COMPLETE BOOK
SANADIYYA
Na fara da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.
1)
"Na yarda da gaske maza sune sanadiyyar yawaitar mata musamman masu aure a cikin matsalar shaye-shaye"
Na faɗa a fili, zuciyata na ƙuna da tafarfasa. A gefe guda kuma zuciyar tawa cukurkuɗe take da ɗimbin damuwa da matsanancin tunanin halin da nake ciki.
Shiru nayi idanuna zube a kan tulin kwalaben magungunan da suke gabana. Wani zazzafan tunani mai haɗe da matsanancin mamaki ne ya ci gaba da yi min saƙa a zuciyata.
'Yau na ga mata mabanbanta a kamanni da shekaru. Ashe akwai mata da yawa da rayuwarsu ke cakurkuɗe da damuwoyi haɗe da matsaloli kala-kala? Kamar dai makamanciyar tawa rayuwar, mai cike da ɗinbin ƙunci da rashin walwala. Irin wacce sanadiyyar damuwoyin da muke ciki har take neman jefa mu ga aikata mummunar rayuwa irin wacce bakin alƙalami ya bushe a kanta.'
"Ko da yake ai laifin maza ne! Don haka alhaki da duk wani zunubi zai rataya a wuyansu ne."
Na sa ke faɗa a fili, a muryata cike da ƙunci.
Sai kuma nayi ƙuri da idanuna akan ɗaya daga cikin kwalaben magungunan, na sa hannu na ɗauki kwalbar tare da ɗaga ta sama ina jujjuyawa. Kamar dai ina karantar wani muhimmin abu daga jikinta, amma kuma a zahirin gaskiya ba karanta komai nake yi ba, idanuna ne kawai akan kwalbar zazzafan tunani ya ci gaba da hajijiya da ni daga tunanin damuwar da nake ciki zuwa matakin da nake ganin na samar wa kaina.
Maganganun matasan mata biyun da na haɗu da su ɗazu da yamma a gidan Hajiya harka ne ya fara dawo min tiryan-tiryan a zuciyata, kamar a lokacin suke faɗa min nauyayan maganganun masu kama da muhimmin karatu. Haka kawai a ganin farko Allah ya haɗa jinina da na su, har ya zama a zaman bin layin jiran Hajiyar da muke yi jefi-jefi suna tsoma ni a cikin hirar da suke yi.
Ɗaya daga cikinsu ce ta fara magana tana wani yayyarfe hannaye haɗe da zazzare idanu kamar wacce ba ta cikin hayyacinta, amma da na ƙara kallonta da kyau sai na fahimci a hankalinta take. Tsananin yanga ko kuma yawan ƙwayancewa ne ya mayar da ita hakan? oho!
'Ƙawata bari in faɗa miki wata magana. Ako wane lokaci kika tashi yin addu'a roƙonki na farko ya zama jimlar Allah ya raba ki da baƙin cikin ɗa namiji. Idan kika yi sa a addu'ar ta karɓu har Allah ya yaye miki to an gama miki komai a duniya.'
Duk sai mazauna tafkeken falon suka kwashe da dariya, har da Hajiyar da rabin hankalinta yake kan wasu ƴanmata tana haɗa musu kayan harka.
Ni kuwa da nake zaune ina karkaɗa makullin motata da zuciya mai cunkushe da ƙatoton damuwa ka sa dariyar na yi, sai nayi ɗan murmushin yaƙe wanda bahaushe yake kira da ya fi kuka ciwo.
Ɗaya matashiyar matar sai ta taso ta dawo kusa da ni ta zauna, ta dafa kafaɗuna, da fuskarta cike da murmushi ta ƙare min kallon sama da ƙasa. Sai ta sake faɗaɗa murmushinta ta fara min magana a tausashe, har lokacin hannunta bai bar kan kafaɗata ba.
'Ƙawata da alama ke sabuwar zuwa ce a gidannan da wannan harkar ko?'
Da sauri na ɗaga mata kai alamar eh, tsananin damuwa ya hana ni mamaki ko tunanin yadda aka yi ta fahimci ni sabuwar zuwa ce a gidan. Muryata a sanyaye da alamun damuwa ƙarara na ƙara mata da cewa.
'Da gaske ban taɓa zuwa nan gidan ba, ke ni wallahi ban ma taɓa shan komai ba. Ya kai tsawon wata ɗaya da maƙwafciyata take ta kwaɗaita min zuwa nan gidan, ta ce idan nazo a karon farko duk damuwoyin da nake ciki za su kwaranye. Duk tsawon lokacin nan ban samu ɓullowa ba sai yau.'
Duk su biyun sai naga sunyi wani murmushi da na rasa gane ma'ana ko kuma inda ya dosa. Ta kusa da ni tayi far da idanunta, ta kalle ni sama da ƙasa ta yi dariya mai ɗan sauti.
'Da gaske gaskiya ta faɗa miki. Tabbas damuwarki za ta kwaranye. Duk matsaloli da ƙuncin da kike ciki za su yaye. A ko wane lokaci za ki tsinci kanki cikin wata sabuwar duniya ce da babu komai a cikinta sai tsananin kwanciyar hankali, nishaɗi, farin-ciki, haɗe da tsabar nutsuwa da walwala. Amma a shawarce ki rage tsawaitawa kanki tunani, idan ba haka ba zai illatar da ke, yawan tunani mataki ne na farko wajen barazana ga lafiyar jiki. Ina fatan dai kin taho da isassu kuma wadatattun kuɗaɗe a jakarki?'
Na ɗaga mata kai alamar 'e' na taho da su.
'Da kyau ƙawata. Kin kyautawa kanki. Yo in banda abinki ma yanzu ai ƙauyanci ne zama a cikin damuwa, don a banza sai ki kamu da ciwon zuciya. Idan silar damuwar namiji ne kina mutuwa ko arba'in baza ki yi ba zai hango wata tsaleliyar mace ya aura. Idan kuwa talauci ne wasu kalolin sabbin kuɗin ma sai kin mutu za a ƙero su. A sauƙaƙƙiyar harshe kuma abinda nake so ki fahimta ko ma miye sanadin damuwarki ƙawata ki nemi hanyar da zai mantar da ke kawai. A taƙaice sai in ce muna miki maraba da zuwa duniyar ƴanci da walwala da gwaggwaɓar nishaɗi. Ki saurari Hajiya harka, za ta haɗa ki da zafafan kaya cikin ƙanƙanin lokaci.'
Ta ƙarasa maganar tana dariya sauran mazauna gurin suna taya ta.
Saboda ni sabuwar zuwa ce duk da sun riga ni zuwa gidan sai suka ɗaga min ƙafa Hajiyar ta fara sallama ta. Wani ƙarin abin ban mamaki da ɗaure kai a gare ni sam Hajiyar bata tambaye ni damuwata ko matsalar da ta addabeni a duniyata ba. Dubu goma sha biyu ta amsa a hannuna, ta haɗo ni da tarkacen kwalaben magunguna masu ɗan dama ta ce inje inyi ta sha har sai na ji na fara manta banbancin da yake tsakanin fari-fat da baƙi-ƙirin.
Duk da ban fahimci me take nufi da maganganunta ba sai ban tsawaita tambayarta me take nufi ba. Muka yi musayar suna da lambobin waya tsakanina da waɗannan matasan matan. Suka ƙara min da cewa duk abinda ban fahimta ba dangane da magungunan in kira su, ƙofarsu a buɗe take don bani tallafi na shawarwari ko kuma wani ƙarin bayani.
Bayan na fito a gidan da mataccen jiki kamar wacce aka lakaɗawa na jaki haka na ci gaba da ragaita da motata a tsakiyar titi, zan tuƙa bazan tuƙa ba haka nake tafiya saboda tsananin sanyin jiki. Tunanin da yayi min katutu a zuciya yasa sai gwama go-slow ga motocin da suke biye da ni nake yi, su kuwa sai danna min mahaukacin hon suke yi a haka dai cikin hukuncin mai duka har na isa gidana lafiya.
Tun da na isa gida ka sa hassala komai na yi, nan na zube a tsakiyar ɗakina na fara tufka da warwara haɗe da saƙawa da kwancewa. Har zuwa yanzu da na kasa tsayar da ƙwaƙƙwaran matsaya guda tsakanin shan kayan mayen ko kuma rungumar kundin mummunan ƙaddarata in ci gaba da kashe kaina da mummunan tunani da damuwa.
Tunawa da na yi banyi sallar la'asar ba ga shi har magriba ta kawo jiki yasa na tattare kwalaben magungunan da sauri na mayar cikin leda, wani abu da ya bani mamaki shi ne ganin lambobin wayar Hajiya Mai Babbar harka da sunanta ɓaro-ɓaro a jikin ledan magungunan, ƙarin wani armashi da sauƙin gane kwatancen inda za a same ta har da cikakken adireshin gidanta. Sai wani ɗan ƙarin bayani da aka yi a taƙaice a ƙasan suna da lambar wayarta
"Domin taimakawa matan da suke cikin matsanancin damuwa da halin ƙaƙa ni kayi a tuntuɓeni ta wannan lambar wayar."
Jinjina kai kawai nayi na watsar da mamakin na faɗa banɗaki da sauri na ɗauro alwala.
Ko da na idar da sallar ban tashi a wajen ba ina ta lazumi har aka kira sallar magriba ita ma na gabatar da ita.
A kan gado na aje hijabin tare da janyo wayata da niyyar dannawa mijina Hashim kira, amma saƙon text message ɗin shi da na fara cin karo da shi ya kwaɓe min duk wani hanzari nawa tare da ƙara ladabtar min da jiki.
"Fatima! Wannan satin bazan samu dawowa ba. Tafiyar gaggawa ce ta sake kama mu ni da Oga Nura zuwa Dubai, amma kyakkyawan albishir a gare ki shi ne baza mu daɗe ba, sati biyu kawai za muyi. Idan mun sauka zan kira ki inji yadda kike. Ga kuɗi nan na tura miki a acc ɗinki ko za ki buƙaci wani abu. I love you Babe."
Ban san da zazzafar hawaye nake karanta saƙon ba sai da na ji gishiri-gishiri na ɗanɗanon hawaye a bakina. Ƙarin tabbatarwa kuma ganin ɗis-ɗis na saukan ɗigon hawaye a fuskar wayar tawa.
A sanyaye na aje wayar a kan gado, domin bana jin zan iya mai da mishi martanin saƙon.
'To me ma zance mishi bayan aikin gama ya gama har sun riga sun tafi?' Don baƙin ciki da damuwa ko adadin kuɗin da ya ce ya tura min ban duba ba. Na tashi tsaye ina tattaki a hankali kamar mai koyon tatata, har na ƙarasa gaban ledan magungunan Hajiya Harka.
Zaman dirshan nayi a kan kafet na ƙurawa ledar idanu, har wannan lokacin zafafan hawaye sunƙi tsayawa daga idanuna. A lalace na kai hannu cikin ledan na fara ciro kwalaben magungunan ɗaya bayan ɗaya har na gama fidda su gaba ɗaya. Na ɗauki ɗaya na murɗa murfin da ƙarfi na buɗe, na ɗaga kwalbar na nufi bakina gadan-gadan, kafin in sha na fara magana cikin matsanancin kuka idanuna suna kallon sama
"Allah kana ji kuma kana gani. Ba da son raina bane amma ba ni da mafitar da ta wuce wannan."
Runtse idanu nayi na kafa kwalbar a baki na fara ɗaɗɗakar maganin ciki ba tare da wani tunani ba, a lokacin babban burina in samu abinda zai gusar min da hankali ta hanyar mantar da ni matsananciyar damuwar da nake ciki.
Kasancewata sha zumamu a gurin son zaƙi yasa nan da nan na shanye maganin gaba ɗaya saboda tsananin zaƙinsa, ban jira komai ba na buɗe wani kwalbar shi ma na kafa a baki na ci gaba da kwankwaɗa, ban cire ba sai da naji ba komai a ciki. Haka na sake buɗe wani kwalbar a karo na uku duk da wani masifaffen nauyi da naji kai da idanuna sun fara yi min, na fara sha ke nan na ji kayan cikina sun haɗe sun ƙulle guri ɗaya, sai wani rugugi da hargitsa suke min kamar wacce za ta ɓarke da gudawa, zuciyata kuma ta fara wani irin tashi kamar mai yaron ciki.
Da na sauke idanu ƙasa ina kallon leda da kwalaben magungunan sai na ga sun fara rarrabuwa min hurhuɗu a idanuna, wani irin juwa ya fara ɗibata ina daga zaune kamar zan tuntsura. A sannu-sannu da lalube kamar makauniya na ajiye kwalbar a ƙasa, na ɗora hannu biyu na tallabe kaina da nake ji yana min wani irin juyi da nauyi kamar zai faɗo ƙasa. Ɗakin da komai na cikinsa ne naga suna juyi da ni daga gabas zuwa yamma sai kuma a buga da ni kudu da arewa.
Cikin ƙanƙanin lokaci na fara ficewa a hayyacina, da naga ba sarki sai Allah kawai sai na zame a ƙasa na kwanta tare da damƙe gargasan kafet ɗin tsakiyar ɗakin da hannu bibiyu ina wasu irin surutai da ni kaina ban san me nake cewa ba. Daga haka ban sake sanin a wane hali nake ciki ba tsakanin matacciya da rayayyiyar mace mai cikakken hankali da nutsuwa.
***** *****
2)
"Fatima ce a gidan na mu?"
Ta tambaye ni da yalwataccen murmushi a fuskarta. Kafin in amsa ta cigaba da cewa
"Maraba lale marhabin"
Ɗan murmushi kawai nayi, jikina cike da matsananciyar kasala na nemi guri na zauna. Na ja wata wawuyar hamma na sauke sannan na amsa mata da
"E ni ce Ammah."
Na amsa a ɗarare, ina sussunƙe kai a ƙasa. Na rasa dalilin da yasa a tsorace nake sosai, wani irin kunya da nauyi nake ta ji a jikina tunda na wayi garin yau, gani nake kamar kowa zai iya ganin abinda na aikata jiya a goshi na.
Kafin ta sake cewa komai da sauri na gyara zama na fara gaisheta, muryata cike da tsananin ladabi da biyayya.
Cike da matsanancin kulawa da ƙauna ta amsa gaisuwa ta, ta ƙara da cewa
"Ina kika fito haka da tsakar ranar nan?"
Ta ƙarasa tambayar tare da sauke idanunta a kan tafkeken agogon bangon da yake maƙale a bangon yamma na falon.
Nima agogon na kalla, ɗaya da minti hamsin na rana, muryata a sanyaye na amsa mata da cewa
"Daga gida nake Ammah."
Domin in katse duk wasu tambayoyi na ta da a yanzu bana jin na shirya amsa mata da sauri na ci gaba da cewa
"Daman na zo ɗaukan Rabi'a ce, Jiya Ya Hashim bai dawo ba. Tafiya ta sake kama su zuwa Dubai, amma ya ce sati biyu kawai za suyi a can."
"Allah sarki Hashim. Yaron kirki ɗan albarka. Allah ya bada sa'a ya dawo mana da shi lafiya."
Bata jira na amsa addu'ar ba ta ci gaba da yi min nasiha kamar yadda ta saba duk sadda na je gidan..
"Mijinki yaron kirki ne Fatima. Tunda ya aure ki bai taɓa gajiyawa da ɗaukar nauyinmu da duk wasu hidindimu na mu da na ƙannenki ba. Ko Abbanku yana faɗin ya daɗe bai ga suruki irin Hashim ba. Jiya da yamma muna zaune ya tura ma Abbanku dubu hamsin wai ya sai ƙananun abubuwa kafin ya zo da kanshi. Duk ga tsammaninmu ma ya dawo ne, ashe wata tafiyarce ta sake kama shi. Sakayyar da za ki ci gaba da yi mana kawai shi ne bin shi sawu da ƙafa kina kyautata mishi. Kar ki manta kullum ina faɗa miki aljannarki tana ƙarƙashin ƙafarsa ne, sai ya ɗaga za ki shige cikin aminci da salama."
"To Ammah. In Allah ya yarda zan ci gaba da kiyayewa."
Na amsa cike da gundura.
'Domin jin irin waɗannan kyawawan kalaman na yabo a kan mijina da tunasarwa akan in bi shi sawu da ƙafa inda sabo na saba da jin su a bakin Ammah da Abba. Zan iya cewa ma na haddace su, kamar karatu ne da in dai zanje gidan tabbas sai sun yi mini tilawarsa.
Hashim ya daɗe da gama kalailayesu da kyakkyawan halinshi na kyautar kuɗi da kyautatawa irin ta ladabi da biyayya da ganin girman na gaba. Yadda ya ɗauke su tamkar iyayen da suka tsuguna suka haife shi. Su kuma hakan da yake musu yake ƙara saka su jin alfahari da ganin babu wasu iyaye da suka yi dacen surukin arziki kamarsu. Tsananin ƙaunar da suke masa tasa sam basa ƙaunar lefinsa ko misƙala zarra.
Tun ina yunƙurin kawo ƙararshi suna kora ni fata-fata ba tare da sun yi wani yunƙuri ko hoɓɓasa don magance min matsalata ba har na haƙura na daina. Na yi ma kaina karatun ta nutsu na rungumi kundin ƙaddarar gidan aure na.
Ba ni mantawa a zuwata na ƙarshe da ƙorafi a kan irin abinda yake min ma Ammah kuka riris ta saka min, ta ce in dai ba so nake ita ma na ta auren ya mutu ba in rufa mata asiri in zauna da haƙuri a ɗakin mijina. Don Abba na ya ce muddin ta barni na kashe aure na ta tabbaci haƙiƙa itama na ta igiyoyin auren guntulewa za suyi. Da ta ga zan tafi ina kuka sai ta fara rarrashi na da tausasan kalamai wai ko wacce matar aure da nake gani haƙuri take yi a ɗakin aurenta. Har ta ƙara min da cewa komai daɗin da zanga wata ɗiya mace tana ji a gidan aurenta tabbas a bayan wannan daɗi akwai wani gaggarumin damuwar da ta ke ciki. Haƙuri da juriya haɗe da mayar da komai ba komai ba da rungumar bautar Allah aure yasa zanga kamar babu matar auren da take cikin matsala sai ni.
