Taƙaitaccen Tunani

21

by @faddabanan

Hannu ya ɗagawa abokansa suka ƙaraso wurin da muke sannan aka yi wa masu kula da wurin magana ya ƙara teburi da kujerun zama a wurin namu, kayan ciye-ciye da suke zuɓe saman teburin ya fi ƙarfinmu har da su ɗin ma gabaɗaya, saboda sun ƙaro wasu.


Bakwai saura muka fara shirin tafiya. Ya Yusuf ya rako mu wurin parking da ke hanyar waje, ya jujjuya sannan ya ce "Ina motar taki? Ko direba ne zai zo ya ɗauke ku?"


Ta ɗan yi shiru, ƙila a tunanin ta ɗaya daga cikinmu zai amsa masa, jin duka mun yi shiru sai ta ce "Motar na gida, motar Daddy muka aro." Kuma daidai lokacin muka ƙaraso jikin jeep ɗin Daddy ɗin.


Ya kalli motar da take buɗewa ya ce "Kai kai kai! Anya Aysha wannan motar ba ta fi ƙarfin ki ba kuwa? Ki taimaka ki rufa mun asiri ki ja ta a hankali." Muka fara yi masu dariya, ita kam murmushi tayi kawai ta haye motar tana gyara zamanta. Mu ma muka shiga a yayin da ma'aikacin wurin ya tattaro kayan da ba'a taɓa ba a leda ya kawo mana kamar yanda Ya Yusuf ya basu umarni. Sai kuma ga abokin Ya Yusuf ya biyo ni da kuɗin ɗazu da ma zube saman teburin don ni har na manta da su ma.


Ya tsaya wurin window ɗin Anty Aysha ya ce "Antyn mu ni dai ina bara, don har da ƙoƙon bara ta nazo, a taimaka a dube ni."


Ya Yusuf ya ce yana dariya "Ji wani ladabi da yake maki kamar mutumin ƙwarai."


Anty Aysha ta ce "kyale shi da dariyar shi, wacce a cikin su?"


Ya ce "Wai da ta gefen ki."


Da sauri ta ce "Kai rufa mun asiri, nan kam babu ruwa domin ajiyar Ya Buhari ce. Idan kuma ka ga zaka iya to Bismillah."


Cikin hanzari Ya Yusuf ya ɗora da "Wane shi? Ka rufa mana asiri kar ja a hanani my whole life Aysha." 


A haka muka yi masu sallama muka tafi sauke Ruƙayya, har ni da Rufaida muna tsokanar ta she's not social, saboda ta ƙi sakewa da kowa a wurin. Da muka sauke ta a gidansu sai Anty Aysha ta ce ta ɗauki ledar kayan gabaɗaya kawai. Amma sam taƙi don abubuwa kawai ta tsinta a ciki ta bar mana ragowan. Har za ta shiga gida Rufaida ta ƙwala mata kira ta juyo za ta dawo, sai Rufaida ta zuro ledar waje a saki a ƙasa har wasu kayan ciki na fitowa ta ce "Ki zubar idan ba ki so." Muka tafi.


Hanyar mu ta dawowa kam wannan karon tuƙin masu nutsuwa Anty Aysha tayi, ko don Ya Yusuf yace tayi a hankali ne? Oho. Ko kuma ƙila don duhun dare ya fara shigowa ne. Sai takwas saura dai muka iso gidan, babu mai jin yunwa a cikin mu.


Muna shigowa muka hango Yaya da direba wurin parking ɗin mota, suka kuma kawo ido su duka suka zuba mana suna kallonmu, ni kam gabana sai ya bada rugugu. Kafin kuma mu gama parking ɗin na ga ya sallami direban, bai saurare mu ba ya wuce falon Mommy. Ƙarin daɗin da muka ji mu duka ganin har lokacin Daddy bai dawo ba tunda ba mu ga motar da ya fita da ita ba.


