07
by @faddabanan
Ina kwance ƙarƙashin bishiyar da ke tsakar gidanmu ina hutawa bayan na share gidan tas. Innarmu kuma zirga-zirgar haɗa abincin rana take yi, ina kallon ta amma na kasa tashi na karɓi aikin abincin, jikina ne ma yayi mun nauyi.
"Salamu Alaikum!" Ba shiri na miƙe zaune don tabbas muryar Gwaggo naji kamar. Tana sako kai cikin gidan na mike da gudu na rungumo ta ina yi mata sannu da zuwa tare da karɓar kayan hannunta. Inna ma daga gefen mu sai cewa take yi "Hafsatu da tsakar rana haka kike tafe? Sannu da zuwa, sannu da zuwa." Bakinta har kunne.
Haka Inna ta koma kan aikin abincin da take yi, a yayin da ni da Gwaggo muke zaune akan tabarma muna ta hirar yaushe gamo. Har ma ta sanar da ni Abba ya je wurin ta jiya, wai yayansa ya aike shi kusa da gida sai ya ƙarasa, ya kuma iske ta tana shirin tahowa Kano yau don haka ya ba da takarda a kawo mun, ta ce a gidanta ma ya rubuta.
Sai bayan da muka ci abinci tare da yin sallah sannnan Gwaggo ta kwance kayanta ta ba ni takardar Abba sannan ta ba ni ainihin abin da ya kawo ta Kano a daidai wannan lokacin, ashe form ɗin diploma ɗin ne da Baba ya siya, ya sa ta kawo mun na cike ta mayar masa da shi. Ina ihu ina rawar murna sannan na tafi ɗakina na bar su su gana.
Ga abinda ke cikin takardar da Abba ya aiko mun
Hey baby girl!
Ya kike? Ya Kano da weather? Hope you are good.
Guess what?! Na samu 202 a jamb ɗina, bana jin neman admission zai zama matsala. Expect me next week, don na ji Ya Saif na ce wa za mu zo.
Later.
PS ban yi missing ɗin ki ba fa, don't let it get to your head.
Your only friend
Ko kina da wani?
Dariya mai sauti nayi, watau Abba sai dai a bar shi, in dai bai yi tsokana ba ba ya jin daɗi. Na taya shi murnar samun nasarar shi ta jamb, nasan ya cancanci wannan nasarar ko ma sama da haka.
Na zauna domin na fara cike form ɗin, amma sai ya kasance na duba ba ni da biro, don haka na leƙa domin faɗawa Inna zan je shagon ƙarshen layin mu na siyo. Sai kuma na ga tunda ina buƙatar na yi photocopy na credentials ɗin da zan haɗawa Gwaggo a form ɗin nan ta tafi da shi, gara na fita gabaɗaya na yi.
Don haka ɗan achaɓa na hau na tafi babban titi don a tsukin unguwar mu babu mai yi. Na samu gefe guda daga gefen shagon ina jiran cikowar da aka yi a cikin shagon ta ragu, ba shi kaɗai ne mai yin photocopy a wurin ba, amma shi kaɗai ne me Generator ragowan sai idan akwai wutar NEPA ne suke iya yi. Ƙarshe ma cewa aka yi na miƙo takarduna a bi mun layi a ciki, don na daɗe tsaye a waje. Hakan da aka yi sai ya kawo maslaha ma, ragowan duk suka fito waje tunda idan an zo kan takardunka za'a kira ka. Ni kuma ganin an sarari sai na samu na zauna a cikin shagon.
Wani na gefe na a tsaye dai-dai lokacin layin ya zo kaina, da yake result ɗina ne a saman takardun, sai naji yana magana tare da kallon result ɗin "Gaskiya kin yi ƙoƙari sosai, a wannan zamanin mutum ya samu result irin na ki abun a yi masa kyauta ya kuma yayata shi ne."
Nayi murmushin jin daɗin an yabe ni na ce "Na gode ƙwarai."
Yana ƙoƙarin biyan kuɗin aikin da aka yi masa ya ci gaba da faɗin "Kana gani kasan no two ways about it ƙwalwa gare ki, Allah ya ƙara buɗe maki ita. Mu ma Allah ya ba mu irin ta."
Na fara murmushi mai sauti na ce "Kai da za kace Allah ya baku wadda ta fi tawa? Kasan ko sa'a kawai na yi?"