Da waɗannan dalilan yasa tun daga ranar na sha alwashin in damuwa zai yi ajalina bazan sake tunkarar Ammah da Abba akan matsalar gidan aure na ba.
Ban jima a gidanmu ba na ɗauki Rabi'a muka wuce gidansu Hashim don in ɗauki ƙanwarshi Aisha. Kasancewarshi ba mazauni ba ga gida tamfatsetse da ya gina ya aje ni ni kaɗai a ciki sai mai gadi a get yasa ƙanwata da ta shi suke taya ni zama a gidan. Idan suka zo basa komawa gida sai ranar da zai dawo. Ko jiya ma mun zaci zai dawo ne shi yasa suka tafi gida da hantsi misalin ƙarfe goma na safe.
"Fatima ya naga idanunki sun canza launi? ko bakya jin daɗi ne?"
Ƙirjina ne ya buga dam! da jin tambayar da Hajiya mahaifiyar Hashim tayi min.
Sake sadda kaina ƙasa nayi a daburce. Ina jin yadda kaifafan idanunta suke yawo a jikina tana karantar duk yanayina. Da sauri na yi ƙoƙarin daidaita kaina na ƙaƙalo murmushin yaƙe, na ce
"Hajiya jiya ne da daddare wani ɗan ƙaramin ƙwaro ya faɗa min a ido, amma lafiyata ƙalau..."
"Kin tabbata haka ne?"
Ta katse ni da tambayar muryarta na baiyana shakkar jin abinda na faɗa mata.
"Allah da gaske nake yi Hajiya. Ki tambayi su Aisha ma lafiya muka rabu da su a jiyan. Kawai dai ƙwaron ne yasa idanuna suka canja launi saboda murzawar da nake ta yi har na samu na daina jin zafin."
"To shi kenan! Allah ya ƙara kiyayewa. Ki zauna ki ƙarasa yini a nan da yamma sai ku wuce can gidan. Aishan na aike ta gidan Raliya ta kai mata saƙo, amma ba na tunanin za ta wuce la'asar bata dawo ba."
"To Hajiya. Na gode."
Na amsa har lokacin ban sake yarda na haɗa idanu da ita ba.
Nagartacciyar mace ce mai cike da kwarjini da ƙima a idanun duk wanda ya kalleta. Sosai Allah ya bata wannan baiwar. Tana da halaye na gari, ga hannun kyauta da yawan alkhairi, shi yasa mutane suke matuƙar ƙaunarta.
Yawan kyauta kamar a jininsu yake, don mijinta Alhaji Yahaya mahaifin Hashim shi ma haka yake. Kusan ko wane lokaci ƙofar gidansa ba ya rabo da jama'a masu zuwa da ƙoƙon bararsu shi kuma yana taimaka musu gwargwadon yadda zai iya.
Banso zaman yinin ba amma haka nan na zauna don bazan iya mata musu ba, sauƙinta ma muna tare da ƙanwata Rabi'a. Nan muka bararraje a falon muna kallo masu aiki sai kaiwa da kawowa suke yi wajen ajiye mana kayan marmari da kayan taɓawa dangin ƙwalam da maƙwalashe. Bamu bar gidan ba sai ƙarfe biyar da minti hamsin na yammaci. Hajiya ta haɗani da kyautar turarukan wuta masu tsananin ƙamshin daɗi da kwalakca. Ta ba Rabi'a dubu biyu wai tasa kati a waya.
Mun isa gida na dake ƴan majalisu unguwar dosa gaf da kiran sallar magriba, ina shiga da motar cikin gida na miƙa musu makullan ɗakunan gidan da ledan turaren da Hajiya ta bani da jakar hannuna.
"Ku shiga ciki, bari in leƙa Maman Khairat. Yanzu zan fito, saƙo zan karɓa."
"To Aunty, a dawo lafiya."
Suka amsa gaba ɗaya.
Ni kuma na fice daga gidan da sassarfa.
Sa'ar da naci ganin get ɗin gidan a buɗe, don haka ban sha wani wahalar ƙwanƙwasa ba na tura get ɗin na shiga cikin gidan. Da yake babban gida ne mai ɓangare uku, ɓangarenta na uwargida shi ne a can ƙarshen gidan, na Amaryarta a tsakiya, sai na mijinsu a farkon gidan. Kai tsaye ɓangarenta na nufa na ƙwanƙwasa ƙofar falon tare da sallama.
Murmushi muka sakarwa juna bayan ta buɗe ƙofar
"Maman Khairat na zo yin godiya ne fa, jiya dai na leƙa gidan Hajiya...?"
"Fati kar dai ki ce kin leƙa gidan Harka?"
Ta katse ni da tambayar idanunta a warwaje da matuƙar mamaki.
"Ƙwarai kuwa na je har na amso kayan..."
A karo na biyu ta katse ni tare da jan hannuna zuwa cikin falon, yaranta su huɗu uku mata da ƙaraminsu namiji ta kalla da suka barbaza takardu a tsakar falon, da alamun aikin makaranta suke yi.
"Oya! Khairat kuje kuyi alwala yanzu za a kira sallah. Kun san dai sallah a farkon lokaci ta fi lada ko?"
Suka amsa da "E" gaba ɗayansu.
"Yauwa ƴaƴan albarka to ayi sauri a je banɗaki a ɗauro alwala."
"To Ummee."
Suka amsa gaba ɗaya.
Ta ja hannuna muka ƙule a cikin ɗakin baccinta.
"Ke Fati ba ni labari. Ya aka yi? ina fatan dai yanzu ba ki cikin wata matsala? Allah yasa dai komai zam-zam?"
Dariya na saka tare da zama a gefen gadonta ina kallon yadda ta zaƙu da son jin labari.
"Kin san Allah? Da farko fa na tsorata sosai. Sai da na farka yau naga ashe har na ɗanyi ɓarna a ɗakina, na ɓarar da ragowar maganin da na buɗe kuma na watsar da kayan kwalliyar da suke jere a gaban madubina. Ban san ma dai ya zan kwatanta miki yadda na tsinci kaina a ciki ba, amma da gaske na samu sauƙin kashi hamsin cikin ɗari na damuwata bayan na farka daga nannauyan baccin da nayi tun magribar jiya har zuwa yau da misalin ƙarfe tara na safe.
Abinda ya ɗan dame ni kawai rasa sallar isha'i da asubah a kan lokacin da nayi. Sai kuma ɗan nauyin jiki da kasala da nake ji har yanzu kamar bai gama sake ni ba. Yanzu dai gaskiya Alhamdulillahi dai-dai gwargwado ina cikin nutsuwa da wani irin farin ciki da na daɗe banyi irinsa ba."
Dariya tayi tare da zama a gefen gadon kusa da ni
"Ma sha Allah. Na ji daɗin jin haka Fatima. Da gaske kallonki nake kamar ƙanwata marigayiya Jamila, shi yasa nake jin ƙaunarki a raina. Sosai nake jin ba daɗi idan na ganki a cikin damuwa. Kin ga daga yau kafin ki sha komai ki tabbatar kin sauke faralin duk sallolin da suke kanki. Kuma jiya don ke sabuwa ce a harkar shi yasa zai ɗan wahalar da ke, amma da kin saba sha komai zai koma miki dai-dai kinji?"
"Tam! Na gode Maman Khairat. Allah ya bar zumunci."
"Ameen ya Allah."
Ta amsa cike da jin daɗi, har lokacin tattausan murmushin bai bar kan fuskarta ba.
"Bari in ƙarasa gida, tare nake da su Aisha. Daman kawai na shigo inyi miki godiya ne gurguje."
Na faɗa tare da miƙewa tsaye, alamun ina da niyyar tafiya.
"Yauwa kinga wata dabarar da za ki dinga yi idan kina so ki dinga jin daɗin komai kina sha cike da shauƙi."
Ta faɗa tare da nufar jikin gadonta, wani ɗan ƙanƙanin frinji na gani ajiye a gefen gadon mai kama da bed side drower. An datse ƙofar frige ɗin da ɗan makulli, ta ɗauko key ɗin a wata durowa ta buɗe.
Abin mamaki a gare ni sai ga kwalaben magunguna irin waɗanda na amsa jiya da wasu kalolin da ban sansu ba masu yawa jere reras a ciki, sun ɗauki sanyi sosai sai fidda raɓa suke yi. Ta yi dariya tare da cewa
"Idan kika yi irin wannan dabarar tawa cike da annashuwa za ki dinga shan kayan Harka. Kin san komai mai sanyi ya fi daɗin korawa."
Dariya muka yi gaba ɗaya, rufewa tayi kamar yadda yake a farko sannan ta ɗauki mayafi ta yafa muka fito dan ta rakani ƙofan get ɗinsu. Hira muke yi ƙasa-ƙasa, gaf da zamu wuce ɓangaren mai Gidan sai ga shi ya fito daga falonsa. Ya kallemu sama da ƙasa ya wani watsar da mu kamar ya ga kashi.
"Alhaji barka da fitowa."
Ta faɗa a sanyaye idanunta a kan shi, ganin yadda ta ƙure shi da kallon yasa na gane alamu ne na fatan Allah yasa ya amsa mata, gudun kar ya yarfa ta a idanuna matsayina na baƙuwarta. Da yake ɗan halak ne kuwa ƙin amsawa yayi, ashe biye a bayanshi busasshiyar amaryarsa ce mai kama da an ɗaurawa muciya zane saboda tsananin rashin shape ɗinta.
Sai wani karairaya take yi tana yauƙi haɗe da far-far da idanu kamar za ta tashi aljannu, shi kuma ƙato da shi da tulelen cikinshi a gaba sai biye mata yake yi yana tarairayarta.
Haushi ne ya ƙara turnuƙe zuciyata, na kalli Maman Khairat dirarriya kuma cikakkiyar mace gaba da baya. Ga tsananin kyau da kyawun jiki, yadda idan ba wanda ya santa ba a kallon farko babu wanda zaiyi tunanin ta haihu har yara huɗu.
'Idan ba namiji ba da kwashe-kwashe mutum mai mace kamar Maman Khairat me za a gani jikin wancan busasshiyar a yi sha'awa?'
Na tambayi kaina a zuciyata.
Haushi yasa nayi gaba da sauri ba tare da na tsaya gaishe shi ba. A sanyaye ta biyo ni a baya har bakin get babu wacce ta sake tankawa, sai da taga fitata sannan ta juya ta koma cikin gidan.
Kamar yadda ta bani shawara bayan na gama komai na al'adata kafin in kwanta bacci yau ban zauna zaman kallo da hira kamar yadda muka saba ba.
"Kai Aunty? kinga fa sun fara shirin da kike so amma shi ne za kije ki kwanta?"
Na yamutsa fuska kawai, na sauke idanuna a kan ƙaton tv da yake manne a bangon falon. Kwana casa'in suke yi a tashar Arewa24, da gaske ina tsananin ƙaunan shirin, amma yau kam bana jin zan iya zaman kallon nan.
"Na gaji Aisha, kaina ciwo yake yi min. Ina so in kwanta da wuri kila rashin baccin da banyi da rana bane. Jibi idan Allah ya kaimu sai in kalli maimaicin shirin."
Fatan samun sauƙi suka yi min duk su biyun, bayan na amsa na wuce ɗakin baccina. Sai da na datse ƙofar ɗakina da key duk da dai bana tunanin wata a cikin su biyun za ta shiga min ɗaki. Tunda ɗakin da suke kwana daban nawa daban, ɗakuna huɗu ne a cikin falon kuma ko wanne an ƙawata shi da setin gado da duk wasu ababen more rayuwa.
Sai da na gama komai na shirin bacci sannan na buɗe durowar gefen gadona na janyo ledan magungunan, a gefen gado na zauna na ciro waɗanda nake buƙata na mayar da sauran. Saɓanin jiya yau ban tsaya tunanin komai ba na buɗe kwalbar na fara sha cike da nishaɗi, ina sha ina sauke ajiyar zuciya haɗe da lumshe idanu, ban dakata ba har sai da naji na isa inda nake burin kaiwa, na zube a kan gadon ina surutai cikin ficewar hayyaci, ban san lokacin da bacci yayi awon gaba da ni ba.
SANADIYYA
Fareeda Abdallah
3
Washe gari kamar jiya haka na sake tafka makara, domin ban farka ba sai ƙarfe bakwai da minti hamsin na safe. A wannan lokacinma mahaukacin bugun ƙofar da su Aisha suke yi min ne ya tashe ni a gigice, don jin bugun ƙofar na dinga yi kamar a mafarki har dai na tabbatar a gaske ne.
Na tashi da ƙyar ina rangaji da layi na je zan buɗe ƙofar, sai da nayi ƙoƙarin daidaita kaina sannan na buɗe ƙofar, na ɗaga idanuna da har lokacin suke min nauyi sosai na zuba su a kansu.
"Aunty? Lafiyarki ƙalau kuwa? Ko har yanzu ciwon kan ne bai sauka miki ba?"
Rabi'a ta jero min tambayoyin muryarta na rawa, da alamun a ruɗe take, fuskarta bayyane da alamun matsanancin damuwa da tashin hankali.
Na kai hannu ɗaya na mutsitstsike idanuna don bibbiyu nake ganinsu, ɗayan hannun kuma na sake riƙe ƙofar ɗakin don kar ma wata a cikinsu ta ce za ta shigo.
"Ban... ban samu nayi bacci da wuri ba ne jiyan... shi yasa yau na makara. Amma na ji sauƙi sosai."
Na harhaɗo maganganun da ƙyar na faɗa musu.
Aisha ta fara magana ita ma cikin damuwa
"Hankalinmu ya tashi sosai Aunty, mun kira ki a waya sau bakwai baki ɗauka ba. Yaya ma ya kirani har sau biyar yana ta damuwar ina kike wai tun jiya yake kiranki baki ɗauka ba. Yanzu ma fa shi ne ya ce muzo mu bubbuga idan baki tashi ba mu kira mai gadi a ɓalla ƙofar ɗakin don a ga wane hali kike ciki."
Ɗan murmushi kawai nayi, cikin dabara na jingina da jikin bango dan jikina ba ƙarfi sosai, ji nake kamar zan faɗi.
"Yanzu dai kuyi haƙuri, ku daina damuwa tunda lafiya ƙalau nake. Bari inyi sallah, inyi wanka sai in fito muyi karin kumallo."
"To Aunty. Amma dan Allah ki kira Yaya don hankalinsa ya kwanta."
"Zan kira shi Aisha. Karki damu."
Ƙofar ɗakin na maida na rufe sannan na tattare kwalaben magungunan na ɓoye a cikin durowa. A gurguje na faɗa ban ɗaki, ruwa na sakarwa kaina sosai don in ji ƙarfi a jikina. Sauri-sauri nayi wanka sannan na ɗaura alwala.
Ko da na idar da sallah na shirya na ɗauki wayata maimakon in bi bayan kiran Ya Hashim sai kawai na buɗe data na hau whatsapp. Kafin saƙonni su gama shigowa sai ga shi ya sake kira. Saboda mugun haushinsa da nake ji sai da na bari wayar tana gaf da tsinkewa na ɗauka, cike da sanyin murya nayi mishi sallama.
"Babyna kin ɗaga min hankali sosai fa, ya ciwon kan na ki? Ina fatan kin samu sauƙi sosai?"
"E na ji sauƙi sosai Hubby. Ya hanya?"
"Alhamdulillahi! Ki ƙara haƙuri da harkokina kin ji Babyna?."
Ya faɗa da tattausar muryarsa alamun rarrashi.
"To Hubby. Babu komai. Allah ya dawo min da kai lafiya."
Bayan ya amsa addu'ar ya so yaja ni da hira na fake da ce mishi ban karya ba kuma yunwa nake ji. Yayi haƙuri zan kira shi anjima. Bai takura ba shi ma yayi min fatan ƙara samun sauƙi ya katse wayar. Muna yin sallama na ja tsaki ƙasa-ƙasa na koma kan whatsapp don in duba saƙonni.
"MATAN ƳANCI"
Na karanta rubutun sunan sabon group ɗin da naga an jefa ni a ciki. Mamaki ne ya kama ni, nan na leƙa ciki don ganin wace wainar ake toyawa don kuma gano wacece tayi adding ɗina a group ba tare da sani na ba?
"Matan ƴanci ku yiwa sabuwar membernmu barka da zuwa. Baby Fatima barka da zuwa gidan Mata masu ƴanci."
Saƙon da na fara cin karo da shi ke nan a cikin group ɗin bayan na gane Nucy ce tayi adding ɗina a group ɗin. Ɗaya daga cikin mata biyun da na haɗu da su jiya a gidan Hajiya Harka.
Daga wannan maganar kuma sai naga duk matan group ɗin sai barka da zuwa suke yi min cike da karramawa,
abinda ya burgeni kenan.
Daga ƙarshe na ga Laby ta ce in gabatar da kaina kuma in tura musu hotuna na.
Ba tare da tunanin komai ba na tura musu hotuna na gudu uku, na rubuta cikakken sunana da taƙaitaccen tarihina na tura musu.
"Sunana Fatima El-Bashir, haifaffiyar garin kaduna. Shekaruna ashirin da shida, kuma nayi aure shekara ɗaya da rabi baya. Har yanzu ban haihu ba. Gida na yana unguwar dosa"
"Waww!
Cute Baby.
I love you Sweetheart, You look very nice."
