IYALAINA

15

by @sadiyanasir



     Kwafa tayi ta cigaba da sakar zuci kafin daga bisani tabi lafiyar gado, cikin dare kuwa haka ta rinka murkususu na ciwon ciki, Amma sabida makirci da mugun nufinta Akan Jidde yasa taki gwada wa Alhaji Goni Abinda take bukata, shi kuwa juyin da takeyi A gado da nishi yasa shi farkawa, murya kasa kasa yace "Subhanallah Falmata lafiya kuwa? Meye ya sameki kike juyi haka?" Ciza lebe tayi tace "Sanyin A.C ya dameni kuma bani so na shiga hakkin ka shiyasa nake juyi amma bakomai"


"Subhanallah haba Falmata meye na shiga hakki anan? Ai da kin kashe meye A ciki? Tunda akwai standing fan ai duk daya, kiyi hakuri barin kashe kawai? kada kai tayi Alamar to, haka ya tashi ya kunna fanka ya kashe A.C ya dawo ya kwanta, inace shikenan?"


"Ehh nagode" Ta Ambata ta juya baya Alamar za tayi bacci "To Allah ya tashemu lafiya?"


"Ameen ya rabbi" Ta Amsa ta runtse idanu gami da ciza lebe, haka dai dake bacci barawo ne sai jin fitar Alhaji Goni zuwa Masallaci tayi, da kyar ta iya mikewa ta shiga toilet tayi alola ta dawo tayi Sallah, tana idarwa ta samu dama ta bude drawer din da kayan da'an ta suke ta kwaso na matsi tayi toilet ta tusa ta dawo. 


Alhaji Goni kuwa kamar yanda al'adarsa take idan ya idar da Sallah yakan tsaya A masallaci yayi lazimi kafin ya dawo gida, shiyasa wani lokacin sai gari ya fara haske yake shigowa, amma Yau dake Akwai sauran Bacci a idanunsa bai jima a masallaci ba ya shigo, dakin Jidde ya nufa tana zaune A bakin gado ta idar da Sallah kenan tana so ta fita ta samu Saddiqa batun zuwan Yara school, zama yayi A gefenta "Barka da safiya Matar so?"


"Barka dai harka dawo?"


"Wallahi dake Akwai sauran gajiya A jiki na bacci zan koma, kin san Allah jiya ko motsi banyi ba tinda na kwanta dana dawo? Haba na wahala hanyar su duk bata da kyau" Dariya Jidde tayi "Kai dai baka saba da wahala ba shiyasa"


"Na saba mana, kice dai na jima ban wahalan ba"


"Hakane kuma"


"Yauwa ya batun tsarin karban girki? kwana nawa zaku nayi? Ya kamata kuyi magana da Falmata ko?"


"Eh hakane Amma yawancin gidajen hausawa kwana biyu sukeyi, to muma sai muyi hakan Ai?"


"Eh to Amma kuyi magana da Falmata ku tsayar tsakanin ku"


"Babu laifi idan mun hadu da safe zanyi magana da ita" 


"Yauwa zan shiga na kwanta sai kin ganni kawai" Dariya tayi "Shikenan afito lafiya" Nagode yace da ita yasa Kai. Yana shiga daki Falmata ta sauke ajiyar zuciya domin zancen zuci take game dashi! kar ya tsaya a masallaci sai gari tayi haske ya shigo, zama yayi a gefen ta "Kinyi Sallah kuwa?"


"Nayi tun dazu, dake naji fitarka, Abinda ya hanani komawa bacci ma jiranka nake" Murmushi yayi "To gani meye za'a bani?" Hanunsa ta kama ta daura a cinyarta "Ga Abinda za'a baka domin yana mar-marin ka" Bata jira meye zaice ba ta haura cinyarsa ta zauna ta fara aika mishi sakon kiss tako ina, abinka da Na Miji lafiyayye tuni ya bata hadin kai suka Lula wata duniyar, haka da bariki ta samu tayi galaba akansa dako ya ya gaji zaiji ba zai iya barinta ba, A haka suka bata tsawon lokaci suna abu daya, sai da suka galabaita gaba daya kafin suka hakura da juna, sun jima a kwance suna hutawa kafin suka nufi toile su kayi wanka suka dawo sai bacci kuma.


