6
*_💋D'AN HALAK💋_*
MALLAKAR
*_UMMU MAHER(MRS GREEN)🍃_*
*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION📚_*
~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159
*_WELCOME TO UMMU MAHER BUSINESS
CENTER_*
_____¥¥¥¥¥¥¥
*TIME TABLE NA KOYON SANA'A*
CLASS 1👇🏻
____________
*KOYON MAYAFI NA BEAD WORK BEAD
WORK*
*MAYAFI NA STONE WORK*
*HULUNA*
*RIGUNA*
*FANTIS*
*WANDO JEANS*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 800
CLASS 2👇🏻
______________
*INVITION CARD*
*3d logo*
*3d mockup*
*3d render*
*Cover book*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 800
CLASS 3
_________
*Turaren wuta*
*Humrah*
*Gyaran jiki*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 1k
a tuntuɓi ummu maher ta lambarta👇🏻
***
*DOMIN SHIGA WHATSAPP GRP ƊINMU👇🏻*
***
vkDAXPthThNQx
5
________da sauri na kalli wanda ya shigo, na haɗe rai jikina har ɓari yake saboda ruwan masifa idanuwana suka canja kala asalin Haidar ɗina ya bayyana baki ɗaya.
"Mu'azzam anya kana da hankali kuwa? wannan fa shi ne wanda naga an rataye hotonsa a wajen folis shi ne wanda ya sanya ka wannan jinyar alhali bakaji ba baka gani ba? To yanzu kuma meye ya kawosa wajen nan? ai kuwa yau aƙwai Inda ba ƙasa"..............
maimakon naga ransa ya ɓaci sai ma naga yayi murmushi mai ma'anoni da dama, ya ƙaraso kusa dani ya ce" Bro Haidar, ka daina kumfar baki domin shi wanda na yiwa abun ya daɗe da yafemun, wallahi ban taɓa ganin bawa me masifar haƙuri irin Mu'azzam ba, bawan Allah ne wanda bai damu da kowa ba, ban taɓa yin tunani akan duk abubuwan dana ke aikatawa ba, ban taɓa tunanin zanyi abun yazo ya dameni ba Mu'azzam ya yafemun yanzu kai kaɗai ya rage Haidar, domin Mu'azzam ya nunamin muhimmancinka arayuwarsa, ya faɗamin tamkar Hassan da Usaini kuke, jini ɗaya ciki ɗaya don Allah ka taimaka ka yafemun".
Haɗa hannayensa waje ɗaya yayi yana neman yafiyata, sai naji duk masifar dana tattaro ta koma na samu waje na zauna, ko dama ni can hukuma ne sai da rarrashi inada zuciya sosai wacce idan ina cikinta bana iya gane hagu balle kuma dama, haka nake rayuwata ni kaɗai ba nida wani aboki wanda zance ina iya gayawa sirrina, ko ayanzu danake jin Mu'azzam tamkar jinina ba komi ya sani na sirrin rayuwata ba, saboda ni mutum ne me masifar zurfin ciki, da wuya kaji cikina in har ba laɓewa kayi kaji saƙon zuciyata ba, ko kuma akayi wani abun agabanka to shi ne zaka ɗorar da wani abun.
na kalli Mu'azzam yana zaune akan gado, yayi wata irin muguwar rama tamkar wanda ya daɗe yana jinya, abin tausayi dai sai naji dama in koma me irin zuciyarsa saboda nasan mutum ne shi me masifar haƙuri da sanin ya kamata, babu ruwansa da rayuwa balle ƙele ƙelenta. nasan kome zanyi bazan taɓa komawa irin zuciyarsa ba saboda dama ni can mutum ne me masifar zuciya balle lokaci ɗaya in canja ta nasan ba abune me yiyuwa ba, sai dai in zama me yafiya ko iya wannan ma na tsaya na daki wani makami na siraɗin rayuwa wajen hayewa da tsani me kyau.
na buɗe bakina tamkar me ciwon baki na ce" ba komi na yafe maka, tunda wanda aka yiwa laifin ya yafe, kaga ni ƙarashe ne nawa saboda haka na yafe maka Allah ubangiji ya yafe mana baki ɗaya".
Sosai naga farin ciki akan kyakkyawar fuskar Mu'azzam, abun ya bani mamaki sai ya shiga bani tausayi kuma, saboda nasan duk inda me haƙuri ya kai to Mu'azzam ya kai kuwa.
abinda yake min yawo bai wuce abinda ya janyo wannan yaƙaddamar ba, tunda ni nasan shi ba mutum ne me faɗa ko neman masifa ba, da dai nine sai ince zan aikata tunda nasan yadda na iya fitina da tada zaune tsaye, domin ɗan abu kaɗan zaka yimin in tada zaune tsaye.