Waɗannan kaɗanne daga cikin irin kalaman yabo da soyayyar da suka yi ta tagging ɗin hotuna na suna furtawa. Abinda ya ɗaure min kai kuma shi ne ko da na koma kan chat ɗin wayata sai naga baƙin lambobi uku daga cikin group ɗin sunyi min magana ta akwatin sirrina.
Biyu daga cikinsu hotunansu suka tura min da neman ƙulla ƙawance tsakaninmu. Duk da abin yayi min wani banbaraƙwai sai ban tankwaɓe ƙoƙon bararsu ba, kai tsaye na ce na amince. Har ma na ce zan adana lambobinsu don samun dauwamammen zumunta.
Ɗayan saƙon da yafi ɗaukar hankalina na wata mata ce da ta rubuto min kamar haka
"Baby Fati sunana Hajiya Ladi A lallatsa. Da gaske ina son ki, tun kafin in ganki a zahiri da ganin hotonki na ji a raina kin kwanta min. Na yi kamu don haka karki kuskura ki ba ko wacce mace ƙofar da za tayi soyayya da ke. Ina da kuɗi, ina da duk wani abu da zaki nema a gurin ko wacece. Ina fatan kin fahimce ni?"
Ban fahimce ta ba fa, ko kusa ban fahimci me maganganunta suke nufi ba. Amma da yake ni ɗin ba mai son jan doguwar magana ba ce da kuma rashin saurin sabo da nake da shi sai kawai na amsa mata da
"Na gode Hajiya. Allah ya bar ƙauna a tsakaninmu."
Daga wannan ban ƙara bi ta kanta ba na kashe data na ƙarasa shiryawa na fice falo gurin ƙannena. A lokacin duk sun gama haɗa abin karyawa ni kaɗai suke jira.
***** *****
Sauri-sauri gudu-gudu ta fito daga ɓangarenta ta nufi gurinsu, kafin ta ƙarasa har sun isa gurin motarsa, ya shiga ciki ɓangaren direba ya zauna.
Amarya Aliya tana tsaye kusa da shi riƙe da hannun ƙofar tana karairaya haɗe da zuba mishi shagwaɓa tana yayyarfa hannaye kamar wacce ta ƙone.
Shi kuwa sai murmushi yake zabgawa yana magana ƙasa-ƙasa, yadda sai wanda ke kusa da shi sosai sannan zai ji abinda yake cewa.
Can gefe ta tsaya tana kallonshi da idanu lumsassu, sai da ta nutsu ta saisaita muryarta kafin ta fara magana.
"Alhaji barka da fitowa. Ina kwana?"
Tayi maganar cike da ladabi da biyayya, muryarta a sanyaye, cike da tsoro haɗe da fatan kar ya tozartata da cewar tana ɗaga mishi murya gurin magana kamar yadda ya saba faɗa mata a mafiyawancin lokuta.
Cikin ƴan daƙiƙu ya haɗe girar sama da ƙasa yayi murtuk kamar kakkauran kamun da aka sheƙawa tafasasshen ruwa! Ya haɗe rai sosai kamar bai taɓa dariya ba. Ya ƙanƙance idanu cike da masifa da tozarci ya fara magana, yana watsa mata wani mugun kallo mai baiyana tsananin tsana da kyara haɗe da hantara.
"Saboda ke isasshiya ce sai yanzu kika ga damar zuwa ki gaishe ni?"
Shiru tayi kawai, cike da rashin abin cewa. Saɓanin kallon tsoro da take mishi sai ta koma yi mishi kallon mamaki, tana kakabin maganarshi a zuciyarta.
'Tun bayan ƙara aurenshi ba daɗewa yayi mata jan ido da ƙwaƙƙwaran kashaidin kar ta sake shiga ɓangarenshi da nufin za ta gaishe shi matuƙar ba ranar girkinta bane. Ko ranar girkin nata ma ta tsaya a ɓangarenta sai ya neme ta. Shi idan yana buƙatar ganinta ko ganin fitinannun ƴaƴanta zai je har ɓangarenta ya gansu.
Watsar da tunanin tayi da sauri ganin amarya ta rufe mishi ƙofa shi kuma yana ƙoƙarin tada motar
"Alhaji daman batun kayan abincin da nayi maka ne, komai na mu ya tasamma ƙarewa, garin semovita ne kawai ya rage sai indomie na makarantar yara..."
"Kiyi tuwo kawai, karki damu da ni kiyi wanda zai ishe ki da ƴaƴanki."
Ya katse ta a gundure cike da ƙosawa a muryarsa.
Cikin ƙanƙanin lokaci idanunta ya kaɗa yayi jajur, ciccike da hawayen da take ƙoƙarin haɗiyewa take kallonshi da maɗaukakin mamaki a fuskarta.
'Sau uku kenan girki idan ya zagayo kanta sai ya ce tayi tuwo, ga yaranta ba wani son tuwon suke yi ba. Ita ba don kanta ma take buƙatar canjin ba ko don ƴaƴan, yaro idan ba ba shi da yadda zaiyi ba bai san babu ko kuma kullum ayi ta cin abu ɗaya ba canji ba.
Wani zamani ne muke ciki wanda yara suke da masifar son girkin ƙwalam da maƙwalashe. Idan ba ana ƙoƙarin ɗan samar musu da shi a gidajensu bane in ba'ayi sa'a ba sai ɗa ya fara saka ido a kayan wasu...'
Ƙarar tada motar da yayi ne ya dawo da ita cikin hayyacinta, daƙyar ta haɗiye wani dunƙulallen abu da ya tsaya mata a maƙoshi, ta buɗe baki daƙyar ta ce
"Maganar kuɗin islamiyar yara yau kwana goma kenan suna zaune a gida."
"Zan biya idan na samu kuɗi"
Amsar da ya bata kenan a taƙaice yaja motar ya fice daga gidan, bayan ya danna hon mai gadi ya wangale mishi get.
Da ido ta raka shi har motar ta ɓacewa ganinta, aka maida ƙofar gidan aka rufe.
Sautin dariyar Aliya da take ji ƙasa-ƙasa yasa ta maida hankalinta kanta, sai taga Aliyar ma ita take kallo tana mata wani irin dariya mai kama da na shaƙiyanci da rainin wayau.
Bata ce komai ba, gyaɗa kai kawai ta yi tayi ƙwafa. Taja sanyayyun ƙafafunta ta nufi ɓangarenta tana harhaɗa hanya kamar mai koyon ta-ta-ta.
Dariya mai ƙarfi Aliya ta kwashe da shi, ta haɗa hannuwa biyu ta tafa, ta kama hanci ta rangaɗa ƙaƙƙarfar guɗa mai bayyana matsanancin farin-cikin da zuciyarta take ciki. Daga ƙarshe ta buɗe murya ta fara rangaɗa waƙar Umar M Sharif mai taken
"Tsohuwa ta zuma ya barki bazai lasa ba, sabuwa ga ta, ita ta zama zaɓinsa."
Duk da kalaman waƙar sun bugi zuciyarta sam bata saurareta ba. Alƙawari ta ɗauka har a sallah take addu'a in Allah ya yarda duk baƙin cikin da za ta ƙunsa sanadiyyar Aliya baza ta taɓa tanka mata ba, tasan a doke idan dambe za suyi bugun farko za ta iya lahanta Aliyar. Idan a musayar magana ne tana da sunƙi-sunƙin zafafan kalaman da idan tace za ta faɗawa Aliyar sai ta kusa kashe kanta don baƙin-ciki. Amma ita a tsarinta dambe ko cacan baki da kishiya ba abin burgewa bane, mijin da ya haɗa su shi ne daidai da ita. Don gudun kar zucuciyarta ya kai ta ya baro ta sai ta ƙara sauri har ta ƙarasa ɓangarenta.
Tana murɗa hannun ƙofar ta shiga ciki bakinta ɗauke da siririyar sallama yaran gaba ɗaya suka taso zuwa gare ta suna tambayarta.
"Ummee! Allah yasa Abba ya baki kuɗin makarantar?"
Shiru tayi bata amsa musu ba, sai ma fuskarta da ya ƙara damalmalewa da yanayin damuwa. A kasalance ta nemi guri kan ɗaya daga cikin kujerun falon ta zauna, ta zuba tagumi da hannu bi-biyu tana bin yaran ɗaya bayan ɗaya da kallon tausayi.
"Ummee kinga mun daɗe fa muna zaune a gida bamu je islamiya ba, ana ta wuce mu a Tahfeez"
Ƴar yarinyarta ta ukun mai suna Sadiya ta faɗi haka fuskarta a kwakkwaɓe kamar za ta saka kuka.
"Kar ki damu Mamana, gobe in Allah ya yarda za kuje islamiya. Da kaina ma zan kai ku, ku daina damuwa kun ji ko?"
Ta faɗa tana kallonsu da murmushin yaƙe a fuskarta.
"To Ummee, Allah ya kaimu goben."
Suka amsa gaba ɗaya fuskarsu na bayyana matsanancin farinciki.
Ƙaramin cikinsu mai suna Abdallah ta janyo jikinta tana shafa kanshi, ta kalle shi da murmushi a fuskarta
"Babana yau me kake so in dafa muku?"
"Ummee dan Allah ki dafa mana cous-cous da vegetable souce, sai kiyi mana farfesun kifi. Irin wanda Imran yake zuwa dashi makaranta. Don Allah Ummee kiyi mana kinga fa kusan kullum tuwo muke ci."
Ya ƙarashe maganar fuskarsa na bayyana kalar tausayi.
Runtse idanunta tayi ta buɗe su a kan yaron, ta sake rungume shi sosai tana kallon fuskarsa, har lokacin bata bari murmushin yaƙen fuskarta ya ɓace ba.
"Babana, ka dinga godiya ga Allah duk abincin da ya samu a gare ka ka ji ko? Banda ƙorafin me muke dafawa kuma banda sa'ido a abincin gidan wasu."
"To Ummee"
Ya amsa da sanyin murya, idanunsa ciccike da hawaye.
Shiru tayi tana tunanin inda za ta sami kuɗi yau, sai tunani take yi amma ta rasa hanyar ɓullewa.
'Ta biya musu kuɗin makaranta, tayi cefane ko babu yawa. Ta ina za ta fara? Ga shi ba wasu wadatattun kuɗaɗe a hannunta, ɗan jarin kayan yara da take sayarwa duk sun tasamma ƙarewa. Wasu abubuwan buƙatunsu da yawa ita take siya, ga kuma siyan magungunanta da shima yake taka muhimmiyar rawa gurin ƙarar da kuɗaɗen hannunta.
Alhaji ya barta sake ne sai sadda yaga dama yake ba ta kudin da yasan bazai isa ko rabin hidimarta da ta ƴaƴanta ba.'
Sauke Abdallah tayi a jikinta ta nufi cikin ɗakin baccinta, Khairat da Aisha wacce take bi mata suka raka ta da idanu, zukatansu cike da tausayin mahaifiyarsu. Da yake sun ɗan fara wayau duk abinda Abbansu yake wa Umminsu suna ji kuma suna gani. Shi yasa basu cika mata ƙorafi akan wani abu da suke so ba, don sun san idan tana da shi tana iyakar ƙoƙarinta akan su.
Zubewa tayi a kan gado, ba zato ba tsammani wasu zafafan hawaye suka fara silalo mata. Ta kasa sabawa, har yau ta kasa sabawa da irin gaggarumin canjin da take gani daga maigidanta. A kullum sabon salon mamakinsa yake shayar da ita.
Kamar ba auren soyayya suka yi ba? A baya can kafin ya ƙara aure ko a irin munanan mafarkan da take yi bata taɓa tsammanin Alhajin zai iya juya mata baya haka ba. Lallai ta ƙara yarda duniya cike take da ababen mamaki, idan baka mutu ba baka gama ganin komai ba. Da gaske halayyar ɗan Adam mai iya canzawa ne ako wani lokaci, kawai mu roki Allah ya dauwamar da mu akan hanya madaidaiciya.
Ta tuna wasu maganganu da yake yawan faɗa mata can baya kafin ya ƙara aure
'Haba Jiddah! Haba Jiddah!! Taya za'ayi don zan ƙara aure ni Muktar in juya miki baya? ke ce fa uwar ƴaƴana, sanyin idaniyata. Wallahi Allah ko kaɗan ba ni da niyyar yin auren nan don in musguna miki. Kuma duk wata mace da zan auro bata isa ta wulakanta min ke ina gani ba. Auren nan zan yi shi ne ba don komai ba sai don raya sunnar manzon Allah SAW, don girman Allah ki yarda da ni!'
Waɗannan kaɗanne daga irin zaƙaƙan kalaman da yasha faɗa mata wancan lokacin da yake neman auren Aliya.
Haka taci gaba da tunanin daɗaɗan lokuta da kuma irin kyakkyawar rayuwar da suka shimfida a baya, zuwa yanzu da irin ƙunci da romon azaban da take sharɓa a zamantakewar aurensu.
Wasu sabbin hawayen ne suka sake ɓalle mata kamar an buɗe famfo. Zuciyarta sai wani irin zafi da tururi yake yi, a haukace tasa hannu ta janyo wani durowa da yake jikin gadonta, ta ɗauko ɗan ƙaramin leda mai ɗauke da wani farin roba ɗan ƙarami, a cikin robar wasu baƙaƙen ƙwayoyin magunguna ne da take sha idan al'amari ya ɓaci mata sosai.
Hannuwanta sai kyarma suke yi saboda sauri, daƙyar ta iya kwance ledar ta ɗauko robar, biyu ta ɗiba ta watsa a baki, ta tattauna ta haɗiye ba tare da shan ruwa ba.
Har wannan lokacin zafafan hawaye basu daina rige-rigen fitowa daga kwarmin idanuwanta ba.
Minti biyu tsakani ta miƙe tana rangaji da layi ta dannawa ƙofar ɗakin key ta kulle ta ciki. Ta ɗauko mabuɗin ɗan ƙaramin frige ɗin gefen gadonta ta buɗe ta zauna a ƙasa kan tiles, ta bubbuɗe ƙafafu kamar ƴar kaciya.
Saboda ƙwayoyin da ta riga ta haɗiye wanda a tsari ƙwara ɗaya ake sha, sai wacce take da ƙarfin jini da ƙarfin ƙwaƙwalwa ke iya shan guda ɗaya da rabi a lokaci ɗaya, amma ita yau tsananin tashin hankali da matsananciyar damuwa yasa tasha biyu a lokaci ɗaya. Daƙyar ta sha rabin kwalban magani ɗaya ƙwayoyin suka fara buga mata kai.
Da farko tsuru ta ƙurawa guri ɗaya ido kamar mai kallo ko kuma karantar wani abu, sai kuma ta miƙe tsaye a zabure tana zazzare idanu, haɗe da mammatse hannu da ƙafafu kamar tana jin fitsari. Lokaci ɗaya ta fara sambatu tana maganar halinda take ciki tana haɗawa da shirme. Sai kuma ta fara watsi da duk wani abu da idanunta yakai kai kamar sabuwar kamun hauka, duk ta farfasa hannayenta saboda yadda take ta kai ma bango naushi a haukace.
Tsawon lokaci tana a haka, daga ƙarshe wani ƙaƙƙarfan jiri ya kwasheta goshinta ya bugu da durowar jikin gado, ta yanka wani rikitaccen ihu ta zube a tsakar ɗakin tana harharba ƙafafu kamar tashin farfaɗiya, tana ta wani zazzafan gurnani da nishi kamar mai naƙuda, tsawon wani lokaci kafin wahalallen bacci ya samu nasarar ɗauketa.
Khairat da ƙannenta kuwa sunyi tsuru-tsuru a falon suna ta kuka suna kallon ƙofar ɗakinta, zukatansu cike da matsanancin tausayin mahaifiyarsu. Aisha ce tayi ƙarfin halin janyo Abdallah jikinta ta rungumeshi suna ci gaba da kuka. Ita kuwa Khairat da gudu ta kunna t.v ta sa tashar Saudi ƙur'an, tashar da ako wane lokaci karatun alƙur'ani mai girma suke yi. Zuciyarta cike da tunanin wasu maganganu da suka taɓa yi can baya ita da mahaifiyarsu a lokacin da suka ji tana makamancin irin wannan buge-bugen da iface-ifacen a cikin ɗakinta.
'Ummee jiya kin bamu tsoro, ni da su Aisha muna ta kuka muna addu'ar Allah yasa wani mummunan abu bai same ki ba. Kuma mun je ƙofar ɗakinki muna ta bubbugawa baki buɗe mana ba.'
Ta ƙarasa maganar wasu sabbin hawayen na silalowa daga idanunta, kamar a lokacin abin yake faruwa.
Sai da uwar ta janyo hannunta ta zaunar da ita gefenta, tasa hannu ta share mata hawaye. Ta fara magana da sanyin murya tana riƙe da hannunta ɗaya.
'Khairat Ya-sayyadi a islamiya ya taɓa faɗa muku akwai mugayen aljanu da suke shiga jikin mutane suna wahalar da su?'
'E ya taɓa faɗa mana. Akwai ma wata Aunty Firdausi a ajin Abubakar-siddik aljanunta da suka tashi sukai ta buga ta da jikin bango. Sai da Ya-sayyadi da sauran malamai suka taru aka yi mata karatu sannan ta koma daidai.'
'Yauwa Khairat, to ni ma aljanu nake da su. Idan kun ji ina wannan buge-bugen ku daina zuwa kusa da ƙofar kuna bubbugawa. Ki kunna karatun alƙur'ani a t.v, sai ku zauna ku dinga min addu'a Allah ya yaye min abinda yake damu na. kinji ko?'
'To Ummee. Ko idan naje islamiya in faɗawa Ya-Sayyadi su zo su yi miki karatu...'
'A'a Khairat.'
Ta katse ta da sauri
'Babanki bazai bari ba. Karki faɗa wa kowa mamanki tana da aljanu kin ji? idan kuna yimin addu'a Allah zai yaye min ya bani lafiya.'
