IYALAINA

14

by @sadiyanasir


    Saratu kuwa kamar yanda tayi Alkawari wa Jidde Ana idar da Sallar la'asar ta dauki himma sai gidan Alhaji Goni, A gate su kayi karo dasu Sabriya za suje Islamiya, haka Motar su ta tsaya suka gaisa da ita suka sa kai, tun kafin ta karasa kofar da zai sadata da Palon gidan ta kira wayar Jidde akan ta fito su shiga tare, matukar ta shiga wata banza ta nemi ta raina mata wayo to zasu dibi yan kallo sai dai Alhaji Goni yace karta sake shigo masa gida.


Jidde tana kishingide A jikin gado tayi sallar la'asar kenan tana cigaba da tunanin rayuwa kiran Saratu ta shigo, da sauri ta dauka "Kawata ya Akayi?"


"Fito mu shigo tare?" Tace da ita ta kashe wayar, mayafi ta dauka ta sauko ta bude kofar, tana hango Saratu tayi murmushi "Yau kuma sai An shigo dake Hajja? Hararanta tayi "Ni kinsan ba kanwar lasa bace yanzu sai nayi illah wa Mata kin san bana daukar raini, to gwara Azo A shigo dani kawai" Dariya Jidde tayi "Baki da dama Saratu"


"Ke dai mu shiga daga ciki, suna shigowa Palon Saratu ta fara waige waige, ina shu'umar take?" Hanu Jidde ta gwada Alamar tana upstairs "Ina ga tunda ya fita bata fito ba" Haurawa sama sukayi zuwa dakin Jidde, a gadon ta suka yada zango Saratu ta cire mayafi ta dubi Jidde "Wai meye yake faruwa ne Jidde? Kwana biyu rak rabuwata dake Amma kin rama? Haba da Allah"


"Huhmm damuwa ce Saratu, wallahi nan gaba sai na zamo bulala tsaban rama idan ba'ayi wasa ba, ke dai barin kawo miki ruwa ki sanyata zuciya kafin kiji bayani"


"Aa kyale ruwan nan muyi magana ina nan har Magrib" Gyara zama Jidde tayi sosai ta dubi Saratu "Wato ina ganin jarabawa daga zuwan Falmata gidan nan Saratu, lokacin da kike bani labarin Hamza da Matar sa sai inaga ba zan fuskanci irin wannan matsalar a gida naba, Ashe dai Mazan duk halinsu daya idan su kayi karin Aure, daga zuwan Falmata gidan nan zuwa wayewar garin jiya sauyin dana gani wajen Abban Abie Saratu ta munana, kin San wani Abin takaici? Huhmm Banso na tona Asirin zamantakewar da muke da Abban Abie ba, Amma ya zama dole ki sani sabida ki fahimci meye nake nufi kuma yake damuna A zuciya. Tsawon shekara 15 kenan Aure na da Abban Abie Saratu, Amma tunda nake dashi bai taba kwanciyar Aure dani A rana sau biyu ba, ke in fada miki gaskiya sai muyi kwana Biyar zuwa shida bai nemeni ba, sabida shi sam ba mai damuwa da mace bane, A Al'adar Malam bahaushe dama Mace mai kunya da tarbiya bata neman Miji A turaka, Saratu tun Abin yana damuna idan na shiga cikin kawaye ko 'Yan-uwa suna hiran mazajen su suna iya saduwa dasu sau biyu zuwa uku A dare har na daina damuwa, sabida na lura halittarsa ce hakan, Amma wai yanzu Saratu Abba Abie ke iya kwanciyar Aure da Falmata sama da Biyar A rana? Ko giftawa tayi yana biye da ita? Matukar yana dakinta to shikenan sai sex? Ta yaya bazanji zuciyata zata bugaba Saratu? Dai-dai gwar-gwado gyaran nan inayi wallahi, Ashe hakuri yake dani dad'inne bani yi masa? Yanzu batun zuwa Mecca yin oumra, jiya sunje gidan Hajjar sa tace za ta biya wa Falmata Oumra muje tare sabida yace mata zanje kawai donta tsani taga ina hutawa, to ni zuwan Falmata saudi bai dameni ba kamar ji da nayi wai har dashi Abban Abie din za'a tafi sabida yace ba zai iya barin Falmata tayi tsawon sati biyu baya kusa da ita ba, wallahi Saratu na fara gundura da zaman gidan nan, kinaga kamar wasa nake fada miki ko? Matukar irin wa'innan sauyin zan cigaba da gani to watarana Kano zan tafi kowa yasan irin zaman hakurin da nake a gidan nan, shiyasa nace barin fada miki sabida nabi duk hanuar da kika daurani Akai babu haske".


