago hawaye na bin fuskarta ta ce, “Su suka ce duk mai buqatar gudu qofa a bude take.”
“Kin san hukuncin wanda ya yi yunqurin gudu daga gidan yari kuwa?”
Shiru ta yi ba ta amsa ba, bai gaji ba ya qara tambayarta da cewa “Tun tsawon wani lokaci kike zaune a gidan nan?”
“Watanni uku da suka wuce…”
“Me kika yi har aka yanke miki hukuncin zama a gidan yari?”
Shiru ba ta amsa ba (sai kuma suka dauke hoton hirar)
Wakilin namu ya sake zantawa da I.G na ‘yan sandan jihar Kaduna, in da ya tabbatarwa da wakilin namu cewa (nan take suka hasko hoton inspector general din tare da 'yan jaridu a cikin gidan yarin.
“Ranka ya dad'e me zaka iya cewa akan wannan abin da ya faru?”
“Wannan shi ne karo na farko da hakan ya tava faruwa da wannan gidan yarin, kuma abin mamaki ne qwarai da muka ji cewar mata ne ‘yan bingidan ba maza ba.”
“Ko akwai wani mataki da zaku dauka akan hakan?”
“Qwarai kuwa, akwai matakan da zamu dauka sosai kuwa.”
“Kamar wadanne irin matakai?”
“Farko dai mun qara ninka tsaro a cikin gidan da wajen gidan don ganin hakan bai qara faruwa ba, kuma mun baza ‘yan sandan bincike na fararen kaya da masu kaki don bincike wadanda suka aikata wannan danyen aikin da kuma ita kanta mai laifin, ba don komai ba sai don mu miqasu a yanke musu hukuncin da doka ta tanadarwa masu laifi irin nasu.”
Yana gama fadin haka ya wuce ba tare da ya qara sauraron 'yan jaridar ba.
wadannan hotunan da zaku gani hotunan jami’an tsaron da harin ya afka kansu ne a kwance a gadajen asibiti, (Take aka dalla hotunansu kwance reras tamkar gawawwaki).."
Cire qarar T.V da muke kallon labaran na yi, sannan gaba dayanmu muka qyalqyale da dariya sabanin Fatima da tun dazu take hawaye.
Tsit! Muka tsaida dariyar da muke yi, lura da halin da ‘yar uwarmu take ciki, kusa da ita muka koma muka rarrsheta, nice na fara dafa kafadunta na ce,
“Haba Fatima, mene ne kuma abin kuka a wannan labari? Ko kina tsoron kar asirin mu ya tonu ne?”
Da hanzari ta daga kai wasu sabbin hawayen suna zuba shar.. Gwanin ban tausayi.
“Babu abinda zai faru da izinin Allah, ki kwantar da hankaliki, wannan ba shi ne hadari na farko da muka fara shiga ba kuma babu abin da yake faruwa.”
Na qarasa fadin haka ina shre mata hawaye, sai da muka tabbatar da ta sami nutsuwa sannan muka koma guraren zaman mu.
“Ban san sunayenku ba?” Fatima ta fadi hakan tana kallona ido cikin ido.
“Oh my God! Sorry ‘yar uwa.”
“Waccen da kike ganinta.” Na fadi hakan ina nuna Rahama, “Sunanta Rahama Muhammad labarinta a taqaice shi ne “Mijinta sun yi aure tun ba shi da komai, shekararsu biyar da aure Allah ya hore mishi arziki fiye da yanda ake zato, lokaci qanqani ya danqara mata takardar saki uku, a fadarshi ba zai zauna da ita mai kashin tsiya ba. bayan kuma suna da yara har biyu mace da namiji a tsakaninsu. Abin takaicin shi ne da ta koma gidan iyayenta sai suka koreta wai lallai ta je ta gyara aurenta, bayan kuma ta sanar dasu saki uku ya yi mata, amma sam sun qi fahimtar ta. Ba komai ya sa suka rufe idonsu a kanta ba illa shi mijin yana musu ihsani ko da ya sake ta ya rigata zuwa gabansu ya fada musu qarya da gaskiya, da ya tashi tafiya kuma ya ajiye musu daurin kudi masu matuqar yawa, baqin cikin haka da rashin samin inda za ta nufa yasa taje jikin wata makaranta Islamiyya tana rusa kuka, a can ne Allah ya hadamu da ita bayan na dawo Islamiyyar, yanzu shekarunta ashirin da uku.
“Ita kuma waccen ( na nuna Safiyya) sunanta Safiyya Nuraddeen, saurayinta ne ya yaudareta ya yi mata ciki, iyayenta suka koreta daga gidansu qwata-qwata, saurayin kuma ya gujeta bayan ya qaryata cikin wai ba na shi bane, baqin cikin haka yasa ta yi niyyar shiga duniya akan ko karuwanci ne za ta yi, tana cikin tafiya Allah ya qaddara na bigeta da mota, tun a gurin ta fara zubar jini har muka isa asibiti likita ya tabbatar min da zubewar cikin da take dauke dashi, da ta farfado ne ta bani labarinta, hakan yasa na taimaka mata, yanzu shekarunta ashirin daidai.
“Waccen kuma (na nuna Sadiya) ita marainiya ce, mahaifiyarta ta rasu, sunanta Sadiya Ibrahim ta rayu cikin tsananin wahala a hannun kishiyar mahaifiyarta, ba ta san dangin mahaifiyarta ba, don su irin fulanin nan ne masu tashi daga wannan jeji zuwa waccen jeji har Allah ya qaddara aure a tsakanin mahaifinta.
Bayan ta girma samari suka fara zuwa neman auranta tana da farin jini sosai, baqin ciki yasa kishiyar mahaifiyar tata ta aura mata wani saurayi, tantiri manemin mata. Shekararsu daya da rabi da aure Allah ya dauki rayuwarshi bayan ya yi jinya mai tsanani harna tsawon wata shida, bayan ta gama takaba sai wasu kuraje masu matuqar qaiqayi suka fara feso mata a jikinta.
Bayan binciken da likita yayi ya gano ta kamu da cutar nan mai karya garkuwar jiki, a ranar kishiyar mahaifiyar tata ta kore ta daga gidan, duk dangin mahaifinta kuma sun qi karvarta, hakan yasa ta yanke shawarar neman na kanta dan ta rufawa kanta asiri, wanke-wanke take wa wata mai saida abinci a bakin titi, a nan ne Allah ya hadani da ita har na taimaka mata, tun daga lokacin ta ci gaba da karbar magunguna a asibiti, yanzu shekarunta ashirin da biyu.
“Waccen kuma (na nuna Nafisa) sunanta Nafisa Khamis, mahaifinta ne ya yi mata ciki sannan ya koreta a gidanshi don ganin asirin shi yana neman tonuwa…………….”
“Mahaifinta fa kika ce?” Fatima ta fadi haka tana zare ido, fuskarta na nuna tsananin mamakin maganar.
“Qwarai kuwa" na bata tabbacin haka ina murmushi.
" Nafisa ba ta labarin yanda abin ya faru.”
Nafisa ta yi gyaran murya ta ce, “Tun wata rana da suka samu sabani shi da mahaifiyata har suka rabu ya fara bibiyata, ina yawan saka kaya mai bayyana surar jikina, ranar da ya fara biyo ni da buqatarsa wuqa ya danna min a wuya wai idan ban yarda ba zai kasheni, ganin da gaske yake yasa na amince a haka har ciki ya shiga jikina, a lokacin ne kuma suka sasanta da mahaifiya ta dawo gidan, kwananta biyu da dawowa ta lura da sauyin da yake jikina, ita ta sanarwa mahaifina, tana ganin kamar ina da juna biyu.
Fada ya fara kamar da gaske, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, hankalinshi a tashe ya daukeni a motarsa muka nufi asibiti, likita ya tabbatar da maganar mahaifiyata, tabbas ina da juna biyu.
Ni kaina hankalina yayi matukar tashi, tunda muka fito asibitin nake rusa kuka, 'uffan' mahaifina baice min ba, abinda ya daure min kai shine ganin ya nufi bayan gari da motarsa, saida yayi tafiya mai matukar nisa sannan ya tsaida motar, ya fito nima ya umarce ni na fita,bingida ya dauko ya yi arresting dina da ita yana zare min idanu, yace muddin ina buqatar ci gaba da rayuwa kar in kuskura in koma gidanmu da zama balle har in tona mashi asiri, in shiga duk inda naga dama a duniya amma banda dangin mahaifiyata ko danginshi, matukar ya sami labari na a nan kusa to wallahi sayya kashe ni.
Daurin 'yan dubu guda daya ya jefo min jikina, sannam yaja motarshi ya tafi bayan ya bade ni da kura, Ina kuka amma bai ko tausaya min ba yayi tafiyarsa, da qyar na fidda kaina zuwa bakin titi, a wannan ranar a hotel na kwana, da safiyar washe gari na nemi wata qawata wacce tun muna makaranta ta taba bani labarin ta zubar da ciki, ta rakani wani voyayyen asibiti na fitar da cikin nan, na sha matuqar wahala kamar ba zan rayu ba, sai daga qarshe Allah ya hadani da Aysa ta taimaka min har kika ganni na zama daya daga cikin yan wannan qungiya.”
