Taƙaitaccen Tunani

10

by @faddabanan

Tun ƙarfe uku da rabin dare muka tashi domin ba mu san lokacin da zasu iso ba. Samosa da spring rolls wrap na yi, Rukky kuma ta kwaɓa cake mai inibi da garin kwakwa a ciki. Ƙannen Rukky watau Maryam da Husna sai da aka yi sallar asuba sannan suka zo suka sa mana hannu a aikin. Ni kuma ina gama haɗe kan abinci sai na kuma kan juice na bar masu ragowan aikin, muna hira kamar ba safiya ba, a haka Mama ta zo ta iske mu. Ai kuwa tayi mamakin yawan aikin da muka yi har tana cewa dama ba mu yi juice ɗin ba, tunda ga shi Alhaji ya shigo da kwali da yawa.


Na amsa "Ba komai ai, su sha na sha su bar mana ragowan don na san abincin nan ba zasu iya cinye shi ba."


Kafin sha biyu babu abinda ba mu jera ba a falon Alhaji, don har wanka su Maryam sun yi, ni da Rukky ne har lokacin ba mu shirya ba. Sai kuma ga wayar Ya Saif kan cewa za su ƙaraso idan an sakko daga juma'a don ma sun kusa Kano.


Kun ga kwalliyar Rukky ta yau kuwa? Wow! Ni kuma sam na manta ashe zan canza kaya a gidan, kayan da na taho da su daga gida kayan bacci, brush da kayan shafa ne kawai. Rukky tayi-tayi ma na sa kayanta bayan na fito daga wanka amma na dage a'a, tunda gidan babu nisa can, ɗan achaɓa kawai zan samu ya kai ne sai na shirya na dawo. Sauri ma zan yi saboda kar su riga ni isowa. Dole ta haƙura ta bar ni.


A daidai ƙofar gidansu wurin sauri na yi karo da mutum, saura kaɗan na hantsila sai Allah ya taƙaita bangon da na bugu a jikinsa ya tare ni, da ba don na yi saurin sa hannu na kare fuskata ba da tuni na buga goshi na a jiki. Zafin buguwar ya sa na ce "Wash Allah na!"


"Sannu, i'm really sorry ban lura mutum na tahowa ba. Kin san idan mutum ya fito daga rana duhu ya ke gani. Mu ga goshin, ya fashe ne?" Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin janye hannun daga fuska ta. Da sauri na zame hannuna ina ƙoƙarin ganin waye don tabbas na san muryar nan.


Kawai gani na nayi na koma cikin gidansu Rukky fa gudun gaske ina ihun cewa ga Yaya Ahmad ya zo, su ma na cikin gidan ban san ya aka yi ba, kawai a tsakiyarsu na ganshi har sun taro shi.


Kallon mamaki yake yi mun har dai ya gaza ya ce da Mama "Wai wannan wace ce ne? Ba Halimatu ba ce?"


"Ita ce mana, ga ni kayi ta canza maka ne?"


"Ai canjin ba na wasa ba, wai ba Halimatu 'yar lukuta ba?" Su Husna suka fara ƙyalƙyala dariya, bai kula su ba ya cigaba da magana "Ai yanzu ɗaya bisa kashi huɗun daa take, domin ta yi uku zuwa huɗun haka before."


Ni kuma ganin lokaci na wucewa sai kawai na yi dariya, na ƙara yi masa sannu da zuwa sannan na fito daga gidansu zuwa namu.


Yaya Ahmad shine babba a gidan su Rukky, yanzu haka yana aiki a Warri ne, kuma yana matuƙar daɗewa bai zo gida ba don ina jin ma sau ɗaya yake zuwa gida a shekara. Yana tare da matarsa da yaransa biyu a can. Mai bi masa Yaya Shamsu ne, kuma a Legos yake aiki, immigration ne, sai Rukky, Maryam, Husna Sai ƙaramin su Abdul.


Ina shiga gidan mu Baba na fitowa zai tafi masallaci, mun gaisa kafin ya wuce ni kuma na shigo ciki, lokacin ita kuma Inna wanka take yi domin na jiyo zubar ruwa a banɗaki.


