009
*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 9*
Tunda Fiddausi ta koma gida ta shiga d'aki bata fito ba tana jin motsin dawowar Ibrahim tayi burus kamar bata ji ba tana zaune tana tunanin maganar Zakiyya da kuma maganar y'an uwan ta akan abinda yake cikin ta, tabbas ya zama dole ta d’auki mataki kafin wankin hula ya kaita dare, bazata bar cikin ba gwara kawai ta zubar tun lokaci bai k’ure mata ba.
Tasan sai yaje yayi sallah ya dawo sannan zai shigo tana zaune aka kawo wutar nepa haske ya gauraye d'akin gabad'aya, tayi ajiyar zuciya ta tashi tayi itama tayi sallar tana nan zaune tana sak’awa da kwacewa har ya shigo d'akin da sallama.
Da kallo ya bita ya zauna kafin yace, "Ya jikin naki? Na kira ki naji yanayin ki baki d'auka ba kuma baki kira ni ba. Me suka ce a asibitin?.” Ta kalle shi tace, "ka bani kud'in katin ne?." Kawar da maganar yayi bai tanka ba kafin yace, "Yanzu dai me yake damun ki?."
"Jinina ne yayi k'asa sunce na dinga shan ruwa sannan inda hali a dinga siyo min hanta kullum ina ci."
"Subahanallah, abun har ya kai haka kenan?."
"Uhum!" Ta bashi amsa a tak'aice ba tare da ta kalle shi ba dan wani irin k’unci take ji a zuciyar ta in ta Tuna tana da ciki.
"Bara na fita na samo miki hantar kici sai ki kwanta” ya fad'a yana tashi ya fita ta bishi da kallo ta tab’e baki tare da jan k'aramin tsaki. Tana ji ya buɗe kofa ya fita tace, "Dole ne na rabu da wannan cikin tun kafin ya farga, maganar Zakiyya gaskiya ce ya akaji dana gidan ma balle a samu wani? Ai komai sai ya sake lalacewa.”
Wayar ta taji tana k'ara ta jawo tana kalla taga bak’uwar lamba bata kawo komai a ranta ba ta d'auka ta saka a kunne, "Amincin Allah ya tabbata a gare ki kyakykyawar sura fara mai farar aniya, ina fatan gimbiya Fidy ta koma gida lfiya?."
Gaban ta yayi mugun fad'uwa ta wara idanu waje jin muryar mutumin da batayi tunani ba ta had'd'iye yawu ta kasa magana tayi shiru kirjin ta na bugawa cikin tsoron da ya bayyana a kan fuskar ta. "Gimbiyata kinyi shiru, baki gane mai magana bane?."
Muryar ta rawa take yi ta kasa furta komai yayi murmushi yace, "Kar ki damu na samu komai a labarin ki, kina da aure kina kuma da yaron mu Amir. Gidan wacce muka je d'azu gidan k'awar kine Zakiyya wacce kuka taso har kuka yi makaranta tare da ita, haka ne abinda nace?.”
Wara ido waje tayi kamar yana gabanta murya na rawa tace, "kasan ina da aure meyasa ka kira ni?."
"Sabida ina sonki tsakani da Allah badan wani abun ba, ina so na aure ki ne in kin amince. Ban kira ki da niyar b’ata miki aure ba, ga gaske auren ki zanyi.”
"Kamar ya ka aure ni bayan yanzu kake shaida min kasan ina da aure?."
Ya sake yin murmushi yace, "Gidan da kike Fiddausi bai dace dake ba, matar manyan mutane ce ke sam baki cancanci zama da wannan mijin naki da kuke tare ba. Ke matar manya ce kowa ya kalle ki a kallon farko zai gane hakan, matar irin mu ce ke kawai ki bani dama.” Fiddausi tace, "me kake nufi?."
"Kinga maganar waya bazata yu ba, yaushe zamu had'u?. Bani nufin cutar dake ko d’aya, ni auren ki nake so nayi."
