Taƙaitaccen Tunani

03

by @faddabanan

Sati na uku a Kano na dawo Zaria, har na gama hutun nan na koma ba Abba babu labarinsa, idan ma nace ban damu ba nayi ƙarya. Ina dira Zaria da maganar Abba na fara tuntuɓar Gwaggo da shi. Ta ce "Ai ranar da ki ka tafi wurin biyu sai ga su Fatima da Safiyya ya kawo su, wai kun yi za ku tafi unguwa, shi ne na ce ƙila kin manta, don yanzu haka na san kina gida a Kano tuntuni."


A Zarian ma sai bayan sati ɗaya da dawowa ta sannan muka koma makaranta. Da wuri naje don ina son na auna fushin Abban. Yana gani na kuwa yayi murmushi mai cika fuska yace "Masu gudun hijira ne suka dawo?"

"A haba? Don gudun hijirar ba wuya ba ne da shi?"


"Hmn! Su Sadiya manya, me ye na guduwa to? Idan kin san ba ki don zuwa da sai ki faɗa kao tsaye don babu amfanin kwana-kwana. Ni kuma Allah ya sani so nake ku shaƙu, tunda kuma ba ki so, an daina. Allah ba ki haƙuri."


Duk sai na ji wani iri, ban san ta haka zai fassara ni ba. Har ya juya zai bar wajen da nake zaune na sa jaka ta na ɗan kare shi, don haka ya tsaya yana kallon tambaya.


Da sauri na ce "Don Allah dai ka yi haƙuri, ban yi da niyyar wani abu ba, akwai wani abin da ya faru...." Da sauri na janye jaka ta tare da sakin ta a ƙasa na toshe baki na, don na manta da wa nake magana.


Sai kawai ya koma saman desk ɗin gaba na ya zauna yana faɗin "Ci gaba, ina jin ki."


Na ruɗe sosai, shi yasa na fara inda-inda "Kawai dama.....dama....kawai haƙuri nake son ba ka dama."


Ya kalle ni ya kaɗa kai "Ba komai, amma duk lokacin da ki ka ga na cancanci ki faɗa mun damuwar ki don't hesitate." Ya miƙe ya juya domin barin wajen.


Da sauri na sake kiran sunansa, ya juyo yace "Hey! Ba fushi nayi ba fa, kar ki wahalar da kan ki...." Ƙararrawar assembly ce ta katse maganar. Har naje assembly ɗin tambayar kaina nake yi, "wai me ki ke yi ne haka Halima?"


Tunda muka dawo second term ɗin, ga shi har ya kusa ƙarewa ba ma wasa, kuma har an fara yi mana lessons, hakan ya sa sai wurin biyar da rabi zuwa shida saura nake komawa gida. Hakan ya sa zama na a gida ƙalilan nan ne don ranar asabar ma muna zuwa da safe.


Ranar wata Asabar mun idar da la'asar muna zaune gindin bishiya, direban gidansu Abba muke jira. Abban ya jingina a jikin bishiyar ya dafe kansa, alamun gajiya bayyane a fuskarsa. Na ce "Abba!" Ya buɗe ido, na ci gaba "Are u sick? Na ga kasa hannu ka dafe goshin ka, ciwon kai ne?"


Ya daɗa gyara zaman sa yanda jinginar zai yi masa daɗi ya ce "Mts! Gajiya ce kawai. Kin ga da ina da wata da mata gare ni da naje tayi mun tausa." Ya faɗa cikin yanayin zolaya,sai kawai na tsuke fuska. Kamar na ƙara masa azama don zama ma ya gyara kafin ya ci gaba "Uhm! Har kin tuna mun, tunda muke da ke ba ki taɓa ni labarin who your boyfriend is ba, ko duk rashin yardar ta kai nan? Na kuma san kwanaki da kika gudu Kano, shi ne ƙarfin tafiyar ki saboda kin yi kewarsa ba.


"Ni ban sani ba, kar ka dame ni, ko don wanda ka iske ya zo ranar da ka kawo mun maths textbook? Kai ko nace akwai alaƙa tsakanina da shi ai ka ce mun Sadiya kar na ƙara ganin ki da wannan."


"Saboda me to?"