“Siyama kuma (na nuna ta yatsa manuniya) mahaifinta Ahmad Allah ya yi masa rasuwa tun tana ‘yar yayayyiya. Mahaifiyarta sanadin hatsarin mota da suka yi ta samu tavin qwaqwalwa, sai riqonta ya koma hannun wan mahaifinta. Mutum ne mai matuqar son ‘ya’yan shi, sam baya yarda a ce dan shi ya yi wani laifi, yana iya sabawa da kowa akan ‘ya’yansa. Yusuf shi ne babba a cikin yaran wan mahaifin nata, tunda ya qyalla ido ya ga makerin budurci ya fara kera Siyama ya kwallafa ranshi a kanta, da wayau da lallami da alqawarin karya a kan zai aureta ya lalata mata rayuwa har ciki ya shiga jikinta, da kan shi ya kai ta asibiti da niyyar a zubar da cikin, gurin fitarwar ne aikin yazo da gaddama sai jini ya balle mata.
Ganin hakan da yayi sayya gigice, hankalinsu a tashe yaje ya samu iyayenshi kan cewa ta yi ciki gurin zubarwa za ta rasa ranta, wai shi ma wani abokin shi ne ya kira shi a waya yake fada masa.
Da kyar likitan ya samu nasarar tsaida jinin, wannan lokacin bata san inda kanta yake ba, bayan an samu nasarar farfadowarta sai wan uban nata ya koreta daga gidanshi, daga qarshe sai Allah ya hadamu da ita.
“Ita kuma waccen sunanta Suhaila Sulaiman, wani azzalumi ne ya samu mahaifiyarta tana tsaka da hauka akan bola ya sadu da ita sai ciki ya shiga jikinta, bayan ta haihu ne ‘yan unguwan suka kaita gidan marayu ta girma a can. Nima a can din Allah ya haxamu da ita.
“Ni kuma sunana Aysha Azzahara’u………………"
Ringing din wayata shi ya katse min tarihina da na yi niyyar ba su
“Hello…” na furta da sanyin murya ina lumshe ido.
“Barka da rana babyna, kin gane mai magana kuwa?’'
Aka fadi haka daga can bangaren.
“Hajiya Danasha"
Na kai tsaye bayan na daure fuskata kamar tana gaba na.
“Qwarai kin canka daidai sarauniyar mata, na jiki shiru har yau ba ki qara waiwayata ba shi yasa na bugo don jin shawarar da kika yanke, Kar ki manta duk matsalarmu daya ne, A Dalilin daa Namiji mu ma muka kafa wannan qungiya don taimakawa junanmu, na san kina da dukiya don haka ban kwadaita miki ita ba, amma kar ki manta ko kogi bai qi dad'in ruwa ba.
Sannan akwai biyan buqatar juna a wannan harkar, kuma za ki qara tsanar namiji fiye da yanda kike a yanzu, muna da manyan mata, masu riqe da manyan muqamai na gwamnati, a wannan qungiyar akwai mata ‘yan siyasa, akwai mata manyan ‘yan kasuwa…. Ke har daga qasashen qetare irinsu India, China, Malaysia akwai wadanda muke harka dasu.
Ki shigo cikin qungiyarmu ke da sauran ‘yan matanki ku ji dad'in rayuwa, ku shana da dukiya, ku yi abin da kuke so zamu tsaya muku.
Wallahi tun sati biyun da suka wuce da Allah ya hadamu sam bana iya barci son ki a kullum dad'a ruruwa yake a zuciyata… ki taima…”
“Dakata Danasha..!!" Na kira sunanta kai tsaye ba tare da inkiyar hajiyar ba, saboda tsananin bacin rai, a zafafe na ci gaba da fad'a mata duk abinda yazo bakina.
“Maganata ta qarshe akan wannan qungiya taku shi ne, wallahi ko da zan yi yawo tsirara saboda tsammanin talauci ba zan tava yin qazantacciyar rayuwa irin ta qungiyarku ba, kuma a cikin ‘yan matan da nake tare dasu ma babu wacce za ku samu hadin kanta. Don haka ki tattara tsufanki ki qara gaba, kuma kar ki qara cewa kina so na idan ba haka ba sai na zubar miki da haqora.”
Ina gama fadin haka na katse wayata ina numfarfashin fusata, Rintse ido na yi na kwanta a kan kujeran da nake zaune, minti biyu tsakani duk suka fara sulalewa zuwa dakunansu.
“Zo mu tafi dakina Fatima, duk abin da ba ki gane ba sai in qarasa amsa miki.”
Rahama ce ta furta hakan, sannan ta janye hannun Fatima suka nufi dakinta, tsawon minti goma sha biyar ina kwance idanuna a runtse daga bisani na miqe na nufi dakina.
“Tsawon wani lokaci kenan da kafuwar wannan qungiya taku?” Fatima ta tambayi Rahama bayan ta zauna a kan kujeran dressing mirror.
“Wata shida kenan.”
Rahama ta amsa mata batan ta zauna a gefen gado.
“Bani tarihin Aysha mana”
Sai da ta yi murmushi sannan ta amsa mata da cewa
“Duk gidan nan ba wacce ta san tarihin Aysha, ko wani lokaci idan ta yi niyyar fada mana sai wani abin ya taso kamar dai yanda ya faru yau, amma duk mun qosa qwarai mu ji tarihinta, bayan sunanta da shekarunta babu wani abu da muka sani a kanta.”
“Shekarunta nawa?”
Fatima ta sake tambayarta.
“Sati biyu ya rage ta shiga shekaru goma sha bakwai.”
Shiru ya ratsa tsakaninsu harna tsawon minti biyu, kowacce a cikinsu da irin saqe-saqen da take yi a zuciyarta.
“Amma kun san tana shan kayan maye?”
Fatima ta sake tambayarta fuskarta na bayyana damuwa da jimami.
“Qwarai kuwa, duk gidan nan mun san haka, a taqaice ma ba ta iya barci in dai ba ta sha kayan mayen ba. wannan yana daya daga cikin dalilin da yasa duk gidan nan muka qosa mu ji tarihinta, akwai abubuwa masu matuqar ban mamaki da daure kai a tattare da ita. Karamin misalin da zan baki shi ne dukkanmu babu wacce ta bata tarihinta da kanta, daga haduwarta dani ta karanto min tarihina daga farko har qarshe, kuma duk sauran ‘yan matan hakan ta kasance dasu, kema ranar da aka yanke miki hukunci ita ta karanta mana tarihinki.”
Ajiyar zuciya ta sauke tana qara jinijna abin a cikin ranta, can kuma ta yi qarfin halin fadin “Wannan gidan qasan da kuke rayuwa a ina kuka samu kudin ginawa?”
Sai da Rahama ta qyalqyale da dariya sannan ta fara tunanin tsarin gidan nasu da Fatima ta radawa gidan qasa.
Daga can kofar gidan dai shi kadai ne kwal a tsakiya dajin, sai ka yi tafiya mai nisa kafin ka tadda wani gida a can gaba. Get ne mai matuqar kyau da girma a jikin qofar gidan, katanga ne mai tsananin tsawo wanda duk wayon barawo bai isa ya tsallakaba, idan ka shiga harabar gidan, rumfuna ne aka yi gurin adana motoci a ko wani kusurwa na harabar gidan. Daga can tsakiya aka yi ginin wani daki wanda shi kadai ne qwallin qwal a duk girman harabar gidan, ko wani rumfa motoci ne guda hudu, sai daga gefe aka jera mashinai ‘wayyo kudina' guda goma. Motoci masu matukar kyau da tsada guda goma sha biyu ne a gidan.
Idan ka bude wannan dakin da yake tsakiyar gidan babu komai a ciki sai wani hanya a tsakiyar dakin daya gangara yayi kasa an jera matakala tamkar dai gidan sama amma wannan ne qasa ne, idan ka miqe zuwa kasan matakalan ba inda za ka tsinci kanka sai a wani qaton falo mai matuqar girma da qyatuwa, an zuba duk wani kayan more rayuwa da ake bukata, a cikin falon akwai dakuna guda guda goma sha biyu, ako wani daki akwai bayi aciki, daga can gefe aka yi kichin hade da sitor dauke da katan-katan na lemuka da buhu-buhu na abinci, a takaice tsaruwar gidan ya wuce in bayyanashi a wannan dan qanqanin littafin.
Ajiyar zuciya ta saki bayan ta gama tunanin tace,
“Duk girman gidan nan da duk wani kayan alatu da siturun da muke sakawa mallakin Aysa ne, yanda kika ga gidan nan mu ma haka muka tarar da shi.”
“Tabxijan!”
abin da Fatima ta iya furtawa kenan sannan ta zabga uban tagumi da hannu biyu.
***
Qarfe biyar da minti ashirin da bakwai muka yi parking din motocinmu a qofar ‘MANGAL PLAZA’ Siyama, Rahama, Safiyya mota daya suka hau, Sadiya, Suhaila, Nafisa suka hau mota daya.
Farar mota kirar marsandi na hau, kamar yanda duk kayan jikina farare ne, wandon jeans ne wanda ya dan kamani daga sama ta kasan kuma sayya bude, T. shirt din dana saka ita ma fara ce an rubuta ‘Baby’ da golden colour a gaban rigar, ban sanya hula ba illa wani farin qyalle dan siriri dana daura a saman kaina zuwa qeyata na fitar da gashin kaina mai matuqar kyau da tsawo ya bazu har saman kafadata, a saman qyallen dana daura an rubuta ‘Azzahara’u’ da qananan rubutu ruwan golden ta gaban goshi.
"kin yi kyau matuqa….. amma a hakan za ki fia?” abin da Fatima ta ce min kenan lokacin da muke gab da fitowa daga gida.
Murmushi kawai na yi mata kamar yanda yanzu ma nake murmusawa bayan na tuno abin da ta ce min, ni ce a gaba sauran ‘yan matan suka rufa min baya, muka nufi cikin qaton kantin.