Jaka na fara canzawa, na kwashe abinda nake buƙata na zuba a ɗayar da na ɗauko yanzu.


Inna ta tsaya bakin ƙofar ɗaki na ta ce "Yaushe ke kuma ki ka shigo? Ban ji motsin ki ba sam. Har sun zo ɗin ne?


"Ban daɗe ba, ina isowa ma Baba na fita. Ba su ƙaraso ba, kaya ma zan sa na koma amma ga snacks na kawo maku ke da Baba, ki ɗanɗana ki faɗa mun ko hannunmu ya faɗa a girki ko da sauran mu"


Ta gutsuri spring rolls ɗin tana cewa "Daɗina da ke zuzuta kai." Ta sa a baki sannan ta ce "Umm...to ba laifi, ga ɗanɗano yana kai wa har ciki kai kuma tafarnuwar da aka yi amfani da shi ya ƙara masa ɗandano.....ummm....." Ta ɗago ta kalle ni kafin ta ce "Ke kika haɗa abun nan."


Na yi ƙaramin murmushi ina ƙoƙarin rufe dariya ta na ce "Daga kin ji tafarnuwa a ciki sai ki ce ni ce na haɗa?"


Ta fara dariya ta ce "Haba Hali dubu, ai in dai kin sa hannu a abu dole ne na gane ko da tafarnuwa ko babu. Ke bari ga naje nayi sallah kar ki tsare ni anan."


Na bi bayan Inna da kallo har ta fice, ina mamakin yanda take sane da komai da ya dangance ni, babba ko ƙarami. Ni ma dai alwalar na yi don so nake sai na yi sallah sai na shirya, domin ƙarar babura masu cewa sun shaida mun an sakko daga masallaci.

********************


Na sauka daga kan mashin ɗan nesa kaɗan daga ƙofar gidansu Rukky saboda motocin da na hango, kenan sun ƙaraso. Babu kowa cikin motocin. Da sauri na sallami me mashin ɗin na kuma doso gidan ina tafiyar sassarfa (sai kace da ni za'a yi maganar auren). Sai kuma na hango Abba yana ƙoƙarin buɗe mota don ma lura da lokacin da ya fito daga gidan ba, kamar abu zai ɗauka a cikin motar don ban ga ya nuna alamar zama ba. Sai na sauya akalar tafiyar tawa zuwa wurin da yake ɗin ina cewa a raina watau ɗan rainin wayo da shi za'a zo yace mun babu shi.


Ina ƙarasowa yana ɗagowa daga duƙen ɗaukar abun da yayi, ban bari ya juyo ba na rufe masa ido. Ya ɗan yi jum kamar yana mamakin waye zai rufe masa ido, ya ce "Na ba da gari ko ma wayw, i really can't guess who is it."


Mamaki ya kama ni, to wai ta ya za'a yi Abba ya canza murya? Na zame hannuna na riƙe ƙugu ina jiran ya waigo.


Yana juyowa ya kalle ni sai da gaba na ya faɗi, ba Abba ne! Tsananin masifar kama ce da ta har ta ɓaci. Sai ka ce twin brother ɗin sa! Shi yana mun kallon mamaki ni ma shi nake yi masa. Da ƙyar na samu baki na ya motsa nace "Ka yi haƙuri don Allah, wallahi na ɗauka friend ɗina ne Abba."


Ya yi murmushi ya ce "Ah! That explains it! I'm his cousin. Abba fitina, Abba tsokana ko?"


Dariya na yi na ce "Amma gaskiya kuna bala'i bala'in kama! Wai! Na yi mamakin da na ganshi don nasan ya ce mun ba zai zo ba ai. Ashe wani sabon Abba ne."


"A'a fa, ni Khalifa nake."

"Ayya. Ni kuma Halimatu sunana."


Ya rufe motar yana cewa "Nice to meet you Halimatu."


A tare muka shiga gidan, shi yayi falon su Alhaji ni kuma na wuce can ciki. Da alama suna da yawa da suka zo, don ina jiyo muryoyi.