Ya amsa "Idan ma sa'ar ce, wa ya ƙi sa'a? Idan mutum na da sa'a ai kullum a cikin samun ci gaba yake. Na bar ki lafiya, sai an jima." Ya kuma biya har da kuɗin nawa (kun dai san kuɗin babu yawa).
*****************
Sai da daddare da Baba ya dawo sannan na zo kusa da shi na zauna na cike form ɗin (duk da bai yi makarantar boko ba amma yayi yaƙi da jahilci, yana gane abubuw ba laifi amma idan ba'a yi zurfi can ba). Ina kuma gama cikewa a take na miƙawa Gwaggo don ta sa a jakar ta kar tsautsayi ya sa a manta tsabar zumuɗi, sannan ga ƙarin albishir na cewa Baba ya siya mun Jamb ɗin, kawai ya ce ta tambaye ni wani course nake son yi a jami'a. Na rasa me zan ce da mutanen nan, tsakani na da su sai godiya da addu'ar Allah ya ƙara fauwala masu, ya kuma basu ikon yin abubuwan alkhairan da suka ƙudara a ransu, Ameen.
Abu guda da wasa wasa yanzu ya fara damu na bai wuce tunda na dawo Kano ba ni da mashinshini ba, ba wanda ke cewa yana so na. Ga shi na yi baya da Rukky, dama kuma da ita kaɗai na aminta a ƙawaye, ragowan bana zuwa gidansu su ma haka. Faruƙ tun zuwan sa biyu da yayi bai ƙara zuwa ba. Allah ma ya sani i'm lonely! A irin wannan lokutan ne nake kewar Abba, zama da shi yana ɗauke hankali na daga abubuwa irin waɗannan. Duk da yanzu kam na gama yarda ni da Abba we are only friends! To wai me ke faruwa da ni ne? Why am i so desperate? Halin da ban taɓa tsintar kaina a ciki ba.
Ranar da su Abba suka zo kuwa kamar ya san ina kewarsa da yawa, Rukky na haduwa da Ya Saif, Abba yace na fito mu je yawo na nuna masa Kano da kyau don ya ga da me Kanon ta fi Zaria.
Sau wurin ƙarfe uku muka dawo gida saboda mun san ana la'asar za su kama hanyar Zaria. Duk girkin da muka yi da Rukky amma sai da na sake miƙo wanda ta girka. Ni da Abba kam cikinmu a ƙoshe yake, abincin Inna ne ma ya ba shi sha'awa ya ɗan zuba kaɗan yana ci.
Ya Saif ya ce "Halima kin san kuwa yau Abba ne ya kawo har garin nan?"
Na amsa "Haba mana Ya Saif, me ye na tsokanarsa tun dai bai batar da kai ba?"
Rukky da sauri ta sako baki "Abin yau har da 'yar goyon baya? Kin fi kowa sanin halin Abba ai, yanzun nan sai ya gwasale ki ya nuna ke ba ta hannun daman sa ba ce."
Ya ɗago kansa daga abincin da yake ci yana kallon Rukky har ta ƙare maganar ta, sai yayi gyaran murya ya ce "Baiwar Allah magana kike yi ne?" Gabaɗaya muka kwashe da dariya.
Lokacin da muke tsaye a waje wurin motar su muna jiran Ya Saif yayi sallama da Ruƙayya, suna cikin gidanmu har wannan lokacin, Abba ke tambaya ta a ina zancen makaranta ya kwana. Bayan na faɗa masa ne yake ce wa "Gara dai ki biyo ta Jamb ɗin, idan ba haka ba diploma shekara biyu ce kuma dolen ki sai kin yi hutun shekara ɗaya kafin a baki admission zuwa level 2, shi ma fa sai points ɗin ki sun kai, if not daga level 1 za ki fara. Kawai ki fara diploma yanzu, jamb ɗin ki na yin kyau ki watsar da diploma ɗin kawai."