"Ka ƙyale ni abeg! Kai ba ka ga yanda yake wani banƙarewa yana yin doro kamar ya goya kwarya ba? Kullum na gan shi sai naji na fara dariya, shi kuma ya ɗauka daɗin ganin....."


Dariyar da Abba yake yi har da sauka ƙasa ce ta katse zancen nawa. Ya ce "To shi kenan!" Yana ƙoƙarin tsayar da dariyar da yake yi ya ce "Jamil fa? Wannan abokin nawa da muka zo tare a ranar, yace mun ma ai yasan wancan a ABU duka suke."


Na murtuke fuska "Abba bana son wulaƙanci, talla ta ka ke yi ashe? Idan ka gaji da ni ba sai ka faɗa mun ba idan ya so na yi nesa da kai?" A fusace na ja littattafai na na doshi hanyar fita daga makarantar. In bacin dariyar shi da ta biyo baya na ko uffan bai ce domin ya tsayar da ni ba.


Ranar Lahadi nayi ta jiran Abba ya zo gida ya ba ni haƙuri, amma ko kalar sa babu balle shi. Hakan ya sa na ƙara sakankancewa lallai tsakanina da shi 'yar ƙaunar ma ta goshe balle nayi expecting abu sabo.


Ranar Litinin ma na ƙi zuwa makaranta don na kara tabbatar wa kaina abinda nake zargi, ita ma har dare bai zo ba. Sai kawai na yi wa kaina faɗa, kan cewa ya kamata na fita harkar shi na girmama kaina na bar sakarcin da nake ƙoƙarin yi, nasan zan wahala ko don wajen karatu, saboda yana koya mun abu duk wahalar shi to na gane.


Kashegari da naje na iske mai Maths yayi test, hankalina ya tashi don ba abinda yake ba ni tsoro irin Maths, don ta malamin ba shi da matsala yana da saukin kai, zai iya mun make up test.


Na jawo textbook ina son duba wurin da aka ce yayi test ɗin a kai da wasu, na hango Abban na doso class ɗin, don haka na bi ta ƙofar can baya na koma bayan classes ɗin 'yan JS 3 kafin a shiga first period. Kuma da naje wurin mai Maths ɗin na yi bala'in sa'a, cikin tambaya biyar da ya bani na amsa uku cikakke.


Ko da na dawo class, bai kula ni ba, haka ni ma ban ce masa komai ba daidai lokacin Malam Habib mai biology ya fice. Sai da aka yi break bayan kusan kowa na ajin ya fice sannan daga wurin da yake zaune ya ce "Malama Halima masu fushi, ya gida?"


Da kamar ba zan amsa ba, amma ban ɗaga kai na daga note ɗin da nake kwafa ba na ce "Just leave me alone, i'm not in the mood, please!"


Ina jin shi lokacin da ya ƙaraso teburina, ban ɗaga kaina ba kuma ban daina rubutun ba. Ya zare biron da nake rubutu da shi, wani gululun baƙin ciki ya tsaya mun a wuya, wai me ya mayar da ni ne? Mahaukaciya? Sai kawai na kifa kaina kan desk ɗin don ba zan kula shi ba yanda yake so.


Ya sunkuya wurin saitin kunne na yana faɗin "Yanzu daga wasa? A harmless joke shi ne kika ɗauke shi kika sa a kai haka? Na zaci zuwa yanzu ai kin san hali na da kyau. Tsokana dai ko na so na daina wallahi ba zan iya ba. It's a part of me. Allah ya ba ki haƙuri."


Daga ɗan nesa kaɗan Kabir (ɗan ajinmu) ya ce "Abba how far? Wetin do you? Ya na ga kaman haƙuri kake bayarwa, me ya haɗa ka da Halima?"


Na miƙe zaune sosai na ce "To Amebo! Babu komai." A tare suka fara dariya. Kuma duk yanda na so na basar da shi ya ƙi yarda, ta dole muka koma yanda muke. Kuma tunda ya gane bana son zancen samari sai ya mayar da shi abun tsokana, tun ina gwada fushi har na haƙura na watsar amma a ƙasan raina kam zuwa yanzu nasan tsakanin mu ƙauna ce kaɗai babu wani abu extra.


