11
by @faddabanan
Ana kiran sallar Isha ina sanya ƙafata cikin gidanmu. Ba yanda ba tayi da ni na ƙara kwana ba amma na ƙi, gara naje na tattara kayana na kuma yi hira da Inna tunda jibi da safe zan koma inda na fito. Na baro gidansu Mama tana ta yi mun godiya, ni kuma nauyin hakan nake ji, ta ya ya tana babba tana dinga gode mun ina 'yar mitsila da ni?
Mama ce kuma ta ce Yaya Ahmad ya maido ni gida, na so na zame amma sam ta ƙi ba ni sararin yin hakan, ita ba ta san gudun duk wani abu da zai mu keɓe da shi nake yi ba. Tsananin kunyarsa nake ji, domin yana cikin sahun waɗanda na wulaƙanta can wani lokaci a baya ko nauyin Rukky ban ji ba. Shi ma ganin nacin sa a kaina ba zai haifar da ɗa mai ido ba, sai ya zaɓi Warri akan Kaduna lokacin da aka samar masa aiki, yanda zai yi nisa da komai. Kuma tun tafiyar shi aikin ban ƙara sa shi a idona ba sai wannan lokacin, domin muddin na ji labarin ya zo Kano to shi kenan na ɗauke ƙafata daga gidansu jar sai ya koma. Sai kuma a can ya haɗu da matar da yake aure yanzu, babanta ogansa ne a wurin aiki, su ɗin ma 'yan arewa ne. Ga shi yanzu har ɗiyanshi biyu. Jiyan ma da muka haɗu da na kwaso zuwa cikin gidan, gudun borin kunya ne (😓).
Tunda na shiga motar ta shi na sunkuyar da kaina ina ta addu'ar Allah ya sa kar yayi mun magana har ya kai ni gida. Ai ko addu'ar ban dire ba naji yana cewa "Halimatu manyan gari, ashe talaka na ganin ku? Na ɗauka fa kin yi aure ai tunda na ji ki tsit ba wani labari. Me ki ke yi ne yanzu?"
"Ina diploma a mass comm nan A.B.U Zaria."
"Kenan yanzu a Zaria kike da zama."
"Eh, amma ina gidan Gwaggo Hafsatu ne, daga can nake zuwa makarantar."
"That's good, shi ilimi ai daɗi ne da shi. Sai a ba da himma a dage a yi karatun sosai sannan kuma a ƙara da addu'a. Ya batun aure....."
Sai na katse maganar da cewa "Ai Allah ne ke kawo lokaci. Ya kids ɗina da matar ka?"
"Suna lafiya, sanin ba daɗewa zan yi a nan ba shi yasa ban tattaro su mun taho ba. Tunda nawa zuwan ma short notice na samu daga Alhaji, ya ce idan da sarari nayi ƙoƙarin zuwa domin wakilan masu son Ruƙayya za su zo."
"Yaushe za ka wuce kenan?"
"Asabar, gobe kenan ko? That was the initial plan, amma Mama ta ce na yi haƙuri zuwa Lahadi don sun daɗe basu ganni ba."
"Ayya. Yaya Shamsu fa?"
"Wai! Ai rabo na da shi tun last year da muka zo yin sallah ƙarama, amma lafiyan sa lau fa, ɗazun mun yi waya da shi. Kuma da wuya idan ba tare da Ruƙayya za'a haɗa bikinsu ba, dama akwai maganar wata a ƙasa sai kuma jin batun Ruƙayya yau sai na ga hakan ya ƙara masa azama." Tuƙi yake yi kamar baya so shi yasa ma muka yi magana mai tsayi. Da muka isa gidan ma cewa ya yi na faɗawa Inna yana son shigowa su gaisa. Kuma ganin ana kiran sallar Isha sai ya shige sallah.
A tare suka shigo gidan shi da Baba bayan an idar, ya so tafiya bayan sun gama gaisawa amma Inna ya dage sai ya zauna ya ci abinci tukunna. Sai ƙarfe tara dai ya samu ya bar gidan. Kyautar kuɗi masu kauri ya yi wa Inna, ban ma lura ba tunda ni na fara yin gaba da zan kara shi waje.
