Kuluwa

8

by @sadiyanasir


Malam Garbati wanka da ruwan d’umin da yayi ya rage kaso kusan arba’in na gajiyar da ya kwaso, yana jin wasu gabb’a na jikinsa da suka rik’e suna saki a hankali, musamman bayansa, Ya fito yana sharce ruwa daga jikin sa, Turus yayi ganin buhun shinkafa da ledoji dake nuni da kayan abinci ya kalli Umma Habiba yace “Wannan kaya kuma Habiba daga ina?”. Yayi maganar yana mamakin daga ina suka fito daga shigar sa wanka ya fito, Ta numfasa tana jan numfashi tace “K’awar KULUWA ce Rabi ta kawo wai YARIMA HALADU ya aiko”. Malam Garbati baki ya washe yace “Madallah ya fara taimako kenan kai amma dai Allah ya biya sa”. Umma Habiba tace “Toh taimako za’ace kuma ba taimako ba amma dai wai KULUWA yake so da aure”. Malam Garbati zancen yaji sa tamkar almara yana sake duban UMMA HABIBA yace “Shi Yariman yake son KULUWA kuma da aure”. Umma ta jinjina kai tace “Haka Rabi k’awarta ke sanar dani”. “Allahu Akbar Kabiran lallai al’amarin Ubangiji bashi da shamaki amma tabbas da mamaki kaf matan dake birni da nan k’auye ya rasa wacce yake so sai Kuluwa”. Umma Habiba wacce har lokacin zuciyarta ta kasa gamsar mata da zancen tace “Ni kaina abun ya bani mamaki Mallam, me ya gani tattare da KULUWA da yake son auren ta”. Malam Garbati yace “Kar ki manta HABIBA Kuluwa bata da wani nakasu tare da ita, a k’auyen nan za’a lissafa ta cikin masu kyau, kuma tana da natsuwa, abu d’aya KULUWA ta rasa rayuwar wadata da arzik’i”. Umma Habiba ta jinjina kai tace “Hakane, amma ni sai nake ganin kamar ba zai so taba”. Malam Garbati kai ya girgiza mata yace “Ki daina magana irin haka Habiba, ki dinga kyautata zato KULUWA ai bata da wani aibu da YARIMA ba zai so auren ta ba, addu’a kad’ai ya dace mu bi ta dashi”. UMMA HABIBA wacce ta fara gamsuwa da zancen Malam Garbati tace “Allah ya shiga cikin lamarin yasa za’a k’ulla alkhairi”. “Amin Amin shine addu’ar da zamu yi”. Ya fad’a yana zama kan tabarma gefen Umma Habiba.


KULUWA dukkan zantukan nasu akan kunnenta wanda take ji ya kamata ta sanar dasu manufar YARIMA HALADU a kanta, a zuciyarta tana jin haushi da mamakin RABI yadda tazo ta had’a k’arya su kalar tasu tarbiyar kenan, na ganin dacewar mace tayi mu’amala da da’ na miji bata hanyar aure ba, har abada ba zata d’auki gurb’atacciyar hanyar da suka d’auka ba, Tashi tayi zata fito tana d’aga zanin da yana k’ofar d’akin kariya, idonta ya sauka kan MALAM GARBATI DA UMMA HABIBA suna bud’e ledojin kayan abincin kowannensu fuska d’auke da tsananin farin ciki, “Allah maji rok’on bawa na tabbatar ya amshi addu’ata na ganin wahalar da nasha ba’a biyani hakk’ina ba, ya bamu abunda yafi biyan da za’a mun wanda bai fi muyi ci d’aya ba da ba k’osar damu zaiyi ba”. “Hakane Malam shiyasa ake so ko da yaushe bawa yayi dogaro ga Allah”. Sukayi murmushi a tare wanda ke nuna farin cikin su sosai, kyautar kayan abinci a yanayin da suke ciki ba k’aramin gata bane gare su, Zantukan iyayen nata ya saka mata rauni sosai a zuciyarta tana jin ba zata iya fita ta sanar dasu abunda zai d’auke far’ar dake kan fuskar su, bata so suyi amfani da kayan YARIMA HALADU sanin ba Dan Allah ya kawo ba amma ba zata iya tunkarar iyayenta da zancen mara dad’i ba, farin cikinsu ya fiye mata komai, Zanin ta sauke ta koma cikin d’akin ta zauna tare da jingina jikin bangon ginin k’asa dake shafe ta lumshe idonta sam zuciyarta babu natsuwa.



