02
by @faddabanan
Yau dai special day ce a gare ni, it's a birthday of my special people, my niece Nuriyya Hussein, my sister Nabilo and also Faddabanan! Lol! Mu 3! Allah ya raya mu da albarka, ya sa albarkar mu ta shafi duk wanda muka zauna da shi, Allah ya ƙara haɗa mu da mutanen kirki ta ko'ina. HAPPY BIRTHDAY TO US!
********************
Ƙarfe biyu ina gidan Gwaggo Hafsatu, irin farin cikin da ta nuna na tarba ta da tayi bayan na isa ba ƙaramin daɗi abun yayi mun ba. Abincin rana na iske tana rabawa don haka sai da na cika ciki na sannan na yi sallah tunda ɗokin tahowa ya hana ni tsayawa na yi karin kumallo, to na dai baro Kano, 'yan tsegumi kuma sai a nema wani babin.
Da daddare muna zaune a tsakar gida mun gama cin abincin dare, Baba (mijin Gwaggo) ya fita majalisar su nesa kaɗan da gidan bayan mun gama gaisawa. Gwaggo da sai lokacin ta fara tambaya ta ya ake ciki? Shin komai sun yi mana sauƙi yanzu ko da saura?
Ina kallon ta naji hawaye yana zuwa idona na ce "Ai Gwaggo sai dai a roƙi Allah ya kawo mafita gabaɗaya, amma abun ya dame ni don shi ne ƙarfin sa ni baro gida zuwa nan ko na samu wurin shan iska. Mutane kai ba su dame ka ba amma su sun sanya maka ido, kaɗan ake jira a kasa ka a farantin gulma ai ta saidawa....." Na ja hancina tare da tallaɓe kaina saboda ciwon kai da ya sauko mun a nan take. Sai kawai na zama na kwanta a kan tabarma ko na samu salama. Gwaggo dai hannu ta sa tana ɗan dukan baya na alamun rarrashi, tana kuma ƙoƙarin yi mun nasiha har ta samu na bar kukan.
Da safe bayan mun gama aikin gida, Baba ya wuce wurin kasuwancin shi, sannan ne na samu damar faɗa mata maƙasudin zuwa na. Sai tace idan Baba ya dawo anjima sai ta shaida masa.
Ko da aka faɗa masa sai ya ce a dakata tukunna, bari yayi wa abokinsa magana da yake principal ne na wata makaranta kusa da gida, don shi gani yake gara nayi internal examz da external ɗin nan da nake son yi yanzu, don ita kam ana yawan faɗuwa. Ko da extra lesson da ake yi wa ɗaliban makarantar sai na shiga cikin su bayan an yi mun rigista kafin a fara jarabawar. Hakan kuwa aka yi, aka ce na bari zuwa lokacin da za'a rigista sai a yi mun na zana a can.
Zama na wurin Gwaggo Hafsatu zama ne na sakewa ba hantara balle ƙyama, ga shi gidan ta cike da yara saɓanin namu na Kano wanda ya kasance ni ce kawai 'yar su.
Da safe makaranta nake tafiya saboda Baba ya ce bai ga amfanin zaman nawa a gida ba, gara na koma makaranta na fara daga farkon aji uku na babbar sakandare watau S.S 3.
Da farko tsoron fara zuwa makarantar nayi saboda su mata da maza ne, saɓanin tamu da zallar mata ne a sashen mu don su ma mazan da nasu sashen su.
Ranar da na fara zuwa kuwa, maƙurewa nayi a ƙarshen ajin abinka da ba-sa-ban-ba, ga sabbin kayan makaranta, duk wanda yayi mun magana sai dai na amsa da "eh! Ko a'a!" A wurin tambayar suna ne nake amsawa da Halima Abubakar, sai kawai suka maida ni abun tsokana, wasu kuma su kare mun. Tun ina jin ɗari-ɗari har na sake ina dariyar abin da suke yi mun. Kafin sati biyu na warware ina iya kula su amma ba wai sakewa irin ta ƙawaye/abokai ba.