Washe gari kam ina ga biyan bashin bacci nayi, don tunda na kwanta bayan asuba sai sha biyu na tashi. Kafin na yi wanka na kimtsa ma an fara kiran sallar azahar don haka sai na yi sallar ma sannan na ɗauko abinci (ga na safe, ga na rana duka Inna ta kammala) da zobo (Inna ba ta rabo da shi, saboda a wurin ta shine lemon karɓar baƙi.)
Yunwar da nake ji ta sa na kwaso duka abincin da aka ajiye mun a babban faranti na fito daga kicin, don ji nake yi duka zan iya cinyewa.
Inna da lokacin ta fito daga banɗaki ta kalle ni ta riƙe haɓa ta ce "Ni Hajaratu, wannan bacci naki kaman ba zai ƙare ba yau, ga shi kuma kin rufe ɗakin ta ciki. Me ya faru ne?"
Na kai loma bakina na ce "Wallahi gajiya ce kawai Inna, kuma jiya ai kin ga tun cikin dare muka tashi kuma ba mu ƙara kwanciya ba."
"Idan na ce ke raguwa ce ki ce ba haka ba, wannan ɗan abun ne ya sa kika dinga bacci kamar kin yi sati ba ki yi ba? Allah ya sauwaƙe maku son jikin nan na yaran zamani, kin yi sallar ko ba ki yi ba?"
Uhm, na daga mata kaina saboda bakina cike yake da abinci.
Ta ɗora "Ga kayan gugar ki can an kawo, na bawa yaron kuɗinsa ma. Bari naje na yi tawa sallar tunda ke kin riga ni yi."
Sai da na kwanta na huta sannan na kwashi kayan da zan haɗa na koma ɗakin Inna (saboda nasan ina fara haɗawa a gabanta za tace na kawo ta taya ni don ban iya haɗa jaka ba 😉). Ilai kuwa hakan ce ta faru, ina zaune ina miƙa mata kaya ita kuma tana jera mun a cikin jakar (da yake ka dawo da wasu kayan daga Zaria, zan kuma musanyasu da wasu).
Muna cikin magana Inna ta ce "Ɗan dakata, kamar sallama nake jiyowa ko kunnena ne?" Muka ɗan saurara kafin muka jiyo sallama. Na leƙa don ganin mai yin sallamar, Yaya Ahmad na gani toge a bakin ƙofar shigowa. Sai da gabana ya faɗi sannan na fara murmushi ina faɗin ya ƙaraso mana sannan na juya cikin ɗakin ina faɗawa Inna waye.
Ya shigo tare da zama kan darduma suna gaisawa, ni kuma ina ƙoƙarin haɗe ragowan kayan da yayi saura na gaishe shi.
Tunda na ga Inna ta wullo mun wani irin kallo na gano mai ya dace nayi, da sauri na fito na nufi kicin domin ɗebo masa zoɓo da ruwan sanyi sai kuma a lokacin na lura ashe a ruɗe nake. Ruwan sanyi na watsa kan fuskata ina faɗin "calm down Halimatu, calm down."
Na kawo mashi ruwan, da na ga Inna na ƙarasa sanya ragowan kayan sai kawai na zauna don mun ci ƙarfin abun ma.
Cikin salon jan hira na ce "Wai ni Yaya ya ma sunan ɗiyanka? Ka je ka sa masu suna masu wahalar riƙewa."
"Kawai dai ki ce ba ki damu da sunayen nasu ba, amma mene abun wahala a ciki? Ko Inna? Domin yanzu kika tambaye su kuma da sunayen na su."
Ban bari Inna ta amsa ba na ce "A'a Yaya Ahmad, kar mu yi haka da kai mana."
"Ai kuwa ba zan faɗa maki ba, duk ranar da ki ka damu da su za ki tuno sunayensu da kanki." Lura da nayi shi da Inna murmushi suke yi.
Na zumɓura baki na ce "Allah kai da Inna tsokanata kuke yi, ba ga shi nan kuna murmushi ba?"
Ya fara dariya "To, yau ga ikon Allah, luka kike son mu yi?"
Na hango wasu kayan da na ware cikin wanda na zo da su zan koma da su, sai na miƙe na ɗauko su na miƙawa Inna. Don haka ya ce "Yanzu Inna, Halimar da girmanta amma sai kin taya ta haɗa jaka? Idan kuma ta yi aure wa zai dinga yi mata da family ɗin ta? Gaskiya Inna ki na barinta tana yin abubuwa irin waɗannan."
