JOƊAFree

ArewaPen original

AdventureFreeOngoing

JOƊA

  • 1views
  • 11chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · SHAFI na 1

           📚JOƊA📚               NA         FATIMA ZARA ALHASSAN           🐟ƳAR MUTAN ARGUNGU🐟NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI GA AL'UMMAR AREWA💖WANNAN LITTAFI NA ƊAUKE DA ƘALUBALEN DA ƳAN AREWA KE FUSKANTA😭GARGAƊI!!!WANNAN LITTAFI ƘAGAGGE NE, SABO DA HAKA BAN YADDA WANI KO WATA SU YI AMFANI DA KALMA ƊAYA DAGA CIKIN SHI BA. YIN HAKAN LAIFINE. A KIYAYE!!!SHAFI NA ƊAYA******************************************بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ******************************************Hadari ne ya haɗu ya yi baƙiƙirin. Ko wane lokaci ruwa na iya sauka. Yanayin damuna shiya ba wa garin wani irin ni'ima ta re da iska mai dauke da sanyin ƙamshi.Rugan malam Jauro kenan...Ruga ce mai ɗauke da ni'imomi wanda ubangiji ya albarka ce ta da samu. Ta na nan yamma kaɗan da Garin Ɗan-Sadau da ke Lardin Zamfara State.Malam Jauro yana ɗaya daga cikin fulanin da suka assasa wannan ruga , sabo da ƙwazo irin na malam jauro, bai tsaya iya kiwon shanu ba, ya haɗa da noma.  Akan noma irin na malam jauro sai ka rantse da Allah cewa, shiɗin bahaushe ne . Domin ko wasu Hausawa ma albarka. Hakan ya sa zan iya cewa, malam jauro na ɗaya daga cikin masu arzikin Rugar su. Shiya sa jama'an gari da ma maƙwabtan su ke kiran rugan da RUGAN MALAM JAURO...JOƊA!JOƊA! Inna ce ke ta ƙwala ma ta kira ya yin da take kwasan tuwo a madafa."Na'am inna."cewar joɗa wadda ke can cikin Bukkar ta.   "Wai har yanzu ba ki gama damun furar ba ne? Cewar inna."Inna saura kaɗan na gama."  Girgiza kai inna ta yi, tana mamakin rashin kama jiki irin na Joɗa. San nan ta ce,"Joɗa rufe furar haka nan ko ba ta damu ba, ki zo ki kwashe min kayan tsakar gidan nan kafin ruwa ya sauka, musamman ƙwarrai kar ayi ruwa su jiƙa su, kin san ƙwarya ba ta da jimirin ruwa .""To inna." Aje langar fura ta yi tare da rufewa . san nan ta fito daga cikin bukka da sauri. Ganin yadda hadari ya haɗu sosai shiya sa ta ce,,"Inna anya za ki gama abinci nan kafin ruwa ya sauka kuwa? Ko dai na gwafce murhu in kai miki shi cikin rumfa kafin ruwa ya sauka?""Haka ne Joɗa amma gama na ki aikin tukunna sai ki zo ki ɗauke murhun miya tun da gashi ina kwashe tuwo.""To" cewar joɗa.Shigowan garken shanaye ,mou...mou...su ka dinga kuka. Bayan sun gama shigowa san nan Gidado ya shigo, bakin sa ɗauke da sallama. Wajen rumfan dabbobin ya nufa ya ɗaɗɗaure su, san nan ya zo madafa inda Inna wuro ke kwashe tuwo.       "Inna barka da gi...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters11
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play