Jidde kuwa dama dake ya fada mata bacci zaiyi shiyasa bata damu da rashin fitowarsa ba, tana gama Abinda za tayi ta nufi dakin Alhajin ta gyara tsaf ta sauya bed sheet, shi dake A tsarinsa Mace ita take biyosa turaka su kwanta, Falmata ma sabida Amarya ce yasa ya kwana a dakinta har tsawon kwana uku.


Tana gamawa dakin Saddiqa ta nufa, a toilet ta sameya tana wankewa "Saddiqa meye ya kamata A tanadar wa Alhaji ne? Kin san Yau nice da girki kuma baya cin Abu mai nauyi da daddare?"


"Eh to Aunty ko za'ayi mishi kunun gyada? Naga kwanaki yaji dadin sa?"


"Kin kawo shawara amma Kunun gyada a yau kam ba zai so ba, dalili kuwa ranar da nace kiyi rabonsa da Abinci tun safiya? Yanzu kuma na tabbata Falmata za tayi mishi Abincin rana, kinga kunun gyada ba zai shiga ba?"


"Hakane kuma Aunty"


"Yauwa kawai kiyi mishi faten dankali da busassen kifi, zan ba driver ya siyo Alayyahu?"


"Shikenan Aunty" Dakinta ta koma ta fito da kayan gyaran Aure da Saratu ta bata tayi Anfani dashi iya wanda zata iya.


Alhaji Goni da Falmata kuwa sosai suke barci, kusan 4 miss call Hajja tayi mishi Amma bai dauka ba, shiyasa ta kira wayar Falmata taji ko lafiya? Ita dinma hakan ce ta kasance kusan sau biyar tana kira babu bayani, Number kubra ta kira, tana zaune A kofar class da kawayenta suna hira taga kiran Hajja, da sauri ta dauka "Hajjata ya Akayi?"


"Auta na kira wayar Yayanki da Matarsa dukan su babu wanda ya dauka, wallahi na shiga damuwa?"


"Lafiya kalau Hajja hala bacci sukeyi"


"Karfe shabiyu saura Kubra baccin rashin lafiya kenan? Ni dai ki kiramin almuran Matar sa ki tambaya min ko lafiya?"


"Shikena Hajja barin kirata, katse kiran tayi ta sake kiran number Falmata, Amma still ba'a daga ba, Number Jidde ta kira, tana zaune a dakin ta hanunta rike cup din hadin daka data hada tana sha tana charting kiran ta shigo, ganin Number Kubra yasa ta ajiye cup din zuciyarta na bugawa, sam bata kaunar wani abu yana hadata da wa'innan Mutane, kusan sau biyu Kubra tana kira kafin ta dauka murya har na sarkewa "Assalamu Alaikum?" 


"Haba Jidde kina ganin kiran Mutane ba zaki dauka ba? Kin san dai babu Abinda za kimin da zan kira wayarki, sanin kanki dai na kanyi shekara curr ban kira number kiba! da har za kimin gadara kafin ki dauka, dama na kira ne ki kai wa Falmata wayar! Ko kice ta dauki waya, na kirata kusan sau 3 bata dauka ba, kuma Hajja take son suyi magana, kuma kimin sauri? Shuru Jidde tayi tana nazarin kalmar daza tayi anfani dashi wajen gyara wa Kubra kalamanta', Jidde baki jinane? Ko tsaban wulakanci ne da rainin wayo?"


