14
by @sadiyanasir
IRO fuska a sake yake duban MALAM GARBATI wanda yake sake jin k'arfin gwiwar cikar burinsa, yanayin Malam Garbati ya tabbatar masa yana cikin uk'ubar da zai so fita wurin nan da gaggawa, Kallon Malam Garbati yayi sosai yace "Nasan kana mamakin zuwana gunka ko". Malam Garbati ya d'aga kai alamar eh, Gefensa ya nuna masa da hannu yace "Ka zauna alkhairi ke tafe dani gun ka". Malam Garbati jin alkhairin da ya fad'a ya saka shi jin natsuwar zuci kad'an, Ya zauna gefen bencin da IRO ke zaune, IRO ya gyara murya yace "Kamar yadda na fad'a maka alkhairi ne tafe dani shine bashin da ake bin ka zan biya maka duka hadda jari zan baka ka kama sana'a wacce zaka rik'e kanka da iyali ka daina cin bashi". Malam Garbati baki ya washe yana kallon IRO tamkar a mafarki yake jin zancen, kowa a k'auyen yasan yadda IRO baya son fitar da kud'i kowa ya shaidesa da rowar masifa, shine zai biya masa bashi, lallai Allah maji rok'on bawa addu'ar da yayi ce Allah ya kawo masa mafita, IRO ya katse tunaninsa da cewa "Amma da sharad'i d'aya". Malam Garbati ba fargaba yace "Ka fad'i kowane sharad'i ne matuk'ar bai sab'awa addini ba a shirye nake na bi, babu babban tashin hankalin da ya kai zama a nan". IRO jin zancen Malam Garbati zuciyarsa ta sake shiga farin ciki ya kalle sa yace "Ba wani sharad'i bane mai tsauri, face ma raya sunnar ma'aiki SAW, KULUWA nake so ka bani aure ni kuma nayi maka alk'awarin fitar dakai wurin nan". Malam Garbati a take far'ar dake kan fuskar shi ta gushe ya d'an ja baya yana duban IRO yace "Ashe yanzu ba'a taimako Dan Allah sai idan kana buk'atar wani abu kai ma". Iro zamansa ya gyara yace "Toh banda abun ka GARBATI kana tunanin zan fitar da kud'i masu yawa ne haka na biya maka bashi hadda jari a banza, ai bazai yiwuwa ba in dai zaka bani auren KULUWA ina tabbatar maka zamanka nan ya k'are, tare zamu koma k'auyen DANHASSAN da kai".
Malam Garbati murmushin takaici yayi ya girgiza kai yace "Gaskiya bazan iyawa KULUWA auren dole ba". IRO da bai tsammaci jin haka daga bakin MALAM GARBATI ba yace "Wa ke zancen auren dole yanzu Malam Garbati, kai da kake cikin wannan uk'uba har ka samu mafita kake zancen ba zaka mata auren dole ba, ba fah fasik'anci nake nemanta dashi ba, raya sunnar ma'aiki nace". Malam Garbati numfashi yaja yace "Ban da abun ka ma IRO KULUWA duka duka nawa take ai kayi mata tsufa sa'ar yar' ka mairo ce, mairo kuwa ko a cikin yaranka itace ta hud'u, a gaskiya ba zan iya aura mata kai ba". IRO ransa yaji ya d'an b'aci amma ya dake shi ke nema dole ya kwantar da kai dan ya saka ransa sosai akan KULUWA cikin murya mai k'ok'arin jan hankali yace "Haba Malam Garbati ya kake magana kamar tashin yanzu, sau nawa akai aure haka, Miji yaba mata shekaru masu yawa ai tafi samun kulawa ma, sau da yawa ma matan da kansu suke kawo masu shekarun gida, kada kayi ma kanka ka taimaki kanka da yarinyarka ka amincewa buk'atata mu koma Danhassan tare da kai". Malam Garbati kai ya sake girgizawa cikin rashin gamsuwa da zancen IRO yace "Bazan iya aura maka ita ba IRO, na gwammace na k'arashe rayuwata anan har na koma ga mahalaccina akan na sadaukar da farin cikin ya'ta akan nawa". Iro kallon Malam Garbati yayi fuskarsa d'auke da mamaki ko kad'an bai zaci haka zai faru ba, Lallai Malam Garbati irinsu ne ake cewa talaka da fad'in rai, Tashi tsaye yayi yace "Shikenan na barka lafiya".