Tun kafin ya daidaita fakin din motarshi a harabar gurin yaga fitowarta daga cikin motar, “Tabbas ita ce” ya fadi hakan a zuciyarshi, kwanaki biyar kenan ya taba haduwa da ita da sauran ‘yan uwanta a ‘check point’, a lokacin ba a mota ya gansu ba, a kan mashina ‘wayyo kudi na’ ne sun goya junansu, abin da ya baiwa duk mutanen gurin mamaki shine, a dokar da yayi tsanani a garin Kaduna shi ne matuqar kana kan mashin idan ka je check point sai dai ka sauka ka tura mashin din har ka wuce sojoji, sannan ka hau ka cigaba da tafiya, Sukam kansu tsaye suke ratsa tsakanin motocin, a lokacin yana can tsallaken titi a tashi motar yana jiran layi ya zo kanshi, Har sun sa kai zasu wuce sojojin biyu suka dakatar dasu a fusace.
A lokacin bai yi tsammanin mata bane don sun sanya hular kwano duk sun rufe fuskokinsu, dakatar dasu din da aka yi ya sanya wacce take gaba ta sanya hannu ta sabule hular kwanon da yake kanta, sai su ma sauran mahaya mashin din wanda suke biye da ita suka fara sabule hulunan kwanon da suke sanye a kawunansu.
Kanannadadden gashin kai mai matuqar kyau da sheqi da tsawo shi ya fara bayyana daga bisani kyakkyawar fuskarta ta biyo baya, idanunta a lumshe tsawon daqiqa goma sannan ta bude su tana kallon sojojin bayan ta qawata fuskarta da murmushi, da hannunta daya ya ga ta yi musu alamar ya aka yi? bakinta yana motsi a hankali, ya ga alamar ta qara furta wata kalmar amma bai fahimci abinda tace ba.
Nan take ya ga sojojin sun yi musu umarnin wucewa ba tare da wani daukar mataki ba, harda karin Sara mata, sannan suka bi ta kallo ido da hanci bude.
Wannan abinda ya faru yaba duk wani wanda ya ke tsaye a gurin matuqar mamaki, A lokacin ya yi tunanin ita din ‘yar gidan wani babban kusa ne a garin Kaduna, tun ranar fuskarta ya qi bacewa daga idanunsa…
“Abdul-Ahad tunanin me kake yi?”
Yasmin da take zaune a gefenshi ta tambayeshi fuskarta ba walwala ko kadan, bayan ta lura da kallon da ya bi ‘yan matan da suka shige cikin kantin da shi.
Murmushi ya jefeta da shi don kwantar da hankalinta daga bisani ya yi qarfin halin fadin “Babu komai, kaina ne yake dan sara min.”
Kallon rashin yarda ta bi shi da shi na tsawon daqiqu sannan ta ce, “Kar dai ka manta watanni shida nan gaba za a daura mana aure, kuma zan iya yin komai ciki kuwa har da kisa ga duk yarinyar da ta nemi rabani da kai, ko da kuwa kai ne ka ce kana sonta.”
Tana gama fadin haka ta bude qofar mota ta fita ta jingina da motar tana jiran fitowarshi.
Share gumin goshinshi yayi sannan ya gyara zaman tabaran da yake sanye a idanunsa ya fito daga motar jikinsa ya yi matuqar sanyi, kai tsaye kantin da ‘yan matan suka shiga ta ja hannunsa suka nufi ciki.
***
Tun daga nesa rigar take daukar hankalina, don haka na qarasa da nufin in dauko ta duk da dai kalar yellow bai cika burgeni ba, dora hannuna akan rigar ke da wuya na ga wani hannu ya riqe rigar, daga faratan kantin masu matuqar tsawo da suke sanye a kunbunan hannun na gane mace ce, sakin rigar nayi na kara gaba ba tare ko fuskarta na kalla ba.
Sai da ta yi qwafa saboda takaici, ta so a ce na tanka mata ta yi min wulaqanci a gaban Abdul don ya tabbar ba cika baki take a kanshi ba, za ta iya aikata duk abinda ta ce za ta aikata a kan soyayyarshi. Don haka ba ta haqura ba ta ci gaba da bin duk inda na nufa.
Hantar cikinshi sai da ta kada saboda tsabar tsorata, lokacin da ya yi arba da hannun Yasmin damqe da rigar da na fara dauka, a zatonshi zan tanka mata, amma wani abin armashi da birgewa a tattare da ni shine kallon ta ban yi ba na sakar mata rigar na yi wucewa ta.
Ganin ta nufi hanyar da na bi ya sa ya fara addu’ar Allah ya sa ba abinda zai faru har sai sun gama abinda ya kawo su su fice, don ya san Yasmin tamkar yunwar cikinshi, fitinanniya ce ta gaban kwatance.
Yanayin tsarin kwalin turaren shi ya fara daukar hankalina, na dauka ina karanta sunanshi, kamar da fada aka fisge kwalin turaren a hannuna… da matuqar mamaki na bi hannun da kallo sai na gane hannun dazu ne.
Raina ne ya fara baci, amma nayi kokarin hadiye bacin ran, ban kula ba na kada kai da nufin wucewa gaba, tsulum na ga hannun nata a cikin kwandon diban kayan siyayyar da na yi, wanda yaron kantin yake biye da ni yana tura wa ina jefa duk abinda na dauka a ciki, wata doguwar riga puple ta dauko a cikin kwandon siyayyata, ta juya da nufin sakawa a nata kwandon.
Da matukar mamaki na bita da kallo, fuskantar abinda take shirin yi yasa na dafa Kafadarta na damqe na juyo da ita muka fuskanci juna, dayan hannuna nasa na damqe hannunta mai riqe da rigar, tun daga qafafuwanta na fara bin ta da kallo har zuwa fuskarta, tasha bilicin, kallo daya na yi mata na gane farinta ba na Allah da Annabi ba ne, a tsaye take single, ba laifi tana da dan kyau a fuska, amma da ta tsaya a baqin da Allah ya yi da ta fi haka kyau, tana sanye da riga da siket na English wears.
Fuskata ba walwala nake kallon yadda take kici-kicin qwace hannunta da na damqe, ganin ta kasa qwacewa ya sa ya tsaya cak tana kallo na, tana sauke numfashi sama-sama, daga bisani ta watso min harara, sannan tace
“Sakar min hannu.”
Tana maganar tana wani yatsina, wanda yake qarawa fuskarta muni.
Shiru nayi mata ban tanka ba, a zuciya ta ina mamakin karfin halinta.
“Ki sakar min hannu na ce.” Ta qara maimaitawa a fusace kamar za ta rufe ni da duka.
Nan ma nayi iskar kare da ita, tamkar da kurma take magana, kuma dukda haka ban sake ta ba.
"Ki sakar min hannu don uwarki.”
Ta fada cikin karaji, batan ta lailaya ashar ta makawa uwata, abin da ya janyo dugunzuma da tashin hankalina, da a ce mahaifina ta zaga ba zai tava zuciyata ba ko kadan, sam babu wanda zai fahimci mugun riqon da na yi mata amma ita din tana ji a jikinta don har ta fara rintse ido tana cije baki, gumi yana diga daga goshinta.
Duk abinda yake faruwa yana daga gefe yana kallo, shi kanshi yayi niyyar roqon alfarmar in sakar mata hannun, zagin da tayi min ne ya dakatar da shi, shi kanshi zagin ya taba zuciyarshi.
Cikin kankanin lokaci idanuna suka kada sukai ka, muryata a zafafe na fara tambayarta da cewa
“Wa ya turoki ki zagi mahaifiyata?”
Na fadi hakan ina qara damqe hannunta iya qarfina.
A jikinta take jin jijiyoyin hannunta suna tsittsikewa ba ta san lokacin da hawaye ya fara tsiyayo mata ba saboda tsananin azaba.
Kukanta ne ya daga mishi hankali don haka ya matso kusa da mu ya ce,
“Ki yi haquri, ki samar mata hannu don Allah.” Ya fadi hakan idonshi yana kaina.
Harara na watsa masa da dara-daran idanuna tamkar zasu fado kasa, sannan na yi mishi kallon ‘Kai kuma a su wa?’ go gefe kaban guri'
A tsorace yaja da baya, hankalinshi a matukar tashe, a zuciyarsa yake Allah wadai da fitinar Yasmin.
“Hajiya don Allah ki yi haquri ki sakar mata hannu.” Masu riqe mana kwanduna suka fadi hakan suna kusanto ni.
“Duk wanda ya matso kusa da ni wallahi sai na kumbura mishi fuska.”
Na fadi hakan da murya mai sauti, cike da hargagi da tsawatarwa.
Hakan shi ya janyo hankalin su Safiyya da Rahma, da gudu suka biyo layin da suka jiyo sautin muryata a lokacin har mutane sun zagaye mu ana magiyar in sakar mata hannu.
Ni kuma na kafe kan sai ta fada min wanda ya turo ta ta zagar min uwa.
Rahma ce ta kama kafaduna ta jingina jikinta da nawa ita kuma Safiyya ta yi bismilla ta vanvare hannuna daga riqon da nayi wa Yasmin, Lumshe ido na yi na nufi hanyar ficewa daga kantin idanuna suna rufe.
Rahma ce ta tura siyayyar tawa zuwa gurin biyan kudi, ita kuma Safiyya ta rufa min baya muka fice daga kantin.
