DUNIYA BIYU

One

by @jeddahlawals

Bismillahir-Rahmaanir-Raheem!


Shimfiɗa


KATSINA STATE


Ruwa aka gama sheƙawa kamar da bakin ƙwarya. Ko'ina ya dauki sanyin nan da ruwan sama ya saba bari idan ya sauka, sai kuwa yayyafi da ake yi kaɗan-kaɗan.

Ameenatu tana tafe akan titi, gabaɗaya kayan jikinta da jakar karatunta dake rataye a bayanta sun jike sharkaf har diga take yi, sanyin da yake kaɗawa da kuma yayyafin da ake yi ya ƙara mata rawar jiki. Tun kafin hadarin ya taso suka tashi daga makaranta, tana tafe a hanya tana ta zuba sauri kamar zata kifa, tana jero addu'ar Allah yasa ta kai gida kafin hadarin ya sauko, sai dai tun kafin tayi nisa ma aka fara sheƙa ruwan sama.

Dole ta nemi mafaka a wata rumfar kara ta rakuɓe cikin tarin mutanen da suma suke neman mafaka a wajen. Da yake ba wani waje bane mai faɗi, rabin ruwan a jikinta ya ƙare gabaɗaya.


Tana hango gate ɗin gidansu ta ƙara ɗaga ƙafa. Babu abinda take muradi a lokacin wanda yafi ta ganta a ɗaki, ta cire kayan jikinta jikakku ta sanya busassu masu nauyi.


Ta miƙa hannunta cikin rawar jiki, ta ɗoki da ta sanyi, ta tura kofar da zata danganata da babban falon gidan. Tana saka ƙafarta ɗaya, mutane uku suka dira a gabanta. Daga gani kasan babu tambaya dama zaman jiranta suke yi. Ƴanmata ne guda biyu da namiji ɗaya. Badi'ah, Fauzah da Affan. Ƴaƴan yayar Babansu ce, Anty Uwani. Dukansu sun girmeta, Badi'a ita ce babbarsu, Affan yana bi mata sai kuwa Fauza autarsu. Duk da cewa watanni biyu ne a tsakaninsu ita da Fauza, amma ta dauki kanta kamar wata yarinya ƴar shekara ashirin ba goma ba.


Badi'a ta kalleta a ɗage, "ina kike tunanin shigarwa mutane falo da wannan jikakkun kayan naki? Sanadin ki jika 'rug carpet' din da Mommy ta bada aka wanke jiya-jiya?".


Zuwa wannan lokacin har hakoranta sun fara hadewa waje daya saboda sanyi. Ta daga baki da kyar, duk da tasan cewa maganarta babu abinda zata sa balle ta hana, hakan bai hana ta fatan wannan karon Allah ya dorata akan dodanniyar ba. Tace "Anty Badi don Allah kiyi hakuri, wallahi da gudu zan wuce in canza kayan jikina. Zan dawo in goge wajen da lema ta taba!".


Wannan karon Affan ne ya riga su yin magana, "naaa! Babu inda zaki je wallahi sai dai ki tsaya anan har sai kin bushe. Kaji wani irin sakarci, da wannan dattin jikin naki kike tunanin zamu barki ki taba mana carpet?".

Basu kara cewa komi ba suka maida kofar suka rufe akan fuskarta, da ba don Allah yasa ta ja baya da wuri ba, da sai ta buge mata hanci.


Zuwa lokacin ruwan ya dauke. Ta koma ta jingina da jikin kofar, iskar da ake kadawa mai sanyi tana bin duk wani bargo da jijiya tata tana kaɗata. A hankali ta lumshe idanunta kamar mai barci, amma a zahirin gaskiya tana ƙoƙarin toshe ƙaran hayaniya da iface-ifacen su dake fitowa daga cikin falon ne, da kuma tsananin damuwa, takaici da bakin ciki da suka cika mata zuciya.


A irin waɗannan lokutan ne ta kan ji dana sani da kuma wani ɓurɓushin haushin mahaifiyarta ya dankare mata a cikin zuciya. Me yasa bata ɗauketa ta tafi da ita inda take ba? Rashin so ne ko kuma rashin kula? Ko kuwa tsabar tsananin ganin girma ne, kamar yadda tace?.


