Taƙaitaccen Tunani

06

by @faddabanan

A haka dai muka ƙare zaman mu a Zaria, idan ba mu je yawo ba to muna da mutanen mu, don babu yanda za'a yi rana ta wuce ba'a haɗu ba. Ya Abdallah kam tunda ya gane abinda ke tsakanin Rukky da Ya Saif sai yake basar da mu, ga kuma ƙarin dama miskili ne ba na wasa ba amma kam yana dariyar diramar mu da Abba koyaushe, don dole idan muka haɗu sai Abba ya tsokane ni sannan Ruƙayya bayansa take bi. Shi Ya Abdallah a bar shi da jin kiɗa, ƙure AC, kallon ball ko game ɗin PS, aikin kenan. 


Rannan ma ina jin Hajiya tana cewa dama shi fa Abdallah tun yana yaro baya son zafi don jikinsa har saɓa yake yi, sannan jikin sa baya son chanji, idan suka yi tafiya tare da shi a baya, ciwo sosai yake kwanta mata. Yanzu ne da ya girma ma abubuwa suka fara yi masa sauƙi.



Laifin daɗi ƙarewa, mun fara shirin komawa Kano amma ji nake kamar kar mu koma. In don ta ni ce kaɗai da zama na zan yi kawai don babu faɗan da su Inna zasu yi. Amma ko don Rukky, don saboda tuwon gobe ake wanke tukunya, idan muna so Alhajin su ya bar ta ta ƙara bi sai mun yi aiki da hankali, ga ƙarin da ba tare muke da ita ba ina zan samu arzikin wannan yawace-yawacen? 


Tsara bar komawa gida jaka ɗaya muka yi mata saboda abubuwa da muka samu ta kowanne ɓangare har da Gwaggo ma. Kuma dai yanzu Hajiya ta gane mene ake ta ɓoyewa don aike takanas ta yi wa Rukky mai daraja (wannan kam ko kaɗan ban ji kishi ba, kar ku ɗauka komai Rukky ta samu ina damuwa).


Faruƙ da wani abu bai taɓa shiga tsakani na da shi na kyauta ba, ban sani ko don idon Rukky ya gani ba, kayan da ya kawo mana a babbar leda har mamaki ya ba ni, haka kuma ya ba wa Rukky kyautar dubu biyu ni kuma aka ba ni dubu takwas (lokacin ba ƙaramin daraja kuɗi ke da su). Baba kam kuɗin mota ya bamu na dawowa Kano har kuma kuɗin cin abinci a mota.


Ranar Lahadi tun safe muka shirya muka karya da wuri muna jiran Ya Saif, don ya ce shi zai kai mu tasha. Bai ƙaraso ba sai wajen ƙarfe sha ɗaya, tare suka zo da Abba. Ba mu tsaya wani ɓata lokaci ba, muka yi wa Gwaggo sallama, Abba ya taya mu kwashe kaya da wasu yaran maƙwabta zuwa wurin motar, Abba kuma yana tsokanar mu wai mun zo Zaria mun cika jaka za mu koma ƙauye. Har da Gwaggo a raka mu bakin mota tana yi mana addu'ar sauka lafiya.


Maimakon mu tafi tasha sai kawai na ga Ya Saif yayi hanyar fita gari da mu, da sauri na ce "Kai! Ya Saif ina ce tasha za ka sauke mu?"


Yana tuƙi bai waigo ba ya ce "Haba my sister, ta ya ya zan bar her highness ta bi motar haya kuma ina zaune ba na komai?" Ya ƙarasa zancen yana kallon gefen da Ruƙayyan take zaune kusa da shi a gaban motar, don ni da Abba ne a baya (Abban na har ya shiga gaban mota aka koro shi).


Da muka iso Kano kai tsaye gidanmu muka wuce, Inna kaɗai muka riske dama nasan dole Baba ba ya gida yanzu. Inna na ganin mu da baƙi ta hau damun fura (Baba na matuƙar son fura, da wuya a iske babu fura a gidan nan) sannan ta ɗora masu girki, dukkan mu kuma muna zaune bisa tabarma a yalwataccen tsakar gidanmu, Abba kam kwanciya yayi akan tabarmar wai shi ya gaji, sai da muka ci abinci muka yi la'asar kafin muka ɗunguma zuwa gidan su Rukky.


Ƙannen Rukky kaɗai muka iske da muka isa gidan, wai Mama sun je kai amarya. Anan muka yi sallama da su bayan an sauke mana ragowan kayayyakin mu. Ban baro gidan su ba sai da aka yi Isha, kuma kayan nawa tsarabar da na taho da shi ya sa dole na hau kan ɗan achaɓa ya kai ni gida.