Shiru tayi bata amsa ba ya sake cewa, "Taya kike tunanin zaki zauna a irin gidan da kike zaune Fidy? Ke kalar hawa manyan motoci ce da hawa jirgi ki bar k'asar meyasa kike zaune da wanda ba ajin ki ba?. Kalli k’awar ki Zakiyya mana bakya sha'awar irin tata rayuwar?. Ina tabbatar miki da matukar na aure ki rayuwar ki zata ninka ta ta rayuwar sau babu adadi.” Shiru tayi bata amsa ba tana shawarwarin ta kashe ko kuma ta cigaba da jin abinda yake cewa kafin ya kuma cewa, "A shirye nake da na aure ki in kika kashe auren ki, baki da wata fargaba domin Allah yasa min sonki lokaci d'aya ba tare dana shiryawa hakan ba. Yaushe zamu had’u mu tattauna?."
Fiddausi duk tsoro ya cika mata zuciya ga tsoron kar Ibrahim ya dawo tace, "ni bazan iya had'uwa dakai ba, kayi haƙuri." Jin zata kashe wayar yayi saurin dakatar da ita yace, "Kar ki kashe dan Allah, ki taimake ni ki kuma taimaki kanki ki amince mu had'u, wallahi ni ba irin wanda kike tunani bane da zuciya d'aya nazo wajan ki. Ki amince gobe mu had'u a gidan k’awar ki domin mu samarwa da kanmu mafita. Da gaske nake ina sonki kuma wallahi auren ki zanyi.”
Numfashi ta sauke tana kallon d'akin ji take kamar Ibrahim zai iya shigowa a lokacin ta sauke numfashi tace, "Shikenan zanzo goben, amma dan Allah kar ka sake kirana." Sautin murmushin sa taji yace, "Bazan kira ki ba gimbiyata sai na tabbatar mijin ki baya nan, yanzu ma an tabbatar min da fitar sane shiyasa na Kira ki. ina sonki ina k'aunar kasancewa dake, kiyi kwanan farin ciki" yana fad'a ya yanke wayar tabi wayar da kallo har lokacin kirjin ta bai daina bugawa ba, babban tashin hankalin ta bai wuce waye ya fada masa tarihin ta? Waye ya fad’a masa İbrahim ya fita?.
"Fiddausi!." A firgice ta juya jin muryar Ibrahim ya k'araso da leda a hannun sa ya zauna yana kallon ta yace, "ya na ganki a firgice akwai damuwa ne?." Kai ta girgiza alamun a'a ya mik'a mata yace, "Gashi kici." Hannunta har rawa yake ta karb'a ganin hakan sai ya rik’e hannun ta yace, "Lafiya kike kuwa?."
Kai ta girgiza alamun babu komai ya bita da kallo ya rik’e fuskar ta yace, "In akwai damuwa ki fada min."
"Babu komai" ta furta a sanyaye ya buɗe mata ledar da kansa khamshin hantar ya daki hancin ta ta fara ci duk da nata tare da nutsuwar ta.
K’are mata kallo yake dan ya tabbatar ba haka ya fita ya barta ba ta koma wani iri kamar mara gaskiya sai zare idanu take yi, "Fiddausi ba lafiya kike ba." Ya sake fad'a yana kallon ta ta girgiza kai alamun babu komai sai ya girgiza kai kawai ya tashi ya fita.
Gabad'aya hantar ta fita daga ranta ta ture gefe ta tashi ta fita daga d'akin ta wanke hannunta tare da dawowa ta kwanta a gefen gado kalaman Alhaji Bello na sake yi mata yawo a cikin kanta. Hasken d'akin taga an kashe sai k'arar fanka da take tashi tasan shine ta lumshe idanunta tana ji ya kwanta a bayan ta amma ta kasa motsin kirki dan bata san me zatayi ba. Tunanin ta gabad’aya yana wajan Alhaji Bello lamarin sa ya bata tsoro sosai gaban ta sai fad’uwa yake yi.
