Taƙaitaccen Tunani

17

by @faddabanan

Tun daga ranar na fara ɓoye mashi amman duk wurin da na sanya ƙafa yana da masaniya don sai na gan shi. Lokacin kuma da ya gane kunyarsa nake ji sosai, sai ya tsiri ba ni kunya a gaban ko na waye ya tarar da ni da shi. Shi yasa da na hango shi ya nufo wurin da nake idan har tare nake da mutane, kaucewa wurin nake yi don gara ya iske ni ni kaɗai yanda komai zai yi ba damuna zai yi ba, kuma idan ya ganni ni kaɗai bai cika damuna ba sam.

*******************


Ranar wata Alhamis da marece ni kaɗai zaune a ɗakina na gidansu Rufaida. Kiɗa me sanyi ne ke tashi iya ɗakin bai cika gidan ba. Takarduna nake rarrabawa wanda na haɗe da hotuna rannan muna sauri za mu fita. A lokacin ita Rufaida na wurin malamin su a farfajiyar gidan suna karatu (Ni yanzu na fi gane naje islamiyya domin ya fiye mun sauƙi na kuma fi ba da himmar karatu). Anty Aysha (kamar yanda ta sa ƙarfi da yaji muka koma kiranta) tana makaranta domin ranar ma sai ta kai ƙarfe bakwai kafin ta dawo gida.


Na duƙufa ina ware takardun da hotunan, na ɗaga ɗaya daga cikin hotunan ina kalla ina murmushi saboda abinda ya faru lokacin da aka ɗauki hoton. Mun yi shi ne tare da Anty Aysha da Rufaida sannan a ɗauke mu hoton a bazata ne ba mu sani ba.


Ranar da Anty Aysha ta fara tuƙa mu a motar ta ne bayan an kawo mata ita tana sabuwa, ta kai mu yawo sannan mun tsaya shan Ice Cream da muka dage sai ya siya mana.


Muna zaune a wurin muna sha muna cewa tuƙin ta ba kai na Yaya daɗi ba, ita kuma tana cewa ba laifin mu ba ne, laifinta ne da ta bari muka shiga motar ta, kuma gara mu sani wannan ce shigar mu ta ƙarshe. Muna dariya muna ba ta haƙuri don Yaya ba ya gari yanzu.


Muna cikin diramar nan ne sai kawai wani abu ya faɗo mana a tsakiyar teburin da muke zagaye da, ban ma yi nutsuwar da zan gane kunama ce ko ƙadangare ko kulɓa ne abun ba. Cikin firgita muke miƙe tare da ture teburin don mu samu damar gudu. Robar Cream ɗina tayi tsalle suka yi karo da ta Rufaida suka dire bisa kawunanmu, sai ga shi har fuska ya kwararo mana da yake ya fara narkewa. Kuma a daidai lokacin ne aka ɗauke mu hoton. Kuma duk wannan gudun ashe na banza ne, wasu yara ke wasa da toy ɗinsu shi ne suka wullo mana. Sai daga baya abun ya zama abun dariya.


Wanda ya ɗauke mu hoton kam shi ne saurayin Anty Aysha a halin yanzu, sun zo wajen yana tare da digital camera ɗin shi. Tunda ya ganmu yake ta son ya ga fuskarta tunda baya ta ba shi, bai samu sarari ba sai lokacin kuma shi ya ɗauki hoton. Ita kaɗai ce jikinta bai ɓaci ba. Hakan ne kuma sanadiyyar haɗuwar su.


Na gama dariya ta na ajiye hoton gefe, sai kawai na ga farin hannu ya miƙo ya ɗauka, na san hannun waye don haka ban ma ɗago ba na ce "Shine ba sallama ko Yaya?"


Ban ji me ya amsa ba saboda kiɗan nan, don haka na rage volume tare da ƙara maimaita me na ce.


"Kin sa kiɗa ta ina za ki ji sallama? Ke kan ki ba kya jin maganar ki bare ki ji ta wani."


Ya kalli hoton ya ce "Aysha da su waye nan?"


"Kaiiiiiiiii! Yanzu ni da Rufaida ɗin ne ba ka gane ba."


Ya gama dariyar labarin da na bashi sannan ya umarce ni da na shirya fita zamu yi. Har na miƙe tsaye da sauri sai kuma na tuna na ce "Yaya ai Rufaida na wurin Malam Habib ba su gama karatun ba."


