10
by @sadiyanasir
Kubra kuwa tsaban gurmi yana damunta tana fita a gidan Alhaji Goni mai makon tayi makaranta gida ta koma, parking Motor tayi A waje Maigadi yana ganinta ya bude mata kofa, kutsa kai harabar gidan tayi, nan ta hango Larai da Hajja zaune a carpark suna kallon yanda Dawisu suke shawagi a tsakar waje, daga nesa Hajja ta hango Kubra tana tahowa "Ikon Allah meye ya dawo da Auta bayan tace makaranta zata wuce?" Kafin Larai mai akin ta amsa Kubra ta iso "Hajja hutawa kika fito yi?"
"Eh Auta ya Akayi dai? Kin fasa zuwa makaranta ne?"
"Aa Hajja daga nan wucewa zanyi sako nazo fada miki?"
"To Larai bamu waje ko?" Da sauri Larai ta mike tabar wajen, zama Kubra tayi ta kama hanun Hajja "Kin san miye Hajja? Idan ba tashi tsaye ki kayi da Addu'a akan Yayan muba wallahi nan gaba kema ba zai miki biyayya ba".
"Kamar yaya Kubra?" Nan ta kwashe Abinda ya faru ta fada wa Hajja "Ni kin San Abinda yafi bani takaici? Jidde ta dubi tsaban Idona tace wai na kawo Abinci A banza, matukar ba ita tace yaci ba bazai ciba, sannan tace daga Yau an daina kawowa Ai Akwai masu girki A gidan, idan Falmata bata son Abincin masu Aiki ta shiga ta dafa".
"Jidden tace haka Kubra?"
"Ai wallahi Hajja Kadan na fada miki cikin abinda ta fada, wannan shi yafi batan Rai shiyasa na tsaneta, gashi sam bayi ganin laifin ta ko kadan" Ajiyar zuciya Hajja ta sauke "Kiramin shi A wayarki?" Zaro ido Kubra tayi "Hajja so kike yazo ya dokeni? Yace da wayata ma aka kira aka tsayar mishi akan Matarsa? Ai wayar ki zan dauko miki cikin hikima ba sai ya fahimci Nina fada miki ba"
"Shikenan dauko min wayar A daki" A hankali Kubra ta mike ta shige cikin gida ta dauko wayar Hajja, tana fitowa ta kira Yaya Goni. Yana Office yana duba wasu file's kiran Hajja ya shigo, cikin girmamawa ya dauka bakin sa dauke da sallama "Hajja Antashi lfy?"
"Alhmdullah ya gida yasu Falmata da Yara?"
"Lafiya kalau Hajja suna lafiya na barosu a gida, ni kuma gani a company nazo yin wani abu"
"Allah sarki baku hadu da kubra ba kenan?"
"Mun hadu ina tsammanin tana gidan"
"Ikon Allah ita daza taje makaranta meye nata na tsayawa daga mika Abinci? Ba matsala gobe wa Larai zan bada Abincin ta kawo muku"
"Um Um Hajja nace da Anbar Abincin haka kinga Akwai Saddiqa babu Abinda ba za tayi ba, idan ma babu Saddiqa Akwai Jidde na tabbata ba zata gajiya ba, sam bani so kina wahala, don Allah Hajja ki huta?"
"Ni nace maka ina bukatar hutu akan haka? Koka manta lokacin da Jidde tazo gidan nan sati guda akayi ana kai muku abinci? Sai yanzu ne za kace a'a sabida ka gwada min ba Kai kake son Falmata ba?"
"Subhanallah Hajja ba haka bane nufi na, Amma kiyi hakuri, wai naga Jidde zata iya komai ne Hajja? Na tabbata babu Abinda Falmata zata nema ta rasa a wajen Jidde"
"Nifa ban gane maka ba? Duk maganar daza kayi saika Anbato Jidde ciki, Ita Falmatan bata da 'Yanci ne? Ko ance maka bata iya abinci bane? Ai idan dafawar take so za tayi, Amma wannan karramawa ce A matsayinta na Amarya, Matarka tana fama da bakin kishi Kai A tunaninka zata tashi da safe don hada wa Falmata abin kari? Sabida bakin hali irin nata Ace Mijin ki zai kara Aure Amma Ace Mutum biyu kika gayyata, Ina fada maka ka shiga hankalinka dani?"