Yatsu biyu ta sanya a baki ta hura ya fitar da qara mai tsananin qarfi tamkar an hura usir (hakan da ta yi inkiya ce da take isarwa da sauwan ‘yan’uwanmu cewa su fito daga cikin kantin an samu matsala) minti daya tsakani duk suka fito daga cikin kantin zuwa gurin biyan kudi, Sai da ya gama total din kudin kayan da na muka dauka gaba daya, sannan ya kalle ta ya ce
“Hajiya an biya kudin kayan, don haka kuna iya tafiya…”
Kafin ya qarasa abinda ya yi niyyar fadi, Rahma ta cakumo wuyan rigarshi tana fadin “An fada maka maula muka zo shagonku?”
Kafin ya amsa ta qara juyo qara irin wacce tayi dazu daga waje, hakan shi ya tabbatar mata da cewa tabbas akwai matsala babba daga gare ni.
Ba shiri ta sakar mishi wuyan riga ya ja gefe yana maida numfashin wahala, Kallon kwandunan siyayyar namu ta yi gaba daya, a ranta ta qiyasta kudi kayan gaba daya, Dalar amurka ta ciro daga aljihun wandonta ta zaro masu yawa wadanda idan canji za a yi zasu kai dubu dari biyar, ta dora a teburin gabanshi ta ce “Idan ka canja ina da tabbacin zasu kai dubu dari biyar”
Tana gama fadin haka ta yi musu inkiyar fita daga kantin, hannayensu janye da kwandunan siyayyar, yaran kantin suna biye da su don amso kwandunan.
Kusa da inda na yi parking din motata suka hangi taruwar jama’a maza da mata, Da hanzari suka juye siyayyar a cikin but din motocin da suka hawo zuwa kantin sannan suka nufi kusa da motar tawa don ganin abinda yake faruwa.
Safiyya tana zaune dirshan a qasa ni kuma ina kwance magashiyan tamkar matacciya, ta dora kaina a jikinta tana hawaye, Tunda take zaune tare da ni ba ta taba ganin hakan ba duk da dai tana tunanin akwai wani babban al’amari a tattare da ni, Fuskokin mutanen gurin kawai za ka kalla ya tabbatar maka da matsanancin tsoron da suke ciki, abu Kamar almara don dai kawai a gabansu ya faru.
Awa daya baya na wuce cikin kantin cike da ban sha'awa, duk Namijin daya ganni ba wanda baiyi sha’awar in kasance matarsa ba, amma kuma ina fitowa ganin idonsu na yanke jiki na fadi kusa da mota ta, abu mafi tsoratar dasu shine, duk wanda ya kusanto garemu da niyyar taimakawa Safiyya ta sanya ni a mota sai turiri mai matuqar zafi da yake fitowa daga jikina ya komar dashi baya, daga bisani kuma sai wani farin haske ya zagayemu ni da Safiyya duk wanda ya matso sai hasken ya komar dashi baya, don haka duk sai suka zubawa sarautar Allah ido, suna kallonmu amma basu da ikon taba mu.
“Bisimillahir Rahmanir Rahim.”
Abinda Rahma ta furta kenan ta nufomu ba tare da wani tsorata ba a tattare da ita.
Ga mamakin mutanen gurin ba abinda ya hanata isowa garemu, hannuna ta riqe sannan ta durkuso da fuskarta zuwa gareni ta ce,
“Mu saka ki a mota?”
Ina jin abinda duk yake faruwa, maganace dai bani da ikon yi don haka na daga mata kai alamar
“Eh.”
Nan take suka sanyani cikin motar da nazo da ita suka kwantar da ni a bayan motar, Rahma ta shiga gaba mazaunin direba ta tayar da motar ta fice daga harabar gurin su Safiyya suka ruufa mata baya a tasu motocin a guje.
***
Duk irin gunjin kukan da take yi da majina tana ihun hannunta zai tsinke bai tanka mata ba, matuqar haushinta yake ji, tamkar ya shako ta ya tsinka mata mari, duk abinda ya faru itace sila, ita ce hatsabibiya wai a dole mai kishin masoyinta.
Shi abinda yafi tsaya mishi a zuciya ma abinda ya faru da yarinyar, duk abinda ya faru da akan idonshi ya faru, kanshi sai caji yake yi, ya rasa waqar farawa, ga kukan Yasmin dake qara qona mishi zuciya, amma acan qasan ranshi yana jin matsanancin ciwo na rashin sanin halin da yarinyar take ciki.
“Me yake damun ta da har ta faxi a qasa? A wane hali take ciki a yanzu?”
Wadannan duk tambayoyi ne da yake buqatar amsarsu daga gareta amma kuma bai da tabbacin ko zai sake ganinta.
Yana ajiye motar bai saurareta ba ya wuce zuwa can bangaren da ake sauke shi idan ya kawo ziyara gidan qanin mahaifinshi, kuma surukanshi mahaifan Yasmin.
Tun daga harabar gidan take rusa ihu harta dire a tsakiyar falon gidan, birgima ta fara yi tamkar qaramar yarinya, tana ihun fadin hanunta zai tsinke.
Bata taba tsammanin yana gidan ba don lokacin dawowarsa shine karfe goma sha biyu da rabi zuwa qarfe daya na dare, Shi yasa ta kara sakin jiki don tada hankalin iyayen nata, saboda ta san ita din ‘yar lele ce.
“Yasmin me ya faru? Me ya faru da hannun naki? Wa ya tava ki? Ko ke da yayan naki ne?”
Wadannan jerangiyar kalaman da Mummy da Daddy suka ringa furta mata kenan hankalinsu a matukar tashe suna qoqarin kamo hannun nata amma sam ta qi ba su damar haka.
Duk yadda suka so rarrashin ta don sanin abinda ya faru taqi saurarawa, ihu kawai take ba qaqqautawa.
"Ko Kun samu accident ne?” Mummy ta sake furta hakan tana qoqarin rungume ta a jikinta.
Tun shigowar ta yana kwance kan tree sitter yana busa sigarinsa hankali kwance, A rayuwarshi ya tsani hayaniya, shiyasa matuqar yana gidan ko TV babu wanda ya isa ya kunna ya qure volume, sai dai idan shi yayi ra’ayin haka.
Ba zato ba tsammani taji an fincike ta daga jikin Mummy, kafin ta wartsake ta gano wanda yayi mata haka taji saukar mari mai matuqar zafi a kuncinta na dama, Tsananin azaba ya sa ta kife a tsakar falon ta yanka ihu mai matuqar firgitarwa, idanunta tsab suka fada cikin na Yayanta Abba tsaye kyam a gabanta yana hucin fusata, alamun a kowane lokaci yana iya rufe ta da duka, ba shiri ta sanya hannunta mai lafiya ta toshe bakin ihun tana makyarkyatar sanyi da tsanani tsorata.
“Abba wannan wane irin zalunci ne? baka da hankali ne? kana ganin yarinya ta shigo tana kukan hannunta don zalunci shine za ka qara mata da mari? Idan ba za ka rarrashe ta ba a matsayinta na qanwarka ai…”
“Shiiiiiii..."
Ya sanya yatsarshi a baki ya dakatar da mahaifiyar tashi yana gwalalo mata idanu, tamkar zai cinyeta d'anye
“Mummy kar ki min ihu, kina jin yarinyar tana neman haddasa min ciwon kai amma kun biye mata sai wani rarrashinta kuke yi, don ubanta idan ba za ta fadi abinda ya same ta ba me ya sa take mana ihu don ta kashen dodon kunne? Duk ku kuka lalata rayuwar ‘yar iskar yarinyar nan amma duk zan gyara muku zama.”
Ya karasa fadin haka yana nuna su da yatsarsa manuniya alamun zazzafar gargadi da Jan kunne.
"Abba mu ne za ka gyara wa zama?”
Mummy ta tambaye shi idanunta suna niyyar kawo hawaye kamar yadda ta saba idan ya tasa su a gaba da kwando-kwando na rashin mutunci.
“Mummy na ce ki yi min shiru ko...?”
“Tasss!”
Saukar zazzafar marin da ya jiyo a kumatunsa na dama ya hana shi ajiye numfashin maganarshi daidai, da jajayen idanunshi ya juya don ganin wanda yayi mishi wannan danyen wulaqancin, hada idanunsu keda wuya ya sunkuyar da nashi qwayoyin idanun yana qwafa a cikin zuciyarshi.
“Ashe har yanzu kana shuka wannan rashin mutuncin?”
Abdul’Ahad ya fadi hakan bayan ya cakumo wuyar rigar Abba hannu bibbiyu yana shakeshi.
“Iyayen naka kake ikirarin zaka gyara wa zama? Ina alqawarin da ka daukar min na daina wulaqanta su?” tunkudo shi gaban Mummy yayi ya duqar da shi kan gwiwoyinshi sannan cikin daga murya yace
“Ba su haquri.”
Zazzafar huci ya fesar, zuciyarsa cike da kuna, kamar bazai tanka ba sai can yace
“Allah ya huci zuciyarki, don Allah ki yi haquri.”
Soyayya irin ta d'a da uwa yasa har tana fadada fuskarta da murmushi gurin amsa yafiyarshi.
Shi ma Daddy bai ja da nisa ba yace ya yafe, dama duk tabarbarewar tarbiyar d'an nasu sune sila, Sun nuna mishi matsanancin gata kasancewar sun dad'e ba su samu haihuwa ba, kuma sunan mahaifinshi ke gare shi, shiyasa suke kiran shi da Abba.
Qwafa Abdul’Ahad ya yi, sannan ya cakumo wuyar rigarsa ya daga shi tsaye,
“Idan baka manta ba zuwana garin nan na qarshe na fada maka zan nemi transfer zuwa garinnan ko don saboda akai, don haka ina yi maka albishiri din dawowa garin nan da aiki, Duk inda ka sa qafa ina sane da kai, Ka san abin da zan iya aikatawa da wanda ba zan iya ba. idan kunne ya ji….”