**************

Motocin MAJOR UMAR a jere suka kutsa layin gidan nasu, kamar ko da yaushe duk sanda zaije gidan nasu sai yan’ unguwa su bi motocin da kallo, mafi yawa na kamile kansu hatta masu motoci da mashina da suke wucewa rab’ewa suke gefe gudun suyi laifin da zai sa sojojin su hukunta su, Unguwa ce ta masu matsakaicin hali Gidan su Major Umar shine babba a kaf layin, mahaifinsa ya zab’i yin gini anan unguwar ne saboda anan ya tashi ya jima a unguwar tun zuwansa garin abuja tsawon shekarun baya da suka shud’e, 


Motar da tayi parking ya shaida masa sun iso gidan, Ya farga daga nisan tunanin da ya tafi yana bud’e lumsassun idon sa, babban gida ne ginin zamani mai cikar tsari da kyau mai d’auke da b’angarori guda uku, Kai tsaye na gaban ya shiga tare da yin sallama, Daga ciki ya jiyo muryarsa mahaifinsa mai cike da dattako ya amsa, MAJOR UMAR ya zare takalmansa daga k’afafun sa ya tura k’ofa ya shiga falon mahaifin nasa wanda ya wadatu da sanyin ac da k’amshin turare mai dad’i tamkar falon wani sabon ango, Major Umar idonsa ya d’an runtse kana ya bud’e zuciyarsa na masa zafi tuna lokutan baya duk sanda zai shiga gidan sa k’amshi irin haka ke mamaye k’ofofin hancin sa sab’anin yanzu da ya rasa meye canza masa Umaimar sa, Gefe d’aya ya zauna k’asan carpet ta saitin k’afafun Mahaifinsa, yana cikin girmamawa da yake ba mahaifin nasa baya tab’a zama kan kujera idan yana kai, Mahaifinsa ya kasance mutum mafi soyuwa a garesa wanda yake ganin ya zama masa babbar majingina kuma madafa abun dafawa, shi ya zame masa uwa ya zame masa uba, ya rasa mahaifiyarsa tun yana wata d’aya kacal a duniya bai san dad’in uwa ba, mahaifinsa shi ya maye masa gurbin uwa da uba, ya d’auki son duniya ya d’aura akan UMAR kusan rayuwarsa duk ya sadaukar akan kula dashi, ya jima baiyi aure ba gudun ya aura wacce zata gallaza ma UMAR, sai daga baya Allah ya had’a sa da Batula wacce mijinta ya rasu itama ya barta da k’aramar yarinya mai suna Saliha tausayin haka ya k’ara saka Alhaji BASHIR LEMA aurenta, ya kuma amince zai kula hadda yarinyarta, wanda a yanzu yaransu biyu mata tare duka suna matakin secondary, tun aurensu da Batula bai samu wata matsala dangane da ita ba akan UMAR tana kula dashi tamkar d’an ta, hakan yasa Alhaji Bashir yaji ta sake shiga ran sa. 