"Ba haka bane Hajja, idan baki bukatar Jidde ta dafa taba Falmata to Ai Saddiqa Aikinta kenan A gidan, Jidde ta dauko tane sabida hidima wa gida, kuma wallahi da nasan zaki kawo abinci dana hanaki Hajja".
"Hakane sabida Matarka tana gwada maka ban isa na kawo abinci kaci ba kenan? Shiyasa tana ganin Kubra ta shiga kitchen sabida munafurci ta hada maka Abin kari? To kaji tsoron Allah? Dafa Kirji Kubra tayi ta zaro ido tana Alama wa Hajja tayi shuru, to bari kaji infada maka daga yanzu ba zance daga Yau ba, idan har ka sake cin Abincin Jidde ranar girkin Falmata bada izininta ba ban yafe ba, kabar kowa ta sami lada ranar girkin ta bani son wariya. kuma Saddiqa da kake fadan cewar tana hidimar gida Ai jidde ce ta kawo ta ba kai ba, Falmata ma zan turo mata wacce zata taimaka mata ta fannin gida"
"Kiyi hakuri Hajja Amma Falmata ce tace miki banci Abinci ba? Lipton kawai nace Jidde ta kawo min sabida zan fita, Amma ni banki cin Abincin ba"
"Allah mai ilko Ashe Akwai lokacin da zanyi magana katuhumeni?"
"Kiyi hakuri Hajja hakan bazai sake faruwa ba"
"Shikenan ya wuce, Amma ka sani ni ba muyi waya da Falmata ba, don haka idan ka canza Mata fuska akan haka nida kai wallahi?"
"Bakomai Hajja insha Allah"
"To Allah ya taimaka ya maka Albarka"
"Ameen ya rabbi Hajjata nagode" Bakomai tace ta kashe wayar.
"Hajja ya akayi haka? Ke da nace ki sakaye zance kar ya fahimci nice na fada miki sai gashi kina fada masa? Haba Hajja?"
"Barni kawai Kurbra Raina ya baci da kalaman sane, maza tashi ki tafi makaranta"
"Shikenan Hajja" Ta mike ta dauki Jakarta ta fita.
Jidde da Yara kuwa suna dawowa A palo suka yada zango, Sabriya ce ta dubi Jidde "Mummy ina Aunty Falmata? Dady yace tana cikin gidan nan? Inane dakin ta?"
"Eh tananan dazu ta fito muka sha hira lokacin kuna makaranta"
"To Mummy muje dakinta?" Shuru tayi tana nazarin barin su zuwa dakin, tunda ga irin halin da Falmata tazo dashi gidan. Murmushi tayi ta dubi Sabriya "Ki bari zata fito Anjima saiku shiga dakin nata tare" To sukace suka cigaba da kallon Film, A haka har Akayi kiran Sallar Azahar. Suna shirin barin Palon Babangida kanin Falmata da Yaranta guda uku Fahad! Lukman da Ja'afar suka shigo, su Sabriya suna ganinsu suka mike sai jikin Babangida suka rubgumea, fuskarsa dauke da fara'a shima rungumesu yana musu Oyoyo. Dan rusunawa yayi yace "Aunty Jidde barka da rana?"
"Yauwa barkan mu Babangida ya gida yasu Gwaggo? Fatan ka barosu lafiya?"
"Lafiya kalau tace agaisheku"
"Muna amsawa, Aa su Fahad ne a gidan namu ya akayi? Ku zo mana mu gaisa?" A kunya ce Yaran suka karaso suka zauna a gefenta tare da gaisheta, Amsawa tayi tana tambayarsu gida da Abban su. Babangida kuwa daga tsaye ya kira Falmata A waya cewar gasu A Palo, bata dauki lokaci ba ta fito sai cika take tana batsewa a haka ta sauko kasa.