Sai da kayan jikinta suka fara bushewa a jikinta sannan taji karan buɗe ƙofar, ta ƙara matsawa daga jikin ƙofar a karo na biyu, tare da juyawa ta kalli wanda ya bude mata ƙofar. Affan ya tsaya yana watsa mata wani kallo da har kullum baya taɓa rabuwa da sanyayar mata da gwiwa, tabbacin cewa basu ɗauketa a bakin komi ba face ƙasƙantacciyar halitta, mara matsayi ko na anini a wajensu.


Ba tare da yace komi ba ya juya, a hankali ta ɗaga kafafunta da suka yi nauyi ta rufa mishi baya. Wani irin jiri da duhu mai haɗe da tartsatsin taurari suka mamaye mata idanu, taji duniyar tana juya mata aka kamar kwallo. Ta tafi gabaɗayanta ta zube a cikin falon, rabin jikinta a waje, rabi kuma a cikin falon. Allah yasa matakin ɗakin ya kasance mai tsananin taushi kamar auduga, saboda haka bata ji zafin faɗuwar ba sosai.


Affan daya fara tafiya, ya juya ya kalleta a kwancen da take, maimakon alamun tausayi ya bayyana akan fuskarshi, sai ma wani kallo daya watsa mata tare da yatsina fuska, ya sake juyawa ya tunkari inda sauran ƴan'uwanshi suke zaune akan kujerun falon suna dariya, bakinshi yana furta 'stupid girl!' (sakarar yarinya kawai!).


Bata kula su ba, kamar yadda bata taɓa kula su ba, ta fara ƙoƙarin tashi tsaye. Saboda tsananin sanyin da jikinta yayi, da kuma yadda gabaɗayanta take jinta kamar wata mara lafiya, gabaɗaya ta kasa tashi.


Daidai lokacin da Kakarsu, Hajiya Ramatu, ta fito daga ɗakin Kakansu hannu riƙe da kwando mai ɗauke da kuloli da kofuna, babu mamaki wani daga cikin ƴaƴanshi ko jikoki ya kawo mishi abincin dubiya.


Ta kalli Ameenatu dake kwance, ta rafka salati, "ke kuwa ƴar nan wata irin shiririta ce haka ta same ki yau? Kizo bakin ƙofa kawai ki kwanta kamar wata mara lafiya? Maza-maza ki tashi anan, kafin inzo in saɓar miki!".


Ameenatu ta kalleta cike da kwalla a cikin idanunta waɗanɗa ta ƙi bari su zuba, duk kuwa da zafin da suke mata. Yarinya ce mai tsananin zafin zuciya da dakiya.

Bata kula da yanayin da yarinyar take ciki ba, ta shura ƙafa ta faɗa ɗakinta tana ƙara maimaita mata tayi maza ta taso ta cire kayanta, taci abinci ta tafi Islamiya.


Har ta gama abinda zata yi a ɗakin, ta sake fitowa, Ameenatu na inda ta barta a kwance. Tuni ta daina fafutukar tashin da take tayi saboda ta kula sauran ɗan ƙarfin daya rage mata ne yake silalewa yana barin jikinta.


Sai ta tsaya a kanta cikin tunani, kafin ta ƙarasa wajenta da sauri tana tambayarta, "wai lafiyarki ɗaya kuwa?".


Da Ameenatu ta samu ta kamo hannunta, sai ta samu ta miƙe tsaye. Wani jirin ya sake kamota, tayi amfani da jikinta a matsayin bango, ta tsaya.


Hajiya Ramatu, wadda suke kira Hajja, ta damƙe hannunta sosai.

"Ikon Allah da bashi da makawa! Ameenatu baki da lafiya ne ko kuwa me? Subhanallahi!!".


Da taimakonta suka wuce ɗakinta, ta gaban yaran suka wuce, amma babu wanda ya bisu da kallo balle wata magana ta biyo baya.


Suna shiga ɗaki, ta ajiye jakar makarantarta akan babban gadon dake ɗakin, ba tare da ta cewa Hajja uffan ba, ta wuce wajen jakar kayanta ta buɗe, kayan makarantar islamiyarsu ta ɗauka, ta shige banɗakin dake haɗe da ɗakin.

Acan ne ta samu ta saki hawayen da suka dameta, dama hanya suke nema, suka fara tsiyaya kamar an buɗe famfo, cike da ƙunar zuciya.