Ajiyar zuciya Saratu ta sauke ta dubi Jidde da Kyau "Ni tunda kika fara bayani kin isheni da Ance ko Kinji? To Aina kika ji? Nifa na dauka Alhajin da kansa ne ya tsiro miki da wasu halayya ta daban yasa kika kira ni kina kuka, Amma duk A bayaninki ni banji wani Abin daga hankali da zaisa har ki tafi kano ba, Maganar yana kwanciya da Falmata sau kusan biyar A rana kince kinji ne? To fada min wata munafuka ce tace dake haka? Sannan kinyi wata magana dafa farko daya sosa mim zuciya, wanda sai da naji kamar na mareki don takaici, haba Jidde sai kace wata rainon kauye? Har kina fadan wai mace idan ta nemi Mijinta A shinfida bata da tarbiya inji Malam bahaushe? Shikenan yanzu ko sha'awa ce ta dameki sabida Malam bahaushe yace miki sai Miji ya nemeki kije shikenan sai ki zauna kamar kayan wanki A engine kina motsi? Imaging wai shekara shabiyar kuke A haka? To Ashe kece kika kashesa da kanki ya zama damuwa, ta Yaya kuma zai samu Mace wayayya wacce zata gwada mishi bariki a shimfida kice ba zata ture zamaninki A wajen sa ba? To wallahi ko rakumi da Akala ya zamo a hanun Falmata wanna laifin kine Jidde, kuma zan gaya miki gaskiya lokaci bai kure miki ba ki dau matakin gyara, idan zaki tashi tsaye ki gyara munanan hakayyarki ki tashi, ta wannan bangaren kam wallahi lafinki ne koma miye Alhaji yace Akan Falmata, wani na Miji ne baya son harka? In kinji shuru kawai bai samu bane Jidde. Mu koma dayar maganar ina jinki ki fadamin wacece take kawo miki zancen Abinda suke da Falmata? Tunda kince kinji ne?"


   "Falmata ce da kanta ta fada min"


"Falmata wai? Falmata Amaryar ki kike nufi ko wata?"


  "Eh ita"


"Innalillahi, na shiga uku Lahaullah walakuwata Anfadi ba nauyi Jidde, Ashe baki da wayo Mata kika rako? Kishiya ta zauna ta kitsa miki makirci har tayi sanadin da zata shiga tsakaninki a Mijin ki? Shekaranku 15 da Aure wacce tazo A kwana biyu ta gwada miki ta fiki sanin Mijin ki?

Na rantse da Allah dake 'Yata ce da sai na miki shegen duka a dakin nan, Mtsww.. taja tsaki, gaskiya kin bata min rai matuka Jidde, ni wallahi da A waya kika fada min daya fi, ni banga Anfani zuwata gidan nan Akan wauta irin haka ba, yanzu ke har yanzu ba zaki gane makircin kishiya ba? Taje ta sha Maganin Mata ta rasa yaya za tayi ya gwada mata shi ba mabukaci bane tazo tana wasa da hankalinki? Da Alokacin ce mata kikayi kema haka kike fama dashi wallahi da A fuska za kiga sauyi, dake ta fiki wayo shiyasa za tayi Anfani da wannan damar wajen shiga tsakanin ku, gaskiya Jidde lamarinki Akwai gyara, matukar baki gane meye makirci ba to kina da Aiki matuka.


Batun Saudi da kike fadan za'aje har da shi to saime? Dama dole fa kiyi hakuri da Abinda za kiga ni game da fallin Miji idan yayi Aure na rantse da Allah. Duk son da yake miki kuwa dole ki sarara mishi ko tsohuwa kuwa ya Aura bare Yarinya mai jini A jika, to gwara ki farga, idan ba haka ba kina ji kina gani Falmata za tayi wuff da zuciyarta Mijin ki, koni da Hamza yamin kishiya yake musguna min sabida ita ban taba bari mun sami matsala Akanta ba, idan kin jini dashi tamuce ta hadamu, Amma bani da lokacin wata 'Yar iska, data fahimci bana fushi dashi sabida yana falli akanta sai ta fito da wata sabuwar salo na raina ni, Anan kuma nace karyar kasa boka ya buga yaga ranar Mutuwar sa, nan na zage mukaci Uwar sabada da kyau, na gwada mata Saratun ta gaske ce ba cartoon ba.


Ina mai baki shawara ta gaskiya Jidde! wallahi ki nutsu ki Aje wani banzan kishi a gefe ki jawo Mijin ki, yanzu kina cewa wai kina fushi dashi shiyasa ba zaki tambayesa za kije gida naba, to in fada miki ko A jikinsa tunda ga sabuwa nan. Yaushe zaki karbi girki?"