Yana gama fadin haka ya nemi guri ya zauna, ya watsawa Yasmin da take tsiyayar hawaye harara, sannan ya fara mayar musu da bayanin duk abinda ya faru da Yasmin.
Kafin qarfe goma na dare sun nemi mai daurin karaya na gargajiya ya duba mata hannun, ya kumbura suntum saboda jinkirin da aka dauka ba tare da an bi ta kanshi ba, Ashe wai karaya ta samu a hannun, Tasha tsananin azaba kuwa kafin a gama gyaran, don saida aka rirrike ta, duk da haushin da take ba shi yayi matuqar tausaya mata, ganin irin wahalar da ta sha gurin daura hannun.
Ya dauki tsawon lokaci yana rarrashin ta, daga bisani ya nufi bangarensu, zuciyarshi cike da tunani kala-kala
“Me yake faruwa da wannan yarinyar ne? anya kuwa ma mutum ce? Daga riqon hannun Yasmin sai kuma a ce ta karya ta?”
Da fari tun a Plaza ya zaci raki ne da shagwava irin na Yasmin, amma tunda mai dorin ya fadi ta sami karaya jikinshi ya yi matuqar sanyi, zuciyarshi ta cika da tunani da tambayoyi iri-iri.
***
Muna zauna a tsakar falo, misalin qarfe goma da rabi na dare, hira muke yi cikin wasa da dariya. Idan mutum ya kalle ni tamkar ba ni ce kwance magashiyan a dazu ba, hatta Fatima a wannan lokacin ta saki jikinta da mu, duk da dai ba ta cika tsoma bakinta a hirar da muke yi ba, amma idan mun yi abin ban dariya ta kan dara.
“Ya dai Fatima? Fadi abinda yake ranki mana.” Na wurga mata tambayar ba zato don tun dazu na lura akwai abinda take son furtawa.
Tsawon daqiqu tana kallon na da motsa bakinta alamun tana jinjina abinda zata fada ne.
Don in qara mata qwarin gwiwa yasa na ce
“Kar ki damu, fadi maganarki kawai”
“Ina neman alfarma a gareki.”
Ta yi qarfin halin fadin haka tana matsa yatsun hannayenta.
“Alafarmar me?” Na tambayeta da mamaki a fuskata.
“Don Allah ki bamu tarihin rayuwarki, don Allah.”
Dan murmushi nayi, sannan nace
“Kwantar da hankalinki fatima, ba sai kin hadani da Allah ba, da ma a yau na yi niyyar warware muku zare da abawa na tarihin rayuwata. Amma ku bani minti talatin in yi wanka….”
WACE CE AYSHA AZZAHARA’U??
Mahaifina Alhaji Sa’ad mutum ne mai matuqar son kudi, a rayuwarshi ba abin da yake so sama da kudi, tsabar son kudi irin na mahaifina yasa ya baro can garin iyaye da kakanninshi ya shiga duniya neman kudi.
Yana iya yin komai matuqar yasan zai sami kudi, shigarsa duniya ba inda bai zaga ba a manyan garuruwan arewacin Najeriya.
Babban matsalar mahaifina shi ne ya san ya nemi kudi ya tara, amma sam bai san yanda zai kashe su ba, baisan ya biyawa kanshi buqata ba, yana matuqar jin ciwon fitar da kudi ya kashe, idan zai kashe qwandala a cikin dukiyarshi yana jin tamkar naman jikinshi yake yanka.
A dole yake kashe naira dari biyu a rana, ko ciwo yake ya gwammace ya shiga daji ya sassaqo ganyayyaki ya dafa har Allah ya bashi lafiya, hatta abinci bai iya cire kudi ya siya mai tsada, sai dai ya sha garin kwaki da suga shi ma kadan saboda maleji.
A yawon neman arzikinshi ne Allah ya hada shi da wani ubangida mai matuqar dukiya a garin Kaduna, Ya tara arziki mai matuqar yawa a dalilin wannan ubangida nashi, shi kan shi ba zai ce ga inda Alhaji Buba (ubangidanshi) yake samun kudi ba, kuma bai san taqamaimai sana’ar ubangidanshi ba, kawai dai kudi yake kashewa bana wasa ba.
Sai da mahaifina ya shekara arba’in a duniya ba tare da ya yi aure ba, tsabar son kudi irin nashi yana jin matuqar ciwo ya kashe naira dubu dari biyar ya yi aure, Sai da Alhaji Buba ya yi masa alqawarin ya nemo matar zai bashi kudin auren sannan ya je gidan marayu ya zabo mahaifiyata ya aura, kudaden da Alhajin ya bashi kuma na hidimar auren ya zuba a account dinshi, yaci gaba da tara dukiya.
Alhaji Buba ne ya bashi kyautar gida mai kyau a unguwar Rimi, kuma yayi masa kashaidi da tsoratarwar cewa matuqar ya sai da gidan nan to qarshen alaqarsu ta zo, wannan shi ne dalilin da yasa ya haqura suka zauna da amaryarsa Aisha (mahaifiyata) a wannan gida, amma kullum zuciyarshi quna take yi don yana ganin almubazzaranci ne.
Duk kyan gidan da suke ciki amma babu abinci mai kyau, sai mahaifiyata ta yi wata uku ba ta ga idon shinkafa ba, kullum girkinta daga tuwon masara miyar kuka ba nama ba kifi, sai jiqon garin kwaki da manejin sukari, ko kuma ta kwadanta shi da kuli-kuli.
Kuma abin da zai baku mamaki shi ne, shi kan shi mahaifina haka yake cin wannan abincin ba tare da wani damuwa ba.
Watan su biyu da aure mahaifita ta samu ciki mai matuqar wahala da laulayi, sam ba ta iya hassala aikin komai a gidan, kuma ba ta iya cin abincin da mahaifina ya bari a gidan, tana buqatar ababen marmari dana kwadayi, mahaifina yayi tsalle ya dire kan cewa ba ta isa ta sashi asarar kudinshi ba, duk yanda taso ta fahimtar da shi ya qi fahimta, daga qarshe ma cewa yayi saidai cikin nata ya zube matuqar sai ya barnatar da kudinshi a kanta.
Wani baqin hali da mahaifina ya ke da shi shi ne na hana mahaifiyata fita ko da maqwabta ne balle gidan marayu inda ya aurota, kuma ba ta da waya balle ta kira hukumar gidan marayun ta sanar da su halin da take ciki, idan zai fita sai ya kulle get din gidan ta waje yanda babu ta yadda za ta iya fita balle har ta sanarwa da wani halin da take ciki.
Cikinta yana girma jikinta yana kara bushewa, kallo daya za ka yi mata ka tabbatar tana fama da qarancin jini a jikinta, duk wannan bai sa mahaifina ya tausaya mata ba.
Idan yaga tayi kwana da kwanaki ba ta iya barci sai ya sami almajirai ya turasu daji su debo mata sassaqen madaci da ganyayyaki masu illah ga mace mai juna biyu ya dafa ya tilasta mata shan su, kuma tunda mahaifiyata ta samu ciki ba ta taba ziyartar asibiti ba, wannan shi ya kara haifar mata da mummunar matsala ba tare da saninta ba.
Cikinta har ya shiga wata na goma sha daya ba haihuwa ba alamarshi, lokacin ta koma tamkar kwarangwal saboda matuqar rama, sai tirtsentsen ciki a gaba wanda har rinjayarta yake wani lokacin.
A wannan lokacin da mahaifiyata take buqatar taimako daga mahaifina shi kuma sai ya tsiri tafiye-tafiye, sai yayi kwana biyu bashi a gida, Duk da hakan dai bai fasa kulle gidan ta waje ba idan zai fita.
Wata rana da daddare naquda ya tasowa mahaifiyata gadan-gadan, gashi kuma mahaifina baya gida, duk yanda taso zuwa ta bubbuga qofar get din gidan ta ciki ko Allah zai sa wani ya jiyota daga waje ya kawo mata dauki ina….!!! Allah bai bata ikon hakan ba, tayi matuqar galavaita yanda ko dan yatsanta ta kasa dagawa.
Abin da ya qara daga mata hankali shi ne yanda jini yake bin qafafuwanta, duk da dai ba ta taba haihuwa ba, kuma ba’a taba haihuwa a gabanta ba ta san akwai gagarumin matsala daga wannan jinin da taga yana biyowa daga qasanta.
Ciwo ya yi tsanani gareta, azaba tayi azaba, kuma haihuwar ta tsaya cak sai azabar ciwon mara da baya da duk wani sassa na jikinta, ta sadaqar da ci gaba da rayuwar duniya, don haka ta lumshe ido tana kalmar shahada a zuciyarta.
Kamar daga sama taji ana gyara mata zaman dirshan din da tayi a kan tiles ana bubbuda qafafunta.
Daqyar ta yi nasarar bude idanunta don ganin mai mata wannan taimakon, tsohuwa ce don a kiyasce ta haura shekaru hamshin da biyar, da taimakon Allah da taimakon wannan tsohuwa mahaifiyata ta haifeni.
Tana haihuwa ta waiwaya don ganin abinda Allah ya ba, na fado duniya cikin riga irin wanda ake haifar wasu jariran da ita, idanuna a bude suke qyar ina kallon ummata yayin da ita ma take kallona, ita kuma wannan tsohuwa ta yi qoqarin yage rigar jikina, kallon dakiku talatin ya ratsa tsakanina da ummata sai ta maida idanunta kan wannan tsohuwa da ta taimaka mata tace
“Ga amanar ‘yata nan a hannunki, Allah ya yi mata albarka…..”