Zuwa lokacin data gama kukan, rabin ɓacin ran data dankare a cikin ranta ya tafi.

Ta duba tukunyar ruwan zafi dake cikin banɗakin. Bata san lokacin data sauke ajiyar zuciya cike da jin daɗi ba lokacin data ji akwai ruwan zafi, duk da dai zafin ba can ba ne.

A hankali ta fara zame kayanta ɗaya bayan ɗaya. Sai data wanke su sannan ta haɗa ruwa mai ɗumi, babu ko sabulu haka kawai ta watsa shi duk don ta samu ƙarfin jikinta ya dawo, ta kuma rage sanyin dake cikin ƙasusuwanta. Cikin taimakon Allah kuma sanyin ya ragu.


Ta sanya kayan data shiga dasu, waɗanda ta wanke kuma ta ɗauke su ta kai can bayan gidan ta shanya su.


Lokacin data koma ɗakin, Hajja bata nan. Ta duba kulolin data shiga dasu ko zata samu abincin ci. Haka ta fita da safe bata ci komi ba saboda sauri, ta makara. A makarantar ma bata ci wani abin kirki ba saboda babu kuɗi a hannunta.

Farfesun kayan ciki ne, faten doya da tarin soyayyiyar hanta a cikin kulolin.

Faten doya ba cimar ta bace, sauran biyun kuma tasan idan ta taɓa su ba tare da izini ba, faɗa ne zata janyowa kanta. Sai ta maida murafan kulolin ta rufe ta tashi ta fita.


Kicin ta shiga, nan ma dai babu wani abin ci a ajiye. Sai taliyar indomie kwara ɗaya da ta lalubo can ƙarshen kabad, babu mamaki ta jima a wajen duba da yadda tayi ƙura sosai. Ƙila shi yasa idanun Fauzah sarkin cin indomie basu kai wajen ba. Indomie ƙarama ɗaya ba zata isheta ba, amma dai zata yi maleji.


Ta kunna wuta, tare da ɗora tukunya.

Tana tsaye tana jira ruwan ya tafasa, Indo ta shigo kicin ɗin.

Matashiya ce ƴar kimanin shekaru goma sha takwas, musamman Anty Zahra ta ɗaukota saboda ta dinga taya Hajja da ƙananun hidindimun gida. Su kuma su Badi'ah suka maida ta ƴar aikinsu ta musamman. Yarinya ce mai matukar haƙuri, kau da kai da hangen nesa, shi yasa tasu tayi matuƙar zuwa da Ameenatun.


Tayi murmushi lokacin da take ƙoƙarin zame hijabin jikinta, yayin da Ameenatu ta mayar mata da martanin murmushin.

Tace "me kike dafawa ne haka da tsakiyar ranar nan?".


Tayi ɗan murmushi, "Anty Indo ina kika ga rana ne har kika san tsakiya ce?".

Tace "tunda dai har ƙarfe biyu na rana ta wuce, aikuwa tsakiyar rana tayi".

Ameenatu ta gyaɗa kai, ta juya mata baya tana ɓare ledar indomie ɗin, ta watsa a cikin ruwan daya tafasa. Sai data gama haɗa komi sannan ta waiwayi Indo.


Tace, "Yau kin shigo da wuri".


A hankali ta gyaɗa kai, "so nake in samu in wanke kayan makarantar su Anty Badi don wajen bikin ƴar ajinmu zan tafi anjima kaɗan".


Ameenatu ta ɗaga kai cikin nuna alamun fahimta, tace "ai da kinyi zamanki kawai, da sai in wanke miki!".

Tace "a'ah, ni da aikina? Ai ba wani mai yawa bane. Ƙila dai ba lallai mu dawo da wuri ba, don haka zan bar miki gugar kayan".


Tana murmushi tace, "babu komi ai, sai kin dawo. Taho mu ci taliya mana!".


Indo ta girgiza kai cikin ƴar dariya, "kin san wannan ba cima ta bace. Bari in hanzarta inyi abinda zanyi kafin lokaci ya ƙure". Ta juya ta shige cikin gida, Ameenatu kuma ta cigaba da girkinta.


Anan ta cinye, ta wanke kwanon da tayi amfani dashi ta maida ta ajiye a inda suke, kafin ta koma ɗaki.