Da wannan dalilin yasa duk sadda irin haka ya faru in dai da wutan nepa sai ta kunna karatu ta ƙure ƙara sosai, idan kuma babu wuta sai ta ɗauko alƙur'ani tana karanta inda ta iya tana hawaye. Ba ta dainawa har sai sun daina jin buge-buge da surutan mahaifiyarsu.
I just published "BABI NA HUƊU" of my story "SANADIYYA". ***
SANADIYYA
Fareeda Abdallah
4
***** *****
"Fati wai me yasa bakya magana a MƳ? (MATAN ƳANCI) bayan kuma kusan ko wane lokaci ina ganinki online?"
Saƙon da na fara cin karo da shi kenan daga Laby lokacin da na buɗe data na hau whatsapp. A fili na yamutsa fuska, kafin in amsa mata tambayarta sai na leƙa cikin group ɗin don ganin wace wainar suke toyawa a wannan lokacin.
Kamar kullum saƙonni ne da uban yawa, naja tsaki ƙasa-ƙasa ina gunguni a zuciyata.
'Ni a tsarin whatsapp chat ɗina sam bana son shiga groups barkatai, idan ma na shiga to gaskiya ban cika son group mai masifaffen surutun tsiya ba. Su kuwa Matan ƴanci gwanaye ne a gurin zuba surutu, tsawon kwana biyar da nayi a group ɗin kusan ko wane lokaci basa rasa chaptar tattaunawa.
Haka jiya da wata Aunty A'i ta kawo ƙorafin mijinta zaiyi mata kishiya bayan tsawon lokacin da suka ɗauka suna faɗi-tashi a tare, wai tana neman mafita da shawarwari da hanya mai ɓullewa.
Yinin jiya rankatakaf sun ƙarar da shi ne akan tsinewa namiji da faɗin muggan kalami akan maza, kowacce da irin mugun shawarar da ta ba ta.
Duk da ban tofa uffan ba amma duk yawan maganganun ɗari tara da sittin haka na ɓata lokaci ina bibiyarsu. A ƙarshen-ƙarshe dai naga Hajiya Ladi A lallatsa ta ce ta kirata a waya suyi magana, za ta faɗa mata sassauƙar hanyar da zai ɓulle da ita tudun mun tsira ba tare da wani damuwa ko tashin hankali ba.'
Watsar da tunanin komai nayi na fara tura mata da emoji mai nuna alamar murmushi, sai na ƙara da rubuta
"Kin san da yake ban daɗe a cikin group ɗin ba, kuma ga ni baƙauyiya ce ta fannin saurin sabo da mutane"
Sticker ta fara turo min na wata mace a kwance tana ƙyalƙyala dariya, sannan maganarta ya biyo baya
"Ke wallahi ki saki jikinki, matan group ɗinnan gaba-ɗaya bamu da matsala. Akwai kyakkyawar fahimta da tsananin ƙaunar juna a tsakaninmu, ba a damuwa da wannan an saba da ita wancan ba'a saba da ita ba. Kamar ƴan'uwa ciki ɗaya haka muke, ƙarin abin burgewa ko waccenmu gashin kanta take ci. Idan kina ji da kuɗi ne akwai mamanki a group ɗin, haka idan da iskanci ko shaye-shaye kike taƙama akwai waɗanda suka dame ki suka shanye. Na tabbatar group din zai ɗebe miki kewa shi yasa na bada lambarki aka saka ki. Don Allah ki saki jikinki. kin ji?"
"To! in Allah ya yarda."
Na amsa a ɗarare. Kafin in sake cewa komai ta sake turo min tambayar
"Yaushe za ki koma gidan Harka? Ɗazu da safe baki lura bane a Mƴ ta bada sanarwar isowar zafafa kuma sabbin kayan harka masu matuƙar aiki cikin sauri kuma a sauƙaƙe."
Gyara zama nayi cike da jin daɗin maganarta, a yanzu kam da gaske ba ƙaramin nishaɗi da ɗebe kewa magungunan da nake sha suke saka ni ba, duk wani damuwa da al'amarin Ya Hashim na tattara na watsar gefe ɗaya.
Ba kasafai nake nacin kiranshi a waya da tura mishi zafafan saƙonni na soyayya kamar da can baya ba, sai dai shi idan ya matsu ya kira ni. Ɗazu da safe har yana min ƙorafin wai na fara canzawa, na rage kula da shi, ko yayi min wani laifi ne? Dariya kawai nayi na watsar da ƙorafin ba tare da na bashi wata sahihiyar amsa na dalilin canjin nawa ba.
Su Rabi'a ma duk sunga canji, ba ko wane lokaci nake zama cikinsu muyi kallo, girki ko hira kamar yadda muka saba a baya ba. A yanzu na fi zama cikin ɗaki, a ɗakinma sai na kulle ƙofata yadda duk in za suyi min wata magana ko za su buƙaci wani abu sai sun ƙwanƙwasa ƙofa ko kuma su kirani a waya in fito in basu abinda suke so.
Nishaɗi na kawai nake yi sosai, ina jin daɗin rayuwata ba tare da wani ƙwaƙƙwaran damuwa a duniyata ba.'
Watsar da zancen zucin da nake yi nayi na tura mata tambayar
"Da gaske kike yi? Wallahi sam ban lura ba, da yake duk yau ban bibiyi chats din ba. Ina ga gobe zan leƙa gidan Hajiyar, daman kayayyakin da ta haɗa min sun tasamma ƙarewa."
Emoji mai nuna alamun mamaki ta turo min, sannan ta ƙara turo na dariya, ta lailayo wani ashar irinna gogaggun ƴan iska ta maka min. Taci gaba da magana tana dariya
"Lallai nan gaba kaɗan ba ƙaramar ƴar iska za ki zama ba Fati, kamar ba sabuwa a harkar ba? Yanzu duk waɗannan tulin kayan harkar ina kika kai su?"
Banza nayi da ita ban mayar mata da amsa ba, ba kaɗan ba na ji haushin zagin da tayi min duk da dai ita a ganinta wasa ne. Na ja wani dogon tsaki raina a ƙuntace, maimakon in cigaba da bibiyar wasu saƙonnin ma sai na sauka a whatsapp ɗin, na rufe data, na ajiye wayar a gefen gado na fice daga ɗakin zuwa gurin su Rabi'a da suke kallo a falo.
Waƙar Hamisu Breaker mai taken Jaruma da naji yana tashi a ɗakina yasa na ankara da kiran wayata da ake yi. Kafin in ce komai ko in yunƙura da nufin zuwa in ɗauki wayar Aisha ta ce
"Aunty kaman ringing ɗin wayarki nake ji, bari in ɗauko miki."
Har ta mike tsaye da nufin zuwa ɗakina na dakatar da ita.
"Aisha bari in shiga ciki in ɗauka. Ina ga Ya Hashim ne."
Na faɗa da tunanin shi ɗin ne, domin tun safe rabon da muyi waya da shi.
"Hajiya Ladi A lallatsa."
Na karanta sunan nata a fili ina murmushi, lokacin da na ɗauki wayar naga ita ke kira na. Inkiyar ƙarshen sunan nata dariya yake bani sosai, har ina ji a raina ina so in san ma'anar A lallatsa, da kuma dalilin jingina A lallatsa jikin sunanta Hajiya Ladi. Ko sunan mijinta kenan?
"Oho"
Na faɗa a fili ina dariya haɗe da ɗage kafaɗa alamun ko a jikina. Ko kafin in gama tunani da dariya har kiran farko ya tsinke, wani kiran ya sake shigowa.
Da hanzari na ɗauka ina murmushi
"Allah ya taimaki Hajiyarmu. Barka da yamma..."
"Hajiyarmu kuma Baby?"
Ta katse ni da sauri muryarta na bayyana ɗan rashin jin daɗin sunan da na kira ta da shi.
"Allah ya huci zuciyarki Suger, First love. Allah ya baki hakuri."
Na ƙarasa faɗin haka ina dariya ƙasa-ƙasa, zuciyata cike da mamakin Hajiyar.
A fili naji ta sauke wani wawan ajiyar zuciya, sannan ta ce
"Yauwa! ko kefa Babyna. Don dai baki san yadda nake tsananin sonki bane, wallahi da baki dinga ƙin yin duk abinda na umarceki ba komai tsananin wahalarsa. Kin san yadda nake jinki a raina kuwa? wallahi Babyna ban ajiye tsananin son ki nan kusa a zuciyata ba. Don ma dai kin ƙi ba ni dama in dinga kula da rayuwarki, ai wallahi da duk yadda kike jin kin kai matsayin wata babbar yarinya haka zan sake cilla matsayinki zuwa can sama ƙololuwa.
Mota sai kalar wacce kike so za ki hau, sutura sai wacce kika so kikayi ra'ayi za ki saka a lallausar fatan jikinki. Abinci sai wanda kike so zanyi oder daga ko wane tsadadden hotel in bada umarni a kawo miki har inda kike. Zan jiyar da ke mafi tsananin daɗin duniya irin wacce tunda aka haifeki baki taɓa ɗanɗana irinta ba. Don Allah ki bani haɗin kai kin ji Babyna?"
Dagwalo nayi riƙe da waya a kunnena ina saurarenta. Ban amsa mata tambayarta ba, a maimakon in amsa ma tsam nayi da raina kamar ko wane lokaci ina tunanin irin maganganun da take yawan faɗa min idan muna magana a waya ko kuma muna chat ta whatsapp.
'A ranar da aka yi adding ɗin lambata a group ɗin Mƴ yini tayi tana min wasu irin maganganu masu kama da na soyayya ta akwatin sirrina. Tun dai ina amsa mata har na tattarata na watsar da ita gefe ɗaya, na daina amsawa, domin na tsani takura a rayuwata.
Washe gari da sassafe ina buɗe Data saƙonninta kusan guda ashirin naci karo dasu, da farko wani dogon tsaki naja da nufin ƙin amsawa sai naga abinda yaja hankalina. Hotunan wata budurwa ta turo min kusan guda goma, da na kalli hotunan da kyau sai da gabana ya faɗi. Na ƙara ƙure hotunan da kallo, kamar ni ce a hoton, amma kuma ba ni bace. Domin irin suturun da suke jikin yarinyar hoton ni ko kusa bani da irinsu, ban ma taɓa saka irinsu ba.
Kuma guraren da aka yi hotunan ban taɓa taka irin guraren ba. Amma munyi tsananin kama da ta jikin hoton sai ɗan abinda baza'a rasa bane ya banbanta mu. Mamaki ne ya kama ni, har na gaza ɓoyewa na tura mata tambayar
'Wacece wannan?'
'Ƴata ce. Fatima Hamza A lallatsa. Tsananin son da nake yi mata, da tsananin kamannin da kuke yi da kuma kasancewarki takwarar Fatimata yasa naji ina tsananin sonki. Amma ita a yanzu tayi min nisa.'
Sai ta turo min da emojis na hawaye da tarwatsewar zuciya. Sannan ta sake rubuto min.
'Mahaifinta balaraben ƙasar Sudan ne, cike da rashin tausayi bayan rabuwar aurenmu ya ƙwaceta ya tafi da ita ƙasarsu.'
Daga nan sai ta bar rubuto saƙonni ta turo min Vn muryarta na rawa, kamar ma kuka take yi.
'Da wannan dalilin dalilin yasa duk inda naga mai suna Fatima sai na yi duk yadda zan yi wajen ƙulla alaƙa da ita. Sai na bi duk hanyar da zan bi wajen ganin na kyautata mata. Ba don komai nake hakan ba sai don buri da fatan nima Allah ya dubi tawa Fatimar ya haɗa ta da masu tsananin ƙaunarta aduk inda take.'
Ta ba ni tausayi, da gaske tayi matuƙar ba ni tausayi. Har ma naji a raina sam ban kyauta ba irin yadda tun jiya take ta bi na ina yanƙwana ta.
Cike da tausayinta na rubuta daɗaɗan kalamai na tura mata
'Kiyi hakuri Hajiya, Allah ya huci zuciyarki. Ina rokon Allah ya baiyana miki Fatimarki aduk inda take. Na gode da soyayyar da kike min, ni ma ina sonki.'
Sai ta turo min emoji mai kyalkyala dariyar jin daɗi da kwaso rawar shoki. Ta ƙara da cewa
'Roƙo da alfarma ɗaya nake nema a gare ki. Daga yau karki sake ce min Hajiya, ki kira ni da Suger ko kuma First love. Domin haka tawa Fatimar take kira na.
Wannan shi ne Mafari, tushe, sanadiyyar ƙara ƙullewarmu da Hajiya A lallatsa. Lura kuma da irin yadda take kawowa mata da yawa maslaha a cikin group ɗin yasa nake ta ƙara ganin girmanta, duk da dai ba a cikin mutane take bada shawarar ba...'
"Babynah kina ji na kuwa???!"
Na tsinkayi muryarta da ƙarfi ta cikin wayar da yake riƙe daf da kunne na.
"Iyee... na'am... E... ina jinki Haj...iya..."
Na amsa da firgicin dake bayyana dawowata daga nisan duniya irinta tunani.
"Tunanin me kike yi haka ina ta miki magana tsawon lokaci bakya ji na?"
"Ba komai."
Na amsa a ɗarare.
"Ko kina da damuwa ne?"
"A'a!"
"To kina bukatar wani abu ne? kamar kudi ko kayan kwalliya ko kayan masarufi? Ko ni kike buƙata?."
Ta sake tambayata muryarta a tausashe.
"A'a bana bukatar komai! Na gode da kulawarki Suger."
"Ok to shi kenan! Yanzu dai ko a wane yanayi kike ciki ina so ki ɗauki hoton kanki ki turo min. Kuma ki saki jikinki sosai yadda zan kalli duk abinda nake so. Kin ji ko?"
Kamar wata wawuya ko kuma wata wacce ake sarrafawa na ce
"To! yanzu zan turo miki."
Na katse wayar na ɗauki hoton kaina na tura mata ta whatsapp, sanye a jikina wata yaloluwar shimi ce ta shan iska.
Sai bayan na tura mata sai kuma na ja tsaki ƙasa-ƙasa ina jin haushin kaina.
'A mafiyawancin lokuta cikin kwanaki biyun nan na rasa dalilin da yasa sam bana iya yi ma Hajiya A lallatsa musu. Duk abinda ta ce inyi yi kawai nake yi ba tare da tunani ko hangen abinda zai je ya zo ba, sai bayan na aikata kuma inzo ina jin ba daɗi a raina. Ko don tsananin tausayinta da nake ji ne? Ko me take yi da hotunana ohon mata.
Duk sadda za ta kira ni sai ta buƙaci in tura mata hotona, wannan abu yana ci min tuwo a ƙwarya, kuma yana bani takaici. Amma daga yau in Allah ya yarda ko ta sake tambayata hoto bazan tura mata ba, sai inga yadda za tayi da ni.'
SANADIYYA
Fareeda Abdallah
5
Shigowar kiran Maman Khairat cikin wayata yasa na watsar da tunanin komai na amsa kiran ina murmushi.
"Amincin Allah ya tabbata a gare ki maƙwafciya ta ƙwarai..."
"Aunty ni ce Khairat. Ina yini?"
Yarinyar ta katse ni, ta gaishe ni da muryarta a sanyaye.
"Khairat lafiya dai ko? ina Mamanki?"
Na tambayeta ba tare da na amsa gaisuwar ba.
"Aunty ga ta nan tun jiya da safe ba ta da lafiya. Shi ne ta ce in kira ki idan kina da lokaci kizo ki kaita asibiti."
"Ok! ok! Gani nan zuwa yanzun nan."
Hankalina a tashe na katse wayar. Saboda gudun ɓata lokaci ga shi yamma tayi ko wanka ban tsaya yi ba. Kaya na canza na ɗauki makullin motata da jaka na fice daga gidan bayan na sanar da su Rabi'a inda na nufa.
Ganin halin da take ciki hankalina yayi mugun tashi. Goshinta ya kumbura yayi suntum, ga hannuwanta da wasu sassan jikinta duk ta ji ciwo. Da na lura dakyau ma sai naga har ɗingishi take yi. Daƙyar take iya magana, tsayuwa idan ya wuce na second goma sai ta tafi luuuu za ta kifa da sauri nake tallabeta.
Sai da na gama balbale su Khairat da masifar barinta da suka yi a wannan halin tsawon lokaci basu zo sun faɗa min ba. Sannan na kira Aysha nace su dafa wadataccen abinci mai sauƙi a kawo ma su Khairat, saboda Abdallah ya ce min tun jiya da safe har yammacin yau ruwan lipton kawai suke sha da indomie jiƙaƙƙe a barbaɗa mai da maggi, shi ma Khairat ce take haɗa musu. Daƙyar na iya canza mata kaya na kama ta muka tafi zuwa asibiti.
Har mun kusa isa asibitin Dialogue saboda shi ne babban asibiti mafi kusa da mu naji muryar Maman Khairat tana cewa.
"Ba asibiti ba, Chemis za ki kaini Fati."
Ta faɗa daƙyar tana ciccije baki, sai kuma ta mayar da idanu ta lumshe, ta sake gyara kwanciyarta akan kujerar motar.
"Chemis dai Maman Khairat?"
Na tambayeta da mamaki. Sai ta ɗaga kai alamar eh! Ban ja da nisa ba sai na juya akalar motar zuwa wani babban Chemis da na taɓa zuwa na sai ma Aisha maganin ciwon ciki.
Maman Khairat ta bani tausayi, ta sha wuya sosai gurin wanke ciwon hannayenta da sa magani. Da aka zo mulmula goshinta kuwa har ƙwallar tausayinta sai da nayi. Wash-wash kawai take iya furtawa haɗe da jan nishi da gurnanin azaba, hawaye kuwa wasu na koran wasu a fuskarta.