Tana gama fadin haka ta yi kalmar shahada ta ce ga garinku nan! Tsohuwa nan ita ta gyara komai na gurin da Ummata ta 6ata, sannan ta yi min wanka ta nad'e ni cikin wani zani na Ummata, ita ta yiwa mahaifiyata wankan gawa stab! Bayan an idar da sallar asubahi ta sanarwa da maza a masallaci akwai jana’iza a gidan mu.
Duk mazan Unguwar ba wanda yake da number wayar mahaifina, domin duk yanda suka so qulla alaqar maqwabtaka da shi ya qi bada fuskar hakan sai suma suka fita daga hanyarshi.
Matan maqwabta su suka hada kayan jarirrai masu matuqar yawa aka ba tsohuwar nan ta ringa saka min, tun ina jaririyata ina da farin jinin jama’a, duk wacce ta kalleni sai ta ji qaunata a cikin zuciyarta, hakan yasa na sami kyaututtuka mai yawa daga iyaye mata da maza.
Har aka yi kwana uku da rasuwar mahaifina bai dawo ba, don haka maqwabtan mu su ka yi addu’o’insu ga mahaifiyata suka watse, gidan mu ya rage daga tsohuwar nan sai ni ‘yar jaririyar kwana uku a duniya, wannan lokacin har na qware a shan madarar jarirai da maqwabta suka tara min katan-katan, na yi ‘yar qiba tamkar wacce ta yi kwana arba’in a duniya.
Kwanan mahaifiyata hudu da rasuwa mahaifina ya dawo daga tafiyar da suka yi shi da ubangidanshi, yayi mamaki tun a qofar get da ya ga qofar gidan shi a bude, ba kamar yanda ya barshi ba, don haka ya fara shirya kwandon bala’in da zai sauke mata idan ya shiga cikin gidan, kamshin hadadden girkin da ya jiyo daga ciki ya sa ya fara mai da masifarshi ciki don dai dama ya qware a son cin banza, ya fitar da kudin shi ya yi cefane ne dai ba zai iya ba.
Tsohuwar da ya gani tana tarairayar jaririya tsakar falon gidan yasa jikinshi ya fara sanyi, duk da dai a ranshi bai kawo cewar mahaifiyata Allah ya yi mata rasuwa ba, ko sallama bai yi ba, ya afka cikin falon yana dan muzurai na rashin gaskiya yana zare idanu.
Kallon kallo suka yi harna tsawon minti uku, ita bata ce mishi ba shi baice mata ba, wanda hakan yayi matuqar sanyayar masa da jiki, kwarjinin tsohuwar ya cika masa fuska don haka ya zame zuwa qasa yana gaisheta ba tare da ya san lokacin da ya yi hakan ba.
“Matarka Allah yayi mata rasuwa! kwanaki hudu da suka wuce, dawowarka na tsaya jira don in sanar da kai, da ba ka zo ka tarar dani a gidan nan ba, ga yarinyar da ta haifa maka, na rada mata suna Aysha.
Kana iya qare mata kallo harna tsawon awa guda, don da ita zamu wuce zuwa gidana, kamar yanda mahaifiyarta tayi min umarni.
Tana gama fadin haka ta miqa masa ni bayan ta kwantoni daga bayanta.
Zuciyarshi ta girgiza matuqa da rasuwar mahaifiyata, amma da yake namijin duniya ne ko qwalla bai yi ba, kuma sam bai alqanta rasuwar tata da laifinshi bane.
A zuciyarshi yake hasaso kalaman rainin wayon da ikon da tsohuwar nan take neman gwada masa akan ‘yarshi, don haka a ranshi yake fadin “Ma ji ma gani….”
Zirga zirgarta kawai take daga kichin zuwa daki ba tare da ta qara kallonshi ba, tana gama girkin abincin da take yi ta sake a kula ta zura hijabinta ta nufo gareshi ta ce,
“Ba ni ita nan, zamu wuce.”
A fusace ya dago kanshi da niyyar yi mata korar kare duk da dai idan ta tafi bai san yanda zai yi da ni ba, amma ya gwammace ko gidan marayu ne ya kaini. suna hada ido da ita wani mugun tsoronta da kwarjininta ya bugi zuciyarshi, ba shiri ya miqa mata ni hannunsa har rawa yake yi gurin miqanin.
Tana gab da ficewa daga falon ta juyo ta ce, “Gidana shi ne na qarshe a wannan layin daga bangaren dama, idan ka yi niyya duk abin da ka siya mata kana iya kawowa a matsayinta na diyarka.”
Tana gama fadin haka ta fice, daman tun safiyar ranar ta nemo almajirai suka kwashe duk wasu kaya da yake mallakina da nata zuwa can gidanta da yake qarshen layi.
***
Kwanan mahaifina uku a gida yana zaman makokin mahaifiyata shi kadai, ba abinda yake fitar da shi sai sallah, a can masallacine maqwabta suka yi mishi gaisuwar Ummata, a kwana na hudu ne da dawowar shi ya shiga kasuwar barci (Kasuwar saida gwanjo a garin Kaduna) ya ciko jakar gana must go guda da kayan jarirai ‘yan naira ashirin zuwa talatin, sai da ya kashe dubu biyu da dari biyar, yana siyan kayan yana cije baki shi a ganinshi ya yi mugun qoqarin azo a gani.
Rabon da ya kashe dubu daya a cikin kudinshi har ya manta, amma yau ya kashe dubu biyu har da dari biyar, sannan yaje ya sai geron kunu mudu uku da sukari rabin mudu, a nan ma dai sai da ya kashe dari biyar, ya hada lissafi gaba daya dubu uku.
Yana tuka ‘yar mota starlet din da Alh. Buba ya sai masa ya ke tunanin lallai wannan rana tana daga cikin ranakun tarihi a rayuwarsa, tun da har ya iya kashe dubu uku, cikin kudinshi.
Yana zaune a kan luntsuma-luntsuman kujerun da suka zagaye tafkeken falon tsohuwar da ko sunanta bai sani ba, da kwarin gwiwa yake wasa da hannuna, don yana ganin ya yi abin a zo a gani.
Tana zaune a can gefe guda akan kujera, a gabanta ta zazzage duk kayan daya kawo tana daddagawa daya bayan daya, tana yamutsa fuska.
Daga qarshe ta tattara duk kayan ta maida cikin gana must go din ta zuge zif din ta rufe kamar yanda ya shigo da jakar, tana kallon ledar ta gane abin da yake ciki saboda irin mai zane zanen nan ce.
Kallon shi take na tsawon mintuna uku shi kuma idanunsa yana kaina, a ran shi ya ke ta mamakin irin blawus masu tsadar da ake sanya min.
“Yanzu Sa’ad ka rasa abinda zaka siyowa Aysha a matsayinta na ‘yar jaririyar diyarka kuma ita kadai da ka mallaka a duniya sai wadannan gwanjunan?”
Shiru ya yi bai amsa ba illah qara durqusar da kanshi qasa da ya yi, a ranshi ya na jin qunar kalamanta amma ko idanu ya kasa hadawa da ita balle har ya iya mayar mata da martani.
“Allah ya wadaran wannan dukiya da kake tarawa tunda kai kan ka ba ka iya amfanawa kan ka balle har ka amfanarwa wani naka, kar ka manta mutuwa za ka yi ka bar dukiyar kuma duk sonka da su a nan duniya zaka bar su.” Tana gama fadin haka ta je har gaban shi ta karbe ni ta juya da nufin shigewa bedroom dinta, har ta kai bakin qofa ta juyo ta kalleshi tace,
“Ka tattara tunmokaranka ka tafi dasu, kuma daga yau matuqar irin wannan tsummar zaka kawowa Aysha to mun yafe maka.”
Ya dauki tsawon minti talatin a zaune yana tufka da warwara shi kadai, daga qarshe ne ya yi qarfin halin miqewa ya dauki jakar kayan da geron ya fice.
***
Tun daga wannan ranar mahaifina ya yanke shawarar daina ziyarta ta, duk wani ragamar hidimata ya barwa wannan tsohuwa, ita kuma hakan bai taba damunta ba, sai da na yi wata shida sannan ya sake kawo mana ziyara a tsaitsaye, a lokacin ganina da yayi ina tsayuwa gwanin ban sha’awa yaji matuqar mamaki, babu wani alamun da zai nuna cewa ina shan wahala, riga da wando ‘yan kanti masu matuqar tsada da kyau a jikina, anyi min kalba a gashina mai tsawon da Allah ya bani.
Tun daga lokacin ya koma baya kawo min ziyara sai bayan wata shida duk da cewa gidaje biyar ne a tsakaninmu, ita kuma tsohuwar nan bata qara taka gidan mahaifina ba tun da ta daukoni ina jaririya.
A haka har na shekara goma a duniya, a lokacin duk wani siga ta kyau ya fara bayyana a jikina, ina da matuqar wayau da hangen nesa da qwaqwalwa tamkar ‘yar shekara goma sha hudu.
Kuma Duk tarihin rayuwata na sani ne ta bakin wannan tsohuwa, kuma ta yi min ishara da mutumin da yake zuwa gidanta duk bayan wata shida shi ne mahaifina.
Na taso cikin wata iriyar rayuwa ce mai rikita tunanin mai tunani, Abin da zai baku mamaki shine tun da na fara wayo ban san wasu mutane ba, daga wannan tsohuwar dana girma a gurinta, sai kuma yaranta ‘yan biyu duk mata da suke kawo mana ziyara duk bayan kwana biyu, Sai kuma mutumin da aka kira mahaifina da yake kawo mana ziyara duk bayan wata shida.