Inna na murmushi ta ce, "Ai sai a hankali, dabara nake koya mata saboda kayan da jakar ta ɗauka yanzu idan ita ce ko rabinsu ba za su shiga ba sai a ce jaka ta cika."
"Duk da haka, da sai ta zauna tana yi kina faɗa tare da nuna mata, wannan ai wahalar da ke take yi."
Muna tare har la'asar sannan ya yi mana sallama ta gabaɗaya saboda gobe da asuba zai ɗau hanyar tafiya garinsu. Na raka shi mota ina addu'ar Allah ya sa kar yayi maganar da zai awkward moment tsananin mu, kuma cikin ikon Allah bai yi ba, kawai nasiha ya yi mun game da rayuwa da kuma jan kunnen na maida hankali sosai a karatu. Ya kuma dunƙula mun kuɗi ya ce ba rage sabgar makaranta da su. Da na nuna ya bar shi ma, sai ya fito mun sak a yayan da yake don haka dole na karɓa na yi godiya da addu'a.
Har zai tafi ya ce "Hisham da Afra ne sunan yaran naki, saura a fake da wahalar suna a sake mantawa, domin sun fi sunan ki sauƙin faɗa ma."
Naira dubu ashirin na gani da na koma cikin gida muka ƙirga da Inna (dole ya ba ni, domin yanzu ya zama mai kuɗi ai. Yo ko motar da yake hawa mutun ya kalla ya san kuɗi sun zauna masa). Yaushe rabon duniya da ayyaraye? Ni Halimatu da dubu ashirin a dunƙule, kuma kyauta nawa na kaina? Yaushe rabo?
Yana tafiya na daɗewa sai ga Rukky ta zo, hayaniyar da muka fara a ɗakin Inna ya sa ta kora mu ɗaki na, wai mu bar ta tana son sauraren wani shiri a gidan radio.
Rukky da kaji soyayyu ta zo mun da su, wai sune tsarabar tafiya da kuma juice na ƙananan kwali katon guda sai coke na gwangwani shi ma carton ɗaya sannan kwalin foster clarks na ginger da coconut. Na rungume ta ina godiya don na ji daɗin alherin nan da tayi mun.
Ta ce "Haba Halimatu, ai kin fi ƙarfin komai a wuri na, sai dai nayi fatan Allah ya bar mu tare, ya kuma tsone idon maƙiya aminiyar." Ta ƙarasa maganar tana laluɓen jakarta ta ciro kuɗi tare da miƙo mun ta ce "Wannan saƙon Mama ne, ta ce ki yi kuɗin mota kuma tana yi maki ban gajiya, Allah ya saka maki da alkhairi."
Tana gidan mu har Isha, hirar Ya Saif ba ta ƙarewa saboda tana matuƙar son shi (idan kana son mutum ba ka gajiya da hirar shi).
********************
Kashe gari kam takwas ma na fiddo kayana, so nake na isa Zaria da wuri, almajirin Inna da take aika ne ya taya ni ɗaukar jaka ta zuwa bakin titi domin samun abinda zai kai ni tasha. Kuɗin da Baba ya ba ni ma ban karɓa ba, nace masa akwai isasshe a hannuna amma ya dahe dole na karɓa na yi godiya. Kafin kuma na tafi na bar wa Inna wani kuɗi a kan ta siyo mun materials masu kyau da zannuwa sai ta aikawa tela na, don yanzu akan hanya ta ta tafiya zan tsaya nayi masa bayani kafin na ƙarasa tasha.
Duk saurin nan nawa amma motar mu bata yi sauri ba sam, don sai da rana ta take muka isa Zaria. Haka da na sauka na daɗe ina neman abun da zai kai ni gidan Gwaggo amma na rasa. Ni abun ma sai ya ba ni tsoro tunda duk zama na ni ban taɓa rasa abun hawa ba.
Na gaji ba na wasa ba, ga sallar azahar a kaina ga yunwa. Ina yamutsa fuska sai ga wata mota wacce gilasanta masu duhu ne kuma na ga tabbas wurina take neman tsaya.