Zama tayi tana tilawar karatun littafin Ahalari har aka kira sallah, nan tayi sannan ta wuce makaranta.



●



Can da dare wajen karfe tara, tana falo tana goge musu kayan makaranta. Daga ita sai Alhaji Kakansu ne kawai a falon. Shi yana zaune akan kujerar hutu da aka ajiye musamman saboda shi a falon, yana sauraron hirar da take zuba mishi suna dariya.

Allah Ya haɗa jininsu da shi sosai. Kowa da kowa a cikin dangi yana mamakin irin wannan shaƙuwa da haɗuwar jini tasu.


Alhaji Badamasi, wanda aka fi sani da Badamasi Turawa. Tsohon ɗan kasuwa ne da aka sha fafatawa dashi a fagen kasuwanci da babu inda sunanshi bai shiga ya ratsa ba. Kodayake, gadon abin yayi daga marigayi mahaifinshi. An san iyalan gidan da neman na kai, duk inda halal take, zasu je su nemo ta. Mutum ne mai tsananin dattako, taƙawa da riƙon zumunci. Har a lokacin da yake a halin yau ciwo, gobe lafiya, tsabar kwarjini, cikar kamala da haibarsa suna nan.


Irin mutanen nan ne da da wuya kaji sun furta so ko ƙi na mutum. Irin mutanen nan da karantar su ma kaɗai jan aiki ne, balle ayi zancen fahimtar su. Shi yasa mutane da dama suke mamakin shaƙuwarsu. Duk cikin jikokinshi, duk da yawansu kuwa, gani suke yi kamar babu wanda ya kai soyuwa a cikin ranshi irinta. Sai kuwa dai Baqeer, wanda shi ba kullum bama ake ganinshi ba. Sun dai fi kyautata zaton saboda tana da sunan mahaifiyarshi ne.


Ko bayan ta gama goge kayan, gefenshi ta koma ta zauna suka ci gaba da hirar duniya. Sai da ƙarfe goma tayi sannan ya umarceta akan ta tashi taje ta kwanta.

Sai data raka shi har ɗakinshi, ya kwanta, sannan ta mishi sai da safe, ta kashe mishi wutar ɗakin tare da rufo mishi ƙofa.

Kayan su Fauzah da ta goge ta fara ɗauka, ta kai musu ɗakin da suke kwana idan sun zo gidan. Babban ɗakine yana fuskantar ɗakin da suke ita da Hajja. Ɗakin babbar ɗiyar Alhaji ce wadda take zaune a kasar Ingila, aka maida shi na manyan baƙi saboda bata ma cika zuwa Najeriya ba. Shine suke amfani dashi idan suka zo hutu gidan.


Ta kwankwasa ƙofar tare da saurarawa jiran a bata izinin shiga, jin shiru yasa ta kara ƙwanƙwasawa a karo na biyu, nan ma taji shiru. Don haka ta tura ƙofar tare da shiga ciki. Fauzah da Badin duk suna kwance suna barci akan makeken gadon dake malale a ɗakin. Shi Affan yana ɗakin dake kusa da na Alhaji.

A hankali ta taka zuwa tsakiyar ɗakin inda babbar kujerar 'sofa' take. Ta ajiye musu kayan ta juya da niyar barin ɗakin.


Idanunta suka sauka akan kwalin cakuletin 'Mars' da sauran tarkacen halawowi, amma ita idanunta akan cakuletin suke. Tana wajen da Magriba lokacin da Daddyn Abuja yazo shi da babban ɗan shi Baqeer, ya kawo musu tsarabar kayan zaƙin. Tunda Badi ta karɓi kayan tayi ɗaki babu wanda ya sake ganinta. Ameenatu tasan cewa kayan sun zama haramiyarta. Babu ta yadda za ayi ta tunkari ɗaya daga cikinsu ta tambayesu zancen haƙƙinta. Ina ta ga fuskar tambaya? Ina ta ga wannan matsayin?.


Sai ta girgiza kanta a hankali, ta juya ba tare da yin wani ƙwaƙƙwaran motsi ba, ta kashe musu wutar ɗakin ta wuce ɗaki.