Mun fara jarabawar WAEC da practicals, abin mamaki yake ba ni ganin yanda ma mayar da hankali a karatu.


Ranar Alhamis jarabawar ƙarfe biyu gare mu amma tun ƙarfe Tara muna makarantar da sunan karatu. Sai ɗaya saura na tuna na baro mathematical set ɗina gida, don haka na ce masa bari na yi sauri naje gida na ɗauko kafin biyu da za mu shiga jarabawa tayi na dawo.


Ya amsa "Mts! Gara kawai mu je waɗannan shagu nan na gefen titi mu siya wani kawai, yaushe har kika ɗauko kika dawo ki ka iya wannan?" Yana nunawa da fensir ɗin da ke hannunsa.


Na ce "Kai haba? Har guda biyu zai zama ina da shi fa? Me zan yi da su?" 


Bai ma saurare ni ba yace "Mu ƙarasa wannan zuwa ƙarfe ɗaya, sai mu je mu siya sannan mu dawo mu yi sallah mu ci abinci sai examz kuma in shaa Allah."


Ɗaya da minti tara har mun siya mun ƙoƙarin barin shagon, sam ban lura da wani na shigowa ba sai da muka yi karo, hakan yayi unbalancing tsayuwa ta ya ja mun kifewa a ƙasa da bugu ba ta wasa ba. Kasa motsawa nayi saboda zafin buguwar, Abba da yake yana gaba na shi har ya fita bai san ma na faɗi ba sai da ya ji ƙara tukunna. Kafin ya ƙaraso kaina wadda muka yi karo ne ya taimaka ya ɗaga ni yana ta jera mun sannu, ni kam sai faɗin wash-wash nake yi. Da ƙyar na tsaya akan ƙafa ta amma ɗan yatsa na kamar in cire in jefar nake ji.


Kafin mu gama jarabawar ranar kuwa ɗan yatsa na babba ya kumbura yayi suntum, ga zugi ko yaya na motsa ƙafar. Da na gama jarabawar ma sai da na ɗan daddana kafar sannan na samu na ɗingisa na fito na nemi wuri na zauna ina jiran Abba, duk da ya riga ni ma fitowa, to ƙafar ba lafiya bare naje neman shi.


Ina nan zaune naji magana ta baya na ana yi mun sallama, na amsa bayan na juya ganin ko waye. Ya ce "Sannu don Allah, tun ɗazu nake neman ki na ƙara ba ki haƙuri. Ƙani na na kawo examz ashe tsautsayin balla ƙafa na zo yi."


Ina dariyar ɓalla ƙafar da yace na amsa "Lah ba komai fa, ina zuwa na gasa ta nasan zan warware in shaa Allah."


Ya kalli ƙafar ya ce "Amma fa kumburin yatsan nan na ki kamar targaɗe kika yi, ko na gyara maki?"


Da sauri na katse shi da yake bala'in tsoro ne da ni, na ce "A'a, na gode! Za'a duba idan naje gida. Just go."


Fahd Badamasi ne ya ƙaraso wurin da muke yana faɗin "Yaya na ga motar ka, tun ɗazu nake ta jira a wurin ban gan ka ba." Ya waigo ya kalle ni, cikin mamaki ya ce "Kasan Halima Abubakar ne dama?" Sai yayan na shi ya labarta masa me ya faru don haka shi ma ya fara yi mun sannu.


Ɗit-ɗit-ɗitttttt! Ƙarar ham ɗin mota ne ya cika wurin, duka a tare muka juya, Abba ne ya ɗan ranƙwafa kusa da direbansu yake dannawa, don haka na miƙe a hankali ina dingisawa bayan na yi masu Fahd sallama na isa domin mu tafi gida.


Mun fara tafiya Abba yace "Wai kumbura ƙafar tayi ne naga kina ɗingishi?" Na karkata yanda zai iya hango ƙafar tawa. Ya ce "Kai! Amma kin bugu fa, sannu. Wancan da yake tare da ke da Fahd ba shi ne ya buge ki ɗazun ba?"


"Shi ne fa. Yayan sa ne. Wai haƙuri yake ƙara ba ni...."


Ya katse ni "Ya isa sarkin bayani." Muka yi murmushi mu duka.


Sai na canza akalar maganar da faɗin "Ya karatun gobe zai zama kenan?"