Rannan mun taso daga makaranta, na taho riƙe da littattafai na a hannu na rungume su kamar wata 'yar jami'a saboda bana zuba su a jaka, na riga kusan kowa na ajin fitowa saboda Abba na can yana ƙarasa masu wani labari da ban san ma me yasa ban tsaya ba. Nasan ma har da ƙarin yunwar da nake ji da ya haifar mun da ciwon kai. Sai da na fito bakin gate ɗin makaranta naji dama ban taho ni kaɗai ba, hayaniyar motoci, rana da hayaniyar ɗalibai da jama'a yasa na ji ciwon kan na ƙaruwa har ma jiri ya ɗan fara ɗauka ta, ga alamar amai ina ji. Hankali na ya tashi, don ban san wa zan nemi taimakon shi ba, ga ƙarin ba na cikin hayyaci na sosai bare na nemi taimakon.
A hankali na fara jan ƙafa domin matsawa can wata inuwa me dutse a ƙarƙashin ta don na samu na zauna har sai na nutsu. Ƙarar ham ne ya cika mun kunne a yayin da jiri mai ƙarfi ya watsar da ni gefe, littattafai na suka yi gaban kan su, na dafe kaina yayin da nake ji kamar ana wulwula ni tare da runtse idona sosai ko zan daina ji.
Ina jin magana sama-sama kamar ana kiran sunana, daga nan ban san wurin da nake ba kuma. Na dai buɗe idona a hankali saboda nauyin da kaina yayi mun kamar an ɗora bulo, sai dai kan nawa kaman yana kan matashi na abin da ban gane ba.
Mutane ne da yawa a kaina ana ta yi mun firfita, mafi yawansu 'yan ajin mu ne, nai ƙoƙarin tashi na zauna na kasa sai da aka taimaka mun, amma fa kayana sharkaf da ruwa.
Na ɗago na ga wanda ya ɗago ni Abba ne na ajin mu, rabin gashi na a waje yake don babu ƙaramin hijabin makaranta ma a jiki na. Abba ne ya ƙarasa da ni a wurin mota ya sa ni a ciki, wasu kuma suka kawo mun littattafan da suka tattaro haɗi da hijab ɗin.
Cike da tausayi Abba ya ce "Sadiya?" Gaba na ya faɗi saboda mutum ɗaya ke kira na da Sadiya! Hakan ya sanya ban ma ji maganar fa yake yi ba sai da ya sake maimaitawa ya ce "Hanyar gidan ku, za ki iya nuna mun ko ki faɗa? Kina ji na?"
Direban ya ɗauki hanyar cikin city kamar yanda na faɗa, da muka isa gida ma shi ya taimaka ya shigar da ni cikin gida, tun kafin mu ƙarasa cikin gidan Kabiru (ɗan gwaggo ne) ya ruga ya faɗa nata wai gani can an ruƙo ni, sai ga ta ta doso hanyar yin waje zanin ta a hannun ta.
Ta riƙo ni tana tambayar da ba wanda ya ba ta amsa har sai da ta dangana da ni cikin ɗaki ta kwantar bisa gado tukunna, shi kuma Abba na tsaye da littattafai na a bakin ƙofar da ta raba tsakar gida da waje yana jiran ta fito yayi mata bayani sannan ya kuma ba ta littattafan. Ta dinga yi masa godiya tana sa masa albarka har ya fita ya tafi.
Washegari ban je makaranta ba, saboda har lokacin ina jin jirin sama-sama, bana jin komai ban da jirin yanzu kuma mun je asibitin tun jiyan, an ɗora ni a magani tare da jan kunnen na rage damuwa ko stress.
Har ga Allah a lokacin ban sa damuwa a raina ba, don hankali na gaba ɗaya yana kan karatu don ba na son abinda zai sa na sake faɗuwa a wannan jarabawar da nake shirin rubuta wa.
Da na tashi daga bacci can kafin la'asar saboda maganin da aka ba ni yana sa bacci, Gwaggo ke faɗa mun wai 'yan ajinmu sun zo duba ni su da yawa. Bayan na yi wanka don naji ƙwarin jikina kuma Gwaggo ta sa a gaba sai na ci abinci duk da ba ɗadin baki na nake ji ba.
Wurin ƙarfe shida kuma wani yaro yayi sallama wai ga Abba ya zo duba jikin Halima. Gwaggo ta hau faɗan don me zai tsaya waje, ai taimakon da yayi ma abun a karramashi ne. Bayan ya shigo kuma ta ƙara jaddada masa da cewa duk lokacin da ya zo ya shigo kawai, ai shi ma gidan su ne, bayan sun gaisa kenan. Ta tashi.
