SHAFI NA 5
Shima murmushi ya mayar ma ta tare da sumbatan bakinta, san nan ya ce;. " Bandade da shigowa ba, sai kuma na tarar dake cikin duhun yanayi.
Babu abun da ke tadamin hankali kamar na ganki cikin tashin hankali Joɗa!
"Bazan iya barin damuwa ba, sabo da ita din tamkar jinin jikina ce Lukman.
Taya kake tunanin bazan yi kuka ba idan ina tuna a halina? Taya hankalina bazai tashi ba in na tuna irin kisan gilla da akayi wa iyayena har da Dan uwana?
Me muka yi musu?
Laifina ne dan na kasance tsatson fillo?
Har yanzu ban fanshe irin abun da akayi min ba Lukman, kai sheda ne, akan ire-iren kalolin azabar da na sha a hannun su!
Har yanzu ban dauki fansa ba!
Rungume ta yayi yana jin tausayinta, ba zai ce be tausayawa kansa ba, sai dai a ko da yaushe yana boye nasa ne sabo da karta ga rauninsa.
Amma idan wata rana abu yayi mata yawa tana zaunawa tayi kuka me isarta.
Ba tada dangin Iya balle na Baba, babu wani mutum da zata kira tace dangin tane.
Sai wasu masu irin matsalolin ta.
Cikin dakewar zuciya ta kalle shi ta ce;
"Su Duna sun shigo gari."
A zabure ya mike tsaye, " Kinsan me kika cewa kuwa? Waya fada miki?"
"Na samu sakone daga abokanan sirri. Abu na gaba, yau akwai fita."
"Cikin fushi ya kalleta! Yaushe kika sanar da Ni cewa yau zamu fita?"
"Yanzu nayi shawara da zuciyata. Tana me kallon cikin idanunsa tana karantan me ke cikin su. Ba ta gano komai ba sai zallan soyayyarta da take hangowa a cikin su.
Ita kanta tasan cewa Lukman na hakuri da ita, duba da yanayin da ta shiga a lokutan baya.
Gwauron numfashi ta sauke...
"Lukman tun ba yau ba na fada maka karka bar soyayyata tayi maka illa, domin Ni din tamkar gawace me rai. A ko wane lokaci zaka iya rasa Ni.
Da ace nasan soyayya ta za tayi maka kamun kazar kurkuku, wallahi da ban baka dama ba.
Amma kaddara ta rigayi fata, bana son idan na mutu kayi min kuka, tare da alkawarin ba za ka tuna da Ni ba, gudun shigan ka wani hali."
Hawaye masu zafi suka shiga kwaranyowa daga cikin kormin idanunsa.
Baya fatan ya ga ranan da zai kasan ce ba tare da wannan kyakkyawar halittar ba.
Hannuwanta ya rike yana me kallon cikin idonta,
" Ke din kin kasan ce jigo a cikin rayuwa ta Joɗa.
Kyakykyawar Zuciya tana rayuwa ne a karkashin inuwar Aminci da Amincewa,
Zuciyar da aka cudanyata da tsarkakakkiyar soyayya tana samar da ingantacciyar lafiya a gangar jikin mamallakin ta, shaukinta yakan bi sassan jini dana ruwa domin cigaba da ginin gangar jiki mai`inganci, So kalmar da tafi komai dadin fade da saurare
shike haifar da zaman lafiya a kowane karni. Keba zinariya ba, keba lu'u-lu'u ba, ke ba a zurfa ba, amma dukkanin su kinfi su kyau
Ni ne masoyin son ki, wanda ba ya da wani aiki sai wannan, domin ban mallaki komai ba, sai sahalewar ki. Bana neman wata Zuciya, sai ta ki, ina hanzarin zuwa gare ki. Ba na jin ƙamshin wani fure sai na lambunki. Teku ya harɗe da ɗigon ruwa, wa zai iya bambance shi Joɗa.
Ba yau ce ranar da ta fara jin ire-iren wadan nan kalmomin ba.
Amma ba tasan me yasa na yau yafi shiga cikin jikinta har da barko ba.
Tabbas, da ace babu ƙura a gabanta da ta tsaya da wannan bawan Allah me cike da kalamai ma'abota So ga kowa.
To amma bakin alkalimi ya ri ga ya bushe, gara ta tunkari mutuwarta tun kafin tazo ma ta, ita ce kaddararta.
"Joɗa, ki ya fe musu muyi rayuwarmu cikin farin ciki, sai kiga Ubangiji yayi miki sakayya ta alkhairi.
A fusace ta mike tsaye har jikinta na rawa. Fuska ta juye tamkar ba ita ba, babu abun da take tunowa sai lokacin da barayi su ka shigo cikin bukkarsu...
Haka suka cillo kyauren kofa tamkar an wurgo mutum sai a fuskan Baffa. Wani irin yanka tayi wa fuskan Baffa, take jini ya fara fesowa tamkar an bude famfo.