"Da cewa nayi saina dawo daga oumra tunda kinga na kusa tafiya, lokacin nayi gyara sosai yanda zaiji yana bukatata kusa dashi, shiyasa nace kano zan wuce naga gida"


"Sannu Jidde, ana dauraki A hanya kina kaucewa? To wallahi na rabaki da wannan sokancin taki, tana cika kwana uku ki karbi girki babu ruwanki da wani sai kin dawo, shikenan kawai idan na Miji yana dakin ka sai anyi Sex? Babu kulawa da jin matsalolin juna? toki karbi girki, kuma idan ya dawo ki bashi hakuri na bata mishi da kikayi, ki saki jiki dashi, zan kuma sake baki wata satar amsa, ko fada kuke da Miji idan kuna tare ku uku karki gwada mata, ki shanye komai idan kun koma daki kuyi, kinga yanzu duk wani Abinda ke faruwa A gidan nan A kunnen Uwar Mijin ki da 'Yan-uwan sane, gwara ki nutsu?"


Ajiyar zuciya Jidde ta sauke "Gaskiya bani da bakin godiya A gareki Saratu, tabbas duk Abinda Falmata ta fada min Akwai makirci A ciki, kuma Insha Allah zan dauki matakin gyara, kinga 'Yar wayar da mukeyi idan ya fita? nayi fushi na daina, sabida A gaba na zanga ya kirata kusan sau 3 Amma ni ko sau daya, shiyasa na hakura da kiransa kwata-kwata, kuma ko ajikin sa"


"Ahaf na fada miki Ai gwanda kinsan meye kike ciki, ni bani ruwa nasha?" Mikewa Jidde tayi ta bude Fridge ta miko mata Drink mai sanyi da Cake, haka suka cigaba da hira Saratu tana kara biya mata karatun zaman rayuwa har rana ta fadi "Jidde dama na fada miki da Magrib zan tafi sabida Yara zasu dawo makaranta, ni barin dauki hanya" Mikewa tayi tasa mayafi Jidde ta diba mata kayan makulashe takai wa Yara, Godiya sosai Jidde tayi wa Saratu suka sauko kasa.


Falmata na zaune hanunta rike da country yoghurt tana sha tamkar wacce bata da lafiya sabida rangwadi, kallon haushi da Saratu take mata yasa tayi murmushi " Jidde bakuwa mu kayi ne, Anyini lafiya baiwar Allah?" ta dubi Saratu fuska A sake, galala Saratu tayi da baki tana Al'ajabin Makirci irinta Falmata, sai kinkayo muryar Jidde tayi ta na ce mata "Eh wallahi kawata ce"


"Eyya Sannu dazuwa?" Ajiyar zuciya Saratu ta sauke tace "Sannu ko? Nagode da gaisuwa, Jidde nikan nasa kai, fitowa Saratu tayi tabar Jidde tana fada wa Falmata rakiya za tayi. A harabar gidan Saratu ta tsaya ta kama kugu, Jidde tana fitowa tace " Gaskiya fa sai kinyi da gaske, kin san masu irin halin Falmata yanda suke tarwatsa zuciyar kishiya? Da wannan halin nata zata saye zuciyar kowa naki, ta yanda idan kika kawo korafinta za'ace kece baki son zaman lafiya, to Allah ya kyauta ni kan zan wuce"


"Hakane shiyasa babu mai fahimtar Abinda zan fada sai wanda ya gani da idonsa, nagode Saratu Allah yabar zumunci barin hadaki da driver ya kai ki gida?"


"Nagode sosai Jidde, Allah kuma ya taimakeki akan Falmata sai munyi magana A waya" Daga inda Jidde take ta kira Driver A waya ya tashi ya dauko Motor yazo inda suke, Saratu na tafiya su Sabriya suna shigowa, shiyasa ta tsaya suka shiga gida. Falmata na ganin su tace "A'a Yarana kun dawo ne?"


"Eh Aunty Falmata" Suka Anbata suka sa kai ciki, A kujera gefen Falmata Jidde ta zauna ta kwala wa Saddiqa kira, da sauri ta iso ta durkusa A gefenta "Aunty gani?"


"Meye zaki tanadar wa gidan mai sauki? Naga kamar babu Abinci?"


"Eh babu bari A dafa ko cus-cus ce?"


"Ba matsala ki dafa. Number Alhaji Goni Jidde ta kira, yana gaf da shigowa gari kiran ta shigo, ganin number jidde yasa ya dauka bakin sa dauke da Sallama, wa'alaika salam Abban Abie ya hanya dai? Na jika shuru ko cinikin bai yuyu bane?"


"Komai dai-dai in fada miki gani gaf da gida Maman Abie, na tsaya na kwashe shanun ne shine dalilin da yasa nayi dare Amma insha Allah nanda 20 minute ina gida, ina su Sabriya?"