Alwala ta ɗaura, tuni Hajja tayi barci. Ciƙin sanɗa da takatsantsan take aiwatar da komi. Bayan ta saka rigar barcinta, ta ɗauko ƙaramar katifar da take shimfiɗawa ta shimfiɗar. Sai ta kashe wuta, tayi addu'ar kwanciya barci ta tofe ilahirin jikinta. Taja bargo ta rufe rabin jikinta tare da lumshe idanunta. Babu jimawa barci yayi awon gaba da ita.



⋆°⋆



Kiran sallar asubahi ne ya tasheta. Tayi addu'ar tashi daga barci tare da tashi ta faɗa bayi. Alwala tayi ta fita, sai a lokacin ta tashi Hajja, bayan ta tashi ta fita ta bugawa su Badi kofa sannan ta koma ɗaki ta tayar da nafila.


Masallacin dake bayan gidan ta bi jam'i. Lazumi taci gaba da yi bayan an kammala sallar har gari ya fara washewa. Hajja ta fita kicin wajen haɗa abin kari.

Ta tashi ta ɗauke kayan shimfiɗarta ta gyara ɗakin. A gurguje tayi wanka ta fito ta shafa mai. Abin shafa hoda kaɗai ta murza a fuskarta tare da zizara kwalli a idanunta. Ba ma'abociyar kwalliya bace ita, ko bayan haka makarantarsu ba'a barinsu suyi kwalliya.


Tana gama shiryawa cikin kayan makarantarta, ta ɗauki safarta fara ƙal ta sanya, ta sungumi jakar makarantarta ƴar goye. Wata tafiya da Daddyn Abuja ya taɓa yi ya sauka a gidan lokacin daya dawo, ya kai mata ita. Ba ƙaramar masifa ta sha wajen su Badi ba kuwa. Sai da Alhaji ya kira shi da kanshi, ya siyo wasu jakunkunan irin nata sak ya kawo musu sannan ta samu sukuninsu.


A kicin ta samu Hajja tana ƙoƙarin soyawa su Badi doya da ƙwai na tafiya makaranta ita da Indo. Ta gaida su suka amsa.

Indo ta miƙa mata damammen kwastad wanda aka saba damawa Alhaji kullum da safe. Da yake ta jima da zubawa, ya fara hucewa. Ta kafa shi a bakinta tana sha kamar ruwa, sai kofin ta miƙa mata.


Hajja ta kallesu a kaikaice, "watarana sai kinje kin ƙona bakinki a banza a wofi idan baki daina yiwa abinnan shan ruwa ba!".


Ta ɗan turo baki gaba, "to ai babu zafi Hajja, kuma sauri nake yi".


Sai lokacin ta ɗaga kai ta kalleta, tace "to ai bani na ƙaƙaba miki tafiya makarantar da kanki ba ko? Tun yaushe nake bin kanki akan ki dinga bin su Badi'atu kuna tafiya? Amma shegiyar kafar kai irin taki, kin ƙi, wai ke kada ki makara, sai kace ke kika kawo boko duniya!".


Ameenatu dai bata ce komi ba, sai murmushi data ɗanyi, tace, "to ni na tafi sai na dawo!".


Ta juya da sassarfarta zata tafi, Hajja tace "dakata in zuba miki ki tafi da abinci mana".


Bata yi musu ba, taja tunga ta tsaya. Da alama yau Allah Ya jiƙanta Hajja bata ce zata ba su Fauzah su tafi mata dashi ba. Kusan kullum sai dai a ba su abincinta su tafi mata dashi. Basu taɓa kai mata ba, hasalima basu taɓa kwatanta gaya mata an basu abincinta ko yadda suka yi dashi ba. Ta taɓa kai ƙorafinsu wajen Hajja, sai dai abinda ya faru bayan nan sai daya sanya tayi dana sanin ɗaga baki tayi magana. Bata manta irin cin mutuncin da Anty Mommy tayi takanas-takano ta tako kafa tun daga gidanta tazo ta sauke musu, kan cewa ita Ameenar tana bibiyar ƴaƴanta da sharri, akan abincin banza dana wofi, bayan tasan cewa sun fi ƙarfinshi.

Bata sake ɗaga baki tayi magana ba daga nan, har lokacin kuma bata sake zani ba.