Babu abinda muka nema muka rasa, amma kuma ban taba ganin lokacin da wani yake kawo mana kayan abinci ba, duk abin da naso ci shi nake ci, sutura kuwa ni kaina ban san iya yawan kayan sawan da nake da su ba, kuma duk kananan kaya ne masu tsada. Hassana da Usaina (yaran tsohuwar nan) suna da matuqar sona, su suke min komai na daga kitso, wanka, wanke kai, yanke farce, koya karatun boko dana arabic. Suna da ilimi sosai, duk ilimin da nake dashi daga garesu na samu ban taba taka makarantar Islamiya ko boko ba.
Ina shekaru goma sha biyu a duniya Allah ya dauki ran tsohuwa Zahra’u, duk zaman da na yi da ita sai a ranar na san sunanta, daga bakin wani farin dattijo mai dogon gemu daya biyo su Hassana zuwa gidan mu.
Shi ne mutum na biyar dana taba gani a rayuwata, su Hassana suna kuka suke nuna masa ni, ina rungume kan gawar tsohuwar ina shessheqar kuka, ina kiran don Allah ta tashi, kar ta tafi ta barni.
Da matuqar tausayi a fuskarsa ya kamo hannuna, sannan ya jani zuwa jikinsa, wata addu’a ya tofa min a tsakiyar kaina, minti biyu tsakani barci mai nauyi yayi awon gaba dani.
Ban tashi farkawa ba sai a wani daki na daban da ban taba gani ba a rayuwa ta, mutumin da aka kira mahaifina yana zaune a gefen gadon da nake kwance yana kallona, fuskarshi ba walwala ko kadan, balle in sa ran kallon kauna da tausayi irinna ‘ya da uba.
“Me ya kawo ki gidan nan?”
Sai a lokacin na gane cewa a gidan mahaifina nake, tuno rasuwa tsohuwar yasa na fara hawaye, da sanyin murya na ce masa.
“Allah ya yiwa Ammi rasuwa.” Dan haka muke karanta, ni da su Hassana
“Allah ya jikanta.”
Ya fada cikin tabe baki, saboda tsabar rashin imani da tausayi irin nasa.
“Ta ina kika shigo gidan nan?”
Da mamaki nake kallosa, tsabar haushi da baqin ciki yasa na yi masa wani kallon mugun tsana sannan na ce.
“Ni da gidan ubana har sai na nemi izinin shigowa?”
Ba shi da na fadawa magana kadai zuciyarshi ta buga ba, hatta ni da na yi maganar sai da zuciyata ta buga saboda tsoro, Kallon shi nake qyam da idanuna na kasa bari bugawar zuciyata ta bayyana a fuskata.
Matukar mamaki ne ya kama shi, don tsayawa ya yi baki da hanci bude yana kallona, muka yi musayar kallo na wasu ‘yan daqiqu, kowa da irin abin da yake sakawa a zuciyarsa.
“Irin tarbiyyar da ta koya miki kenan?”
Ya fada yana zare min ido fuskarshi ba walwala, bai bani damar furta komai ba ya ci gaba da cewa,
“Ni mahaifinki ne, don haka ba zan dauki iskanci da rashin kunya ba, dole ki saisaita kalaman bakin ki idan za ki yi magana dani, matuqar kina son mu daidaita, idan kuma ba haka ba zan dauki mummunan mataki a kan ki.”
Yana gama fadin haka ya sa kai ya fice daga dakin ba tare da ya kara kallon inda nake zaune ba.
Tabe baki nayi cikin rashin nuna damuwa da barazanar da ya yi min, a zuciyata na ce, “Wallahi babu wanda ya isa ya takuramin, mu zuba ni da kai.”
Sannan na yi qwafa na fara bin dakin da kallo.
Abin da ya bani mamaki shine, Komai da yake cikin dakin kamar gado da madubi da jakunkunan kaya duk nawane wadanda nake amfani da shi a gidan tsohuwa Zahra’u, har da karin wasu sabbin jakunkunan manya-manya wadanda ban san ko mene ne a ciki ba.
Yunwa nake ji don haka na miqe don in samarwa kaina abinda zan ci, idona ne ya fada kan agogon bango dake maqale a dakin, karfe biyar da kwata na yamma, wannan ya tabbatar min akwai bashin sallar azahar da la’asar a kaina wanda ban yi ba, don haka na fara tunanin yanda zan tambayi mahaifina ina ne ban daki?
Ina fitowa daga cikin dakin dana farka barci naga wani qofa a kusa da gurin, don haka na bude da tunanin ko bandakin ne? Ganin shine yasa na yi murmushi domin na tsani hurdar da zai hadani da wancan mutumin (mahaifina).
Ina zaune akan sallaya bayan na idar da sallar la’asar, hawaye ne mai zafi yake bin fuskata, ba kowa da komai nake tunawa ba illa tsohuwa Zahara’u, da rayuwar farin cikin da na yi a gidanta.
Amma wai yau gani a gidan mutumin da sam bai damu dani ba, kuma a hakan zan ci gaba da rayuwa har Allah ya kawo min mijin aure in bar qarqashin kulawarsa.
Addu’a nake ina shassheqar kuka ina nema mata gafara a gurin Allah madaukakin sarki, turo qofar dakin da aka yi ba tare da sallama ba yasa na dago idanuwa ina kallon mai shigowa.
Yana tsaye riqe da wani dan qaramin kofi da wasu qulle-qulle a hannunsa, nan take na shafa addu’ar ina goge hawayen fuskata da hijabin sallata.
“Ga abincin ki nan! Ban san da dawowarki ba don haka shi kenan ragowar garin da ya ragemin a gidan nan! A niyyata daman shi zan sha yau sai gobe idan na fita in auno wani, don haka tun da kin dawo ni na haqura ki sha kawai, ga quli-quli da ragowar suger nan na san zai isheki zuwa gobe.”
Tunda ya fara maganar nake kallon bakinsa bana ko qiftawa, domin ko kadan ban fahimci mai yake nufi ba, na ji yana batun gari da quli-quli da suger, na san dai suger domin muna amfani da shi ko a gidan Ammi, gari kuma qila yana nufin garin tuwo ne na semovita wanda tsohuwa take tuqa mana tuwo dashi lokaci zuwa lokaci, amma abin da ya kira quli-quli ban taba jin sunansa ba tun da aka haifeni. Domin in tantance ko meye yasa na matsa zuwa gabansa na amshi kofin da ledojin don in gani ma idanuna, da cokalin cikin kofin na ringa juya abin da ya kira gari ina ayyana yanda zai dankare min a cikin cikina matuqar na kuskura nasha wannan abin, dunqulallan abinda ya qira quli na ringa kallo da ido ina mamaki, daga bisani na kara a hancina don a zatona kashi ne aka shanya ya bushe, rashin jin wari yasa na gane ba kashi bane wani abin ne daban!
“Baba mene ne wannan?”
Na tambaye shi ina nuna masa garin da quli-qulin.
Ya kai maqura wajen zuciya da fusata, jira yake a ce qyat ya yi bindiga, don haka ya bani amsa da cewar
"Ubanki ne.”
“Daga tambaya sai zagi? Ni fa wallahi ban san ko me ye wannan ba, don ban taba ci ba, ni ban ma taba ganin irinshi ba"
“Shi uwarki taci ta rayu har ta haifeki.”
Bai bari na ajiye numfashi ba ya bani amsa da hakan, yana numfarfashi, kamar zai rufeni da duka.
Jin ya fara ambato uwata dake cikin kabari yasa raina ya fara baci, ina sonta duk da ban yi rayuwa da ita ba, na kalleshi tsawon daqiqu kafin nace,
“Ni kam wallahi ba zan ci abinda na tabbatar ba zai narke min a ciki ba, wadannan irin muggan abincin daka ringa turawa mahaifiyata shi yayi sanadin mutuwarta, bayan Allah ya taimaketa ta haifeni...”
“Ni kike fadawa wannan maganar?”
Hanunsa ya dago da niyyar wanke fuskata da mari.
Ganin hakan yasa na rintse ido ina jiran saukar mari a fuskata, karo na farko da wani hannu zai sauka a jikina da niyyar duka, Minti daya biyu ban ji saukar marin ba don haka na bude ido don ganin abin da ya dakatar da shi.
A tsaye yake, sai zufa yake ketowa daga kowace qofar gashi na jikinsa, hannunsa kuma miqe a iska ya tsaya qyam kuma daf dani da niyyar marina, qoqari yake ya maida hannun nasa baya ko kuma ya aiwatar da abin da ya yi niyya tunda farko amma babu dayan daya yiwu, hanun na maqale a iska.
Wani matsanancin tsoro ne da mamaki ya ziyarceni don haka na ja da baya zuciyata tana bugawa Fat!Fat!Fat! kamar za ta faso waje ta fito.
Dana qara kallon fuskan mahaifina kuwa sai abin yaso ya bani dariya, ya matuqar galabaita, a fuska kawai za a gane matuqar tsoratarshi balle kuma a kai ga yanda jikinsa yake mazari, rashin sanin abin yi da kuma ganin lokaci yana kara qurewa har ana kirayen sallar magariba a masallacin unguwar yasa na matsa kusa da shi.
Ruwa da yake bin qasan tiles din tsakar dakin ne ya bani mamaki, sai a wannan lokacin na tabbatar fitsari mahaifina yayi, duk yanda naso kar in yi dariya sai da na dara.
Hannuna na daga na tankwa6ar da hannun nasa zuwa qasa kamar an yi ruwa an dauke jijiyon da suka sagar masa da hannun suka saki. Da gudu ya fice daga dakin, ni kuma na ci gaba da qyalqyala dariya.