Tun shigowar Major Umar falon kallo d’aya mahaifinsa ya masa ya hango damuwa tattare dashi, ya masa wani irin sani da babu wanda ya masa shi a duniya, daga kallo yake fahimtar yanayin sa ko bai furta ba, “Baba barka da Rana”. Yayi maganar a ladabce yana sunkuyar da kai alamar girmamawa, “Barka kadai Umar, ya aikin naku?”. “Alhamdulillah”. Ya fad’a yana sake tankwashe k’afafunsa gu d’aya, Alhaji Bashir idonsa na kan UMAR dan’ sa mafi soyuwa gare sa yace “Allah ya cigaba da yin jagora”. Umar yace “Amin Baba”. Addu’o’in da yake samu gun mahaifinsa ya tabbatar su suka kawosa matsayin da yake yanzu tunda ya rasa na uwa, Alhaji Bashir ya numfasa ya kalli Umar yace “Ina fatan damuwar da nake gani tare dakai ba daga wurin aikin ku ba ne”. Baiyi mamakin jin haka daga mahaifin nasaba yasan irin sanin da ya masa da yadda yake karantar duk wani yanayi nasa, Yaja numfashi yana k’ok’arin danne damuwarsa yace “Ba daga wurin aiki ba ne Baba, wani ne ya b’ata mun rai a hanya”. Alhaji Bashir murmushin su yayi na manya wanda suka kwana biyu a duniya yace “A rage zuciya Umar, ka dinga hak’uri da mutane, ba komai zaka dinga fushi akansa ba”. Ya d’an shafa k’eyarsa yana jin sa wani iri karon farko da yayi ma mahaifinsa k’arya yace “In Shaa Allahu Baba”. Alhaji yana da yak’inin akwai abunda ke damun Umar baya son fad’a ne kawai, Shiru ya d’an ratsa falon wacce salamar Batula wacce suke kira da Mama ya sauka kan kunnensu suka amsa a tare, Ta shigo hannunta rik’e da bowl na kayan marmari da aka yanka, tayi shigarta fes cikin atamfa d’inkin riga da zani ta ajiye bowl d’in akan tebur dake gaban Alhaji Bashir, sai a lokacin ta kula da MAJOR UMAR dake gefe, Cike sakewa da far’a tace “Yau soja ne a gidan namu”. Fuskarsa ya d’an saki yace “Barka da Rana Mama”. “Yawwa Barka, ya aiki dan bana ce mutanen gida ba dan alamu ya nuna daga gun aiki kake”. Yace “Alhamdulillah”. Yana murmushi, “Bara na saka Saliha ta yanko ma fruits d’in kai ma”. “A’ah Mama a barshi”. Da mamaki ta kalle sa tace “Duk yadda kake son fruits Soja kaine da cewa a’ah”. “Cikin nawa ne a cike”. Yai maganar ba dan baya son sha ba, sai dai Saliha ce baya so ta kawo masa tun tsawon lokutan baya ya yanke duk wata alak’a tsakaninsa da ita, a da ya d’auketa tamkar k’anwarsa da suka fito ciki d’aya, a yanzu gaisuwarta kad’ai yake amsawa shima ba ko da yaushe ba.


************


Agogo ta kalla dake manne jikin bangon office d’inta uku saura minti biyu, lokacin tashin ta yayi, Teburinta ta soma kimtsawa tana ajiye wasu takardu a muhallin su, Ta shiga band’aki ta wanke fuskarta, ta fito ta jawo wata drawer da take ajiyar kayan kwalliya, ta gyara fuskarat tayi kyau sosai, tabi jiki da kayanta da turare wanda a take office d’in ya d’auki k’amshi, Ta d’auki mukullin motar da jakarta wacce ta jefa wayarta ciki ta fito, tana umartar secretary d’inta tayi locking office d’in,


A farfajejiyar ma’aikatar tasu ta tarar da ZULAI tare da SARATU dukkansu sun chab’a sabuwar ado bakinsu ya wadatu da janbaki mai d’aukar ido, ZULAI ta kalli UMAIMA tace “Ya naga bakin naki ba wani colour”. Umaima kai ta girgiza tace “Ku barni haka kunsan fa akwai igiyiyon aure uku a kaina dole nabi a hankali”. Zulai ta tab’e baki tana kallon Saratu tace “Uhmm hakane kinga mu kuwa ba takurar kowane gardi a kanmu muyi yadda muke so”. Ta mik’awa Zulai hannu suka tafa suna dariya, Umaima kallonsu tayi jikinta na yin sanyi fuskarta ta nuna alamun rashin jin dad’in maganarsu amma ta b’oye hakan tace “Muje ko”. Zulai tace “Hajajju Saratu ke kika san wurare ina ne best restaurant daza muje”. Saratu cikin nuna jin kai na cewar ta isa tace “4GUYS we should try chinese dish”. ZULAI tace “Then muje can”. Kowaccensu ta shiga motar ta suka ja, UMAIMA hankalinta kwance take tuk’i ba tare da fargaba lokacin komawarta gida yayi ba, ko tunanin tambayar izinin MAJOR UMAR.



