7
by @sadiyanasir
Bakinta dauka da sallama ta shiga palon ta zauna gefen Jidde, Alhaji Goni kuwa tunda Falmata tayi sallama ta shigo idanunsa yake kanta, ji yayi ba zai iya kauda idon sa daga kallon ta, tabbas tayi mishi kyau, kuma kwalliyarta da kayanta sunbi jikin ta, kuma dama Falmata mai kyau ce "Amarya baki lefi ko kin kashe Dan masu gida, Sannu da fitowa? Alhaji Baba Gaba ya Ambata, Murmushin jin dadi Falmata tayi ta Dan sun kuyar da Kai, Alhmdullah dukkan godiya gareka Ubangiji Mahalicci daka bamu aron Rai ka gwada mana wannan rana cikin koshin lafiya da aminci, Jidde da Falmata ina yi muku fatan Alkairi da fatan mun yini lafiya?"
"Alhmdullah! Lafiya kalau"
"Masha Allah! Abokina ina tayaka murnar babban cigaba daka samu na karin iyali a Rayuwarki, Allah ya baka ikon Adalci A tsakani! Ya kuma baku zaman lafiya. Jidde ga kanwa an kawo miki, ki riketa tamkar 'Yar-uwarki da kuka fito ciki daya, nasan zaki iya, sannan Bahaushe yace idan kana da kyau to kara da wanka, kina da hakuri kamar yanda abokina ya ambata kuma ni shaidane, toki kara akan Wanda kike dashi, kece Babba dole nace kiyi hakuri Jidde, ko ba'a zamantakewa ba Jidde kin girme wa Falmata, ki jata A jikinki ki daurata a hanya, domin kece kika san halin Mijin ki, da Abinda yake so da wanda baya so, dole Sai kin Fahimta da Falmata wannan.
Ke kuma Falmata ya zama dole kiyi biyayya wa Jidde, domin ke ki kazo kika sameta a gidan, don haka tana gaba dake, duk Abinda ya shiga miki duhu ita zaki tambaya sabida ki samu mafita, ku hada kanku ku sama wa Mijin ku farin ciki yaji cewar yayi dacen Aure, Allah ya kade fitina ya baku zaman lafiya".
"Ameen ya rabbi" Suka Amsa gaba daya "Abokina inaga na fadi Abinda zan iya fadi, Jidde da Falmata Sai da safe ni zan wuce sabida dare ta soma, Allah ya Baku zaman lafiya ya kauda fitina A tsakani".
"Shikenan kuje ciki ina zuwa? Zan rakasa?" To sukace ko wacce ta mike tayi hanyar kofa, Sai da yaji sun jawo kofa kafin Alhaji Goni ya dubi Baba Gana "Har yanzu mamaki nake wai nine da Mata har biyu Abokina? Ban taba tunanin haka A rayuwata ba, sabida ni bani son Matsala, ina ganin yanda kake gudanar da rayuwarka da iyalanka, wallahi shiyasa Mata daya ta isheni" Dariya Baba Gaba yayi "Tabbas idan Mace ta wuce daya A gida dole sai anyi hakuri kuma ankai zuciya nesa Goni, domin za kaga abubuwa iri da kala, da kyawawan halayya da munanan halayya wasu Matan sai anyi musu abokiyar zama suke fitowa, sabida kishi babu Abinda baya sawa, ko Jidde da kake gani bata da hayaniya to ba Abin mamaki bane ka fara karban Shari'a nanda wani lokaci, dalili kuwa idan Falmata ba mai hakuri bace dole ta kai Jidde Makura har ta fara tanka maka, kai dai kawai Allah ya kyauta ya baka ikon Adalci".
"Huhmm to kai wata hanya kake gani zanbi don ganin an samu zaman lafiya a gidan? Inba Hajja ba duk duniya babu wanda zai sani a damuwa haka ina zaman lafiya ta"
"Ko ba Hajja Abokina dole sai ka Aure Falmata, domin tana cikin kundin Kaddararka, don haka ka daina ganin lefin Hajja, ita kawai sanadi tayi. Magana ta gaba idan har kana son gidan ka A samu zaman lafiya dole ka kasance mai Adalci, Auren ka da Falmata Kaddarar kace ba wai kana Sonta bane, Amma Abinda na keso ka sani Yau da gobe ta wuce wasa, dole Akwana a tashi za kaso Falmata musamman idan tana kyautata maka, to Abinda nake so da kai shine ko da wasa kada ka nuna wa Falmata cewar kafi son Jidde ita Auren hadi akayi muku, ita ma Jidde koda wasa kada ka nuna mata cewar zaman hakuri kake da Falmata, idan ba haka ba kuwa kai zaka fara kunno matsala a gidan ka, duk wacce zata kawo maka sukar daya kace dukan su So ne yasa kake tare dasu, to inaga idan ka daure kayi haka zaka samu sauki". Ajiyar zuciya Alhaji Goni ya sauke, domin dai Jidde tasan bayar wani son Falmata, duk da yasan bayi da matsala da ita sabida tana da hankali, ya tabbata ba zata goranta wa Falmata ba "Nagode Abokina kuma insha Allah zanyi Abinda kace Allah ya taimakeka Akai".