Hajja na miƙa mata ƙaramar kular data zuba doyar a ciki, ta zuge jakarta ta saka a ciki. Da sauri ta musu sallama ta juya ta bi ta babban falo. Lokacin data wuce ta ƙofar ɗakinsu, ta jiyo sautin hayaniyar su Fauzah, da alamun tashinsu daga barci kenan. Ko dai tashinsu kenan, ko kuma sun koma barcin bayan sallar asubahi. Ta wuce zuwa ɗakin Alhaji.


Yana zaune akan abin sallarshi yana jan carbi. Yahya matashin yaron da yake musu share-share yana gyara mishi ɗakin. Tayi sallama ta durƙusa a gefenshi, a nutse ta gaida shi. Ya amsa cike da fara'a.

"Har an fito za'a tafi ne, mai babban suna?". Duk duniya shi kaɗai ne da marigayi mahaifinta suke kiranta da wannan sunan.


A ɗan kunyace ta gyaɗa kai, yace "to Allah Ya tsare hanya, a dawo lafiya. A kuma kula da hanya, banda biyewa abokanan banza".


Tace "to", a hankali ba tare data motsa ba.

Tunda yaga haka yasan cewa da magana, sai ya gyara zaman shi sosai. Yace "Yaya aka yi ne mai babban suna?".


Ta ɗan ciza leɓen bakinta, wata ɗabi'a tata idan tana fargaba ko cikin damuwa. Tace, "uhm...! Dama ince ko ka yiwa Daddyn Abuja maganar?".


Gabanta ya hau dukan uku-uku lokacin da taga ya ɗan zare idanu, alamun sai lokacin ya tuna da ko wace magana ce suka yi.


Yace "kiyi haƙuri mai babban suna, da yake jiya suna sauri zasu tafi, kwata-kwata na manta. Amma kada ki damu, zan sa Yahya ya kamo min shi a waya sai in mishi maganar, kinji?".


Ta ƙaƙalo murmushi a sanyaye tace "to Alhaji. Sai na dawo".

Har ta fara tafiya taji ya kirata, ta juya. Gefen abin sallar da yake kai ya ciro naira ɗari biyu sabuwarta ƙal, yace "duba min ki gani nawa ce nan?".

Da yake ganinshi ya ragu sanadiyar rashin lafiyar da yayi matuƙa.


Bata san lokacin da tayi murmushi ba, tace "naira ɗari biyu ce Alhaji".


Ya ƙara ɗauko wata ɗari biyun ya miƙa mata, "to ungo, ki sayi abinci ki ci, ki kuma hau abin hawa da sauran. Kada ki kuskura inji kin sake tafiyar ƙasa irin na jiya, kina ji na?".


Komawa tayi ta tsuguna a kusa dashi, ta zari ɗari biyu daga ciki ta soka ta a cikin aljihun jakarta, tace, "Alhaji ka ajiye kuɗinka, waɗannan ma zasu ishe ni".


Yace "babu abinda zaki buƙata a hanya? Kin tabbata sun ishe ki?".


Ta gyaɗa kai a hankali, zuciyarta na lulluɓewa cikin ƙaunar tsohon, bata san me tayi ba yake mata wannan tsagwaron kaunar. Cikin dakushewar murya tace, "sun isheni Alhaji, har ma sai nayi sauran canji".


Jin haka sai ɗan tsohon ya saki murmushi, yace "to madalla, maza ayi haramar tafiya, a kula da hanya sosai, banda tsallaka titi sai an duba hagu da dama kina jina?".


Ta saki ƴar siririyar dariyarta mai ban sha'awa, tace "to Alhaji!".

Daga haka ta tashi ta fita daga ɗakin. Tana fita taci karo da saitin idanuwa biyu suna watsa mata harara kamar zasu zazzago ƙasa. Bata kula shi ba, ta buɗe ƙofa ta fita.


Isiya yana farfajiyar gidan yana goge motar da yake kai su Affan makaranta a ciki. Ta gaida shi ya amsa. Da sauri-sauri ta buɗe kofar gidan ta fita.


Tafiya ce ta kimanin mintuna goma sha biyar daga nan zuwa bakin titi inda zata tari motar haya zuwa makarantarsu. Shima yana ɗaukarsu mintuna sha biyar zuwa ashirin.


Ganin babu mutane sosai a cikin unguwar sai jifa-jifa da suke wucewa, kuma yawancinsu a mota. Sai ta dinga haɗawa da sassarfa har da ɗan gudunta. Tana zuwa bakin titi, ta tari mota ta haye.