Cikin tashi hankalin Inna wuro da Gidado da joɗa su ka rike shi su na yi mishi sannu.
Dankwalin kan Joɗa gidado ya cire ganin Inna wuro ta rude ya daure rabin fuskan Baffa.
Daya daga cikin barayin ya daka musu tsawa ganin sun raina musu wayo, a ce warsu ai rainine a gabansu su na taimakon dan uwansu.
Cikin fushi Wanda aka kira da Duna ya je gaban Baffa kamar zai taimaka mishi ya tashi, amma sai ya haushi da duka yana kwallo da Shi, badan yayi ma sa komai ba.Ganin haka ya sa Gidado ya fusata ya kai wa Duna naushi a baki sai ga jini.
Sauran barayin su na gefe tsaye su na kallon su.
Shafa bakin sa ya yi yaga jini, take ya fara zuba ruwan alburusai a kirjin gidado, ganin haka ya saka joɗa rugowa da gudu tayi kan gidado wanda ke zube a kasa cikin jini rai na kokarin fita. Hannunta ta daura akan ramin kirjinsa wanda jini ke zubowa.
Tana faman kiran sunan sa. Kallonta ya ke yi hawaye masu zafi na zubowa ta gefen kuncinsa tare da motsi da bakin sa, kunnenta ta kai daidai bakinsa tana sauraron abun da yake cewa...
Sai kuma numfashin sa ya tsaya cak!
Kukan inna wuro ya sa ta juyo, ganinta tayi rungume da gawan Baffa tana jijjigawa.
Runtse idonta tayi tana son yin kuka amma ba halin yi, ashe kuka ma rahama ne.
Rungume inna tayi wadda ta ke kuka bilhakki...
Sai can taji ta ja numfashi me tsawo san nan ta sauke a hankali. Ganin yadda jikin Inna ya saki, shi ya tabbatar mata cewa Inna tabi su Baffa...
Duk wannan abun da ke faruwa akan idon barayin.
Daka mata tsawa daya daga cikin su yayi, tare da buga mata kan bindiga, take jini ya fara zuba daga hancinta, tafin hannunta ta sa ta goge jinin amma haka wani ke sake zubowa.
ke tashi mu tafi bamu da lokacin batawa cikin tsawa yayi mata maganar, Amma tamkar da dutsi yake magana.
A fusace ya sake kai mata wani bugun akai take ta zube a wajen sumammiya.
A wahalce take bude idanunta wadanda suka kunbura , hannunta ta kai don murzawa, sai dai kuma me? Hannun taji daure , cikin sauri ta bude idanunta tabbas a daure take, tamkar yadda ake daure dabbobi.
Girgiza turken da aka daureta da shi ta fara yi...
Za kiji wa kanki ciwo idan kika ci gaba da jijjigawa, taji maganar daga gefenta.
Sai yanzu ta tsaya kallon wajen da take.
mutane ne birjik maza da mata yara da manya dukansu an daddaure su a turaku,
tamkar yadda ku kasan kasuwar dabbobi haka wajen yake.
Dukan da ake yiwa wani dattijo shi ya ja hankalin mutanan wajen, sauran barayin dake can gefe suna cewa wanda ke dukan ka kashe shi tun da yan uwansa ba zasu kawo kudin fansa ba.
Duk sun farfasa mishi jiki, beyi awa daya da mintuna ba tsohon nan ya ce ga garinku. haka su dauke shi a wulakance su ka haka rami suka birne shi.
Can zuwa yamma yan uwan dattijon can da aka kashe suka kira waya, cewa a dan Allah a rage musu kudin fansa zuwa million daya wlh su talakawa ne.
Da kyar suka amince su karbi kudin haka nan, duk da sun kashe mutumin.
Haka jama'a ke ta kiransu sabo da su samu su karbi yan uwansu.
Wasu koda zasu kawo kudi anriga da ankashe yan uwansu, kuma a hakan zasu karbi kudi.
Haka wajen yake a koda yaushe tamkar kasuwa.
Kullum da safe sai an zane su, san a kawo musu shinkafa fara gaya sai a kawo dussa ta dabbobi a zuba acikin abinci sosai, kuna ci ana dukanku, har sai kun gama.
Su kashi da fitsari ba a maganar su, kowa a wajen zaiyi abun sa.
Wasu ma kazantar wajen ke kashe su.
Shiya sa ko an saki mutum da wuya yayi sati biyu a duniya, sabo da shi kadai ya san irin azabobin da ya sha.
*SHARE
**COMMENT
**LIKE
**VOTE
** FOLLOW
San nan ku garzaya #Arewabooks domin samu sauran littafai na.
ko kuma ku je #wattpad acan ma zaku samu.
ko kuma a YouTube channel di na
#YARMUTANARGUNGU.
NAGODE 🙏