Ya kalle ni ta gefen ido "Kin ji nace Rufaida ne? Ina ce Sadiya nace ta zo mu fita? Kar ki ɓata mun lokaci, nan da minti biyar na same ki a wurin mota." Ya fice. Mayafi kawai na ɗora akan riga da siket na 'yan kanti da nake sanye da su (yawanci sun fi yawa a kayanmu ko don tsarabar da koyaushe Daddy yake kawo mana duk tafiyar da zai yi).


Kafin na ƙarasa bakin motar sai da na biya wurin su Rufaida na faɗa mata a kunne za mu fita. 


Tunda muka fita idan na yi masa magana sai dai ya amsa da 'eh ko a'a' ko yayi mun shiru. Da na gane maganar ce ba ya so sai kawai nayi shiru na bar shi yana bin waƙar da ke tashi a motar, don ma babu alamar damuwa a fuskar shi. Na ji haushi ba ɗan kaɗan ba.


A ƙofar super store Al Abiyad da ke zoo road ya tsaya, mun saba da zuwa nan saboda anan ake siyayyar kayan amfanin gida ko da yaushe. Ya sauka bai ce mun ƙala ba, whistling na waƙar da ya gama ji a motar yake yi ƙasa-ƙasa ma, don haka na sauka ni ma.


"Me zamu siya ne? Na buƙata bayan mun shiga ciki.


"Ki ɗaukar maku abubuwan ku ke da 'yan uwanki amma Aysha tace tana buƙatar sabbin turaruka sai ki sauya mata. Idan kin riga ni gamawa sai ki nemi wurin da nake, idan na riga ki za ki ganni wurin cashier."


Ban ce komai ba na juya na tafi neman turaren Anty Aysha saboda nasan wanda tace za ta saken, rannan ma da muka zo kuɗin mu ne bai isa ba shi yasa ba ta ɗauka ba. Na Rufaida kam nasan kayan gyaran gashinta ne suka yi ƙasa, wanda yayi saura bai fi tayi amfani da shi sau biyu ba. Sannan na fara tura keken kayan ina bi layi-layi ina duba kaya saboda na ga ko akwai abinda suke buƙata da ban tuna ba. Ganin na kasa tuna ko ganin komai sai kawai na ɗaukarwa koya irin chocolates ɗin da ya fi so. Amma ni da Rufaida na ɗaukar mana turare biyu biyu.


Da na tabbatar na gama sai na turo kayan ina neman Yaya, can na hango shi ya ɗaga kwalin abu yana karantawa.


Na ƙarasa kusa da shi na ce "Na gama namu, akwai abinda zan taya ka da shi?"


Ya kalli keken da na turo ya ce "Shi kenan abinda kuke da buƙata? Kin tabbatar?"


Ban kai ga amsawa ba na hango wata na doso wurinmu. Allah ya sani sai da na ɗan tsaya na kalleta don ba ƙaramin kyau gare ta ba kuma kwalliya ta zauna a mazaunin ta. Da ta ƙaraso kuwa turarenta ne ya cika wajen, duk kuwa da cewa kafin zuwan nata na Ya Buhari ne ya cika wurin. Farin cikin da ke fuskar ta ne ya ba ni mamaki, kafin kuma na ga ta sa hannu ta dafa kafaɗar Buhari ta ce "Long time no see, ina ka ɓuya haka?" Kunsan dai ana cewa mutum tara yake bai cika goma ba, amma wannan tun daga suffa, murya kai da komai goma bisa goma take sai dai idan a wurin hali ta rasa ɗayan.


Ya juyo cikin dariya ya kuma rungumo ta kamar yanda turawa dai ke gaisawa idan sun haɗu da abokan su. Ya ce "Wow! Hamida! You are looking at your best as always, ashe kina gari?"


"A'a, kar ka nemi yi mun wayo, tunda muka yi hutu ina Kano babu wurin da naje. Kai da ba ka duba mutane, ta ya ya za ka san ko ina nan ko bana nan?"


"Afuwan Hamida. Ai kin san meye matsalata tun ba yau ba ai.... Au (ya dafe kai), ga ƙanwata. Ku yi haƙuri gabaɗayan ku, na ɗan manta manners ɗina for a while ne. Ita Sadiya sunanta."