Sai da ya murza gurin sosai sannan ya ɗauko ƙanƙarar pure water yayi ta mannawa a gurin, tsawon lokaci yana manna ƙanƙarar sannan ya ɗauko wani magani ya shafa a gurin. Cikin hukuncin Allah da na kalle ta sai naga sosai kumburin ya ragu. Yayi mata allura ya haɗa mana magunguna na sallameshi muka taho gida, bayan ya faɗa mana ta dinga yawaita danna gurin da ƙanƙara sai ta shafa maganin da ya bata. Hakan shi zai sa jinin da ya kume yayi saurin bajewa.
Ko kafin mu isa gida har ta fara bacci, hakan yasa ban ajiye motata a waje ba. Hon nayi ma mai gadinsu ya buɗe get na shiga da motar har cikin gidan, sannan na tashe ta ina riƙe da hannunta muka nufi ɓangarenta.
Tun shiga da motata cikin gidan na ganshi tsaye a ƙofar falonshi, fuskarsa a murtuke yake watsa mana wani mugun kallo. Ni kuwa ban nuna na san yana gurin ba har na kaita ɓangarenta na kwantar da ita, nayi ma su Khairat sai da safe na fice daga gidan. A lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar isha'i a masallatan da suke kusa da mu.
Washe gari da sassafe muka shiga kicin da taimakon su Aisha na shirya break fast mai rai da lafiya na aikawa su Khairat. Duk tunanina za su tafi islamiya da safe, tunda ranar ta kama asabar ce. Na faɗawa Rabi'a kuma ta tabbatar kafin ta dawo ta gyarawa Maman khairat ɓangarenta, ta share ko ina tayi mopping, sannan ta wanke duk abinda yake buƙatar wankewa.
Ban shiga gidan don in ƙara duba jikinta ba sai ƙarfe goma da rabi na safe. Yadda na ganta na ji daɗi sosai, jikinta da sauƙi sai ɗan abinda baza'a rasa ba. Da mamaki na dinga kallon yaran da suke zagaye da ita, har na gaza yin shiru na ce
"Khairat me yasa baku je islamiya ba?"
Tsalam Aisha ta ce
"Aunty ai yau kwananmu goma sha biyu bamu je makaranta ba. Babanmu ya ƙi biya mana kuɗin makaranta, ita kuma Mamanmu ba ta da kuɗi..."
Wani mugun bugu da Maman khairat ta kai ma bakin yarinyar yasa ta fasa kuka ba tare da ta ƙarasa maganar ba. Da sauri na ja yarinyar jikina ina rarrashinta, fuskata na bayyana rashin jin daɗin abinda Maman Khairat ɗin tayi. Raina a ɓace na fara magana ina kallonta da yanayi mare daɗi
"Ashe bamu zama ɗaya kamar yadda kike faɗi ba, tunda don an faɗa min wani ɓangare daga cikin damuwarki har zaki iya fasa bakin yarinyar da ba ita ta kar zomon ba."
"Ba haka bane Fatima, kiyi hakuri. Wallahi ba haka bane. Idan ban kwaɓa mata ba yau tayi a gabanki gobe ban san a gaban waɗanda za tayi irin wannan maganar ba."
"Uhmmm!"
Kawai na iya furtawa na sauke yarinyar a jikina na kama hanyar ficewa daga falon.
"Haba Fatima, kiyi haƙuri mana don Allah."
"Ba fushi nayi ba fa. Yanzu zan dawo."
Na amsa a tsaitsaye ina ci gaba da tafiya.
Ko da na fita kai tsaye islamiyarsu Khairat na tafi na biya musu kuɗin makarantar. Duk zangon karatu dubu biyar ne ko wane ɗalibi ɗaya, dubu ashirin na biya na karɓi shaidar biya na fice daga makarantar. Har da zan tafi kasuwa inyi musu siyayyar kayan abinci sai kuma naga dacewar in ba ta kuɗin, ita za ta fini sanin abinda suke buƙata. Don haka na koma gida kai tsaye daga nan.
Bayan na nutsu na huta na kira Ya Hashim, a taƙaice na kora mishi bayanin duk irin halin da Maman khairat take ciki ita da ƴaƴanta. Ba don komai na faɗa mishi ba sai don sanin halinshi na tausayi da taimako ga duk wanda yake buƙatar taimakon. Sosai ya tausaya mata sannan ya jinjina min irin ƙoƙarin da nayi wurin taimaka musu. Ya ƙara da cewa idan ya dawo zai mayar min da dubu ashirin ɗin da na biya musu kuɗin makaranta, a yanzu kuma in bata dubu talatin tayi cefane. Har mun gama magana nayi mishi godiya na katse wayar sai ya sake kirana
"Baby kar fa ki ce mata ni ne na taimaka mata. Kawai ki bata kudin a madadin ke ce kika bata."
"To Hubby. Allah ya ƙarawa dukiya albarka."
Nayi masa addu'ar cikin farin ciki da ƙauna.
Da yake ina da lambar account ɗin Maman Khairat tun wani lokaci can baya da na sayi kayan yara set huɗu na kai ma ƴar'uwar Ya Hashim. Dubu hamsin na tura mata, daman nayi niyyar bata dubu ashirin sai kuma Ya Hashim ya ce in tura mata dubu talatin. Sai da na tabbatar kuɗin sun isa sannan na tura mata gajeren saƙo
"Gobe su Khairat su shirya su tafi islamiya, an biya kuɗin makarantar. Ga kuɗi nan babu yawa ki ƙara kiyi cefane. Zan shigo da yamma."
Don ma kar ta kira ni ta ishe ni da kalaman godiya kawai sai na kashe wayata. Na tashi na gabatar da sallar azahar, na tsakuri abinci sama-sama na haye gado da nufin yin bacci. Bayan na gargaɗi su Rabi'a duk tsawon lokacin da zan ɗauka ina bacci kar wacce ta tashe ni. Na sharara musu ƙaryar jiya ban samu isasshen bacci ba saboda tunani da damuwar halin da Maman Khairat take ciki.
Ledar magungunan ɗauko, dafe kai nayi da naga saura kwalabe biyu kawai suka rage min. Yau ya kamata in leƙa gidan Harka amma ban samu nutsuwar zama ba, yanzu kuma rana tayi ga gajiya na nuƙurƙusata. Da yamma kuma ina so in ƙara leƙa Maman khairat. Amma na sha alwashin gobe ina tashi da safe bayan wanka da karin kumallo abu na gaba da zanyi shi ne zuwa gidan Harka.
Da yake yanzu na san daɗin magungunan sam bana iya bacci mai cike da nutsuwa idan ba maganin nasha ba. A dole ba yadda raina yaso ba na shanye kwalba ɗaya a yanzu, da nufin da daddare zan shanye ɗayan. Tsawon wasu mintuna da na ɗauka ina tunani banji na fara yawo a daddaɗar duniyar ƴanci da yalwar ƙamsasan furanni ba yasa dole na buɗe ɗayan kwalbar na kafa a bakina. Ina sha ina tunanin dole da yamma komai ƙurewar lokaci in ziyarci gidan Hajiya, idan ba haka ba aiki kwaɓe min zaiyi, idan ban kora ba tunani da kewa da damuwa za suyi min sallama. Na san daƙyar idan zan iya bacci, ko zan yi baccinma a wahale ne mai cike da mafarke-mafarke. Idan na kora kayan harka kuwa bacci nake yi lafiyar Allah.
A ƴan kwanakinnan na riga na saba shan kwalabe uku, huɗu a lokaci ɗaya. Shi yasa yanzu da nasha kwalba biyu nake jin har yanzu ban kai inda nake son isa ba. Ni ba mai bacci ba ni ba ido biyu ba, ƙwaƙwalwata ta tsaya cak daga duk wani tunani ko wani damuwa na al'amarin duniyar da muke ciki. Iska-iska mai daɗi nake ji yana huda kafofin gashin jikina duk da ban kunna a.c ko fanka a ɗakin ba. A haka dai har wani sararren bacci yayi awon gaba da ni.
***** *****
"Gaskiya yarinyar nan tayi ɗari bisa ɗari. Kuma ta dace da irin yarinyar da na daɗe ina bada kwangilar a nemo min irinta. Amma har yanzu me kika tsaya jira A lallatsa? Yau tsawon kwana bakwai kenan fa da kika nuna min ita. Idan ta gagara a miƙa sunanta mana."
Wani dariya mai haɗe da shewa ta saki, hannu ta miƙa ta karɓi wayarta ta ƙurawa hoton idanu, fuskarta cike fal da murmushi. Sai kuma tasa hannu ta matso da hoton sosai daidai saitin ƙirjinta. Lashe laɓɓa ta fara yi kamar wata tsohuwar mayya, tana ƙure wani sashe na saman ƙirjinta da ya bayyana ta saman rigar baccin jikinta da kallo.
Tsawon lokaci tana kallon hoton sannan ta fara magana, har lokacin idanunta bai bar kan abinda take kallo ba.
"Raliya kina yawan manta tsarin soyayyata. Duk soyayyar da zaki gina tsakaninki da yarinya matuƙar ba true love bane duk shirmen banza ne, aikin malaman nan suna ci amma na wani ƙayyadadden lokaci ne mai iyaka, matuƙar ba kina yi kina sabunta aiki bane.
Ni fa a tsarina miƙa sunan wacce nake so gurin Malam don ya janyo min hankalinta shi ne mataki na ƙarshe da nake bi, bayan na gwada duk wata dabara ta jan hankali, kyauta, haɗe da zaƙaƙan kalaman soyayya irin waɗanda duk taurin zuciyar mace dole ta rusuna ta amshi tayin soyayyata.
Yarinyar nan da kike gani a harka irin tamu sabuwa ce dal a leda, kafin in sallamata ga kowa ni da kaina nake so in fara ɓare ta a leda, in kwankwaɗi romon ni'imar jikinta in ƙoshi. Daga baya kuma in mayar da ita kadarar da za ta janyo min manyan kuɗaɗe gurin ire-irenki da waɗanda suka ninka ki abin duniya.
Burina mai girma ne akan Fatima, shi yasa kika ga ina ta bin ta sannu-sannu, mataki-mataki kamar ɓarawo da mai kaya. Duk da kullum da matsanancin ƙishin ruwanta nake kwana nake yini alƙawari ne bazan taɓa yin garaje a kanta ba. Tunaninta ƙuƙumi ne har yanzu ƙaramin sani take da, duk yadda nake ta mata hannunka mai sanda ta kasa fuskantar dalilin da yasa nake mata wasu abubuwan.
Kin san wahalar da na sha kafin in kawo wannan lokacin da ita? Ke gaskiya Fatima ta ciri tuta, da gaske ina tsananin son yarinyar, son da na daɗe banyi ma wata ƴa mace irinshi ba."
Ta kai baki ta sumbaci fuskar Fatima a hoto, sannan ta ajiye wayar ta tattara hankalinta gaba ɗaya kan aminiyarta Hajiya Raliya.
"Matsanancin taurin kai ne da Baby Fatima, amma duk ta yadda tazo min haka nake bi da ita. Domin ciki da bai ɗinta a tafin hannuna take. Ɗaya daga cikin dalilan da yasa kika ga har yanzu ina jan ƙafa a kanta tana da wanda ya tsaya mata ne, daga irin motar da take hawa da yadda take wasa da kuɗi za ki san ba ƙaramar yarinya bace. Duk da iyayen yarinyar talakawa ne amma tana auren matashin mai arziki, sosai ya riƙe mata kan maciji tana ta wasa da jelar yadda take so.
Da wannan dalilin yasa ko kusa ban yi gigin kwaɗaita mata kuɗi don in janyo hankalinta ba. Inda mijin ya rage ta kawai rashin zamanshi a kusa da ita, yau yana wancan garin gobe yana wancan ƙasar. A tamfatsetsen gidan da ya gina ya aje ta daga ita sai mai gadi da ƙannenta mata biyu. Ki gane idan naso har gidanta zan iya zuwa in gusar mata da hankali, inyi yadda nake so da ita akan gadon aurenta amma sam bazan yi haka ba. Idan naso har gidanta zan tura a ɗauko min ita salin-alin inyi yadda naga dama da ita, amma duk ba haka nake buƙata ba.
So nake da kanta ta kawo kanta gare ni, so nake in gudanar da komai da yaddarta da amincewarta. Babban kuskuren da mijinta ya tafka shi ne yadda ya bari damuwarsa har yayi sanadiyyar fara zuwanta gidan Hajiya harka. To ki rubuta ki ajiye, tunda har ta ziyarci gidan Babban harka, ta afko group ɗin Mƴ, tabbas za ta afka hannun Hajiya A lallatsa. Na ɗana mata manyan tarkuna waɗanda duk wayonta baza ta iya tsallakewa ba.
Kafin in samu ta fara saurarata sai da na miƙa hotunanta gurin Rabency ya canza mata shiga da wani ɓangare na kamanninta da photo shop. Na tura mata hotunan a matsayin ƴata ce ta jikin hoton kuma itama sunanta Fatima."
Nan taba Raliya labarin duk irin matakan da ta bi har ta samu ako wane lokaci Fatima na saurarenta a waya ko a whatsapp.
Tsananin mamaki da al'ajabi ne ya kama Raliya, duk da ta san A lallatsan zalamammiya ce gurin iya bin duk wani hanyar da ta san zata bi don samun abinda take so bata taɓa tsammanin zata iya shirya wannan rikitaccen ƙarya da yaudarar ba. Da ta rasa ta cewa kawai sai ta ɗaga manyan yatsunta biyu ta tana yi ma A lallatsa jinjina mai tafe da zazzafan kirarin da suke mata aduk lokacin da tayi wani abu da ya jijjiga tunaninsu.
"Hajiya A lallatsa.
Sarauniyar alfasha.
Kaicon duk yarinyar da ta shiga tarkonki. Ba ki da kyau! A lallatsa ba ki da kyau"
Taƙarasa kirarin tana ƙyalƙyala dariya.
"Uhmmm! Kina wasa da ni Raliya. Ke kin san tunda raina ya biya sai na ɗanɗana na ji ya take, waɗannan manyan kayan da take ɗauke da su lokuta da dama har mafarki nake yi wai gani ina damuƙa da tumurmusasu yadda nake so. Idan ban lallatsa ba ai ƙwarnafi na bazai kwanta ba"
Ta ƙarasa maganar tana lumshe idanu, a zuciyarta take hasaso ƙirar jikin Fatima da har yau a hoto kawai take gani.
Kamar wacce aka tsikara zumbur ta miƙe tsaye. Ta ɗauki wayarta ta riƙe a hannu, jakarta kuma ta rataya a kafaɗa, tana gyara yalolon mayafin jikinta ta kalli Raliya da fuska mai cike da fara'a.
"Da gaskiyar masu iya magana da suka ce tattaunawa da musayar ra'ayi tsakanin mutum biyu na ƙara buɗe ƙwaƙwalwar mai basira daga cikinsu. Kinga a yanzu ɗan hirar nan da muka yi har na sake samun wani zazzafan tarko da zan ɗana ma Fatima. Yaushe ne ma nake ce miki zanyi bikin murnar ƙara shekarar haihuwata?"
"Sati mai zuwa laraba idan mai duka ya kaimu."
"To a wannan ranar tabbas za ki ga Fatima gurin taron bikin murnar ƙara shekarar haihuwata. A wannan ranar zan tallata hajarta a tsakanin manyan Hajiyoyi masu duniya a tafin hannu. Kuma a wannan ranar zan buɗewa Fatima zallar gaskiyar abinda yasa nake bibiyarta da soyayya. A wannan ranar zan ba ta dama mai kama da tilastawa ta ƙarshe, dole ta karɓi buƙatata ko in ɓullo mata ta bayan gida.
Hmmm! Ke in Allah ya so ni da rahama ma a wannan muhimmiyar ranar zan kwankwaɗi romon ni'imarta da na daɗe ina burin kwankwaɗa. Zan jiyar da ita matsanancin daɗin da mijinta bai taɓa jiyar da ita ba. Za ta fahimci wata zazzaƙar harka da bata taɓa ɗanɗanawa ba duk kasancewarta da mijin aurenta. Ke dai Raliya Allah ya kaimu wannan rana... abubuwa da yawa za su faru."
Ta ƙarasa maganar tana dariya.
"Hmmm! A lallatsa na ƙara yarda ke hatsabibiya ce, ba ki da kyau! Allah ya kaimu wannan rana, na san za mu raƙashe mu raƙarƙashe da zafafan ƴanmata sabbin jini irin waɗanda kika saba rabarwa aduk wata hidima da ta shafe ki. Don Allah ni dai roƙo na idan kin kashe ƙishin ruwanki a jikin Fatima kar ki manta da ni. Kin san dai kafin wata ta fara nuna sha'awarta ga yarinyar ni na fara fito da maitata a fili, don Allah in zama ta biyu gurin mayar da mugun miyau."
Ta ƙarasa maganar tana dariya.
"Kar ki damu, ai ke ta hannun dama ta ce. Ba ki da matsala. Bari in ƙarasa gida, wancan yanƙwanannen tsohon yana nan. Duk da ba wani abu yake tsinana min ba ina gudun ƙanƙanan maganganunshi. Kin san shegen mita gare shi kamar cin ƙwan makauniya."
"Au! Wai kina nufin har yau Malam Saleh yana zuwa gidanki? na zaci tun kwanaki kika ce za ki tsinke duk wata ƙaddararriyar igiya da take ƙulle tsakaninki da shi?"
Raliya tayi tambayar tana kame da haɓa, alamun mamaki.
"Hmmm!"
Ta ja nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, fuskarta na bayyana matsanancin takaicin da zuciyarta take ciki. Tayi wani ƙaƙƙarfar ƙwafa tana cije gefen bakinta na dama.
"Bari ke dai Raliya. Wallahi kamar Tsohuwa Dada (Mahaifiyarta) ta san abinda nake niyyar aikatawa, sai ga ta kwatsam a gida na rana ita jiya. Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, wai tana da labarin duk irin tsiyar da nake tsulawa Saleh. Tayi min furuci mai kama da baki kamar dai abinda Ɗanbaba(mahaifinta) ya faɗa min kafin ya tunkuyi burji. Wai ko bayan ranta na raba aure na da Saleh da gangar bata yafe min ba.