Ko don akwai yarinta ne a tattare dani a wancan lokacin sam ban dauki abin da ya faru da wani muhimmanci ba, ina gama dariya na sake dauro alwala na gabatar da sallar magariba.
Bayan na idar ne na zauna a nutse na fara bubbbude sabbin jakunkunan dana gani wadanda na san ba nawa bane har guda uku a cikin dakin.
Farin ciki mai tsanani ya wadaci fuskata ganin abincin gwangwanin dana leda kala-kala shaqe da babban jakar da saboda girmanta da qyar na iya zage zip din.
Jaka ta biyu sabbin kaya ne english wears masu matuqar yawa shaqe da jakar.
Jaka ta uku kuma dangin drinks ne shaqe a ciki, irin wadanda na saba sha a gidan tsohuwa Zahara’u.
Farin cikin daya cika zuciyata yasa na manta da babin mahaifina da halin da yake ciki, sai da na ci na sha na qoshi sannan na gabatar da sallar isha’i, na kwanta a gado da nufin yin barci. Tunanin tsohuwa Zahara’u dasu Hassana da Usaina, da irin rayuwa mai dad'in dana gabatar a gidanta ne ya dawo a zuciyata.
"Yanzu waye zai riga rarrashina yana shafa min kai har in yi barci? Waye zai ringa bani abinci a baki? Waye zan ringa yiwa shagwaba yana rarrashina? Waye zai ringa min kitso da kwalliya? Wa zai ringa koya min karatun boko dana larabci? Wa zai ringa dafa min duk kalar abincin dana buqata da wanda ban buqata ba masu dad'i? Wa zai...... wa zai.... wa zai..?
Ganin abubuwan dana rasa a rayuwata suna da matuqar yawa yasa na fashe da kuka ina kiran “Ammi (kamar yanda nake kiran tsohuwa Zahara’u kafin in san sunanta) Ammi don Allah ki dawo gareni.... Anty Hassana... Anty Hussaina... ku dawo gareni don Allah...” abin da nake mamaitawa kenan ina kuka ina birgima a kan gado.
Sai da nayi kuka ya isheni wanda ya daukeni tsawon awa uku, amma duk cikin wadanda nake kiran ba wacce ta amsani.
Shiru na yi ina ajiyar zuciya, idanuna sai zafi suke min saboda kukan dana dauki tsawon lokaci ina yi, rintse idanu na yi ina jiran barci ya daukeni ko zan sami sauqin baqin cikin da yake cunkushe a zuciyata.
Tsawon lokaci ba barci ba alamarsa daga qarshe dana gaji da juye-juye sai na tashi na zauna na sanya kaina a tsakanin cinyoyina na fada duniyar tunani mai zurfi.
Abu fa kamar wasa karamar magana na neman zama babba, kwana biyu ana wasan buya tsakanina da Abbana, kuma a wadannan kwana biyun ko barcin minti biyar ban samu ya daukeni ba.
Idanuna duk sun tashi saboda barci ba a cin bashinsa, duk iya tsawon awoyin da zan dauka a kwance ina jiran barci ya dauke ni sai dai in gaji in tashi zaune amma barcin ba zai zo ba.
Ina matuqar son in yi barci don har layi na ke yi idan ina tafiya a tsakar gida, kuma a wannan ranar tun daga sallar asubahi da mahaifina ya fita gida bai dawo ba, hankalina a tashe yake matuqa, na yi kuka harna gaji ba wani sassaucin dana samu.
Misalin qarfe biyu na ranar dana cika kwana uku a wannan hali na yanke wa kaina shawarar fita qofar gida ko zan sami mai taimakamin.
Sanye da riga t- shirt da wandon jeans wanda ya fito da dukkan suroin jikina, rigar ta kamani sosai, 'yan kananun kirgan dangin dana fara suna tsaye cas cas a qirjina.
Hula ne sanye a kaina amma duk da haka sai da ya tona asirin dogon gashin da nake dashi.
Qafata sanye da silifas din wanka na tura qofar get din gidanmu na leqa kaina waje a hankali, da yake layi ne na masu hannu da shuni, kuma ranar litinin ce ranar aiki unguwar tsit babu alamar mutane, ko na masu gadin gidaje.
Ina tsaye a qofar gidanmu ina hawaye na rasa ina zan dosa? kamar daga sama naga qofar get din gidan da yake kallon namu ya bude, wani kyakkyawan saurayi matashi ya fito sanye da kayan motsa jiki.
Kallon kallo ya gudana a tsakaninmu idona share-share da hawaye.
“Qanwata lafiya?”
Ya tambaye ni da kulawa a muryarsa.
Shiru na yi ban amsa masa ba, kuma ban daina kukan ba.
“Ko kina kukan tafiya da abbanki yayi ne?”
A bakin sa na ji wai mahaifina ya yi tafiya don haka na yi qarfin halin girgiza masa kai alamar a’a.
“To mene ne? Kina jin yunwa ne?” kai na sake daga masa alamar a’a.
Bai gaji ya sake tambayata
“Ko baki da lafiya ne?”
Da hanzari na daga masa kai alamar, “Eh.” Na qara da fadin “Don Allah ka taimaka min da maganin da zan samu in yi barci, yau kwana ina ta so inyi barci amma ko gyangyadi bana iya yi.” Ina gama fadin haka na rushe da kuka mai tsananin qarfi na tsuguna a qasa, hannu biyu na dora akai ina shassheqar kuka.
“Oh, sorry qanwata mai kyau, ba dai barci kike son ki yiba?”
“Eh.” Na fada bakina har rawa yake yi gurin fadin haka.
“Jirani a nan ina zuwa.”
Cikin gidan da ya fito ya koma ya tattaro min kwalaban magungunan tari da qwayoyi masu gusar da hankalin mutum leda guda ya kawo min.
“Ki yi ta sha har sai kin ji barci mai nauyi yana fizgarki sannan za ki daina sha.”
Abin da yace min kenan ya fara tafiya gudu-gudu zuwa inda ya nufa.
"Wannan rana ita ce ranar farko ta fara shaye-shaye na"
Ina fadin haka na fashe da kuka su Fatima suna tayani, sai da muka yi ya ishe mu, sannan na ci gaba da basu tarihin rayuwata.
"Tun daga wannan ranar matsalar rashin barci ya kau daga gareni, sabo mai qarfi ya shiga tsakanina da Mahfuz (kamar yanda ya bayyana min sunansa) ina kiranshi da “Yayana” shi kuma yana kirana da “Qanwarshi mai kyau”
Tun daga lokacin ya zama idan zan yi barci sai na sha wadannan kayan mayen nake yin barci, idan sun kusa qarewa zan sanar da shi, shi kuma bai tava gajiyawa gurin kawomin wadansu ba.
Idan mahaifina baya nan har gidanmu yake shigowa, kai har cikin dakina, amma ni ban taba kwatanta shiga gidansu ba.
Mu’amala tsakanina da Abbana kuwa ba yabo ba fallasa, daga gaisawa babu abin da yake hadani dashi, babu ruwanshi da ni, naci abinci ko banci abinci ba duk bai damu ba.
kuma baya kwana biyu a gida, kullum cikin tafiye-tafiye yake, yayin da ni kuma kullum qara shaquwa muke da Mahfuz.
Wata rana da daddare misalin qarfe tara da rabi na dare, a wannan lokacin na shekara har da wata biyu a gidan mahaifina, kuma har a wannan lokacin sai na sha kayan maye nake iya barci.
Mahaifina baya nan, don haka tun qarfe takwas na dare na rufe gida da qofofin dakunan mu, Kamar a mafarki nake jiyo qwanqwasa get din gidan mu a hankali, lokacin na yi mankas da kayan maye barci kawai nake shirin yi, jin bugun qofar ya qi qarewa yasa na miqe ina tangadi na fita zuwa gurin get din.
“Wa...ne...ne..?” Na tambaya da muryar maye.
“Qanwata mai kyau ni ne.” Ya amsa muryarshi qasa-qasa.
Bude masa qofar nayi ya shigo, ni kuma na lallava na koma ciki don ji nayi ina shirin faduwa qasa warwas, shi ya mai da qofar ya rufe ya biyo bayana zuwa cikin falo.
Bani a falon don haka ya bini zuwa cikin dakina.
Ina kwance nayi daidai a kan gado ina sharar barci, sanye nake da kayan barci masu matuqar ban sha’awa da nuna surar jiki.
A wannan dare Mahfuz ya yi niyyar keta min haddi kota wane hali. Amma ina Allah bai bashi sa’a ba, daga inda yake tsaye a tsakar dakin yana kallon surar jikina sanye da dan pant fari da farar best wacce ta kamani tsantsan. A saman best da pant din ne na dora rigar barci mai nuna tsiraici.
Yana tsaye yana kallonta cike da sha'awa, idan ya yunqura da nufin fadawa gadon kusa dani sai wani farin haske ya dakatar dashi. Wannan shi ake kira ga “Qoshi ga kwanan yunwa” ya fadi hakan a zuciyarsa,
“Ina... wallahi ba za ta savu ba, tsawon shekara daya da wata biyu ina wahala da yarinya amma lokacin fanshewa kuma ya gagara? Wannan sam ba zai yiwu ba.” Ya fadi hakan a fili yana maganan yana tube kayan jikinsa.
Yana tsaye haihuwar uwarsa a tsakar dakin, yana safa da marwa da tunanin ta inda ya dace ya afkamin don samun nasarar aiwatar mummunan manufarsa a kaina.
Rintse ido yayi ya yi miqa sannan ya daka tsalle da niyyar fadawa kaina, wanna karon ba haske bane ya tare shi, shoking ne da w…