Na ɗaki na iske Ruƙayya ta yi tsuru-tsuru kamar mara gaskiya. Ina dariya na ce "Ya ya ne ta Saifullahi takobin Allah? Ko don ba ki ga rabin ran naki ba ne ki ka wani takure? Ko naje nayi sallama nace ya fito ga Rukky na nemansa ta kasa numfashi?"


Duka ta kawo mun na kauce ina ƙara ƙarfin dariyar ta wa, ta ce "Haba wuce nan, ai suna shigowa na leƙa ta taga na hango shi, na kuma ga Abba da wasu da ban san su ba, amma na gane Kawun su."


"Oh! Rasa kunya ɓeran tanka, watau har leƙen surukan ki kike yi ko?....." Da sauri ta rufe mun baki tana cewa "Ki yi magana a hankali mana, kar ki ja mun mitar Mama idan ta jiyo ki, kin san halin ta dai."


Ina dariyar dai na amsa "Kamar kin san da gayya nake ɗaga murya, don so nake ta ji. Kuma ba Abba ki ka gani ba don ya ce ba zai zo ba....."


Ta katse ni "Dallah Malama, Abban ne ban sani ba?" Tana hararata.


"To ni ma yanzu na gama abun kunya a ƙofar gida, na je na rufe masa ido na ɗauka Abba ne, ashe wai cousin ɗin sa ne Khalifa."


Ta dinga yi mun dariya tana tsokana ta kafin ta ce "Wace irin kunya ki ka ji don Allah?"


"Yo kamar ƙasa ta tsage na shige ciki mana, don ma Allah yasa yayi making situation ɗin less awkward."


Ganin akwai wuta sai na kunna wani fim da muka fara kalla jiya da daddare aka ɗauke wutar ba mu yi nisa ba. Kallon ne kuma ya ɗauke mana hankali har ba mu lura lokaci ya tafi ba sai da muka muryoyi ana fitowa ana sallama. Kawai sai hankalin mu ya koma can. Sai bayan minti kusan goma sai ga Abdul an ce ya kira mu ni da Ruƙayya inji Alhajinsu.


Ta jawo babban mayafi jikin ta sai rawa yake yi, ni kuma ina tsokanar ta "inye, ka ga amarsu mai daɗin tuwo. Angon dai ya wuce bai ga amaryarsa ba, hankalin amarya ya tashi." Sam ba ta kula ni ba, ta wuce gaba na bi ta a baya.


Tunda muka doso falon muka lura da alamar cewa har yanzu akwai mutane a ciki. Ruƙayya na ganin haka ta koma bayana tare da turo ni gaba, don haka ni nayi mana jagora zuwa ciki. Daga bakin ƙofa na ɗan tsaya ina leƙen ciki ta labule haɗi da sallama da murya ba mai ɗagawa ba, sai kuma na lura Alhajin su Rukky ba ya ciki.


Daga ciki a ka ce "Ku shigo mana, na zo na ga ɗiya ta ne ai.". Kawun su Abba ne yayi magana. Muka shiga a hankali muka durkusa kusa da ƙofa. Muka gaisa duka kanmu a ƙasa.


Ya sake cewa "Wai wace ce ɗiyar ta wa a ciki?"


Ya Saif ya amsa yana dariya "Yanzu Daddy ba ka gane ta ba?"


"Bari na duba da kaina to, duk wacce ta cika rufe fuska nasan ita....." Tun kafin ya ƙarasa maganar ma har Rukky ta daɗa dunƙulewa, hakan ya sa gaba ɗaya kowa a ɗakin ya fara dariya. Shi da Khalifa murmushi yayi kawai kamar irin shi bai ma gane me ake yi ba.


Ina ganin Ya Saif ya doso mu sai na tashi a hankali na koma ɗayan gefen, ita kuma da yake kanta a rufe yake ba ta san ma na tashi ba. Ya riƙo kafaɗun ta yana ƙoƙarin ɗago ta ta tashi tsaye ya ce "Ta so muje ku gaisa da Daddy da ragowan 'yan uwana."


Ta fara ƙoƙarin zamewa daga riƙon da yayi mata, hakan kuma ya sa mayafinta ya sauka daga fuskar ta, da sauri ta fara ƙoƙarin mayarwa amma sai ya riƙe. A haka ya ƙarasa da ita gaban Daddy.