Da wannan dalilin yasa na watsar da tunanin datse ƙaddararrun igiyoyin aurennan, amma na sha alwashin babu abinda zan fasa daga cikin shaƙatawata har sai ya gaji ya sallameni da kanshi. Ba dai ni ce basa so in nemi sakin ba? to shi da kan shi zai sake ni ba duka babu zagi ba baƙar magana, gashin ƙuma kaɗai ya ishe shi. A sannu-sannu zan soya mishi ɗanyar gyaɗa a tafin hannu har sai na samu abinda nake so."
"To Allah ya kyauta! Amma gara dai ki ƙara zage dantse, ni inda za kiji shawarata ma ko ƴar ɓoyon harka da kike yi idan yana gidanki wallahi ki daina. Na tabbata idan yaga abinda kike yi a take zai sallameki shi kuma ya ƙarata da ciwon zuciya, idan ma anyi sa'a bai haɗiye zuciya ya mutu a take ba. Me ke cikin auren wannan zamanin in banda wahala da zaman ƙunci haɗe da rashin ƴanci? Ba da ni ba, haka kawai ina zaune lafiya ace in tashi in tsaya? Taɓ! Ga ƴanmata nan masu cike da kayayyakin marmari kala-kala. Me zanyi da wani miji gayyar wulaƙanci da iya shege? Ina da inda zan samu gamsuwa sosai inyi yadda nake so fiye da namiji ɗan babansa."
"Ke dai bari. Nima Komai ya kusa zuwa ƙarshe, na san ƙwaƙƙwaran matakin da zan ɗauka. Bari dai in wuce, yamma tana ƙara yi, sai kin ji ni kawai."
Da haka suka rabu ta raka ta har tsakar gida inda ta ajiye motarta. Suna ta ɗaga ma juna hannu har ta fice daga gidan.
SANADIYYA
Fareeda Abdallah
6
***** *****
"Kin ga wannan?"
Ta sake nuna min wani farin leda mai ɗauke da tulin fararen ƙwayoyi, fuskarta cike da murmushi.
Gyaɗa kai kawai na iya yi kaman ƙadangaruwa, alamar na gani. Na ma kasa magana, lallai da gaskiyar bahaushe da yake cewa wani garin ya fi gaban kunu. Haka wata tambayar ta fi ƙarfin amsawa da baki sai dai a gyaɗa kai.
"To waɗannan ƙwayoyin a harka irin ta mu su ake kira Sha fara kiga aljan. Sabbin shigowa ne. Kin gansu nan? Duk ƙwarin ƙwaƙwalwarki idan kina son kanki da lafiya rabi za ki ɓalla ki sha a lokaci ɗaya. Shi kanshi rabin da kika sha irin caji da nishaɗin da zai cilla ki a ciki duk shaye-shayenki na tabbata baki taɓa shan mai ƙarfi da saurin saka cajin wannan ba. Wata kyakkyawar duniya sabuwa zai jefa ki mai cike da kayayyakin more rayuwa da korayen ganyayyaki, kin san koren ganye akwai saka nishaɗi da annashuwa a zuciya.
Sai mace mai tsananin ƙarfi da ƙwarin ƙwaƙwalwa wacce ta daɗe a cikin shaye-shaye za ta iya shanye ƙwaya ɗaya a lokaci ɗaya. Sharaɗinshi duk wacce tasha fiye da ɗaya idan ba wani iko da hukunci haɗe da tsarewa ta Allah ba kin san me zai kasance ƙarshenta?"
"A'a Hajiya."
Na amsa a wahalce, cike da nauyin baki.
Su Laby da Nucy da sauran matan da suke zaune a falon kuwa mai za suyi ba dariya ba. Da alamu ganin irin ruɗewar da na shiga ba ƙaramin dariya na saka su ba.
Hajiya mai babbar harka kuwa ɗan murmushi kawai tayi, ta ci gaba da magana a hankali yadda ni kaɗai nake iya jinta sosai. Kamar dai ba ta so sauran matan da suke zazzaune a falon su ji me take cewa
"Duk wacce ta yi gigin shan ƙwaya fiye da ɗaya kuma a lokaci ɗaya ƙarshenta Hauka tuburan!"
Zaro ido nayi a tsorace, kayan cikina suka tattaru suka cure a guri ɗaya. Marata ta cika dam da fitsari, sai motse-motse nake yi kamar wacce tayi ƙarya a gaban sarki.
Ba tare da wani damuwa da halin da nake ciki ba ta ci gaba da nuna min kayayyakin. Ta sake ɗauko wani ƙullin farin leda mai cike taf da baƙaƙen ƙwayoyi ta nuno min
"Duniya duka lebur!"
Sai kawai na fara waige-waige kamar mai neman wani abu, ina kallon falon da kuma kayayyakin cikin falon. Wai ni a nufina da gajeren tunanina zan ga duniyar ta zama lebur.
A wannan karon ita da kanta Hajiyar ta fara ɓaɓɓaka dariya tana kallona
"Sunan waɗannan ƙwayoyin kenan fa. Duniya duka lebur! Shi bai kai sha fara kiga aljan ƙarfi ba. Za ki iya shan guda ɗaya lafiyar Allah. Duniyar ce dai za ki ganta ta zame miki fili fetal babu kowa sai ke kaɗai, ki zaga duk inda kike so ba ruwanki da wata damuwa a wannan duniya. Sai damuwa ya kai matuƙar damuwa mace za ta sha guda biyu, amma fa za ta iya shiga gaggarumin hatsarin da sai dai Allah ya tsare. Waɗannan kuwa"
Ta nuna sauran tarkacen magungunan da hannunta, da alamun ta gaji da yi min bayaninsu ɗaya bayan ɗaya.
"A zaune cikin falon nan da kike ganina wata babbar dakta ce a fannin magungunan kwaranye damuwa da wanke ƙwaƙwalen mata masu damuwa. Ƙwayoyi ne dani kala daban-daban, kama daga Valium tabs, D5 tabs, Diazepam tabs, Exol 5 tabs, Tramadol tabs, Pemoline tabs da sauran tarkacen ƙwayoyi. Duk dai na ɗebe duk wata hargitsattsiyar damuwa da take yiwa ƙwaƙwalwar ɗan Adam katutu, musamman ƴaƴa mata, ta ɓangarensu harkata tafi ƙarfi.
A fannin magunguna na ruwa ire-iren waɗanda na haɗa miki wancan karon kin ga irinsu, Emzolyn expectorant, Tutolin expectorant, Codeine syrup, Benalyn syrup, Pacaline syrup. Ke har alluran kawar da damuwa daga ƙwaƙwalwa ina yi, ga ni da, Pento injection, Legatine injection da sauransu da yawa waɗanda ba sai na faɗa miki sunayensu ba.
Hmmm! Na san kina ta mamakin me yasa nake yi miki waɗannan dogayen bayanan ko? da kuma bayanin wasu ƙwayoyin har ina faɗa miki illar da za su iya yi miki idan kin kauce ƙa'ida gurin sha ko?"
A wannan lokacin bata jira na amsa da baki ko in gyaɗa kai ta ci gaba da cewa.
"A tsarin kasuwanci irin nawa sabuwar costomer ce kawai idan tazo gidannan zan haɗa mata kayayyakin da za su gusar da damuwarta cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da na faɗa mata illolinsu ba. Amma idan kika fara zama ƴar gida a harkar komai duk wani ƙwaya ko magani ko alluran da zan baki sai na ankarar dake illolinsa.
Saboda ko da kin kauce ƙa'ida mummunan abu ya biyo baya to babu ruwana, daman tun farko na gargaɗeki. Kin ganni nan har lauyoyi gare ni masu tsaya min tsayin daka gurin ƙwatar min haƙƙi da ƴanci ga duk wacce ta nimi tayar min da zaune tsaye. Da gaske ban ɗauki sana'ata da wasa ba, ni da kike ganina komai idan zanyi mai lasisi nake yi.
Yanzu dai tunda na ankarar da ke duk abinda ya kamata kayan nawa zan haɗa miki? Nawa kike tafe da su? Gara inyi in sallameki ga sauran costomomi nan suna jira na."
Nannauyar ajiyar zuciya na ja na sauke, a hankali na zame tagumin da nayi, na ƙara gyara zama akan kujera. Abinka da zuciya da ba ta da ƙashi kuma wacce linzamin shaiɗan ya fara zame wa ragama duk yadda ta ankarar da ni ƙarfin ƙwayar Duniya duka lebur, da Sha fara kiga aljan sai naji ina burin in sha su don tantance yadda suke a jiki.
"Hajiya yau dai ban zo da cash na kuɗi ba, transfer zanyi miki. Allah yasa dai za ki yarda da hakan?"
"Karki damu, ni fa sana'ata sassauƙa ce. Kuɗi ko kayan kuɗi ko transfer na kuɗi duk babu wadda ba na karɓa. Ga lambar akawun ɗina"
Nan take ta fara karanto min ni kuma ina shigarwa a cikin wayata. Dubu talatin na tura mata a take, sai da na tabbatar sun shiga har itama banki sun sanar da ita shigar kuɗin sannan na ce
"Hajiya a haɗa min da Sha fara kiga aljan da duniya duka lebur."
"A'a to yarinya da alama za ki ƙaro kuɗi. Wannan ƙwayar na sha fara kiga aljan duk ɗaya dubu da ɗari biyar ne. Ita kuma duniya duka lebur duk guda dubu ɗaya. Guda nawa zan zuba miki? Kuma kin ce kina so a haɗa miki kayan da za ki kwana biyu kina amfani da su ba tare da kin waiwayo gidannan ba."
Ba tare da wani ɗar ko damuwa ba na ƙara tura mata dubu ashirin. Dai-dai gwargwado ina da kuɗi, tunda kullum Ya Hashim cikin tura min kuɗi yake, duk tunaninshi su kaɗai ne manyan matsaloli da damuwata.
Ringis ta haɗa min kayayyaki a leda. Cike da farinciki da annashuwa nayi sallama da su Nucy da sauran matan falon nai ficewata. Ina gani suka raka ni da wani irin kallo da na rasa gane ma'ana ko inda ya dosa. Ni dai ko a jikina, abinda ke gaba na kawai nake yi.
Sai da suka ji tashin motarta da ficewarta daga gidan sannan suka kwashe da dariya, cikin dariyar Laby ta fara magana tana kallon Hajiya.
"Gaskiya Hajiya ke ƙarshe ce. Kawai ganin yarinya da kuɗi yasa duk kin ninnika mata kuɗin kaya saboda tsananin zalama da haɗama."
"A'a dakata ! ke kinga laifina? Kina ganin yadda take walle kuɗi bisa ga dukkan alamu bata san zafinsu ba. Ni kuwa daman tun da daɗewa ina kan tsarin farashin sayarda kaya ga masu kuɗi daban! farashin sayarwa da talakawa daban! Kuma ko ba haka bama ai riba halas ne a musulunci, ko da kuwa zai ninka uwar kuɗi ya sake ninninkawa."
Ta ƙarashe maganar tana fari da idanu da watsa hannaye kamar ƙaramar yarinya. Su kuwa duk sai suka sake kwashewa da dariya suna faɗin
"E...! Wannan ma gaskiya ne Harka."
Daga gidan Hajiya kai tsaye gida na nufa, amma kafin in shiga gida sai na fara shiga gidan Maman Khairat. Don in ƙara duba jikinta.
Ina shiga gaba ɗaya yaran suka taho da gudu suka rungumeni, suna ta godiya akan kuɗin makarantar da na biya musu. A wasance na harari Maman Khairat, ita kuwa sai tayi murmushi kawai.
Sai da suka natsa sannan muka shige ɗakinta, gefen gado na nema na zauna ina faɗin
"Wash Allah na..."
"Da alamun kin kwaso gajiya, halan ba daga gida kike ba?"
Ta tambayeni cike da kulawa, bayan ta zauna a kusa da ni.
"Kamar kin sani wallahi. Na gaji tuɓus! in banda fitar ta zama kamar dole bazanyi ta ba."
"Ayyaa... Sannu! Allah ya huta gajiya."
Kafin in amsa ta ci gaba da magana muryarta na rawa
"Ke Fatima irin wannan hidima da ɗawainiya haka? Me yasa za ki wahalar da kanki..."
"Don Allah don Annabi ki bar maganar nan. Haba! Idan ita za ki ci gaba da yi ni wallahi sai inyi tafiyata. Yanzu dai ya jikinki? Duk da na ga alamun da sauƙi sosai sai dai rashin ƙarfin jiki, ga goshinki ma kaɗan ya rage ya ƙarasa bajewa."
"Jiki fa Alhamdulillahi! na ji sauƙi sosai sai ɗan abinda ba za'a rasa ba. Amma fa na sha wuya."
Ta ƙarasa faɗin haka tana dariya. Kafin inyi magana ta ci gaba da cewa
"Baki tambayeni dalilin buguwar tawa ba?"
Alamar mamaki ne ya bayyana a fuskata, na kalleta sosai sannan na ce
"Ni fa duk a tsammanina Baban Khairat ne ya taɓa lafiyarki..."
"Ina...!"
Ta katse ni da sauri.
"Wane shi ya ce zai dake ni ai sai dai muyi doki in doka. Wani magani Duniya duka lebur nayi ma shan hauka, da gaske na wahala iya wahala. Ban taɓa tsammanin zan dawo daidai cikin ƙanƙanin lokaci haka ba. Ke dai Fatima Allah ya biya ki, Allah kuma yabar zumunci."
"Ameen."
Na amsa ina dariya.
'A zuciyata nake tunanin ashe dai Harka da gaske take yi? lallai zan kiyaye kar in lahanta kaina a banza.'
Ban daɗe a gidan ba nayi mata sallama na shige gida. Ina shiga na iske abinda ya ɗaga min hankali kuma ya nemi dagula min lissafi. Ya Hashim ne na tarar ya dawo, kwance shame-shame a cikin bedroom ɗinsa yana bacci.
Rashin ganin su Rabi'a yasa na gane har sun tattara kayayyakinsu sun wuce gida. Da saurin gaske na shige ɗakina nayi ma magungunan mummunan ɓoye duk da bana tunanin zai gani, saboda yana daɗewa bai shigo ɗakina ba. Kuma shi ba mutum bane mai yawan bin ƙwaƙƙwafi da bincike.
A gurguje na watsa ruwa, nayi sallah, sai na faɗa kicin don in haɗa mishi sassauƙar abinci saboda ƙurewar lokaci.
Ina aiki a kicin ni kaɗai nake ƙunƙuni a zuciyata.
'Dawowarshi a daidai wannan lokacin kamar rushewar duk wasu tsare-tsare nawa ne. Bazai taɓa barina in sake ni kaɗai a ɗakina kamar yadda nake so ba'
Na sake jan tsaki a karo na barkatai, sai kuma na tattara laifin gaba-ɗaya na ɗora akan Aunty Rabi, ƴar'uwar Ya Hashim.
'Jiya da yamma ta kawo mana ziyara, bata bar gidana ba sai bayan isha'i. Wannan dalilin ya hana in ziyarci gidan Hajiya harka saboda ƙurewar lokaci. Sai yau da rana na je gidan.
Shi kuma Ya Hashim da abin haushi kawai ya wani dawo ba tare da ya sanar da ni ba. Duk da bani da ikon hana shi dawowa amma ai da na tsara yadda abubuwan za suci gaba da tafiya min yadda nake so. A yanzu kam kaina duk ya kulle, bisa ga dukkan alamu ƙulluna yana gaf da yin ruwa.'
Banji motsin shigowarsa kicin ɗin ba, sai saukan tausasan hannayenshi naji a jikina, yasa hannu daga bayana ya riƙe ni ya zagayo da hannayen saitin cikina, sai ya kwantar da kanshi a kafaɗuna yayi shiru.
Lumshe idanu nayi ina shaƙan daddaɗan ƙamshin turaren jikinshi wanda ya alamta min shi ne. Sanin wanda ya riƙe ni shi yasa ko kaɗan ban tsorata ba. Sannu-sannu nake ta sauke ajiyar zuciya ina jin wani baƙon al'amari yana ratsa duk wani lungu da saƙo na gaɓoɓin jikina.
I just published "BABI NA BAKWAI" of my story "SANADIYYA". ***
"Tunanin me kike yi?"
Ya tambayeni muryarsa a tausashe.
"Ba komai! Barka da yamma. Ka tashi? Ya hanya?"
Bai amsa ni ba, a madadin amsa ma sai ya birkito ni na juyo muna kallon juna ido cikin ido. Kasa jurewa nayi na saukar da ƙwayoyin idanuwana ƙasa, saboda wasu irin saƙonni da yake ta aika min da su ta cikin idanunsa masu kama da na mage.
"Faɗa min gaskiya Fatinah! (Da yake wani lokacin haka yake kira na) Ban sanki da faɗin ba dai-dai ba. Don Allah faɗa min, tunanin me kike yi? Ummm? Tun ɗazu ina ta sallama baki ji ba. Damuwar ta kuɗi ce?"
Ya tambaye ni fuskarsa na bayyana yanayin damuwa.
"A'a! Wallahi ba ni da matsalar kuɗi Hubby! Kawai tunanin rayuwa ce. Don Allah kar ka wani damu kanka da tunanin da nake yi."
"To shi kenan! Na ƙyale ki tunda baza ki faɗa min ba."
Sake ni yayi ya juya kamar zai fice daga kicin ɗin, alamun yayi fushi.