"Ke Kubra? Bafa tsoronki na keji ba? Da zaki zauna kina kanwar bayana kina fada min magana son ranki haka? Wayata kika kira Amma kina min Abu da gadara to bazan kai wayar ba Aikin banza" Tana gama fadin haka ta kashe wayar ta ajiye tana sauke numfashi, ji tayi kanta yana sarawa sabida tashin hankali, bata taba tsammanin a rayuwarta zata iya bada Amsa haka wa Kubra haka ba, da sauri ta dauki wayar ta kashe karma Kubra ta sake kira ta cigaba da sauke numfashi. 


Kubra kuwa galala tayi da baki tana kallon screen din wayarta, Sai Abin yana mata kamar mafarki, wai Jidde ce take bata Amsa haka? Yaushe ta samu 'Yanci haka? Lallai kuwa za kisan dani kike! wayar Hajja ta kira tana dauka tace "Hajja bani so ki bani hakuri, na rantse da Allah sai na goge wa Jidde baki A garu, idan tana cin tsakuwa ta kiyayi ta shuri, har ta isa in kira wayarta ince Hajja keson magana da Falma ko Yaya Akai musu tace babu uban da ya isa tana hutawa ya tasheta? Waye Jidde da har zance mata Hajja ke bukatar haka ta bijire? Na rantse da Allah sai naga wanda ya daure mata gindi"


"Kubra wai Jidden ce tace haka?"


"Kwarai Hajja kin San bazan fada miki Abinda ba'ayi ba"


"Shikenan bakomai ki kwantar da hankalin ki zai zo Har inda nake ya sameni, zanji idan shine ya daure mata gindi ta rainani shikenan, kiyi hakuri karki damu?" Kwafa Kubra tayi "Shikenan Hajja".


Kubra na kashe waya Hajja ta sake kiran number Falmata, wannan karo anci sa'a tana juya fuskarta taga wayar tana jaske, A hankali ta jawo, ganin number Hajja yasa ta dauka da Sauri "Hajja barka?"


"Falmata ina kika saka wayar ki? Na kira harna gaji zan fada miki ya mu kayi da Larai baki dauka ba?"


"Kiyi hakuri Hajja wallahi bacci nake, yanzu ma haskenta na gani na dauka"


"Ikon Allah Ashe gaskiyar Kubra ce da tace kuna bacci, to ina yake?"


"Gashi barin basa, Yaya Yaya?" Ido rufe yace "Falmata bacci na keji ki kyaleni?"


"Hajja ke kira gashi?" Jin haka yasa ya bude idanu ya karbi wayar ya dauka "Hajja Antashi lfy?"


"Lafiya kalau ba wannan ba, Kasan meye Matar ka tamin yanzu? Na kira wayar ku baku dauka ba nasa Kubra ta kiramin ita tace ku kirani, amma sabida raini da rashin sanin darajata nace Akai maka tace babu wanda ya isa ya tasheta tana hutawa? Kai ne ka bata damar taci fuskata har haka?"


"Innalillah Hajja don Allah kiyi hakuri? Yanzu zan tashi naje na sameta"


"Au samunta za kayi kaji ko karya nayi mata ko? To maza tashi kar Quda ya rigaka isa?"


"Ba haka bane Hajja kiyi hakuri, abinne yamin zafi, babu yanda za'ayi tayi miki haka na kyaleta, shine dalilin da zai kaini wajenta"


"Uhum fada a baki babu Aikatawa Allah yasa da gaske kake, kalma daya zan fada maka ka fada mata, duk Abinda Jidde za tayi tsakaninta dasu Kubra ko da wasa karta sakani ciki? Wallahi nafi gaban raini tunda na haifeka"


"Kwarai kuwa Hajja yanzu zan sameta kuma zan daukota har gida tazo ta baki hakuri"


"Bani wani bukata, yanda nake jin takaici idan tazo Inda nake zata karbi kalamai marasa dadi, wanda za taji dama bata sanni A rayuwa ba"