Daddy ya ce "Kar ki ji kunyar kowa anan, gara mu gane ki, ke ma ki gane mu. Kuma babu zancen kunya tunda mun zama family yanzu, formalities kawai za'a yi ya zama binded."


Ta sake gaishe shi cikin nutsuwa shi ma ya amsa da kuma sauran na ɗakin, sannan Ya Saif ya fara gabatar da wasu na falon a wajen ta.


Ya fara ta kan wani da gani ya girmi Daddy, ya ce shine Baba Malam (yayan mahaifinsu ne). Kuma daga Baba Malam sai Daddy ne manya a ciki don haka suna gama gaisawa suka fice su ka bar mu. Tare da jaddada masu kar su ɓata lokaci, don basa son yin tafiyar dare a hanya.


Don haka suna fita ya fara wani introduction ɗin na samarin da suke tare da su. Ya fara ta kan Khalil da kusan kai ɗaya suke da Saif ɗin ya ce mata cousin ɗin sa ne tare suka gama karatu kuma yanzu haka dukkan su serving suke.


Sannan Habib, Ishaƙ da suke ƙannensu sau Khalifa da aka ce shine ƙarami cikin waɗanda suka zo, kuma dukkanninsu dai a Abujan suke. Khalil ne ya fara tsokanar Ya Saif yace sai wani rawar kai yake masu, Habib ma yana taya shi. Shi kam Khalifa sai dai yayi murmushi kawai (habawa, ai sam halinsu ba iri ɗaya da Abba ba ne, iya kama kawai abun ya tsaya).


Sai da muka fara shirin baro falon don zasu tafi sannan Ya Saif yace "Oh my God! Na yi babban laifi ban gabatar maku da ƙawar mu ba, friend ɗin Abba ce, Halimatu kenan."


Ishaƙ ya ce "Gaskiya kina fama, Abba ne abokin ki? Kuma har yanzu bai haukata ki ba?" Suka fara dariya. Ya juya wurin 'yan uwan shi ya ce "Ai Abba da tsokana, ina jin kaman numfashi da zuciya ne. Yaron nan ciwon kai ne nake faɗa maku."


Habib ya ce "Kai kukan daɗi kake yi, ni me ye maraba ta da kakansa? In dai ya zo Abuja har dare nake yi, saboda ban isa na zauna na hutawa raina ba. Khalifa ne kawai baya tsokana kamar yanda ya mayar da mu."


Karo na farko da tun shigowar mu ɗakin ya yi magana. "Wa yace ba ya tsokana ta? Ina jin gara ku da ni, ni da yake ganin kamar kan mu ɗaya ne? Ina jin dai ya ɗauka ni sa'an sa ne, kuma ga shi abokansa su yi ta ɗauka ni ne. Ni fa yanzu ko a hanya ka kira ni da Abba amsawa nake mu gaisa na wuce, na daina wahalar da kaina bayanin cewa ba shi ba ne."


Y Saif ya ce "Halima ke ta ya ya kika gane ba Abba ba ne? Da wuya mutun ya gane a ganin farko fa."


Dariya ni da Khalifa muka yi, sannan na ce "Ni da har ido na rufe mashi na ɗauka Abba ne." Aka dinga yi mun dariya. Har sai da Abdul ya yi sallama ya shigo ya ce wai Daddy ya ce su ja motocin su wuce ne?


Da sauri suka fito waje, ba mu raka su har ƙofar gida ba saboda su Daddy da Alhaji da ke tsaye a waje. Ganin sun fita yasa muka juya domin komawa cikin gidan, amma sai na ji kamar ana kiran sunana, na waigo sai na ga Khalifa, na dawo ina murmushi.


"Me zan faɗawa twin brother na? Ko friend ɗin ta shi ba ta da saƙo ne?"


"Kawai ka ce ina gaishe shi, ai Sunday zan koma Zarian."


"Au, a Zaria dama kike?"


"Ina ABU ne tare da Abban."


"To zan faɗa masa, sai gani na biyu. Bye."