Yadda bata da kwarin jiki zuciyar ta ma babu k'arfi da wannan damar yayi anfani ya samu abinda yake so a wajanta ita kuma tana can duniyar tunani tana sakawa da kwancewa domin samarwa kanta da goben ya mafita mai kyau.
Washe gari.
Matashiya ce wacce bazata wuce shekara ashirin da bakwai zuwa da takwas ba doguwa mai kyaun jiki duk da bata da kib'a amma tana da kyau daidai gargwado. Tsaye take a bakin fanfo a tsakar gida tana zuba ruwa a bokiti kafin ta kashe fanfon ta d'auki bokitin ta wuce zuwa d'aki.
A falon Umma ta tarar da ita a zaune ita da k’annen ta biyu Zuhra da Sajida ta kalli Sajidan tace, “yaushe kika shigo?.” Sajida da take zaune tace, “Ban jima da zuwa ba.” Zuhra ta kalle su tace, “Yaya Ruky ki gaishe ta mana.” Ta wata idanu waje tace, “Sajidan zan gaisar?.”
“Eh mana, in kin girme ta a shekarun yanzu ai yayar kice” ta fad’a tana k’unshe dariya.
Rukayya ta kalli Mama dan taga ki zata tsawatar sai taga shiru kawai sai ta dauki bokitin ta tazata wuce tace, "Rukayya me zakiyi da ruwan zafi naga kin kuma dafawa bayan d'azu kinyi wanka?."
"Wankan janaba mana Umma, in ba shi ba me zatayi?" Zuhra ta fad’a Tana kallon ta
Umma ta kalli yarinyar tace, "Ke bana son shirme wacce irin magana ce wannan?." Shiru tayi tana kallon Rukayya kafin Rukayya ta wuce d'aki zuciyar ta na zafi sosai amma bata nuna ba haka ta shiga band'akin tayi wanka tana fitowa Mama ta shigo ta bita da kallo ganin kanta a jike tace, "Da gasken da maganar Zuhra ta fito wankan janaba kika yi ga kanki nan yasha ruwa."
Rukayya kamar zatayi kuka tace, "Umma me zai had'a ni da wankan janaba?." Umma tayi murmushi tace, "Rukayya kenan, yadda kika jima babu auren nan duk sa'anin ki daga mai yara biyu sai mai guda d'aya ai dole wanka ya kama ki wani lokacin. Shekara ashirin da bakwai ai ba wasa ba.”
Hawayen da take b'oyewa suka sakko ta share Umma ta sake kallonta tace, "Ba kuka nace kiyi min ba malama, tashi zaki ki shirya na aike ki gidan Anty Salamatu" ta fad'a tana zama a kusa da ita ta kuma cewa, "mun yanke shawara zamu had'a ki da Lawan na wajan ta ayi auren nan a rufawa juna asiri, ke kina zaune ba miji babu wanda yake zuwa yana cewa ana sallama ballantana mu saka rai gwara ayi auren nan kowa ya huta kema ki huta."
Hawaye ya sakko mata sharrr ta share tana kallon gefe tace, "Umma yanzu kin amince na auri Lawal? Matan sa uku fa, kuma kin san mata uku ya saki.”
"Dan matan sa uku sai me? Har ke ba hud'u ba kenan, ko haram ne dan ya k'ara ta hud'u?. Shi kuma saki ba zuwa yake ba?.”
"Amma Umma da kanki kike cewa bai tsarewa gidan sa komai ba sabida bashi da sana'ar kirki amma kike cewa na aure shi?."
"Nufin ki kinfi k'arfin sa kenan?."
Yadda Umman take kallon ta ya saka ta sauke idanu k'asa tace, "Ba haka bane Umma, amma bana fatan irin wannan auren Allah ya sani." Umma tayi tsaki tace, "Ya zama dole ki amince da auren Lawal domin na gaji da ganin ki a gabana muna had'a kafad'a nida ke da k'anwar ki, in kina zaune ita kanwar ki waye zai kula sta har tayi auren?, ko so kike yadda kike zauna kika dankare a gida itama ta zauna?."