Yaranta suna ganinta suka nufi Inda take suka rungumeta, ganin haka yasa su Sabriya ma mikewa zuwa gareta, fuska A washe tace "Aa Sabriya kun dawo daga school ne? Amman ya gida? Kuzo mu haura sama?" Kama hanunsu tayi suka nufi sama harda Babangida. Ganin sun watse a palon yasa Jidde mikewa ta nufi daya daga cikin daku nan dake gefe tayi sallar azahar, tana fitowa ta nufi kitchen don ganin meye Saddiqa takeyi har Azahar, tana shiga ta samu Saddiqa ta hada musu jalop rice yaji busasshen kifi sai kamshi yake, haka ta tsaya ta taimaka mata suka karisa sauran Aikin. Komai gwanin sha'awa Saddiqa ta jera a dinning, Jidde tana ganin komai ya kammala tace "Saddiqa ki haura sama kice Auntyn su da Yara su fito lunch is ready" To tace ta haura tayi knocking din kofar, Sabriya ce tazo ta bude, ganin Saddiqa yasa ta matsa mata ta shigo, a dadare ta tsaya tace "Aunty barka da Rana?"
"Yauwa Barka ya Akayi?"
"Aunty Maman Amaan ce tace Abinci ya Kammala Ku fito" Kallon Saddiqa tayi sama da kasa kafin tace "Cikin ku wacece ta dafa Abincin? Sannan meye aka dafa?"
"Nice na dafa Aunty" Ta ambata da sauri "Okey to a wani dalili yasa baki tambayeni meye nake Son a dafa A gidan ba? Da girmanki kinsan idan Miji ya kwana A dakin mace to itace za tayi girki, Amma kizo kina fada min wani Angama Abinci? To Indomie zanci bani bukatar Jalop, daga yau matukar kinsan nice A kitchen ko ruwa ban Amince ki dafa ba tare da sanina ba?"
"Kiyi hakuri Aunty zan kiyaye, Abinda yasa nayi Jalop din time table nabi" Tabe baki Falmata tayi "A tunaninki Alhaji ne zaici jalop rice?"
"Yana ci Amma idan kince A canza zan mishi nashi"
"Okey to ki bari zan tambayesa meye yake so sai Adafa mishi".
"Shikena Aunty"
"Alright Yaran suna fitowa yanzu, ni kuma ki dafamin Indomie yanzu ki kawo min" To tace ta fice da sauri, haka Falmafa ta hada kan Yaran ta turasu down step. a zaune suka sami Jidde tana dakon jiransu, zama su Kayi gaba dayan su Saddiqa ta soma serving dinsu, kallon Saddiqa tayi "Ina Autyn nasu?"
"Tana sama tace baza taci Jalop rice ba Indomie zan dafa mata" Murmushi Jidde tayi "Shikenan to babu matsala" Saddiqa tana gamawa dasu ta wuce kitchen ta daura Abinda Falmata ta sakata ta dauki Abincin Babangida ta kai masa daki, yana dafuwa ta zuba A Plated ta kai wa Falmata daki, tana Ajiyewa tace "Tsaya ina zuwa? Wayarta ta dauko ta kira Alhaji Goni, yana Motor tare da Baba Gaba suna wani lissafi kiran nata ya shigo, ganin number Falmata yasa ya dauka Hello Yaya?"
"Na'am Falmata ya Akayi?"
"Lafiya Yaya dama tambayarka zanyi meye za'a dafa maka kafin ka dawo? Shuru yayi yana kara gaskata tare suka shirya komai da Hajja, kayi shuru Yaya?"
"Falmata ki dafa duk Abinda ya kwanta maki a rai zanci, amma kar kiyi da yawa"
"Shikenan saika dawo, Allah ya tsare min kai a duk inda kake! ya kuma dawo min da Kai lafiya Mijina"
"Ameen ya rabbi Falmata, Allah ya miki Albarka" Ya Ambata cike da jin dadin Addu'arta "Ameen Yayana" Tana katse kiran ya dubi Baba Gana "Kasan wani Abin mamaki Abokina? Yau da safe kawai Hajja ta Aiko da breakfast sai kace Budurwa na Aura ko kuma Auren Fari? Hajja harda jin Haushi sabida banci ba? Kaji fa kamar bani da Mata a gidan? Wallahi abin ya bani mamaki Baba Gana" Dariya Baba Gana yayi "Ikon Allah kuma?"