Bayan ya tambayi ya na ƙara ji sai ya ƙara da cewa "Ai ɗazu mun zo duba ki muka taras kina bacci, har Gwaggo za ta tashe ki aka ce a bar ki tunda kin samu baccin."
"Ai dama kun bari an tashe ni...."
Ya katse ni "A haba sai kace bin bashi? Kin kuwa san yanda muka same ki da muka fito bakin gate ɗin school?"
Ya girgiza kai "Wallahi ni ban taɓa ganin abinda ya ɗagan hankali ba kamar faɗuwar ki, saura ƙadan ɗan express (acaɓa) ya taka ƙafar ki garin kaucewa har faɗuwa yayi. Muna ƙarasowa kan ki kina suma. Shi ne duk a rabu, wasu suka samo ruwa mai sanyi aka zuba maki, wasu na yi maki firifita. Dama kina yin irin ciwon ne?"
Na ce "A'a, kawai yin Allah ne. Ko lokacin da na fito ciwon kan ba wani mai yawa nake yi ba ma."
Ya ƙara faɗin "Ai kam kin tsorata ni, don ina zuwa gida Hajiya na fara faɗawa don na yi zaton mutuwa ce ma da farko."
Maganar sai ta ba ni dariya, shi ma ya fara taya ni kafin ya ɗora da cewa "Ai har ta ce ma za ta zo ta duba ki."
Na ce "Hajiya ai ba ta sanni ba bare ta zo dubiya."
Yayi wata irin dariya da har sai na ƙara kallon shi ya ce "Anya akwai wanda Hajiya ba ta sani a ajin mu ba kuwa? Kowa ta gani za ta kira shi da sunan shi ban da ke, saboda ke sabuwa kuma ba kya cikin hotunan ajin na baya. Domin idan zan bata labari sai na nuna mata mutum ta gane shi tukunna."
Ina dariya na ce "Sannu reporter!"
*********************
Bayan sati guda na koma makaranta, kuma tun abinda ya faru sai hakan ya zama silar wani shiri tsakani na da Abba. Riba biyu ce abun, yana da raha da abun dariya da jama'a sannan kuma yana da bala'in ƙwaƙwalwa, don shi yake kowa mun abubuwa da yawa. Ashe zan iya karatun dama tsabar lalaci ne ya hana ni yi a baya kenan?
Kullum bakin shi a labarin 'yan gidansu yake, yanda suke da family ɗin shi kuma ba ƙaramin birge ni abun yake yi ba. Ni kam sai dai na ba shi labarin Rukky kaɗai, ko maganar Inna da Baba ba ta taɓa haɗa ni da shi ba balle kuma abinda ya shafe ni.
Ƙannensa Safiyya wanda nake kira da auntie saboda sunan su ɗaya da ƙanwar innar mu da suka yi jinya ta a asibiti da kuma Fatima sun sanni sosai domin sau biyu ma suna zuwa gidan mu ban da musayar saƙonni da muke yi ta hannun Ya Abba (yanda suke kiran shi).
Sannan akwai babbar yayar su Ya Khadija tana son ta gan ni, ba yanda bai yi ya zo ya kai ni wurinta ba naƙi, bayan yayi fushi ya gama ya ce na bi su Fatima su kai ni nace ya bari mu yi hutu tukunna. Haka ya gaji da nacin sa ya ƙyale ni. Da yake Allah yayi shi da wasa, zolaya ga tsokana, hakan ya sa kowa nasa ne, kuma shi ne makangin da ya hana a ce da wani abu tsakani na da shi.
Ranar Juma'a na dawo daga makaranta, Gwaggo ta faɗa mun Ruƙayya ta bugo waya ta gidan su Yusuf (maƙotan Gwaggo ne) amma ta ce za ta sake kiran ki bayan an sauko daga Juma'a.
Ana sakkowa kuwa na tafi na jira kiranta saboda ba sai an zo kira na ba idan ta kira na ba (wayar landline). Muna hira da maman Yusuf ko minti goma ban yi da zuwa ba ta kira ba, sai da na jira maman Yusuf ta ɗauka ta tabbatar ni ake nema tukunna, tunda ba'a ganin lamba ta landline ɗin.