*************


KULUWA ayyukan gidan nasu yau sukuku take yin sa sam babu kuzari ko walwala tare da ita, Dole kad’ai tasa tayi amfani da kayan abincin da YARIMA HALADU ya aiko ta d’aura musu girki bisa umarnin UMMA HABIBA, ta rasa ta ina zata tunkare su da zancen, k’asan zuciyarta tana jin zafi kada ya d’auki iyayenta kwad’ayyayunta na amsar kayan sa, Ba zata iya tuna yaushe rabon da taga far’ar da ta gani yau kan fuskar mahaifinta wanda farin cikin sa saboda KULUWA ne yana ganin zata samu hutu babbar damuwar sa ko da yaushe dama itace, Ita kanta Umma Habiba tana jin sanyi a ranta na tunanin idan aurensu yayi da YARIMA HALADU ta huta da babun da ta taso cikin sa, KULUWA kwanon shinkafar dake gabanta loma uku tayi shima na dole ne ganin idanun iyayen nata akanta kada su fuskanci wani abu, amma tamkar tana zuba ma bakinta mad’aci haka take jin abinci sanin dalilin kawo sa saboda yana son yin fasik’anci da ita, Mik’ewa tayi da zumar tashi ta kai abincin ta ajiye, Malam Garbati yace “KULUWA ba dai kin k’oshi ba”. UMMA HABIBA tace “Kai ma kasan hali, ta k’oshin take nufi”. “Haba Kuluwa me kika ci da har kin k’oshi”. Fuska ta d’an yatsina kad’an tace “Cikina ke ciwo”. “Subhanallah”. Malam Garbati da Umma Habiba suka fad’a a tare, “Ki d’auki kanwa ki jik’a ki sha zai lafa miki”. Umma Habiba ta fad’a cike da kulawa, KULUWA tace “Toh”. Tana barin wurin da kwanon abincin.



*****************

UMAIMA sun shafe fin awa d’aya a restaurant d’in sunyi order abinci wanda kad’an ne babu a dubu d’ari biyu, a take ZULAI ta bada ATM d’inta tace a cire ba tare da ta jira ba, UMAIMA yadda suke harkar girma yana matuk’ar burgeta, godiya ta ma ZULAI wacce cikin nuna ko in kula tace “Haba UMAIMA meye 200k dan na mana spending”. Sun d’auki hotona sosai tamkar yan’ mata masu tashin k’uruciyar su.



MAJOR UMAR sun d’an tattauna tare da mahaifinsa ya nemi shawarwarin sa kan kasuwancin sa, wanda yaji wani kaso na damuwarsa ya rage, ba k’aramin dad’i yake ji a ransa ba a duk sanda yake tattaunawa ko wata hira da mahaifin sa, Bayan sun idar da sallar la’asar a masallacin dake had’e da gidansu wanda mahaifin nasa ya gina, Ya buk’aci tafiyar su gida ba tare da ya koma ciki ba, Sukai sallama da mahaifin sa.



Hakimce yake a seat na baya, kallonsa na kan window yana kallon gilmawar motoci dan hana ma kansa tunani, Wayarsa ta fara k’ara, Hannunsa ya janye daga kanta yana duban sunan mai kiran MAJOR JABEER ya gani, Yasa hannu ya d’auki wayar tare da amsa kiran ya d’aura kan kunnensa ba kasafai yake saka wayarsa speaker ba saboda bai san maganar ko ta sirri ba ce, sai idan yana shi kad’ai yake sawa, “HELLO Major yanzu naga madam anan 4GUYS nazo nima ni da familyna zamuyi having lunch ina ta dubawa ko zan ganka, come over mu gaisa”. Zancen yaji ya daki zuciyar sa UMAIMA a 4 GUYS, “Hello kana ji”. Muryar MAJOR JABEER ta fargar dashi tunanin da ya tafi, Yayi saurin cewa “Ohh yes na barta ne wurin Baba ya kirani kiran gaggawa”. “oh ok ok na d’auka kuna tare sai anjima”. Major UMAR ya kashe wayar yana jin ransa ya harzuk’a sosai, mugun b’acin rai na mamaye sa baisan sanda ya dunk’ule hannu ya naushi bayan seat ba, wanda sai da yasa driver da sojan dake gaban mota waigowa, idonsa runtse hakan yasa bai gansu ba, suka juya suna mamakin meya b’atawa ogan nasu rai haka.



***********


“Yaya Rabi wallahi ki bani d’ari biyu ta, yau kwana uku kenan da kika amsa daga cewa anjima zaki bani”. K’anwarta tai maganar cikin tsiwa tana kallon Rabi wacce ke zaune d’akin mahaifiyarta a ranta tana wassafa yadda zatayi da dubu hamsin d’in da Yarima zai bata, Harara ta gallawa k’anwarta tace “Kar kice zaki mun rashin kunya na fasawa yarinya baki wallahi, anjima daddare zan baki tsiyar d’ari biyun ki”. K’anwartata ta fita tana tura baki tana gunguni, Rabi tabi bayanta da tsaki tace “Anjima hannuna dumus da bugun habuja, yau kam hak’ata zata cimma ruwa, KULUWA in kinsan wata baki san wata ba”. Tayi shu’umin murmushi.