"Shikenan Hajja Allah ya baki hakuri? Ameen ta Amsa ta katse kiran, kama kai yayi ya furta Innalillahi wa'inna ilaihi raju'um" Dafa kafadarsa Falmata tayi "Kayi hakuri ka kwantar da hankali ka, kaje ka sameta kaji meye ya faru, babu mamaki Kubra ta fada Abinda ba haka ba, kai kanka kasan hali, Amma koma miye Yaya ka fada mata duk abinda ya hadasu da Kubra ta daina saka Hajja ciki, domin Hajja Uwar muce, ko babu Alaka ta girmeta" Ajiyar zuciya Alhaji Goni ya sauke "Wallahi Falmata kaina ya daure, zuciyata taki amince min Jidde za tayi haka"


"Huhmm kwarai Jidde tana da hankali da hakuri, Amma zan fada maka gaskiya don ayi gyara, Mutanen da Jidde take rayuwa dasu Akwai masu zugata, babu mamaki wata tace mata tayi haka, Amma da Mamaki kam Jidde ta Amsa wa Kubra har Akai matakin haka". Kallon Falmata yayi sosai " Tabbas Abinda kika fada akan Jidde hakane, sam bata da hayaniya, babu mamaki akwai masu zugata, sabida tunda nayi Aure Jidde take tsiro da wasu halayya, Amma bakomai zan bincika".


"Uhum ni bani so daga zuwata ace na fara kai zance ba'a tambayeni ba, Amma jin kunena bakuwar da Jidde tayi jiya tana fada dole sai ta zama Mara kunya kafin su dai-daita dasu Kubra, tace Abin zaiyi mata yawa, ace ga kishiya ga bakin cikin familyn sa, A lokacin kam Jidde ta gwada mata ba za tabi Abinda tace ba, Amma kasan halin rai, babu mamaki ta canza shawara"


"Wata mata ce tazo wajen Jidde jiya?"


"Naji kamar tana fada maka A waya Ai? data kira take tambayarka yaushe zaka dawo"


"Au Saratu kike nufi?" 


"Yauwa sunan kenan"


 "Amma Abin da mamaki ace Saratu ke zuga Jidde tayi wa Hajja rashin kunya, sun jima da Jidde fa? Inda tana da mugun hali da Jidde ta jima da zamowa wata iri?"


"Uhumm Amma idan kaje daha yananyin kalamanta zaka san Aikin zugi ne wannan, sabida har kai naji tana ce maka idan Abu ya hadata da kanneka ta gwada maka yanzu wuyanta ya isa yanka, Uhumm Yaya kenan, da kake fadan sun jima bata yunkurin bata munanan shawara Ai lokacin baka aure ba, yanzu kuwa za'a cemata dole ta mike tsaye kafin wata ta kwace gida".


"Shikenan ina zuwa? Mikewa yayi ya fice a dakin ya nufi dakin Jidde, yana shiga ko zama bai yiba yace "Jidde meye ya hadaki da Hajja? Ta kira waya ta yanda take shiga ba tanan take fita ba? Meyasa Jidde kike so ki bata tsallenki da wayo? Yaushe fada zai hadaki da Kubra har ki hada Hajja?" Tafa hanu tayi "Sharri kayan kwalba dama nasan dole za'ayi haka, sam Kubra bata tsoron Allah, Abinda ya faru shine! Kubra kirata tayi da gadara tana cemin na kai wa Falmata waya, Kubra Aiba Uwata bace da zata aikeni a gadarance, kuma wallahi ni bata cemin Hajja bace za tayi magana da ita, Abinda yasa na tsaya har mu kayi musanyar yawu da Kubra na gwada mata yanzu da baya da daya bace, na jima ina hakuri Amma yanzu wallahi ba zanyi ba, dame Ake so naji?"


Mamaki da Al'ajabi ne suka baiyana akan fuskar Alhaji Goni, kenan maganar da Falmata ta fada gaskiya ne.


Falmata kuwa tunda Alhaji Goni ya fito daga dakinta tabiyo bayansa don taji wainar da za'a toya, jin kalaman da Jidde take mayar wa Alhaji Goni yasa tayi tsalle tace "Tarkona ya kama kurciya........