Ai fa na ba ta labarin Abba sosai, don yanzu komai da shi nake yi ba. Ta nisa ta ce "Anya Hally ba son ki yake ba?" (Ku yi afuwa, yan shillar 'yan mata ne, maganar kullum ba ta wuce soyayya 😂🤣🤣)
Na ce "Ni ma abinda zuciyata ke faɗa mun kenan, amma shi bana tunanin yasan ina ya sa gaba. Menene na damu na da zuwa gidan sister ɗin shi, ga shi kuma 'yan gidansu duk sun sanni. Ke in taƙaita maki Hajiyarsu har gidan mu tazo, wai sun je bayan layin mu shine yace ta zo ta ganni ta gaisa da su Gwaggo. Kuma fa yaro ne wallahi, da me kwaɗo ya girmi gaya to?"
Rukky tace "Bari mu daina wahalar da kan mu mu jira mu ga abinda zai je ya zo kawai, amma dakata, ke kina son shi ne?"
Na ce "Idan gaskiya zan faɗa maki ban da mutum ɗaya da na so, kuma son na shi bai gushe ba har yanzu sai wannan Abban. Hakan ne yake tsorata ni, amma duk yanda muka yi za ki ji."
Tunda muka fara shirye-shiryen first term examz shi yake taimaka mun ta ɓangaren karatu, har ma ya kai ko a gida ba na iya yin karatu sai na zo makaranta tukunna. A haka muke har aka gama jarabawar aka yi hutu.
Ranar hutu bayan mun fito bakin gate mun taho wurin da direban su ke jira, don kullum sai sun ajiye ni suke wucewa, yake cewa "Sadiya rana ba ta ƙarya.... In ji hausawa, sai ki jira su Fatima ranar Lahadi ko Litinin zasu zo ku je gidan Ya Khadija."
Har zan yi musu sai kuma na ce "Babu damuwa, Allah ya kai mu."
*****************
Ranar Lahadi takwas ɗin safe a tasha tayi mun, don ƙarfe sha ɗaya ina tsakar gidanmu na Kano ina cin abinci. Inna sai nan-nan take yi da ni, na rasa wanda zan aikawa Rukky na dawo, sai kawai na bari idan yamma tayi rana tayi sanyi sai naje da kaina.
Wurin ƙarfe biyar na fito domin zuwa gidan su Rukky, ina ankare da jama'a, amma da alama na gama yayi na na zama topic of gossip, kamar kowa yau harkar gaban shi yake yi. Watau da gaskiyar bahaushe da yake cewa duniya juyi-juyi.
Ruƙayya ta dinga nan-nan da ni ita ma, sai murna take yi har da ita da zuwa siyo mun zoɓo, zoɓon da sai nayi ta roƙon ta Allah annabi sannan ake yarda a siya mun.
Tana dawowa ta zauna tana cewa "Ke wai ya zancen Abba ne?"
"Hmm, bari kawai! Ai yau su Auntie za su zo mu je gidan yayar su shi ne na tsero."
Rukky ta ce "Kai amma kin ɓata mun rai, meye a ciki? Cinye ki za'a yi? Yanzu haka ma kin ja yayi fushi da ke."
"Fushi kam sai dai kar a ƙara. Kin san ma wani abu? Duk wannan yarintar ta shi da nake gani, idan yace mun kule to kuwa da cas zan chafe, kin ga kyan shi kam?"
Rukky ta zauna sosai ta ce"Ki ce dogo ne, ba shi da ƙiba kuma babu sirantaka, kuma idan zan ƙarasa canka daidai sai nace fari ne ko?"
Na amsa "Ke daɗina da ke kenan, fari fa ba shine kyau ba, shi ruwan wankan tarwaɗa ne, kin ga idon shi? Yanayin fuskar shi? Girar shi? Hmmm.... Ya haɗu iya haɗuwa." Muka yi wata shewa muka kwashe da dariya.
"Kin san wani abu?" Rukky ta buƙata.
"A'a."
"Idan ya damu da ke zai biyo ki Kano."
"Kai anya? Na riga na san ya yi fushi sosai, kin san shi da jama'a, mawuyaci ne yayi kewa ta da har za ta sa ya biyo ni Kano."
"Idan yana son ki zai zo, ki yarda da ni."
"Let's wait and see, there is no point arguing, mu bar shi kawai, idan ya zo shi kenan, idan ma bai zo ba ma shi ke nan, abinda na sani ba zan taɓa rabuwa da shi ba, akwai ƙauna mai ƙarfi tsakanin mu daga Allah kumá ga ƙaruwar da nake yi da shi.
Takaitaccen Tunani!