*****************
Ya Saif ya fara service ɗin shi a Abuja, yana kuma zaune gidan ƙanin baban su (shi ne a matsayin uba a gare su yanzu haka tun bayan rasuwar babansu). Shu ne kuma ya ke kula da mafi rinjayen dukiyarsu da mahaifin su ya bar masu, sannan zuwa karatu England duka shi ya ɗau nauyin Ya Saif da Ya Abdallah. Yanzu ma dirama ake yi akan karatun Abba, so yake yi shi ma ya tafi kamar 'yan uwansa amma Abba sam baya son matsawa daga kusa da Hajiya (tunda kusan shi ne kaɗai namiji a gaban ta yanzu sannan akwai special bond tsakanin shi da Hajiya), Hajiya ma ba ta son a ɗauke mata shi, amma dai Kawun nasa yayi shiru bai ce komai har yanzu, duk da Abba ya karaya saboda gabadaya tun daga gidansu zuwa gidan Kawun nasa ba wanda bai fita waje karatu ba a mazan. Kuma kaf cikinsu Abba ne yayi lattin gama Sakandire, don sun gama da ƙarancin shekarun da basu kai wanda Abban yake ciki yanzu ba.
Ni kumabta ɓangare na sai haɗa kayan zuwa jami'a nake yi, komai na raruma sai nace wannan na makaranta ne. Na yi matuƙar ƙagara a ce admission list ya fito sannan kuma a ce nayi sa'a ya fito da sunana a ciki, don ban san ma wani irin farin ciki zan yi ba. Allah ya ba ni ikon ba maƙiya kunya! Ameen Ya Allah!
**************
BAYAN WATA UKU
Kwanci tashi duk wurin Allah suke, kuam sai wucewa lokaci yake kamar ƙiftawar ido. Cikin kuma ikon Allah List ya fita kuma sunana ya fito a ciki. Satin da ya wuce ma da Ya Saif ya zo, Abba ya ce a faɗa mun ya karɓo na shi admission letter ɗin sa (da yake shi sunan shi a first batch ya fito), an ba shi political science, sannan a faɗa mun yana nan yana jira na.
Satin da na samu saƙo daga Zaria cewa second batch ya fito da sunana,ba wani ɓata lokaci na tattara yana-wa-yana-wa sai Zaria, don da dama tuntuni nake ta haɗa kayan tafiya. Woo Allah! Burin Halimatu ya cika ta zama 'yar Jami'a!
Duk wani hawa da sauka na registration Abba ne ya taya ni duk da cewa ba department ɗaya muke ba, don ni mass communication aka ba ni. Ni dama ban wani damu ko ma me za'a ba ni ba, burina bai wuce na ga na zama ɗaliba ba, kai ko cewa aka yi nake shigowa ina fita kawai a matsayin ɗaliba yarda zan yi! Burina kuma ya cika tunda ga ni a jami'a, jami'ar ma ta Ahmadu Bello!
Ɗinkuna kuwa da nayi saboda fara makaranta da kun gani sai ya ba ku mamaki. Wannan giringiɗishi da rawar kan da nake yi yana daga cikin halayyar da na daɗe da bari ko nake tunanin na watsar, ashe kwanciya suka yi, sarari ashe su ke nema su nuna kan su. Lallai gaskiyar bahaushe da yake cewa ko bayan shekaru ɗari ka ga mu da mutum, kar ka tambaye shi halayyar shi sai dai ka tambaye shi arziki, don hali ba ya sauyawa. Hmn! Rayuwa kenan!
Hatta venue na wurin da zamu dinga ɗaukar darasi sai dai Abba ya ja ni muka dinga tambaya har muka gane kowanne sannan ya damƙa mun jadawalin karatuna a hannu na, ya mayar da ni kamar wata ƙaramar ƙanwar shi, don acting ɗin babban Yaya yake yi. Idan ba ni da lectures har bin shi tasu nake na shiga, amma shi bai taɓa bi na ba ko da kuwa free yake. Kuma yanayin saurin sabon shi ya sa ya sake da mutane da yawa, sai a ɗauka ma ya daɗe a makarantar.
Nayi-nayi Baban Zaria ya bar ni na zauna a hostel amma sam ya ƙi yarda sam, don cewa ya yi daga gidan zuwa can ya wuce minti talatin zuwa arba'in ne? Sannan Abba da ya fi ni nisa da makarantar ma ya zo gida ya zuge Gwaggo wai idan aka bar ni na zauna ƙawaye ido za su buɗe mun (yana sane fa, ya san ba hakan ba ne zai faru, halin Abba ne kawai, watau tun bai zauna ba ni ma ba zan zauna ba). Dole na haƙura da batun zaman, tunda Gwaggon da za ta taya ni roƙo ita an sa ta ƙyamaci zaman nawa, tunda ta haye kan zancen Abba tayi ɗare-ɗare har da ƙara zuga Baba. Shi ma kuma yace idan ba zan dinga tafiya daga gida ba sai dai a bar karatun.