"Ameen ya rabbi" Mikewa su kayi Alhaji Goni ya rakasa har jikin Motor ya dawo ya dauki Kazar daya saya musu ya shiga side din. Dakin Jidde ya nufa yasa key ya bude, kishingide a bakin gado ya hangota tayi tagumi da Alama dai tunani take, sallama yayi ya karaso ya zauna A gefenta gami da Ajiye Mata ledar kaza guda daya "Lafiya kuwa Jidde?" Dago ido tayi tare da Murmushi "Lafiya kalau Abban Abie, Akwai gajiya a jiki na shiyasa na dan kishingide nasan zaka shigo muyi sallama, na tabbata idan na kwanta barcin zanyi" Kare mata Kallon yayi! Nan yaga idanunta sun canza launi Alamar tayi Kuka "Amma ya naga idonki haka?"
"Ni kuma Abban Abie?" Ta fada adan razane "Eh naga kamar Hawaye ke saukowa?" Murmushi tayi "Yanzu fa nake fada maka na gaji barci ne A idona, shine dalilin da yasa idon yake ruwa" Kama hanunta yayi "Nasanki da boye damuwa Jidde, na san ba Lallai ki fada min gaskiya ba, Amma ki sani bana son kisa damuwa A zuciyarki game da wannan Aure, sanin kanki dai babu wata Mace mafi soyuwa A zuciya ta bayan ke, idan ina ganin damuwa A fuskarki zuciyata ba zata taba samun nutsuwa ba? Don Allah?" Ya kareshe Maganar fuskarsa dauke da damuwa. Murmushi Jidde tayi "Bakomai Abban abie, babu wata damuwa da nasa A zuciya ta, Ai Aure sunnan ce ta ma'aiki (S.A.W) babu yanda za'ayi nace bana so kaji, don haka karka damu, ya kamata ka isa zuwa ga Amarya, kaga bakuwa ce kuma dare tayi" Ya Dan jima yana kallonta kafin yace "Allah ya miki Albarka ki rakani dakin mana?" Zaro ido tayi "Ni Jidde inje inyi me? Koso kake Yau daya Falmata ta tsaneni? Jeka kaji Malam?" Murmushi yayi "Shikenan saida safe"
"Allah ya tashemu lafiya" Mikewa yayi tabi bayansa zuwa kofa don ta rufe, suna isa ya jawota jikin sa ya manna bakin sa A nata, sosai yake kissing dinta yana shafa ilahirin jikin ta, tun tana kame jikin ta tana gwada mishi bata So harta saki jiki ta bashi hadin Kai, sosai suke gwada wa juna so, sun jima A haka har sai da ya tabbatar data samu nutsuwa kafin ya saketa ya koma gefe yana mayar da numfashi, kallon ta yayi yana jin Kaunarta na dukan zuciyar sa "Ina sonki Jidde" Ya fada murya A shake tare da daukar ledar Kazar sa ya fita.
Rufe kofar tayi ta dawo gefen gado tana sauke numfashi, tadan jima a haka kafin ta fashe da Kuka mai tsuma zuciya, wani irin Kishi da Kaunar Mijinta ne ya tokareta A kahon zuciya, shikenan Yau Abban Abbie zai kwana da wata Mace ba ita ba? Sosai take kuka tana jin takaicin Falmata, musamman yanda taga Abban Abie ya kasa dauke idanunsa daga barin kallon ta lokacin data shigo palon, kuma yanzu yazo ya isheta da dadin baki wai yana Son ta? Na Miji kenan?. Haka dai tacigaba risgar kukan ta daga karshe ta mike ta dauro Alola tayi nafila raka'a biyu ta kwanta.
Alhaji Goni kuwa kai tsaye dakin Falmata ya nufa, dake yana da key a hanunsa da kansa ya bude kofar ya shiga, babu kowa a dakin Sai karar Ruwan dake tashi a toilet. waje ya nema ya zauna yana jin sassanyar kamshin turaren dake dakin, A haka har Falmata ta fito, a razane ta dago ido ta dubesa domin ba tayi tsammanin ganinsa a dakin ba, sunkuyar da Kai kasa tayi ta karasa A hankali "Sannu da shigowa Yaya?"
"Yauwa Kanwata Sannu ya gajiyar dawainya?"
"Alhmdullah Yaya?"