Da sassarfa na rungumeshi ta baya ina sake bashi haƙuri, cike da shagwaɓa a muryata na ƙirƙiro ƙarya na kantara mishi
"Wallahi Matarnan maƙwafciyarmu da na baka labari jiya ce take bani tausayi. Daga gidanta nake ɗazu. Na kai mata kuɗin da kace in bata ne. Idan kaga yadda suka baibayeni ita da yaranta suna murna da godiya ga hawaye abin zaiyi matukar ba ka tausayi. Tunaninta ne kawai ya tsaya min a rai. A gefe guda kuma ina ƙara godewa Allah bisa ga ni'imar da nake ciki."
"To ai ba damuwa da tunani za ki tayi ba Baby, addu'a za kiyi mata. Kin ji?"
Da sauri na gyaɗa kai, alamar na gamsu. Kafin ya sake cewa komai na koma na rage ƙarfin gas ɗin da nake girki, na ja hannunshi muka nufi hanyar fita daga kicin ɗin ina ci gaba da magana haɗe da zuba mishi shagwaɓa
"Hubby dawowa ba sanarwa ko? Ba haka ake yi ba Allah ba haka ake yi ba. Yanzu dai muje in taya ka kayi wanka, sai in baka abinci. Ka ga da ka sanar min tun jiya yau za ku dawo tun safe zan ƙarar da awoyi ne gurin haɗa maka daddaɗan abincin da sai kunnenka ya kusa tsinkewa don daɗi. Yanzu kuwa sai dai kayi haƙuri da jagwalgwalon da ya samu."
"Ai ko minti biyu kika yi a kicin in dai da niyyar girki ne na yarda da ƙwarewarki Fatinah, ko me kika girka min zan ci ina santi. Batun dawowa ba sanarwa kuma wai nayi nufin in baki mamaki ne, ashe dai banyi gwaninta ba?"
Ya ƙarashe maganar yana kyaɓe fuska, kamar wani ƙaramin yaro.
Hakan da yayi sai ya saka ni dariya sosai, ina dariyar na amsa da
"A'a ka yi gwaninta mana, na ji daɗi. Kuma na yi farinciki da dawowar mijina abin ƙaunata."
Sai da na ƙara wanke banɗakin duk da ba wani datti yayi ba, sannan na haɗa mishi ruwan wanka. Kakkaɓe ɗakin nayi na kunna turaren wuta kafin ya fito, na fitar mishi da ƙananun kaya na shan iska na ajiye a gefen gado. Jin kiraye-kirayen sallar magriba yasa na fice daga ɗakin na nufi kicin, ganin girkina ya kammala sai na kwashe komai a kula na jera akan teburin cin abincin da yake falo. Na faɗa wanka a gurguje na haɗa da ɗauro alwala.
Bayan mun gama komai ya ɗauki tsarabar su Hajiya ya buƙaci inyi mishi rakiya ya kai musu, ban wani so zuwa ba saboda gajiyar da nayi. Amma ko a fuska ban nuna mishi ba, na canza ƙananun kayan jikina na yafa mayafi muka tafi.
Ko da muka isa bamu wani daɗe a gidan ba ya ba su tsarabarsu muka nufi gidanmu. Can ma tsarabarsu ya ba su muka kama hanyar komawa gida. A hanya yake tambayata
"Akwai abinda za mu buƙata a gida yanzu kafin gobe da safe mu shiga kasuwa?"
A dai-dai za mu gitta wani babban shagon provition store a hanyarmu ta komawa gida yayi maganar.
"Babu komai. Akwai komai da za'a buƙata. Ko gobenma ba sai an shiga kasuwa ba, ƴan ƙananun abubuwan da bamu da su tun rannan na ba su Rabi'a suka siyo komai."
"Ok ba laifi."
Daga haka bai sake cewa komai ba, ni kuma sai na mayar da hankali kan wayata da nake daddannawa har muka isa gida.
***** *****
"Ki kwanta kiyi barcinki Baby, kaina mugun ciwo yake min, ga kuma gajiyar da ke nuƙurƙusar jikina. Kuma kin san na faɗa miki gobe sammakon tafiya Abuja zan yi. Akwai saƙo mai muhimmanci da Oga ya bani zan kaiwa Hajiya Asma'u. Kinga da waɗannan dalilan bai kamata in hana kaina samun wadataccen bacci a daren yau ba."
Ya faɗa da murya mai bayyana iyakar gaskiyarsa kenan, har yana jan bargo daga saman cikinsa zuwa ƙirjinsa.
Kamar wata sakarya haka nayi zaune a tsakiyar gadon ina kallonshi, a hankali sannu-sannu nake jin wani dunƙulallen baƙin-ciki da damuwar da ya daɗe da bajewa a zuciyata saboda magungunan da nake sha yana sake taso min sabo fil a zuciyata. Nan take idanuna suka cicciko da hawaye, shar hawayen masu zafi suka zubo a saman kumatuna.
'Wannan wace iriyar rayuwa ce muke ciki ni da Ya Hashim? A ce a matsayinshi na mijin aurena da Allah ya halasta min bazai taɓa tsayawa ya sauke nauyin haƙƙina na aure da yake kan shi ba? duk da kuwa ya san yanayin halittata? A cikin jerin halitta ina cikin mata masu yawan sha'awa, da wannan dalilin yasa kafin inyi aure nake yin azumi irin na Annabi Dauda, yau ina azumi gobe ina hutu. Azumin shi yake ɗebe min kewa daga tayar da sha'awa da kuma duk wani abu da zai iya ɗauke min hankali.
Tunda nayi aure sai nayi tsammanin matsalata ta zo ƙarshe, amma ashe na yi kuskuren tunani. Wasa farin girki! A watan farko na aurenmu mun ƙarar da shi ne wajen tsananin kulawa da tarairayar juna, da gwadawa juna wata iriyar zazzafar soyayya mai matuƙar tsayawa a zuciya.
A lokacin har ji nake anya akwai wata mace da ta kai ni sa'ar gidan miji kuwa? A bayan tsananin kulawar da yake gwada min ga dukiya da ya sakar min ina yadda nake so, ban nemi komai na rasa ba. Abinci da abin sha sai irin wanda naso nake girkawa.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya mayar da ni wata babbar yarinya a cikin ƙawaye da ƴan'uwana. Da gaskiyar masu iya magana da suka ce idan mace ta ci, ta sha, ta ƙoshi da kwanciyar hankali abu na gaba da za ta buƙata shi ne lafiyayyen namiji a kusa da ita.
Ni da na kai wannan matakin sai nawa mijin ya fara yawan tafiye-tafiye cikin gida Nigeria da ƙasashen ƙetare. Ba ya cikakken sati biyu a gida ba tare da yayi wata tafiyar ba.
Sai ya zama duk wannan kulawa da tattalin da yake min yana sauke nauyin haƙƙina da yake wuyarsa a hankali ya janye. Kuɗi da kayan abinci da manyan suturu ne dai har lokacin bai daina sakar min ba, sai ma ninninkawa da yayi. Mota ba ta wata uku a hannuna zai canza min da wacce ta fita, ƴan kunnen gwal, sarƙa, zobba da awarwaro kai har sarƙar gwal na sakawa a ƙafa ina da ita.
Iyayena kuwa ya ruɗa su da manyan kyaututtuka na kuɗaɗe da kayan masarufi, kafin kayan abinci su ƙare zai sake aikawa da wasu. Da wannan dalilin yasa ako wane lokaci zancensu ɗaya ne.
"Fatima idan kina son farincikinmu ki rungumi mijinki kiyi masa biyayya sau da ƙafa."
Tun ina jurewa wajen mayar da komai ba komai ba, ina bin shi da yadda yake so, har dai na gaji, hakurina ya tasamma kai wa ƙarshe. Duk wannan gatan da yake min ba su nake buƙata ba, na fi son ganin mijina a kusa da ni saboda yanayin halittata. A wani dare na yanke hukuncin yi mishi ƙorafi, amma a cikin yanayin jirwaye mai kama da wanka saboda kunya da nauyin maganar. Amsar da ya bani yasa sai da na shige bayi na sha kukana sannan na koma na kwanta.
"Fatima me kika nema kika rasa a gidannan? Ta ya ma zaki ce ko wane lokaci kinfi so in dinga zama a kusa da ke? idan na zauna wa zai nemo mana abinda za muci tunda zara ba ya barin dami? idan kewa da zaman kaɗaici ne ya fara isarki gobe kafin in wuce zan ɗauko miki Aisha da Rabi'a su dinga taya ki zama idan bana nan."
Wannan shi ne sila kuma sanadin fara zama na da su Rabi'a.
Da tafiya tayi tafiya naga kullum al'amarin ƙara taɓarɓarewa yake yi, wani lokacin har sai ya dawo ya koma wata mu'amala ta aure bata shiga tsakanina da shi ba yasa nayi ƙumajin tarar mahaifiyata da zancen abinda yake damuna. Ita ma dai kunya bai barni nayi mata bayanin a fili ba, amma nayi iya ƙoƙarina har ta gane inda na dosa.
A lokacin ta nuna ta fahimce ni, kuma ta tausaya min. Amma da shigowar mahaifina ta tunkare shi da maganar rufe idanu yayi ya dinga masifa, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Daga ƙarshe ya fatattakeni gidana bayan yayi min wankin babban bargo tare da faɗin ni butulu ce na ƙi godewa ni'imar da Allah yayi min.
Haka na tattara na koma gida da kukana, tare da alwashin bazan sake kai ƙorafin damuwata gidanmu ba, idan mutuwa zanyi gara in mutu.
Da tafiya ta ci gaba da tafiya ba rashin ci ba rashin sha sai na fara ramewa, ga yawan zama shiru-shiru ina tunanin damuwata. Ɗai-ɗai daren da bazan kulle kaina a ɗaki inyi kuka ba idan abin ya motsa min. Zuciya da mugun saƙe-saƙe babu irin saƙar da bata yimin akan hanyar da zan bi gurin magance damuwata. Shi kuwa Ya Hashim babu abinda ya dame shi, neman kuɗinshi kawai ya saka a gaba, lokaci bayan lokaci yana tura min manyan kuɗaɗe cikin akawun ɗina duk don wai kada in nemi wani abu in rasa idan baya nan. Abinda ya kasa ganewa duk waɗannan ba su ne a gaba na ba.
A karo na biyu da kukana na sake kai ƙorafi gidanmu, a wannan lokacin kai tsaye gurin mahaifina na tunkara duk da ina da tabbacin bazan sha da daɗi ba. Ilai kuwa, guzuri na farko da ya fara bani kyawawan maruka ne a kumatuna guda biyu. Sannan ya rufe ni da zagi kamar ba shi ya haifeni ba, ina kuka ina majina na fice daga gidan. Mahaifiyata uffan bata ce ba saboda tsoron mahaifina.
A daren wannan ranar zuciyata tayi min saƙar in nemi wani namijin ya ɗebe min kewa yafi sau shurin masaki. Daƙyar na yakice tunanin na watsar na ɗaure alwala na fara salloli ina yi ina kuka haɗe da kaiwa Ubangiji roƙona da fatan ya share min hawaye. A wannan daren na ɗauki wayata na turawa Yaya Hashim dogon saƙo mai ɗauke da bayanin halin da nake ciki da irin ɗaukar alhakina da yake yi, duk da ya san ina cikin jerin mata masu sha'awa.
Na ƙara da sanar da shi idan bai gyara ba wallahi zan ɗauki matakin da bazai yiwa kowa daɗi ba tsakanin ni da shi.
Sai da saƙon ya kwana ya wuni sannan na sami gajeren martaninshi kamar haka
"Kiyi haƙuri Fatee, zan gyara in Allah ya yarda."
Kamar yadda yayi alƙawari bayan dawowarshi ya gyara na kwana biyu, nan da nan walwalata ta fara dawowa. Na fara ciccike inda nayi rama saboda kwanciyar hankalin da na fara samu.
Daga baya kuma sai al'amarin ya ƙara taɓarɓarewa har ma fiye da da can baya, domin sai ya dawo ya koma ya sake dawowa har ya koma bai neme ni don ya biya min buƙatata ba. Zura mishi idanu kawai nayi, na yi alƙawarin bin shi da duk yadda yazo min.
Amma fa acan ƙarƙashin zuciyata ina nan da ƙudurin nemawa kai na mafita da hanyar da zai ɓulle da ni. Wani mummunan jarabta da Allah yayi min kuma a yanzu sam ba na iya yin azumi kamar lokacin da nake gida, ko na ɗauka daƙyar nake iya kai azumin saboda tsananin wahala da rashin nutsuwa da kwanciyar hankali.
A karo na ƙarshe na sake tunkarar mahaifiyata kai tsaye da bayanin damuwar da nake ciki. Na kuma faɗa mata duk irin mummunan halin da na faɗa suna da kamasho tunda dai na faɗa musu ga damuwata kuma suna da iko amma sun ƙi ko da yunƙurin ɗaukar mataki.
Hankalinta ya tashi matuƙa, ta kuma ɗaukar min alƙawarin za tayi iya ƙoƙarinta gurin ganar da mahaifina don ayi wa tufkar hanci gudun kada in faɗa wani mummunan hali. Ta rarrasheni da tausasan kalamai ta ce in koma gida in jirayi kiran wayarta.
Da murna na koma gida, saboda ina tunanin komai ya kusa zuwa ƙarshe, ganin yadda ta ɗauki maganar da muhimmanci kuma tana ta faɗa nasan dole ma Abbana ya saurareta. A wannan ranar na yi bacci cike da nutsuwa da farin-ciki.
Washe gari da farkawata da asuba kiran wayarta da ya shigo yasa naji gabana ya faɗi, sanyin da jikina yayi yasa na fara taraddadi da addu'ar Allah yasa ba ƙin amincewa Abbana yayi ba.
Ashe kuwa hakanne, sai da kiran ya tsinke nabi bayan kiran da gaggawa kafin ta sake kira. Yadda naji muryarta sanyi-sanyi tana min doguwar nasihar da sam ba fahimtarta nake yi ba yasa jikina ya ƙara sanyi. Daga ƙarshe naji ta ce Abbana ya sha alwashin duk ranar da na kaso aurena da Hashim tabbas shi ma zai datse igiyoyin auren da ke tsakaninshi da ita. Ta rufe da cewar in rufa mata asiri kar inyi sanadin da za ta fada a rayuwar zawarci bayan shekarunta talatin da biyar da yin aure.
Ba tare da sallama ba ta ajiye wayar ni ma daga ɓangarena na ajiye da saukar wani zazzafan hawaye a idanuna.
Washe gari da yamma na shiga gidan makwafciyata Maman khairat, fuskata babu walwala. Duk wani mai hankali idan ya kalleni zai fahimci danƙararriyar damuwa ce a ƙarƙashin zuciyata.
Maman Khairat ta damu sosai, duk yadda taso in faɗa mata abinda ke damuna na ƙi. Daga ƙarshe ta kwatanta min gidan Hajiya harka da cewar idan naje da kuɗi za ta haɗa min magungunan da za su taimaka min gurin gusar da damuwata cikin ƙanƙanin lokaci...'
"Fatima! Tunanin me kike yi haka?"
Ya tambayeni bayan ya girgiza kafaɗuna da ƙarfi don dawo da ni daga nisan da nayi a duniyar tunani.
Nannauyar ajiyar zuciya na sauke, nasa bayan hannu na sharce hawayen idanuna. Na kalleshi kawai, daƙyar na iya buɗe baki na ce
"Ba komai."
Na sa hannu a kasalance na ɗauki wayata dake ajiye can ƙarshen gadon, na zura ƙafafu ƙasa da nufin sauka daga kan gadon.
"Ina za ki je?"
Ya tambayeni da alamun mamaki a fuskarsa.
Sai da na kalle shi sosai sannan na tamke fuskata
"Ɗakina zan tafi. Tunda kwanana a nan ɗakin ba shi da wani amfani."
Na ƙarasa maganar ƙasa-ƙasa, amma duk da haka ina da tabbacin ya ji abinda na ce, saboda kunnenshi kamar na miciji ne wajen jin magana.
Bai yi yunƙurin dakatar da ni ba, sai da yaga da gaske ficewar zan yi sannan ya fara kiran sunana da alamun dakatarwa
"Fatima! Fatima!! Kar ki fita daga ɗakinnan"
Ban amsa kiran ba, haka kuma ban tsaya kamar yadda ya umarceni ba har sai da na kai ɗakina. Ina shiga na kulle ƙofar na danna key, zuciyata cike da addu'ar Allah yasa kar ya biyo ni.
Da yake ɗan halas ne sai bai biyo ni ba, hakan ya ƙara hassala zuciyata, wani ƙululu mai zafi da ya tokare ni a maƙoshi yasa na fashe da wani ƙaƙƙarfar kuka. Tsawon lokaci ina kuka sannan na ɗauko ledan magunguna, ina kuka na haɗiye ƙwayar duniya duka lebur guda ɗaya, na kora da kwalban magunguna biyu. Irin yadda kaina ya fara ɗaukan wani zazzafan caji da ban taɓa shiga yanayin ba yasa komai na wannan duniyan ya ɓace daga ƙwaƙwalwa da idanuwa na, na faɗa wani sabuwar duniya da ban taɓa tsintar kaina a ciki ba, daga haka dai ban sake sanin abinda ya biyo baya ba.
Ban farka ba sai ƙarfe goma sha ɗaya da minti uku na safiyar washe gari, a gurguje nayi wanka da sallah sannan na buɗe ƙofar ɗakina.
Ban tarar da Ya Hasheem a falon ba, sai ƴar guntuwar wasiƙa da yabar min a gaban tv mai ɗauke da sallahun ya wuce abuja.
Tsarabata tana nan cikin ɗakinsa a babbar jaka da yake ajiye a gefen gadonsa, akwai kuɗi a ƙarƙashin filonsa in ɗauka in ƙaro cefanen gida. Kwana biyu zaiyi idan kuma ya daɗe bazai wuce kwanaki uku ba.
Wani dogon tsaki naja cike da takaicin wasiƙar, na cukwuikwuiyeta nayi cilli da ita a tsakar falon ina masifa ni kaɗai.
