FreeArewaPen original
DUNIYA BIYU
- 1views
- 41chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Assalamu alaikum Sunana Hauwau Shafiu Lawal. Ni Marubuciya ce, Mahaifiya, and a proud scientist. Ina zaune a garin Daura, Jahar Katsina. Rubutukana are all about romance, (coz am a sucker for it, lol). So I hope you guys will sit tight, and enjoy our beautiful ride in shaa Alla...
Sample · One
Bismillahir-Rahmaanir-Raheem!ShimfiɗaKATSINA STATERuwa aka gama sheƙawa kamar da bakin ƙwarya. Ko'ina ya dauki sanyin nan da ruwan sama ya saba bari idan ya sauka, sai kuwa yayyafi da ake yi kaɗan-kaɗan. Ameenatu tana tafe akan titi, gabaɗaya kayan jikinta da jakar karatunta dake rataye a bayanta sun jike sharkaf har diga take yi, sanyin da yake kaɗawa da kuma yayyafin da ake yi ya ƙara mata rawar jiki. Tun kafin hadarin ya taso suka tashi daga makaranta, tana tafe a hanya tana ta zuba sauri kamar zata kifa, tana jero addu'ar Allah yasa ta kai gida kafin hadarin ya sauko, sai dai tun kafin tayi nisa ma aka fara sheƙa ruwan sama. Dole ta nemi mafaka a wata rumfar kara ta rakuɓe cikin tarin mutanen da suma suke neman mafaka a wajen. Da yake ba wani waje bane mai faɗi, rabin ruwan a jikinta ya ƙare gabaɗaya.Tana hango gate ɗin gidansu ta ƙara ɗaga ƙafa. Babu abinda take muradi a lokacin wanda yafi ta ganta a ɗaki, ta cire kayan jikinta jikakku ta sanya busassu masu nauyi.Ta miƙa hannunta cikin rawar jiki, ta ɗoki da ta sanyi, ta tura kofar da zata danganata da babban falon gidan. Tana saka ƙafarta ɗaya, mutane uku suka dira a gabanta. Daga gani kasan babu tambaya dama zaman jiranta suke yi. Ƴanmata ne guda biyu da namiji ɗaya. Badi'ah, Fauzah da Affan. Ƴaƴan yayar Babansu ce, Anty Uwani. Dukansu sun girmeta, Badi'a ita ce babbarsu, Affan yana bi mata sai kuwa Fauza autarsu. Duk da cewa watanni biyu ne a tsakaninsu ita da Fauza, amma ta dauki kanta kamar wata yarinya ƴar shekara ashirin ba goma ba. Badi'a ta kalleta a ɗage, "ina kike tunanin shigarwa mutane falo da wannan jikakkun kayan naki? Sanadin ki jika 'rug carpet' din da Mommy ta bada aka wanke jiya-jiya?".Zuwa wannan lokacin har hakoranta sun fara hadewa waje daya saboda sanyi. Ta daga baki da kyar, duk da tasan cewa maganarta babu abinda zata sa balle ta hana, hakan bai hana ta fatan wannan karon Allah ya dorata akan dodanniyar ba. Tace "Anty Badi don Allah kiyi hakuri, wallahi da gudu zan wuce in canza kayan jikina. Zan dawo in goge wajen da lema ta taba!".Wannan karon Affan ne ya riga su yin magana, "naaa! Babu inda zaki je wallahi sai dai ki tsaya anan har sai kin bushe. Kaji wani irin sakarci, da wannan dattin jikin naki kike tunanin zamu barki ki taba mana carpet?".Basu kara cewa komi ba suka maida kofar suka rufe akan fuskarta, da ba don Allah yasa ta ja baya da wuri ba, da sai ta buge mata hanci. Zuwa lokacin ruwan ya dauke. Ta koma ta jingina da jikin kofar, iskar da ake kadawa mai sanyi tana bin duk wani bargo da jijiya tata tana kaɗata. A hankali ta lumshe idanunta kamar mai barci, amma a zahirin gaskiya tana ƙoƙarin toshe ƙaran hayaniya da iface-ifacen su dake fitowa daga cikin falon ne, da kuma tsananin damuwa, takaici da bakin ciki da suka cika mata zuciya. A irin waɗannan lokutan n...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.