"Masha Allah zoku zauna? To tace ta nemi waje ta zauna, kare mata Kallon yayi daga sama har kasa kafin ya fara magana, muyi salati wa Annabin Rahma (S.A.W) don nuna godiyar mu wa Allah (S.W.A) daya gwada mana wannan rana. Hanu suka daga su kayi salati wa Annabin Rahma. Falmata Yau kin zama Matata Allah ya Amsa, ina Addu'a Allah yasa shigowarki gida na ya zama Alkairi, Allah ya bamu zuri'a masu Albarka, ya kuma bamu hakurin zama da juna"
"Ameen ya rabbi" Ta amsa "Falmata ke kanwata ce ko bani kike Aure ba nasan baza kiso Abinda zai daga min hankali ba, za kiso farin ciki na , bare kuma Aure ya hadamu, don Allah Falmata ku hada kanku da Jidde ku zauna lafiya? Idan kuka min haka zanji dadi! kuma zaku sami yanda kuke so A wajena, wallahi Falmata bana son damuwa Sam". Murmushi tayi "Bakomai Yaya insha Allah zaka sameni mai bin duk Abinda kake so"
"Yauwa Yar Albarka, muje muyi Alola muzo mu kara nuna godiyar mu wa Allah?" To tace suka mike tare zuwa toilet. sosai Alhaji Goni yayi Addu'an samun zaman lafiya tsakaninsa da Matansa biyu. Bayan sun idar ne ya jawo ledar Kazar ya Umurci Falmata data zauna suci tare, haka dai tadan tsakura wai ita kunya. Suna kammala ci suka cigaba da hiran yanda hidimar bikin ta kasance, daga bisani suka kwanta barci.
A wannan dare Falmata taji jiki, domin Alhaji Goni bai san tayi gyara sosai haka ba ya kusanceta a matsayinta na Bazawara mai Yara Uku, shiyasa tayi matukar galabaita, shi kuwa banda Albarka babu Abinda yake saka Mata, domin ya sami nutsuwa wuce tunani A wajen Falmata, bai taba tsammanin Falmata zata bashi farin ciki kamar yanda Jidde take bashi ba. Bayan sun yi wanka sun dawo sun kwanta haka ya jawo Falmata jikin sa ya rungume, ita kuwa tuni barci ya dauketa sabida wahalar da tasha.
Washe gari kuwa Makara Alhaji Goni yayi domin bai samu damar zuwa Masallaci ba, shiyasa yayi sallah A gida ya koma ya kwanta. Jidde kuwa tun Assalatu data farka bata sake rintsawa ba, tana idar da Sallah ta nufi dakin da Hafsa take Kwana. zaune ta sameta tana gyara kayan su A Akwati, domin Mijin ta yace ta koma Yau, zama tayi A gefenta "Ya naga haka Hafsa?"
"Wallahi Aunty Bashir ya daga min hankali tun cikin dare akan na dawo Ummi ba lafiya, nace ya dauketa ya kaita wa Mama yaki yace kawai na dawo, shine nake hada kayana idan na fito gaisuwa saina fada Niki".
"Ikon Allah to meye ya sameta?"
"Wallahi ban sani ba"
"Gaskiya banji dadi ba, nida na dauka zaki kai sati?"
"Ni kaina hakan nake so Amma ya zanyi?"
"Hakane ciwo yafi komai, ki koma bakomai Allah ya bata lafiya".
"Ameen"
"So nake na jirayi Abban Abie idan ya dawo Sallah in tambayesa meye za'a dafa wa Amarya sai in saka Saddiqa tayi?"
"Eh hakane, to ki duba koya dawo?" To tace ta mike ta fita. Palo ta nufa ta zauna domin tasan yakan dan tsaya lazimi A Masallaci! zuwa shida saura yake dawowa, Wayar ta ta kunna Data ta cigaba da ganin Video's A Tictok, Amma Abin Mamaki har rana ta fara fitowa babu Abban Abie babu alamarsa, dialing call ta shiga ta kira Number sa, harta tsinke bai dauka ba, da sauri ta sake kiran sa.
Falmata na kwance A gefensa taji vibration na wayar, da kyar ta iya bude ido ta jawo wayar, Final choice taga Anrubuta, wani uban tsaki taja ta dannan busy, domin tasan Jidde ce, tashi tayi ta zauna, to inba munafurci ba meye na kira da farar safiya haka tasan yana dakin Amaryarsa? Tsaki taja ta sauko daga gadon ta wuce toilet da wayar "Ni kika samu Jidde, wallahi na fiki bariki".
Jidde kuwa faduwa gabanta yayi jin ansaka mata busy a wayar Abban Abie, take ta fara tunanin anya lafiya? Ko Aiki Abban Abie yake baya saka mata busy! amma Yau busy? Hankali a tashe ta sake kira.
Falmata na isa toilet wani kiran ta sake shigowa, Rai a bace ta dauka tayi nesa da wayar "Baby ina kasa wayarka? Jidde Ta fada murya A sanyaye, Kwafa Falmata tayi, har za tayi Magana sai wata zuciya ta bata shawara, Ajiyar zuciya ta sauke tayi dariyar Mugunta. Abban Abie baka jina?" Jidde ta sake Anbata.
"Wallahi kana da Abin dariya, ka bari na dauka na fada mata kayi nisa A kogin soyayya ta sake kira Anjima, ni kaina ban koshi ba sabida kana da dadi Yaya. Falmata ta Ambata tare kai wayar kunnenta. Malama wai lafiya? Ya za'ayi Mutum yana dakin Amarya yana hutawa ki wani damesa da kira? To bani son haka?" Tayi tsaki ta kashe wayar.......