"ina son jin abinda ya kawo wannan taƙaddamar"?.
ɗan murmushi duka sukayi, Mu'azzam ya ce" ni ne da laifi Haidar ni na shiga gonarsa domin bai sakoni a harkarsa ba ni na shiga nayi kane kane, duk abinda babu ruwanka daɗin ji gareshi ban zama me kauda kai akan ɓarna ba, daman ni can haka nake in har za'ayi abinda ba dai dai ba agabana zan faɗi gaskiya, amma ta cikin nutsuwa da neman maslaha nake komi, amma inason ya faɗa maka komi da bakinsa kada na faɗa ba dai dai ba kasan na fara jin sauƙi kada na karkace in faɗo ƙarya".
dukkansu sukayi ƴar dariya.
"Sunana Hammud Mai Nasara, mahaifina yana da kuɗi sosai ta inda baka tunani amma halin rayuwa yasa yanzu ya samu karayar arziƙi, ina ɗaya daga cikin masu safarar miyagun ƙwayoyi daga wata ƙasar zuwa Nigeria, na tara kuɗi sosai ta wannan harkar bana tsoron kowa harkar gabana kawai nake, mahaifina yayi yayi in daina wannan harkar naƙi na daina, alhali ni kaɗai ne ɗansa namiji wanda yake tunƙaho dashi gashi ina karatu wanda daga baya na daina karatun ma baki ɗaya, abinda ya kawoni na daina sa sai shashanci da kule kulen ƴammata, babu ruwana da karatun da mahaifina ya ƙwallafa rai akansa ayanzu haka silar abinda nake ya sanyawa mahaifiyata mummunan hawan jini, Mu'azzam shi ne mutum na farko daya karyamin alƙadarina saboda babu wanda yake iya kallon cikin idona ya faɗi laifina sai shi, depertment ɗinmu ɗaya dashi ganin bana karatu yasa ya ke janyonu ajiki tare da nunamin abinda nake bai kyautu yinsa ba, amma na rufe kunnuwana na sanya musu toka na daina ganin kowa da jin komi, ahaka har na daina zuwa makaranta jin na daina zuwa yasa Mu'azzam bibiyata yaji ina nake zuwa? babu inda bai tambaya ba kowa yace baisan inda nake ba, har aka samo wani ya faɗa masa amma ya nemi daya ɓoye sunansa domin kowa tsorona ya keji, ahaka yazo ya sameni ya dinga yimin nasiha, ko ɗaya ban ɗauki nasiharsa ba sai ma niyyar fansa danaso ɗauko akansa, saboda sanin inda nake da yayi zai iya tonamin asiri domin wannan ƙasar ba irin ƙasarmu Nigeria ba ce, duk harka da manya da kake idan har kayi laifi ko kai waye sai an ɗauki mataki akanka, daga nanne na sanya aka ɗakkominshi nayi ta azabtar dashi, amma da yake Allah ba azzalumin bawansa bane sai gashi ya shiryenu cikin gaggawa, aɗan zaman danayi dashi haka ya cigaba da yimin nasiha duk da ina azabtar dashi ta ko'ina amma bai gajiya wajen daina yimin nasiha ba, cikin nasihar tasa yana yawan faɗamin.
_KAJI TSORON ALLAH HAMMUD, KA SANI ITA DUNIYA BA WAJEN ZAMA BACE WAJEN ARO CE DOMIN SHI KANSA RAN ARO AKA BAMU, BA DON ARO AKA BAMU BA DA TUNI BABU MUTUWA TUNDA RAN NAMU NE, SANNAN DUK ABINDA KAKE KA TUNA DA CE WA ALLAH YANA GANINKA, KAJI TSORON ALLAH KA GYARA MU'AMALARKA DA KOWA DUK DA WANI KO GOYASA ZA KAYI VA ZAI DAINA JIN ZAFINKA BA TUNDA DAMA KOWA YANA DA MAƘIYI, TUNDA MANZON TSIRA YAYI MAƘIYA DOLE KOWA MA YAYI SU SHI DA ALLAH YA WANKE BAI TAƁA LAIFI BA, KAJI TSORON ALLAH KA TUNA RANAR MUTUWA. RANAR DA ZA A ƊAUKEKA BA KADA BAKI BA KADA IDO BA KADA HANNUN AIKATA LAIFUKA IDAN KAYI AIKI NE KYAU KAYITA KUKA KANA CEWA KADA SU KAIKA, IDAN KUMA KAI ƊAN ALJANNA NE KAYI TA MURNA ZA A KAIKA INDA ZAKA HUTA DA FITIN TUNU DA WAHALAR RAYUWA....._
ire iren waɗannan nasihun yake mun, bai taɓa gajiyawa ba har Allah yasa ayanzu na gane komi ina kuma roƙon Allah ya shiryi dukkanin masu hali irin nawa, Allah kuma ya daɗo irin masu halin Mu'azzam domin da ana samun irinsu da munafunce munafunce baiyi yawa ba".