"A'a madam boko, sai ranar Lahadi kuma, tunda mu da jarabawa sai ranar talata mai zuwa, ga ƙarin cewa biology ne, best subject ɗin ki. Ai ina jin ma ke ce za ki koya mun don ni in ban da germination babu abinda na iya."


"Ba wani nan, wayo kawai kake so ka yi mun ka yi karatun ka kai kaɗai."


"To kin san me, ki yi naki karatun, ni ma zan yi idan muka haɗu sai kowa yayi wa ɗan uwansa bayanin abinda bai gane ba. Shikenan ai ko?"

******************


Tunda Gwaggo ta ga ɗan yatsan tace akwai targaɗe, tayi-tayi na bari a gyara, ni kuma na dage ba targaɗe ba ne, ina gasawa da ruwan zafi sai saki.


Ai kuwa washegari na tashi da ƙafa tayi tsami ba na wasa ba, sam ma ƙafar ta ƙi takuwa. Ai kuwa Gwaggo tayi ta faɗa har tana faɗin yau ko suma zan yi sai an nemo mai gyara ya gyara ƙafar. Baba ma yayi faɗa don faɗan da yayi wa Gwaggo ma bai yi mun ba, don me za'a wani biye mun. Ina ji ina gani aka aiki Kabiru ya kira mai gyaran, saboda Baba fita zai yi a lokacin, ya tafi yana jaddada na tabbatar lokacin da zai dawo an gyara ƙafar. Sai kuma ga Kabiru ya dawo wai an ce mai gyaran ya fita amma idan ya dawo za'a faɗa masa.


Bayan la'asar Abba ya zo duba ni, a lokacin kuma ban daɗe da gasa ƙafar ba domin ba ta takuwa in dai ban gasa ba. Zuwan nasa kuma ba daɗewa sai ga mai gyaran ya iso. Tunda na gan shi ido na ya raina fata, tunanin irin zafin da zan ji yasa na dinga nadamar mai yasa ban tsaya jiya an yi an wuce wajen ba?


Ina ji ina gani, Gwaggo ta riƙe ni, amma mai gyaran na yi wa ƙafar damƙar farko na saki wani irin ihu tare da janye ƙafar da watsar da Gwaggo gefe. Abba dai ganin sai wahalar da kowa nake yi na ki bari a gyara ƙafar, haka ya sa ya taimakawa Gwaggo suka danne ni, tsabar zafin gyaran ko hawaye babu a ido na sai ihu da kwarmato da na cika masu kunnuwa da shi. A take zazzafan zazzaɓi ya rufe ni, ana kammala gyaran sai amai.


Da daddare bayan na yi bacci ne zazzaɓin ya sake ni, kuma sai ga Faruƙ yayan Fahd wai ya zo duba ni (nasan ma Fahd ne yayi masa kwatance saboda da shi aka zo duba ni lokacin da na faɗi a school). Kabiru ne ya riƙe ni har muka fito wajen. Ni kamar gyaran ma ƙara kumbura ƙafar yayi, shi ƙafar yake kalla ta cikin hasken ƙwan lantarkin da ya haska wurin yace "Look at your feet! Subhanallah! Dama nace targaɗe ne da gani jiya. I'm so very sorry."


Ya tsaya har na zauna akan dakalin ƙofar gida kafin ya zauna shi ma. Ina ta nuna masa ba komai ai, tsautsayi ne, shi kuma sai ƙara ba ni haƙuri yake.


Shi ma tubarkallah akwai surutu, mu ɗan daɗe a wajen tare, mu ba laifi nasan abubuwa game da shi kamar irin cewa ya kammala digiri ɗin shi a ABU Zaria, yanzu kuma yana aiki da Zenith Bank a Jos amma duk ƙarshen sati yana Zaria saboda yanzu haka yana ƙoƙarin kammala Masters ɗin shi ne. Ranar mun rabu akan zai zo gobe tunda jibi Lahadi zai koma wurin aikin shi.


Kuma kafin mu kammala aji shida wata shaƙuwa ce take wanzuwa tsakani na da Faruƙ, domin duk lokacin da aka ce Juma'a ta zo, gaba ɗaya hankali na ya koma kan dakon dawowarsa.


*****************