Malam Garbati ba tare da nadamar hukuncin sa ba ya tashi aka maida shi cell aka rufe, Gefe d'aya ya zauna tare da jingina kansa da bango ya rufe idon sa, Tabbas zamanin nan sai dai mutum yace Allah ya sauwake, taimako yayi wuya, kowa k'ok'arin gyara tukunyar sa yake, masu imani da zuciyar taimako k'alilan ne, "Har abada bazan iya sadaukar da farin ciki KULUWA ba, idan nayi haka bazan tab'a gafartawa kaina ba". Yayi zancen zuci yana sake damtse idonsa da ambaton Allah.
Iro jiki babu k'wari ya bar ofishin yan' sandan ya nufi wurin hawa mota, ba jimawa suka tashi zuwa k'auyen DANHASSAN, wanda ya k'udurta a ransa ba zai tab'a hak'ura da KULUWA ba, wata shawara tazo masa wacce yake ganin idan yabi zai samu cikar burin sa.
*******
Major Umar bayan tafiyar Malam, duk wani kuzari na jikinsa yaji yana ragewa tamkar ba soja ba, ko a cikin sojojin jajircacce wanda baya karaya ko jin kasawa akan dukkan wani abu da ya shafi aikin sa, amma yau akan Mace yana jin komai na kwance masa, yana jin ina ma mafarki yake ba gaske bane UMAIMAN SA ta canza, canzawar da ko a mafarki bai zata ba, UMAIMAN sa ta baya Mace ce mai natsuwa da sanyi, mai ladabi da biyayya da nuna masa tsantsar so da kulawa gare sa amma lokaci d'aya ta canza zuwa wata sabuwar UMAIMA, kuma ba sihiri ba, ba shafar jinnu ba, Ya zame dole ya zaunar da ita ya tunasar da ita yana da yak'inin zata sauarare sa a haka yabar zancen zuciyarsa, Ya mik'e tare da shafa sajen sa da yake zagaye da fuskarsa ya k'ara masa zama cikakken na Miji mai kyau da kwarjini, yana fitowa tsakar gidan sojoji biyu masu jiran fitowar tasa sukai saurin sare masa, Kai kawai ya d'aga masa, D'aya daga ciki yai saurin bud'e masa mazaunin baya ya shiga, kana ya rufe, Motocinsa uku suka jeru suna fita daga gidan.
***********
UMAIMA hankali kwance ta shigo ma'aikatar tasu, kai tsaye ofishin SARATU ta nufa, bata jira iso ba kamar yadda su ukun basa jiran iso wurin shiga ofishin juna, A ciki ta sami ZULAI suna zaune kowacce hannunta d'auke da k'aramin mug suna shan shayi mai zafi, suna hira, "Matar Soja". Zulai ta fad'a cike da zolaya tana kallon UMAIMA, SARATU tace "Ko matar kulle ba". Dariya Umaima tai tace "A da kenan kafin nasan yancin kaina, yanzu na wuce amun kulle". Hannu Zulai da Saratu suka tafa suna dariya suka ce da kyau, Umaima hannu tasa taja kujera ta zauna, tana ajiye jakarta kan tebur dake gabansu, Tana tab'e baki tace "Baku san me Gogan yayi ba yau". Zulai tace "Bamu mu sha". Tana tattaro hankalina kan UMAIMA, itama Saratu kallonta ta maida kan UMAIMA wacce tai wata dariya tace "Wai Malam ya d'auko amun rukiya ya d'auka sihiri ne ko shafar jinnu". Dariya Zulai da Saratu suka saka a tare, UMAIMA ta kwashe komai ta sanar dasu, "Kece dai bakya masa da wasa". Zulai tai maganar cikin nuna bajintar UMAIMA, "Ai kad'an ya gani ma muje zuwa dai". Saratu tace "Yanzu kika fara sanin kanki UMAIMA, matuk'ar kina son rayuwar yanci kema ki dama cikin manyan mata kiyi fice da suna dole ki ture wata soyayyar UMAR ranki". Umaima tana gyara zama tace "Tuni nai bankwana da ita, cikar burina shine gaba". SARATU kai ta jinjina tace "Kunga motar da na siya zata iso jibi". Ta karkata fuskar wayarta zuwa ga Umaima wacce ta zaro ido ganin dalelliyar mota, Tace "Wow amma gaskiya motar ta had'u". Saratu tai dariya ta juya wayar zuwa ga ZULAI wacce tashin farko tace "Nawa kika siyeta dan gaskiya ta tafi dani". "Miliyan ashirin da biyar". "Ki musu magana na tura kud'ina a kawo mana tare". "An gama hajajju". Saratu tai maganar tana dariya, Zulai tace "Nima ba za'a barni baya ba, gara mu faso gari tare". Sukai shewa, UMAIMA shiru tayi tana jin ba dad'i a ranta tamkar ta muzanta, aminanta biyu zasu mallaki motar ta da ita bata da halin siyan ta, shaid'an ya cigaba da yi mata hud'uba a zuciya, Wanda har ta kasa b'oye rashin jin dad'in ta fuskarta ta bayyana haka k'arara, Mik'ewa tayi tace "Bari na tafi office akwai ayyukan da jiya ban k'arasa ba". Ta d'auki jakarta ta wuce, Zulai da Saratu suka kalli juna sukai dariya.