Tun daga wannan ranar muka zama abokai, duk da bayan lokacin sai da Hammud ya shiga hannun hukuma tunda ba irin ƙasarmu Nigeria bace, ko da kaida kayi report ka yafe to suma suna da hakki, idan baka haɗa da addu'ah bama har gidan yari zaka tafi tunda su can laifin gidan yari ba wahala ne dashi ba.
Bayan an gama shari'ah bisa addu'ar da muka dingayi Allah ya taimakesa da kansa sukace ta tafi.
Mun haɗe kanmu tsintsiya ɗaya maɗaurinki ɗaya, saboda haka a makaranta aka sanya mana suna TRIPLET ƴan uku kenan, kowa da haka ya sanmu duk dani halinmu ya banbanta dasu domin su suna da haba haba da jama'ah, ni kuma sam ba nida fuska kullum fuskata aɗaure, sannan ba nida sakin jiki da kowa idan ba da triplet ɗina ba, bana shawara da kowa sai su Mu'azzam yana ƙara mana karatu sosai cikin ikon Allah sai gashi har mun haddace ƙur'ani azaman shekara 6 da mukayi tare.
cikin abinda na ɓoye musu shi ne asalina, ban taɓa nuna musu ni ba ƊAN HALAK bane, duk wanda yake hirar mahaifinsa sai dai ni inyi shiru saboda ba nida abinda zance sai dai damuwa ce fal araina domin nasan ina cikin rayuwa mafi tsanani.
Domin acikin babbar ƙaddara ta rayuwa rashin fitowa ta hanya tsarkakkiya ita ce babba, domin kowacce ƙaddara ta biyo bayan wannan domin su iyayen da suka aikata ɓarnan basa jin daɗi da kuma rashin ƙwanciyar hankali, sannan uwa uba shi yaron daya zo ta wannan hanyar rayuwarsa na lalacewa ne tamkar dai yadda abinci yake lalacewa idan yayi wasu ƙwanaki.
asannu duk zurfin cikina suka gano komi, sun tayani alhini kuma sun shiga cikin tashin hankali fiye da yadda nake ciki, saboda suna ɗaya daga cikin manya manyan masoyana.
mun gama makaranta lafiya, kowa yana ta murna amma mu muna cikin tashin hankali na rabuwa da juna, har gwara ni da Hammud saboda muna ƙasa ɗaya state ɗaya, shi kuma Mu'azzam yana wata ƙasar daban duk da muna kusan maƙota da Niger, har tsokanarmu akayi tayi.
*BAYAN RABUWA*
Haka kowa ya dawo gida, sakamakonmu yayi kyau sosai tunda dukkanin bama saka wasa adukkanin harkokinmu, Mu'azzam yana yawan ziyartarmu akoda yaushe har na bashi shawara ko zan bashi manaja a kamfanina, tunda ni da kaina inada kamfanin da bansan adadinsu ba a ƙalla zasu kai ɗari ko ma sama da haka domin ina da dukiyar da nima ban san ta yadda aka samota ba, tasowa nayi na sameta na cigaba da kula da ita ban fara tsorata da rayuwa sai bayan dawowa ta daga ƙasar Italy, rayuwata ta zama abar farauta domin duk waɗanda Ammi ta ɗora kan kasuwancina macuta ne ta yadda suka dinga aikata ɓarna babu ruwansu, domin sai yadda sukayi da Ammi kuma ko sisi basa kawo mata, domin ita bata ma damu da kuɗin ba tunda tana dasu har ta rasa ma yadda za tayi dasu.
Ganin wannan ɓarnar yasa duk na koresu na ɗauki aminai na Mu'azzam da Hammud suka zama masu kula da komi sai dai ni inzo kawai in duba, sannan ina kula da hada hadar kasuwancina na ƙasashen waje...............
*SHARE🥰*
*$HAIDAR*
*$MU'AZZAM*
ƊAN HALAK GRP LINK
***
cnDvlFNqL0Enq7llnpAVe
*UMMU MAHER*