"Tsarabarka da kuɗinka na banza da wofi? idan kaga dama ma kar Allah yasa ka dawo."
Na faɗa a fili, sannan na wuce kicin da sauri, saboda wata masifaffiyar yunwa da nake ji tana sakuɗar kayan cikina kamar wacce aka yiwa yasa.
Wani abu da na ƙara fahimta dangane da magungunan da nake sha shi ne, aduk lokacin da na sha na bugu nayi bacci. Duk irin ƙoshin da nayi kafin insha maganin zan farka ne cikina wasai, a daddafe nake yin wanka in gabatar da sallah. Abu na gaba da zanyi kuwa neman abinda zan ci ne.
Bayan na gama komai na gyara gidan ɗaiɗai nayi akan gado na buɗe data ina shige da fice a kafafen sada zumunta. Zuciyata gwargwado ina cikin nishaɗi da farin-ciki. Damuwar jiya duk na nemeta na rasa sai ɗan abinda baza'a rasa ba. A wannan karon sam bani da niyyar ɗauko su Aisha don su tayani zama, na ƙudurce a raina zan zauna ni kaɗai kawai, tunda ba daɗewa zaiyi ba.
I just published "BABI NA TAKWAS" of my story "SANADIYYA". ***
SANADIYYA
Fareeda Abdallah
8
Bayan haka ma a yanzu da na fara nisa cikin shan magungunana zamansu a gidana zai kasance ƙarin takura da sa'ido a gare ni ne. Tun da dukkansu ba yara bane, duk wani canji da wani muhimmin motsi nawa idanunsu yana kaina.
Kawai sai na yanke shawarar da kaina dai bazan sake zuwa in ɗauko su ba, idan kuma sunzo bazan kore su ba.
Wani kyakkyawan katin gayyata da ya shigo group ɗin MƳ ne ya ɗauki hankalina. Da yake data ta a auto take, duk wani hoto ko vidio, ko vn da zai shigo kafin in danna buɗewa zai buɗe da kanshi. Shi yasa lokuta da dama a maimakon in zauna zaman chat ɓata lokaci nake yi gurin duba hotuna da vidion da suka zauna a wayata, na ban dariya inyi dariya, na takaici inja tsaki, na tausayi in tausaya, na wa'azi in ƙaru.
Sai da na gama ƙarewa katin kallo sannan na fara karantawa, ashe katin gayyata zuwa gurin gaggarumin bikin da Hajiya A lallatsa ta shirya don murnar ƙarin shekarar haihuwarta ne.
"Uhmmm! Masu kuɗi suna sha'aninsu."
Nayi maganar a fili ina dariya.
"Tabbas abincin wani gubar wani. Da ni ce ina kamar Hajiya A lallatsa tsofai-tsofai da ni banga wani abin shirya biki don na ƙara shekara ɗaya cikin shekaruna ba. Amma da yake daidan wani karkacewar wani, inji masu iya magana"
Ganin ita ta tura katin da kanta sai na danne saƙon nayi tagging da nufin inyi mata reply ta akwatin sirrinta. Sai kawai na ci karo da katin gayyatan ta tura min ta akwatin sirrina. A ƙasan katin ta ƙara da cewa
"Babyna da fatan za ki samu halarta? Domin kina ɗaya daga cikin manya-manyan baƙin da za su halarci gurin."
"Na gode Hajiya. In Allah ya yarda zan zo."
Har na tura sai kuma na ƙara da tambayarta
"Ranar larabar nan mai zuwa ko?"
Sai da ta turo emoji mai nuna alamar rawar murna, ta ƙara da turo mai nuna alamar godiya da fuska cike da zanen love. Ta sake turo min emoji mai nuna alamar sumba.
Dariya kawai nayi ban mayar mata da amsa ba, sai ma na fice daga akwatin sirrinta na koma cikin group ina karanta saƙonnin fatan alkhairin da ake tayi wa babban admin Hajiya Ladi A lallatsa. Kowa da irin kalaman da yake yi a bayan fatan alkhairin, daga masu cewa
"Allah ya kaimu. Lallai za mu raƙashe. Wannan babban taro baza'ayi ba mu ba. Ga bikin zuwa ga zanin ɗaurawa."
Da dai sauran maganganu kala-kala masu bayyana murna da tsananin goyon bayan da ake bata akan duk wani abu da tasa a gaba. Ganin shigowar wani saƙon daga Hajiya A lallatsa yasa na fita a group ɗin na koma akwatin sirri don ganin abinda saƙon ya ƙunsa.
"Babyna duk manyan baƙin da za su halarci gurin bikin birthday ɗin akwai ɗinkin anko na musamman da na ɗinkawa ko waccenku. Don haka gobe ke ma zan aiko miki da naki, ko za ki faɗa min size ɗin inner wears ɗinki?"
Wani banbaraƙwai na ji maganganun nata, ba ma kamar ƙarshen jimlar maganganunta da ta dire da tambayar size ɗin inner, ina ruwanta da size ɗina. Na ja tsaki kawai, nan take na ƙudurce a raina ko ankon ma bazan karɓa ba.
"Na gode Hajiya. Ki barshi kawai, gaskiya ba na anko. Kuma ba na saka duk wani kaya da na tabbatar anko ne muka yi da wasu. Ina da wadatattun kayan da zan saka inzo gurin taron ba sai na karɓi komai daga hannunki ba. Idan kinji ba daɗi don Allah kiyi haƙuri."
Ina ganin saƙon ya shiga sai na kashe data, na sauka a online ɗin don ma kada ta sake min wasu maganganun da za su karyar min da zuciya har in amshi kayanta. Tunda ita gwana ce wajen iya sarrafa harshe da tafi da mutum duk yadda yakai da zillewa.
Saboda kada ta kirani a waya ma sai na saka wayar a jirgi (Aeroplane mode). Na shige banɗaki nayi alwala na gabatar da sallar azahar. Ina zaune akan dadduma na janyo wayar na kunna kallon wani series da na daɗe da saukewa a youtube amma ban zauna na kalla ba.
Kallon ne ya ɗauke min hankali har zuwa ƙarfe uku na rana, sama-sama nake jin yunwa. Ko da na shiga kicin sai na rasa abinda zan girka mai sauƙi, kawai sai na ɗauko ragowar kazar da take ajiye cikin frige na ɗunɗuma a oven, na haɗa lipton na koma falo ina cin naman ina korawa da ruwan lipton har na ƙoshi.
***** *****
"Babyna har yanzu ba ki iso ba? Manyan baƙi duk sun gama hallara, ke kaɗai ake jira. Yanzu kina ina ne?"
"Hajiya ga ni nan isowa. Go slow ne ya riƙe ni a hanya. Kiyi haƙuri, komai ƙurewar lokaci zan iso in Allah ya yarda."
Na ƙarasa maganar tare da danna hon wa motar da take gabana don dai ta ƙara yarda da gaske ina tsakiyar go-slow ne.
"To ni dai don Allah kiyi sauri, wallahi an dakatar da komai saboda rashin zuwan ke kaɗai kawai."
Tana gama faɗin haka bata jira cewa ta ba ta katse wayar.
Ni ma aje wayar nayi na ci gaba da ƙoƙarin kutsawa ta duk wani ɗan sarari da na samu don dai in samu in isa akan lokaci. Ina ta ƙara janjanin fitina da damu haɗe da naci irin na Hajiya A lallatsa.
'Cikin kwanaki ukun da suka wuce da gangar na danna lambar wayarta a black list don kawai kar ta dinga samu na a waya. A whatsapp kuwa tana ganina online sai ta turo saƙo sau talatin ban buɗe ba. Idan ta dame ni da kiran whatsapp vidio call ba na ɗauka, voice call ma ba na ɗauka.
Sai naga masifaffen nacin ya yi yawa sai in buɗe saƙonin in amsa ɗaya biyu in ƙyale ta. Duk yadda taso taji size ɗi na don ta aiko min da ɗinkin anko na ƙi faɗa mata, kuma na ce ko ta aiko bazan karɓa ba. Sai da na rantse mata da girman Allah idan har sai nasa ɗinkin ankon da za ta min sannan zan samu shiga gurin taron to bazan zo ba.
Da wannan kurarin da na yi na samu ta shafa min lafiya da maganar anko, har zuwa yau da ya kasance ranar taron bikin murnar ƙara shekarar sannan na cire lambarta a black list yadda idan ta kira za ta same ni.
A jikin katin gayyatan ƙarfe huɗu na yamma suka rubuta za'a fara taron, babu african time. Amma tun sha biyun rana ta addabe ni da kiran waya, sai kawai na kashe wayar, bayan nayi sallar azahar na shige kicin na shirya ma Ya Hashim lafiyayyen abinci saboda ina tunanin yau zai dawo.
Ban samu nutsuwan gama duk ayyukan da gyaran kicin ɗinba sai ƙarfe huɗu saura minti goma. A lokacin ne na kunna wayata na faɗa wanka. Ina wanka na dinga jiyo kira yana shigo min akai-akai, tsaki nayi don nasan bazai wuce ita ba. Ilai kuwa ita ce, misscall takwas kafin in fito wanka. Ko kafin in danna bin bayan kiran wani kiran ya sake shigowa, da sauri na ɗaga na fara magana tun kafin ta isheni da karaɗi
Hajiya kiyi haƙuri. Mijina yayi tafiya ne kuma ina saka ran dawowarshi a yau, da wannan dalilin yasa na tsaya na shirya mishi abinci. Yanzu na fito wanka sallah zanyi in shirya, ga ni nan tahowa komai ƙurewar lokaci.
Ko kafin ta ce komai na katse wayar na zura hijabi na tayar da sallah. Shiryawa nayi a gurguje na saka wata doguwar riga ta ƴar dubai da tabi jikina ta lafe, na naɗe siririn gyalen rigar a kaina, sosai rigar ta fito min da shape ɗin jikina.
Na kalli kaina na sake kallo, ni kaina na san nayi kyau sosai. Kuma tunanin cikin taron mata zan shiga ban ɗauki matsewar rigar a wata matsala ba. Na ɗauki makullin mota, wayata, gift ɗin da na siyawa Hajiyar jiya da na shiga kasuwa. A guje na figi motar na harba kan titi ganin har huɗu da rabi da minti biyu.
Tunda ta kira na ce mata ina hanya ba ta cikakken minti biyar bata sake kira don jin ina nake ba, har Allah yasa na isa gurin lafiya.'
Guri na nema a harabar gurin da ke cike da manyan motocin da kallonsu kawai zai bayyana maka masu tsada ne. Gyaɗa kai nayi, a raina na ƙara tabbatar da lallai Hajiya Ladi A lallatsa ba ƙaramar mace ba ce.
Ko da naje zan shiga cikin gurin wasu ƴan sanda mata su uku da suke gadin bakin ƙofar hana ni shiga suka yi, wai sai na nuna ƙaramin katin da ke nuna lallai an san da zuwa na, an amince in shiga, gayyata ta aka yi ba gayyar soɗi nazo ba.
Mamaki da haushi ne suka ƙume ni lokaci ɗaya, na koma jikin motata na tsaya sannan na kira Hajiyar a waya don sanar da ita halin da ake ciki.
"Na iso! Amma sun hana ni shiga. Da yake ma naga yamma tayi bari in koma kawai, mijina yana hanya. Ina miki fatan alkhairi da tsawon kwana. Allah ya ƙara miki shekaru masu albarka."
Ban jira cewarta ba na katse wayar. Har na buɗe ƙofar motar zan shigo na hango tahowarta da sassarfa, wasu mata su biyar suna biye da ita. Da farko waige waige ta fara yi tana neman inda nake, ko da ta hango ni sai ta ƙara sauri don ta iske ni.
Ƙura mata idon da nayi yasa na hango yadda take ta gurɗewa da takalmi mai tsinin da ta saka a ƙafarta saboda saurin da take yi.
Dariya ne ya kama ni, fuskewa na yi ban yi dariyar ba, sai na saki murmushi kawai. Hajiya A lallatsa an tsufa amma duk hanyar da za'a ɓoye tsufannan bin shi ake yi sawu da ƙafa. Wani kwaɓaɓɓen kwalliya da aka tsantsara mata a fuskarta wanda ya fito da zallar muni da tsufanta shi ya ƙara faɗaɗa murmushina har ta ƙaraso kusa da ni bai ɓace daga fuskata ba.
Ita ma tun daga nesa murmushin take ta dallare ni da shi, ko da ta ƙaraso kusa da ni sai na lura da wani irin kallo da take min wanda na rasa gane ma'anarshi. Ko kafin in ankara ta rungumeni a jikinta tana shafa tudun mazaunai na.
A tsorace na janye jikina na raɓe kusa da motata ina dariyar yaƙe. Sai rarraba idanu nake yi a tsakaninsu.
Ko ta lura da halin da na shiga ne kawai sai naga ta fara wata sakaryar dariya, tana magana tana far-far da idanu tana kallona ƙasa-ƙasa
"Yi haƙuri murnar ganinki ne Baby Fatima. Kin san na daɗe ina burin haɗuwa dake a fili ba'a hoto ba."
Sai kuma ta juya gurin ƙawayenta da suke ta bina da wani fitinannen kallo ta ce
"Ita ce wacce nake faɗa muku! To ya kuka ganta?"
"Wallahi ta yi sosai ma, har ma ta wuce yadda muka ganta a hoto."
A tare suka haɗa baki gurin faɗin haka.
Sai wata ƙatuwar Hajiya a cikinsu ta ƙaraso kusa da ni ta kamo hannuna na dama ta ƙurawa tafin idanu
"Wannan da gani kankana ce, kunsan kuma uwar ruwa, da an latsa ta za ta bulbulo. Wani ƙarin armashin shi ne komai ya ji ya cika dam-dam! Sosai za'a sha zazzaƙar zuma da ita."
Gabana ne ya yanke ya faɗi, da sauri kuma cike da tsorata na ƙwace hannuna. Basu bani damar wani magana ko tunani ba Hajiya A lallatsa taja hannuna muka shige ciki wajen taron, zugwui-zugwui na bita a baya jikina babu inda ba ya rawa. Tsabar sanyin jiki kamar wacce aka zarewa laka.
"Barka da zuwa... Lale marhabin! Muna yiwa Gimbiya Fatee barka da shigowa wannan guri mai albarka. Wannan ƴar ƙaramar tarba ce gare ki Fatima El-bashir."
Karaɗin maganganun da ya cika kunnena kenan daga cikin bututun lasifikar da mc take magana da shi.
Wani abu da ya ƙara ba ni mamaki kuma ya ɗaure min kai rankatakaf mazauna gurinnan mata ne, hatta mc da take gabatar da shirye-shiryen mace ce.
Da ganin irin matan da suke zaune a gurin za'a gane taro ne na manyan mata jiga-jigai waɗanda duniya take damawa da su, da ƙasaitattun mata ƴan siyasa, masu hannu da shuni waɗanda ake kiran sunansu suna amsawa.
Duk macen da idanuwana suka sauka a kanta sai inga gwala-gwalai ne zube a jikinta, wuya, hannu da ƙafa.
Can inda ake zaunar da manyan baƙi Hajiya A lallatsa ta kai ni ta zaunar da ni a kujerar da ke kusa da na ta, sai naga ta matsa can gefe guda wasu gungun mata sun yanyameta suna magana ƙasa-ƙasa. Abinda ya ƙara tsurar da ni hankalina ya ƙara tashi yadda lokaci bayan lokaci suke juyowa su kalleni, sannan suyi murmushi, sai su ci gaba da maganar da suke yi.
Tunda na zauna cikin matan da ke kusa da ni duk wacce idanuna suka yi kuskuren sauka a kanta sai inga ta haske ni da tattausan murmushi. Idan ma ba gizo idanuna suke min ba sai inga kamar har signal suke min, tamkar saurayi ya ga budurwar da ya ƙyasa.
Tsoro da ruɗanin da nake ciki yasa kaina ya kulle gam, na ma rasa wane irin tunani ya kamata inyi. Kawai sai na fara janyo duk addu'ar da tazo zuciyata ina roƙon Allah ya tsare ni daga dukkan sharri, Allah ya maidani gida lafiya. Sai a lokacin naji da ma na sani da ban zo ba.
Ban lura da isowar Hajiya A lallatsa kusa da ni ba sai saukar hannunta naji akan cinyata tana shafawa a hankali. Kamar wacce wutan lantarki ya ja haka nayi firgigit tare da matse ƙafafuna guri ɗaya, sai zare ido nake yi kamar ƙwai a ledar biredi.
"Ya dai Babyna? ina fatan baki takura ba?"
Ta tambayeni da murmushi a fuskarta, da na kalleta sai naga ba fuskata take kallo ba, kamar idanunta zube suke akan ƙirjina.
Rigar jikina bayan matseni babu inda ya bayyana a jikina, amma irin kallon da take min yasa naji kamar tsirara nake zaune a gabanta. A ɗarare na kalli agogon fuskar wayata, ƙarfe shida saura kwata. A zabure na miƙe tsaye kamar wacce aka zurkuɗawa allurar ba-zata.
"Hajiya ina ga zan koma gida. Mijina ya dawo..."
Saukar hannayenta a kafaɗuna yasa na kasa aje numfashin maganata dai-dai, sai kallonta nake yi cike da wani irin mugun tsoro.
Zaunar da ni ta sake yi daɓas akan kujera, tasa hannu ta shafi gefen kumatuna na dama har zuwa kan laɓɓana, ta sanya ɗan yatsarta manuniya ta zagaye laɓɓana da yasha man baki, tun daga sama har ƙasa. Ta zura yatsar a bakinta tana tsotsa kamar ta sami alawa, sai da ta tsotse man bakin da ta lakato a laɓɓa na tsaf sannan ta fara magana da wani irin salo mai ruɗarwa da jan hankali.
SANADIYYA
Fareeda Abd…