Ta dafa ni a kafaɗa tana murmushi ta ce "Ki yi haƙuri Sadiya, Yayan naki ya iya ɗaukewa jama'a hankali ne. Ina ragowan sisters ɗin ki? Ina ga na taɓa ganin hoton su sau ɗaya, Aysha da Rufaida ko? Su biyu sun yi kama sosai. Ke kuma kamar daban kamar yanda Buhari shi ma daban. But sorry to say, duk ya fi ku kyau."


Ni kawai haushi nake ji da ban san na menene ba, ni ba na wani son magana da ita. Na daure dai na ce "Ina wuni?" Na fara tura keken kayanmu ina ce masa "Yaya me zan ƙarasa ɗauko maka? Sai ka same ni a wurin cashier ɗin idan ka gama."


"Shaving stick and cream, can you help me with that?" Ban amsa da baki ba, kai tsaye na wuce don nasan wanne yake so.


Tunda naje wurin cashier nake jingine ina kallon su suna surutu suna zagaye tana ɗaukar abubuwan da take buƙata cikin sauri, ƙilan sauri saboda sun san ina jiran su ne.


A wurin biyan ma sai da suka ɓata mana lokaci saboda jayayya, kowa a cikinsu ya dage shi zai biyawa ɗan uwansa, ƙarshe dai kowa sai na shi ya biya. Na taɓe baki kawai.


A wajen ma sai da suka daɗe suna magana tsaye jikin motarta da tayi parking kusa da tamu, kuma kafin ta tafi saitin window da nake zaune nake zama jiran gawon shanu ta ƙaraso ta zura mun leda kafin tayi mun sallama. Na ce na gode kawai. Tana tsaye har muka fito kafin ta zaga ta shiga motar ta.


A yanayin da muka tafi a haka muke dawowa, yau dai ya zama Micheal Jackson 🙄. Ni kuma ƙirjina yayi mun nauyi, watau ni ce ba zai kula ba sai wata Hamida ko? Na rufe ido na nayi baya na jingina da kujerata sosai. Ina jin shi yayi parking tareda fita daga cikin motar amma ban buɗe idon ba don nasan tafiyar nan ba isa kawo mu gida ba.


Shirun da naji yayi yawa ne ya sa na buɗe ido na don ganin ko ina yake, can na hango shi da wani mutum a bakin wani gate. Ni dai nasan na ji wani abu a maƙogwaro na ya tare wurin, sai kuma naji abun yana yiyowa sama yana narkewa yana zama hawaye. Ni kuma jin kukan yana narkar da abun sai kawai na saki jiki nake kuka na hankali kwance.


Haka ya dawo cikin motar ya iske ni kace-kace cikin hawaye. Ya girgiza, don karkace wa yayi ya fiddo hankaci ya sa mun a fuska yana faɗin "Sadiya me ya faru? Me ya sa ki kuka? Gida ki ke so mu koma? Kan ki ne ke ciwo?" 


Ni kuma waɗannan tambayoyin sai suka daɗa karyar mun da zuciya, maimakon kukan yayi ƙasa sai ya ƙaru, ya rasa yanda zai rarrashe ni sai ya kifa kan shi a sitiyari ya bar ni nayi kuka na har ya isheni sannan na share hawaye na.


Na ce "Mu tafi gida kar ka rasa jam'i"


Ya ɗago ya kalle ni, kalar idanunshi a wannan lokacin sai da suka tsorata ni nayi baya har ina bige ƙeya ta da bayan kujerar da nake zaune. Yanzu kuma ni ce na gigice na ce "Yaya? Ba ka da lafiya ne? Innalillahi! Na shiga uku! Yanzu wa ye zai kai mu gida? Na samo taxi za ka iya shiga sai mu rufe wannan a nan sai a zo a ɗauka?" Ganin bai amsa ba hakan ya daɗa ruɗa ni na fara ƙoƙarin fita daga motar neman taimako, riƙo hannuna da ya yi ne ya dawo da ni hankali na.


Na ce "Taimako zan nemo mana, ka ji?"


Bai saki hannun nawa ba ya ce "Ni nace maki ba ni da lafiya ne?"


"Ba ga idon ka ba? Kuma jikinka ya zama sharaf!"


"To ta yaya ba zai zama haka ba? Kin sani a gaba sai kuka kike mun kuma kin ƙi faɗa mun me aka yi maki. So kike Momy tace na je na zane ki ne?"