***************
Ladidi na zaune tsakar gida tare da yaranta su hud'u wanda su suka rage gabanta uku sunyi aure, ta hud'un wata mai kamawa za'ai nata, sauran yaran da babu iyayensu mata gidan suna daga can gefe, kowane yana gu d'aya da wanda suke mama d'aya, yara biyu maza da kowane mahaifiyarsa daban basu da d'an d'aki d'aya suna tare, Yaran LADIDI kad'ai ke jin dad'i a gida duka sauran yaran a tsangwame suke hatta abinci sai taga dama take basu, mafi yawa daga ciki an sha kawo k'ararsu sun saci abun wani, LADIDI ko a jikinta sai ma zama da take ta dinga yadawa IRO habaici cewar aure aurensa yasa ya tara yara yan' iska, LADIDI babu wata natsuwa sosai tattare da ita, hankalinta ya karkata ga jiran dawowar IRO, wanda jin sallamarsa ya sakata sauke ajiyar zuciya mai nauyi, Yaran dake tsakar gida suka soma yi masa sannu da zuwa, Yana amsawa da yawwa, Ladidi kallon hadarin kaji ta masa zuciyarta na sake jefa mata zargin sa, "Lafiya kike man kallo haka Ladidi". Tsaki taja tace "Kai ba kallon nawa kayi ba kasan ina kallon ka, munafuncin banza mara gaskiya kawai". "Bana son rashin mutunci fah LADIDI ki fita idona". Tashi tai tsaye gabansa zaninta na neman sab'ulewa ta gyara sa tace "Ba zaka ga rashin mutunci ba ma sai kace aure kaje nema KURA". Tsaki yai ya wuce d'aki, Yaran na binsu da kallo dan su yin abun kunya gaban yaran bai dame su ba, duk wani rashin mutuncin LADIDI akan idon yara take zubawa IRO, shima kuma baya raga mata, sau tari watarana idan sunayi yaran har dariya suke, Ladidi ta dinga tsine musu tana aibatawa.
Iro kayan jikinsa ya soma cirewa, ya rage daga shi sai gajeran wando, ko kwanon abincin dake d'akin bai kalla ba, ya fito yana k'walawa d'aya daga cikin yaran kira, Yaron ya taho yana tsayuwa gabansa ba ladabi na tunanin ya d'an russuna, "D'auki bokiti ka d'ibo tsaftacen ruwa ka kai mun band'aki". Ladidi zumb'ur ta mik'e tana kama baki tace "Laa yau ni Ladidi naga abunda yafi k'arfina, yanzu IRO abunda kaje ka aikata kenan ka gama da aure auren yanzu taushe mata ka koma, yau na boni ni LADIDI, yaseen kuwa bazaka d'ibo cuta ka k'ak'aba mun ba, wayyo ni LADIDI na shiga uku IRO ya zama kwarto". Yaran kowa ido a kanta maganar ta sosa ransu sosai, IRO a fusace ganin tana zubar masa mutunci gaban yaransa yace "KE LADIDI bana son iskancin banza da rashin mutunci, ki shiga hankalin ki wallahi". Mugun harara ta watsa masa tace "Tabarmar kunya dama ance da hauka ake nad'eta wallahi kaji kunya kuma kayi asara, kaje har KURA dan kai lalata tir da kai". Ta tofar da yawu, IRO banza yai da ita ganin idan ya tsaya biye mata b'ata lokacin zai, Ya wuce band'akin dake tsakar gidan ya barta tana masifa da mita, tare da jefarsa da mugayen kalamai, ba kunya ko tunanin tana koyar da yaranta muguwar d'abi'a,
IRO wankan sa yayi ya fito ya shiga d'aki ya sake shiga cikin koriyar shadda wacce tun sallar bana da ya sakata bai sake sawa ba sai yau, ya d'auko hula ya saka, ya zura takalmansa masu kyau, Ya fito yana karkad'e riga, LADIDI kallonsa tai zuciyarta na bugawa da k'arfi tamkar zatai tsalle ta fasa k'irjin ta, "Ina kuma zaka sake zuwa". "Inda kika aikeni". Yai maganar yana yin hanyar fita ba tare da ya koma kanta ba ko ya saurari maganganun da take, Ladidi ashariya kala kala ta dinga dannawa a tsakar gidan, ta kasa zaune ta kasa tssye sai fama zirga zirga take tana sak'a da warwara.