"Yanzu suka dawo gida Saratu ma tazo mun sha hira"


"Allah sarki ta kyauta"


"Wallahi kuwa sai ka dawo?"


"Yauwa Allah yayi albarka" Tana katse kiran ta kalli Falmata don taga ya fuskarta zata kasance "Ashe sun shigo gari? Last wayar damu kayi dashi suna hanya, lallai sunsja gudu, Amma tunda ansami biyan bukata Masha Allah, barin hanzarta tunda ya fada miki yana gaf da shigowa! Indan samu in hada masa Abin tabawa" Ta kashe maganar tare da mikewa tayi kitchen. kama baki Jidde tafi "To wai ita wannan Falmatar Aljana ce kome ? Saratu tace idan na rama Abinda tamin zan gani a fuskarta? Tabe baki tayi koma miye dai yanzu taji da kunnen ta ba fada mu keyi ba" Mikewa tayi ta haura sama ta fada toilet ta dauro Alola tazo tayi Sallar Magrib.


Alhaji Goni kuwa ba karamin dadi kiran da Jidde ta mishi ya jiba, sam bayi so yaga tana fushi dashi bare akai matakin haka. Cike dajin dadi ya kara so gidan, A masallacin gidan sa ya tsaya yayi sallah kafin ya shigo ciki.


Falmata tana tsaye A jikin dinning taji sallamar sa, ajiye komai tayi tazo ta rubgumesa "Oyoyo Yaya Sannu da shigowa?dama nace wa Jidde ba za kufi 20minute ba zaku karaso? Sabida tace kuna gaf Sannu da hanya?"


"Yauwa Falmata gaskiya na kwana biyu banyi tafiya haka ba"


"Allah sarki to ka haura kayi wanka sai ka samu kaci Abinci?"


"Hakan za'ayi please ki tanada mun Lipton first?"


"Angama Yaya" Da sauri ya haura ita kuma ta koma kitchen cigaba da Abinda takeyi, yana fitowa Jallabiya ya saka ya nufi dakin Jidde, yana shiga da murmushi ta tarbesa "Ashe ka dawo kenan?"


"Wallahi na dawo ya gidan?"


"Lafiya kalau Alhmdullah, zama yayi A gefenta na gaji ne ina so nayi Sallar ishai kafin nasa wani Abu a ciki na, yanzu za'a kira naga bakwai ta wuce?"


"Eh insha Allah, Kama hanunsa tayi "Abban Abie don Allah kayi hakuri da Abinda ya faru dazu? Na zauna nayi tunanin ban kyauta ba?" Murmushi yayi ya jawo ta jikin sa "Bakomai Jidde ni tun Anan na mance komai, nasan ba halinki bane watakila wani Abin nayi miki?"


"Komai ya wuce tunda kace ka yafe?"


"Kwarai da gaske, Jiya da mu kaje gidan Hajja nake ce mata za kije Oumra tace na hadaku da Falmata kuje, shine bayan mun fito Falmata tayi wani tunanin mai kyau tace muje duka harda Yara, to yanzu gobe insha Allah zan dauki Yaran muje magana E passport, na biya kudi ayi musu na gaggawa kawai"


"Gaskiya tayi tunani mai kyau! hakan yayi Allah ya baka lada"


"Ameen Jidde na, zaki kwanta ne o idan naci abinci nazo muyi hira?"


"Huhmm kaje ka huta tunda ka gaji ba gobe A daki na zaka kwana ba? Sai mu kwana muna hira?"


"Kwarai kuwa 'Yar Albarka" Mikewa yayi ya fita zuwa Masallaci. Yana dawowa ya samu Falmata ta hada komai shi take jira, zama yayi ta zuba masa yana ci tana mishi hira harya kammala, tare suka nufi dakin Yaran sa ya duba lafiyar su kafin suka haura sama, Toilet Falmata ta shiga tayi wanka, tana fitowa ta samu Alhaji Goni har barci ya daukesa, kama kugu tayi, 'To yanzu ya kwantar Maganin da nasha inyi yaya dashi? Gashi ciki na ya soma ciwo? Miji kawai nake bukata?' Tsaki tayi tasa kayan barci ta kwanta a gefensa cike da takaici.


Tana runtse idanu fuskar Jidde ta baiyana mata lokacin da suke waya da Yaya Goni, gaba daya farin ciki ne kwance A fuskarta, bude idanu tayi da sauri ta tashi ta zauna ta kura wa Alhaji Goni idanu "Ba Jidde kyarkyara take ba? Tunaninta gobe gobe Miji zai koma mata su cinye juna? To za taga bariki, wallahi yanda nasha kayan mata saina karar dashi kaf kafin yabar dakin nan, Ai bayi data cewa tunda yasan Yau babu Abinda ya hadani dashi".