Na zumɓura baki na ce "To ai kai ne, ba kai ne tunda muka baro gida ka ƙi mun magana ba kawai ka dinga jin kiɗa ba. Kuma da muka haɗu da wata ka dinga yi mata hira har dariya. To ni nayi maka laifi ne? Fushi kake yi da ni Ya Buhari?"


Cike da mamaki yake kallona ya ce "To ba ki yi tunanin ko yau maganar ce bana son yi ba?"


"Allah ba haka kake yi idan ba ka son magana ba."


"To yaya nake yi?" 


Na mayar da fuska ta yanda yake yi idan baya son a dame shi da surutu. Ya dinga dariya yana kallo na har yanzu mamaki na yake yi.


Ya ce "To shikenan, ki yi haƙuri ba zan sake ba. Matsalar ki tun kin 'yar mitsitsiyar ki da ke kishi, Allah Sadiya kishin ki yayi yawa. Da za ki zama me wayo da kin ɗauke hankalin ki daga kansu, duk abokan rakiyar rayuwa ne kawai. Wayon ki a wasu ɓangarori kawai ya tsaya, a irin nan kishi kaɗai kika sani. Oh ni Buhari!"


Har muka dawo gida murmushi yake yi yana satar kallona, har abun ya fara damuna ko dai wauta na yi ni ban ma san na yi ba?


A falonmu na zubar da ledojin siyayyar domin yin alwala da sallah, su har sun idar suna zaune akan abun sallar ne. Ban damu da kayan da zubar a wajen ba domin idan za su shekara babu me sa hannu ya buɗe ko ma mene idan ba ni nace masu ga kaya ba. Haka Momy ta miƙar da mu, ta ce muddin ka ga abu ba kuma kai ne ka ajiye ba, kar ka taɓa har sai an yi maka izini don bincike babu kyau.


Sai da na idar sannan na fitarwa da kowa kayanshi, Anty Aysha har da rugume ni saboda murna ta ce "Allah sarki my sister, shi yasa nake son ki! Ashe ba ki manta ba. Thank you darling!


Ita kam Rufaida mamakin ta yanda aka yi nasan kayan gyaran gashi take buƙata tunda kowa da banɗakin sa a ɗakinsa. Rufaida na da surutu sosai, hakan yana taimaka mata wurin mita, don kusan kullum sai tayi complain abu kaza ya kusa ƙarewa ko kuma ka ji tana cewa idan za mu je shopping abu kaza da kaza take son siya.


Turaren mu da na siya mana ni da ita, ita na fara ba wa ta zaɓa (shi ma duka aikin Momy ne, har mun saba. In dai kaine ka siyo sai dai a zaɓa a bar maka ragowan ko kuma ka siyo maku iri ɗaya). Kowa ya ja chocolates ɗin shi ba tare da jiran a miƙo masa ba.


Ledar da Hamida ta bani kuma kuma kayan ciye-ciye ne na zaƙi kawai sai kuma ledar scrunchie me guda shida a ciki.

*****************


Tun daga wannan ranar kuma sai Ya Buhari ya zama baya jin wani kunyar nuna cewa ni special ce a wurin shi. Zuwa yanzu kam kowa ya sani, babban girman lamarin gare ni ganin yanda Momy ba ta damu ba sai cewa da tayi idan akwai alkhairi Allah ya tabbatar. Anty Aysha da Rufaida ko a keyar su su ma. Rufaida ce ma nake tunanin ko za ta ce wani abu amma daga "Idan kin ga za ki iya da lodin 'yan matansa, to ke kam ba ki da matsala." Ba ta ƙara cewa komai ba.


A can ainihin gidanmu kai ma ka sanzasu fi kowa farin ciki da hakan, ni ban ma san sun san da maganar ba sai rannan da naje gaida Inna tunda na kwana biyu ban je ba, take faɗa mun wai Daddy da kan shi ya zo ya samu Baba da zancen. "Shi baban ki ma cewa yayi kina gama ƙaramar sakandare (JSS 3) a aura masa ke kawai, tunda sanin da yayi wa Buhari da makaranta ya san ba zai taɓa hana ki ba, sai ma idan ke ce kika gaji don kan ki. Amma Daddynku ya ce a'a, yanzu ma kawai don mu sani ya faɗa mana, daga nan zuwa lokacin da za ki kammala sakandaren gabaɗaya dai."