FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuciya ce
Sample · 3
Da yawa daga cikin yan' matan da suka so ace Yarima Haladu ya kula su basu so tafiyar sa ba, musamman Rabi wacce taci buri, amma sun k'udurta a ransu gobe zasu dawo ko dan Yariman, Karime ta kalli saitin da KULUWA take tace "Mutuniyar har ta tafi kenan". Rabi ta yatsina baki tace "Idan kina wata maganar kamar baki san wacece ita ba, kinfi kowa sanin dama ba wani daɗewa take ba ko tazo". Karime ta jinjina kai tace "Hakane, ni ina mamakin rayuwa irinta Kuluwa, da nice mai kyau da farin jininta ai da babu macen da zata kaini saka suturu da ado a k'auyen nan". Rabi tace "Ai bata da wayo ne ita, muje mu siyo rake". Rabi ta nunawa Karime gun masu rake dan bata so Karime na yawan yaba KULUWA da fad'in irin baiwar kyau da Allah ya mata da farin jini, sai taji bak'in ciki ya cika mata zuciya.Cikin natsuwa take tafiyar ta, tana tunanin Mahaifinta tausayin sa na cika mata zuciya, ta d'auka zuwanta ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.