Rukayya tace, "Umma ai aure nufi ne na Allah" ta fad'a tana fashewa da kuka. Umma tace, "na fiki sanin nufi ne na Allah amma akwai niya, sai kin saka a zuciyar ki kin kuma amshi wanda yazo miki sannan zai nufa ki tashi. Ke Rukayya! Bana son wannan ranin hankalin, kowa yazo kice bai miki ba wa kike so yazo inda kike? A gida kike so ki gama tsofewa?."
Rukayya bata ce komai ba sai kuka da take yi Umma ta nuna ta da yatsa tace, "Ko bakya so sai kin amince da auren Lawal domin na gaji da ganin ki a gaban idanuna, naji da k’annen ki ma da suke tasowa ke zaman gida ba naki bane. Duka k'awayen naki su wacece bata da miji? Dukkan su yara ne dasu amma ke an samu Lawal din ma ya amince kice wai ke ga zance ga magana. Ga kanwar ki Sajida haihuwa ta biyu take niyar ki ke kina gida. To wallahi na gaji kinji na fad'a miki" tana fad'a ta fita ta barta sai mita yake yi.
Rukayya tabi Umma da kallo tana kuka zuciyar ta nayi mata mugun zafi, k'anwar ta Zuhra ce ta shigo ta k'araso kusa da ita tace, "nikam da zaki ji shawara ta da kin amince da auren Lawal d'in tunda dai babu wani bayan shi."
Rukayya ta kalli Zuhra tace, "Zuhra meyasa kika raina ni ne kwana biyu?." Ta tab’e baki tace, "Gaskiya nake fad'a miki fa, babu wanda yake zuwa inda kike meyasa baza ki....."
Saukar marin da taji ya hanata k'arasawa zuhra ta zaro ido tana kallon Rukayya cikin mamaki itama kuma kallon ta take cikin zallar b'acin rai da k’unar zuciya tace, "Kar ki sake saka min baki a cikin lamarina, ni ba sa'ar ki bace bana son rashin kunya."
"Dan na fad'i gaskiya kawai sai ki mare ni!? Karya nayi, naga ai babu wanda yake zuwa inda kike d'in baki tab'a yin saurayi ba. Wallahi kar ki sake marina dan in aka sake bazan k'yale ba!" Ta fad'a cikin ihuu tana kallon ta.
Rukayya kallon take yi cikin k’unar zuciya tace, "Zuhra dake ni."
"Bazan dake ki ba amma wallahi karki sake marina."
"Malamai lafiya nake jin ihun ku da safiyar nan?" Umma ta fad'a tana shigowa tana kallon su.
Rukayya tace, "Umma ki mata magana babu ruwanta da lamarina, bana son rashin kunya dan taga ina kyale ta.” Umma ta kalli Zuhra tace, "Malama bata haƙuri." Zuhra kamar zatayi kuka ta bata haƙuri tana fita daga d'akin.
Umma ta kalle ta tace, "Tana ganin ku kai d'aya ku kwana waje d'aya ku tashi waje d'aya, ki saka braziya itama ta saka, ki saka pad itama ta saka to me zaki nuna mata?. Aure ne zai banbanta ku amma kin ki har kina da bakin cemin Lawal bai dace dake ba sai kace in an Baki dama ki kawo wanda ya dace dake d’in zaki samo, samarin da baki yi ba tun kina y’ar sha takwas zuwa ashirin yanzu da kika tafi talatin ai baza kiyi su ba. Dole ki amince da duk wanda yazo wallahi na gaji da ganin ki a gidan nan” ta fad'a tana fita daga d'akin ta bar Rukayya a tsaye tana kuka.
A fusace ta k'arasa wajan kaya ta saka tana kuka ta saka dogon hijjabi ta d'auki kud'in ta da suke cikin kayan ta ta fita daga gidan da ji take zuciyar ta na mugun tafasa in ta zauna a gidan zata iya fashewa gwara ta fita kawai daga gidan.
#Vote
#Share
#Comments
#F5
#Book1
#Nana Haleema