Sai dai ban baro gidan ba sai da na cikawa Ya Saif alƙawarin da ya sa na ɗaukar masa watau na sanar da shi a wurin Mama. Ya ce zai dawo domin ya gaishe su, kawai yana son a san da zaman shi ne, kuma tunda yanzu Rukky take ND 1 yana ganin zuwa lokacin da zai kammala bautar ƙasa sai zo ɗaya da lokacin da za ta kammala diploma ɗin ta.


Farin cikin fuskar Mama bai ɓuya ba (Allah sarki iyaye, burinsu bai wuce su aurar da ɗiyansu lami lafiya ba), ta kuma tambaye ni ya halayyar mutanen gidan da ya fito daga ciki, ya sanar da ita amma na shi halin iyakar abinda ya bayyana a gare ni mutumin kirki ne, amma ban san ko yana ɓoyayyen hali ba dai (ya daɗe a ƙasar waje with full freeedom).

Da daddare bayan Baba ya dawo ne na ɗauko masa sakamakon jarabawa ta na kawo masu shi da Inna don su gani, ni na mance ban nuna mata tun ɗazun da na dawo ba muna ta hira.


Baba ya sa albarka, ya kuma yaba dagewa ta akan karatun. Sai kuma zancen Baban Zaria na siyan Form ɗin diploma kafin na zana jarabawar Jamb, yanayin fuskar Baba sai na dinga jin ƙwarin gwiwa ta na sacewa ina tsoron kar ya canza ra'ayi, amma sai kuma yayi maganar da ta kwantar mun da hankali "Na so ko makarantar su ƙawar ki ce ki jona amma ba za'a watsar da ƙoƙarin baban naku ba. Allah ya saka masa da alkhairi ya kuma sa hakan ma fi alkhairi."


Ita Inna tana son zama a can wurin su Gwaggo saboda su suna kwaɓa ta idan nayi abu ba daidai ba, amma kasancewa ɗiyar su guda ɗaya jal ya sa suka shagwaɓa ni.


Ya Saif da wuya ya yi cikakken sati bai zo Kano ba, a gidan mu suka fi zama saboda muna da ɗakin baki ta kusa da ƙofar shigowa ɗakin (an yi ɗakin ne lokacin da aka sake fasalin gidanmu wani lokaci can baya), saboda idan gidansu Rukky ne sai dai su tsaya a waje, kuma ba zai yi wannan doguwar tafiyar a ajiye shi a waje ba, bayan ya kamata a ba shi abinci da ruwa.


Duk zuwan da zai yi da irin tsarabar da zai kawo mana har mun saba, hakan kuma ya sa mana azama da dagewa da yi masa abinci duk lokacin da zai zo ba tare da mun gaji ba. Faruƙ ni ma ya zo sau biyu a sati uku da barowar mu Zaria.


Wannan zuwan da Ya Saif ya yi waya ya kawowa Rukky! Handset fa! Ko nace maku ban damu ba ai kun san ƙarya nake. Ku tuna fa lokacin handset ko layin ta kaɗai dubu ashirin ake siyar da shi bare kuma ita kan ta wayar, ga shi ma sai wane da wane ke da ita.


Lalle gaskiyar bahaushe da ya ke cewa duniya rawar 'yan mata. Da nice nake samun waɗannan tagomashin, domin irin kyautar da samari ke mun sai ku ɗauka asirin karɓar kayan hannun su nayi. Kayan kwalliya sai dai na bawa Rukky, kai har kayan sawa nake ɗin ka mana a tare da ita a lokacin.


Zama yayi ya koya mata yanda ake amfani da wayar, wai yanzu zai tafi bautar ƙasa ba zai dinga samun sararin zuwa akai-akai kamar yanda yake yi yanzu ba.


Mama kam da ta ga wayar dagewa tayi sai Rukky ta mayar masa da wayar ko kuma ta kashe ta ajiye, saboda kashe kuɗin yayi yawa. Da ƙyar ta yarda ta haƙura bayan na yi ta roƙon ta tare da nusar da ita su ba masu rashin mutunci ba ne, bare idan Allah bai ƙadarta aure tsakanin su zai dawo yace a biya shi ba ne.


Baya-baya na fara yi da Rukky, domin zuciyata na rasa yanda zan yi da ita game da Ruƙayyan, illa na dage da roƙon Allah ya yaye mun wannan cutar, kuma cikin ikon Allah sai na fara jin sanyi a zuciyata, abubuwan na ta sai suka fara daina damu na.