Fushi kam nayi da Abba har ya kusa na sati ɗaya amma sai yayi ta nuna kamar bai san ma ina yi ba don kullum cikin tsokana ta yake bai daina ba, ni kuma ganin ya mayar da ni mahaukaciya dole ta sa na watsar da fushi muka koma yanda muke.
Kuma kasancewa yanzu an sakar masa mota don zuwa makaranta sai ya zama kusan koyaushe shi yake maida ni gida, idan ɗaya daga cikin mu ya gama da lectures ɗin sa na ranar sai ya jira ɗan uwansa ya kammala. Idan muka ya ɗauko ni da safe sai dai idan ya zama lokacin lectures ɗin mu sun yi kusa, amma ba ya biyowa ni da kaina nake kai na makaranta koyaushe.
Yawancin 'yan ajinmu da muka kammala makaranta tare duk suna ABU ɗin a mabanbantan departments. Habiba tare suke da Abba a department ɗaya, abin da yake ƙona mun rai bai wuce yanda take wani nuna tafi kowa kusanci da shi. Mts! Ba su da aiki sai yawo, su cika motarsa ita da ƙawayenta su yi ta fita, ni fa ina jin wani lokacin ma tsallake lecture suke yi su yi tafiyar su. Na kasa zama na yi ƙawaye a nawa department ɗin, idan naje neman sa a nasu sai na iske sun fita da su Habiba. Abun na matuƙar masifar soya mun rai! Ƙ! Sai kawai na share na daina zuwa neman sa, kuma idan na tashi na daina jiransa.
Rannan Allah ya taimake ni ina shigowa daga main gate lokacin wurin ƙarfe uku ne, zan je Ribaɗu Hall ne karɓar wasu kaya da zan yi style ɗin, muka ci karo da shi yana fitowa tare da wata da ban shaida ko wace ce ba.
Na wuce su ba tare nuna alamar nasan Abba ba bare ya sa rai zan kula shi. Da sauri yayi parking ya kuma biyo ni a baya yana ƙoƙarin tsokanata kamar yanda ya saba. Na ci gaba da share shi kamar da wasu yake yi ba da ni ba. Ganin ina ƙoƙarin crossing zuwa hostel ɗin ya sanya shi riƙo ni ta gefen hannu, a ƙoƙarin hana ni ci gaba da tafiya. Da sauri na doke hannunsa tare da rage girman idona, alamar bana son rainin wayo na ce "Wai me ka mayar da ni ne? You have no right! Bana son irin haka. Ni kawai ka ƙyale ni ka je ka ƙarata da ko ma su waye, don ni ba irin su ba ce! Kai ni fa ba ka dame ni ba, komai ka yi ai ka san ka kai ka yi ne."
Tunda nake da Abba ban taɓa ganin ya zama serious akan wani abu ba sai a daidai wannan lokacin, bai ma jira na ƙara buɗe baki ba ya fara ba ni haƙuri (abinda bai taɓa yi ba).
Sai kuma naji a raina i overreacted! Idan ba'a sanin sabbin mutane a rayuwa, to shi da zan san shi ne? Ko ma meye nawa a ciki? I was just being selfish ne, ta ya ya zan so na tattare shi a wurina kaɗai? Ta ya ya? Kawai kewarsa ce ta sani nayi abinda na yi saboda yana matuƙar fuskantata ko da kuwa ban faɗi abu da baki ba. Dole na na haƙura, don na ga lamarin nawa babu adalci.
Na juya ban ce masa komai ba ina ƙoƙarin gangarawa hostel ɗin, sai shi ma ya sake biyo ni yana faɗin "Ba kin tashi ba? Ki zo mu tafi mana."
"A'a, ka bar shi. Akwai abinda zan yi ne yanzu don sai an jima can zan wuce gida ma."
"Ba ki haƙura ba ne har yanzu?"
"Ni wace da ba zan haƙura ba? Kar ka wani damu. Ka tafi ka bar mutum a mota, kuma kasan darajar mutum har kullum yawa ne da ita."
Na wuce na bar shi, duk yana biye da ni yana magana ban tsaya ba, haka na wuce kai tsaye cikin hostel ɗin. Dolen shi ya tsaya a bakin ƙofa tunda maza basa shiga ciki. Kuma har wannan lokacin raina ba ya mun daɗi, watau wasu sun fi ni a wurin sa ko?