*********
KULUWA na kwance d'akinta shiru tana tunani da nazarin rayuwa, Ta soma jiyo sallamar yaro a tsakar gidan nasu, Tashi tayi tsaye ta fito a tare suka fito da UMMA HABIBA wacce itama sallamar taji ta fito, "Wai IRO ne yake sallama da KULUWA". Gaban KULUWA ne ya fad'i, yana cikin mazan da suka saka mata ido sosai a k'auyen zata iya cewa duk cikin mazan dake cewa suna sonta babu wanda ya kai IRO naci da kallon masifa, Yaron tacewa "Kaje kace masa bana nan". Umma HABIBA tai saurin cewa "A'a je ka ce masa tana zuwa". Yaron ya juya ya fice, KULUWA kallon UMMA HABIBA tayi a raunane, UMMA Habiba ta kalli KULUWA tace "Ba'a haka KULUWA baki san meke tafe dashi ba, watak'ila kan maganar MALAM ne". "UMMA kin manta waye IRO kowa ya shaide sa k'auyen nan fa da rowa, ba zai tab'a taimakon Malam ba, sai idan shima hanyar da YARIMA HALADU ya biyo ita shima zai biyo". Umma HABIBA tayi saurin girgiza mata kai tace "Yana da kyau ka dinga kyautatawa Bawa zato, ba kyau munannan zato, saka hijabinki kije kiji meke tafe dashi". KULUWA tsananin biyayyarta ga iyayenta da sanyin halinta yasa ba zata iyawa UMMA HABIBA musu ba, D'akinta ta shiga jiki babu k'wari ta sanya hijabi ta fito,
IRO yana ganinta far'ar dake kan fuskarsa ta fad'ad'a yana bin ta da kallo mai cike da tsananin sha'awa yana jin tamkar ya rungumeta, KULUWA bata d'ago kai ta kallesa ba kanta na sunkuye k'asa tace "Ina wuni?". "Lafiya lau KULUWA". Yana maganar yana washe baki kyawunta na sake jan ra'ayinsa gare ta, Ya d'an ja numfashi yace "D'azu na kaiwa Malam Garbati ziyara". Bata san sanda ta d'ago kai ta kalle sa ba, Ganin yanayin da tayi daga cewa yaje gunsa yasa ya marairaice fuska yace "Amma yanayin da na gansa wallahi ba dad'i, Malam Garbati yana cikin uk'uba ya rame ya canza kamanni ni kaina da farko ban gane sa ba, a tak'aice ma ko da naje ihunsa na fara cin karo dashi ana jibgar sa". KULUWA a take hawaye suka wanke fuskarta tana fad'in "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah sarki Malam". Zuciyarta na shiga wani irin yanayi na bak'in ciki da tsananin tausayin mahaifinta, "Ki daina kuka KULUWA, indai mahaifinki ne idan kinso yau bazai k'ara kwana a can ba". Kallon IRO tayi tace "Dan Allah kada kaima kace sai na baka kaina zaka fito dashi, Dan Allah ka taimake mu ba tare da ka buk'aci fasik'anci dani ba". Kai IRO ya girgiza yace "Ko kusa bashi zan nema ba, ni aurenki nake so yi, idan kin amince da aurena yau d'in nan zansa a fito da Malam Garbati". KULUWA zuciyarta tayi rauni wurin son ceton mahaifinta, aure ne ba zina ba, zata iya sadaukar da farin cikinta ta rayu gidan IRO komai munin halinsa ta kub'utar da mahaifinta, a take tace "Na amince zan aure ka, Dan Allah ka fitar da mahaifina". Dariya IRO yai ta farin ciki yace "Ai ba ma bashin dake kansa kad'ai zan biya masa ba, har jari zan bashi, amma ki fara mun alk'awarin zaki aureni, dan wallahi idan na biya bashi aka fito dashi kika canza magana, ba zan k'yale ba sai dai ya koma inda ya fito". KULUWA tana sharar hawaye tace "Nayi alk'awari zan aure ka wallahi". Baki IRO ya washe yace "Kizo yanzu muje gunsa ki sanar dashi yaji daga bakin ki zaki aure ni, idan ya nuna amincewarsa ni kuma zan biya bashi mu dawo tare". KULUWA ba musu ta amince tace "Bari ta shiga gida ta sanar da UMMA HABIBA". Iro yabi bayanta da kallo yana lasar baki yana dariya ji yake kamar ya taka rawa tsabar murna..