"Huhm sabida nace tayi hakuri ta daina kawowa shine har tayi min umurni, matukar ranar girkin Falmata ce bata Amince naci Abincin Jidde ba tare da saninta ba, ni kuma Abinda yasa nace Jidde ta kawo min breakfast sabida naga Falmata jiya tazo gidan, ya kamata ace ta samu hutu A matsayinta na Amarya kafin ta soma dawainya dani"
"Kayi hakuri Alhaji Goni dole zaka rika samun abubuwa irin haka, musamman yanda Hajja take son Falmata dole wani Abin hakuri za kayi kana fahimtar da ita A hankali. Magana ta gaba kaima kayi kuskure Abokina, ko Falmata ta kira Hajja A waya ta fada mata abinda kayi mata bata da laifi, dalilin meyasa kasan A dakin Falmata ka kwana za kaci Abinci A dakin Jidde? Ayi domin Allah fa? Ai dole Ran Falmata ya baci, domin za taso rana irin ta yau taga tarairaya A wajenka sabida kunyi kwanan sunna, gaskiya ka gyara. Kuma tunda Falmata ita taga bata bukatar hutun shikenan ta shiga ta dafa Ai hutun Jidde ce, batun kawo Abinci kuma gaskiya kaje ka samu Hajja ku fahimci juna sam hakan bai dace ba, gida kamar wannan Ga Mace A gidan Amma ace sai andafa Ankawo a waje? Abin baiyi tsari ba.
"Hakane insha Allah zan sameta zanyi Mata magana ta fahimta"
"Yana da kyau hakan" Hira su sukacigaba dayi kafin suka bar wajen suka nufi gida. Wani Abokin su da matarsa ta haihu dubiya.
Falmata kuwa suna gama waya da Alhaji Goni ta sauko zuwa kitchen, ko sannu ba tayi wa iidde ba ta wuce Abinta sai kada jiki takeyi, domin ta dau dammara a zuciyar ta matukar Jidde ta sake gigin kaiwa Yaya Goni Abinci ranar girkinta sai dai Ayi wacce za'ayi, babu Abinda ya dameta da jiya tazo gidan. Jidde na ganin ta nufi kitchen tace wa Sabriya maza taje ta kira Saddiqa tazo, da sauri ta mike ta nufi dakin Saddiqa ta kirata, tare suka fito Saddiqa ta durkusa "Aunty gani?"
"Maza kije naga Auntyn su ta shiga kitchen, idan wani Abin take so kiyi mata?"
"Shikena Aunty. kitchen din ta nufa ta sami Falmata sai dube-dube take, Aunty wani Abin kike bukata?" Tabe baki tayi "Babu Abinda nake bukata so nake ki gwada min komai dake kitchen din nan na Anfani, zan hada wa Mijina Abincin, sannan inba nice na kiraki ba bani son shisshigi"
"To Aunty Angama Insha Allah". Duk wani Abinda Falmata zata bukata ta fannin girki tsaf Saddiqa ta gwada mata, tana gamawa ta fito ta bata guri, haka ta shiga kicinyar Aiki, nan ta samu ta hada mishi Cus-cus da kayan lambu da miyar hanta, side din dasu Halima suka Ajiye mata kayan anfanin kitchen ta nufa ta dauko sabon flak's da tire, haka tazo ta jeresu gwanin sha'awa. Abarba ta dauko A fridge ta gyara ta zuba A blender ta markada ta hada misa juice ta Ajiye cikin fridge.
Saddiqa kuwa tana fitowa Jidde ta tambayeta meye dalilin fitowarta bayan tace ta tsaya tayi Mata Aiki? Nanta kwashe yanda su kayi ta fada Mata, murmushi Jidde tayi "Karki damu duk lokacin da take bukatar taimakonki kiyi Mata Saddiqa"
"Shikena. Aunty.....