A bakin falon na tsaya na ɗan leƙa, Yayan dai na hango shi zaune saman dining table, hakan ya sa ni shigowa kaɗan sannan na ce "Momy mun dawo, barka da gida." Tana amsawa kuwa ban jira komai ba na falla da gudu zuwa sassanmu na bar Anty Aysha tana yi wa Mommy bayani tare da ba ta makullin motar, ita ma Rufaida sak yanda na yi ta yi, ba wai don tana tsoron faɗa ba sai gudun kar yau ya sa duka don mun hango fuskarsa babu Rahma.


Ɗakina na shige, ina kuma idar da sallah ban tsaya wata-wata ba na kwashi kayan baccina a hannu na saka slippers na arce da gudu sai gidan Inna, domin yau ba zafi ba ko tururi ake yi a gidanta haka zan haƙura na kwana.


Innarmu tayi mamakin ganina ƙwarai da gaske. Har cewa tayi "Yau kam lafiyar ki ƙalau kuwa? Me ye naga kina ta wani ɓare-ɓare?"


Na ce "Babu komai Inna, yau dai a nan zan kwana."


Tana nazarina ta ce "Wani abu kika yi a can gidan?"


"Ni fa Inna ba wai laifi na yi ni kaɗai ba, ni, Rufaida da Anty Aysha ne muka yi wa Ya Buhari laifi. Ni kawai na zo nan ne sai ya huce sai na koma na ba shi haƙuri."


Ta ce "To ko shine dalilin zuwan shi ɗazu da magriba, muka ɗan gaisa haka yayi ɗan jim sai ya tafi bai ce mun komai ba. Buhari ma da bai cika ɗaukan zafi ba, me kuka yi masa haka?" Sai na faɗa mata me muka yin amma sama-sama.


Har na ɗora haƙarƙarina kan katifar Inna ina jiyo ta tana maganar cewa mu daina yawon mana tunda baya so. Sai yanzu na daɗa gane katifaf inna yayar tabarma ce don da kaɗan ta fi tabarmar, kawai sai na fara dana sanin baro gado na mai laushi saboda gudun faɗa.


Inna kuma ta ci gaba da cewa "Dama ina ta son mu keɓe da ke, kin ga yanzu ai kin fara hankali da sanin ya kamata don haka ina son ki saurare ni da kyau, kina ji na? Lokaci yayi da ya kamata ki raba kan ki da zaman gidan Alhaji. Tun ina ɗauke ido da rufe kunnuwa yanzu maganganu sun fara yawa sosai, an ce saboda son abun duniya mun bar ki kin je kin tare a gidan masu kuɗi ko leƙo mu ba kya yi. Har ce mun aka yi yadda ki ke facaka da kuɗi ko su yaran gidan ba sa yin haka, sannan wulaƙanci ki ke salo-salo...."


Tunda na fara jin ina maganar ta dosa na tashi zaune ina kallonta cikin ɓacin rai matuƙa, ina ga canzawar fuskar tawa ce ta sa ta katse maganar da take yi. Na ce "To ke Inna sai kika ɗauki zancen su da mahimmanci kenan ko? Domin idan ba ki ɗauke shi haka ba ai da ba za ki tunkare ni da maganar ba. Kuma ban da abin ki Inna kamar ba ki san masu gulmar ba? Ina ce fa5i sune masu cewa kin bar ni ina yawo a titi kin ƙi sa ni makaranta? An bar ni ba abinda na sani sai wasa. A cikin akwai mai taimakon ki? Ko akwai wanda a lokacin ya taimaka maki da sani makarantar boko ko ta allo? An ce maki idan nasu ne ya samu damar nan zasu bari ne? Ko za ki ji suna gulma irin haka? Gara ma ki sani su magulmata ko munafukai ba'a iya masu, domin kullum a sa ido suke suna jiran sabon abu ya ɓulla su ɗora akan shi."


Inna ta numfasa ta ce "Hmmmm! Amma ai zancen masu kamar da alamar gaskiya a ciki, kin san rabon ki da gidan nan yau kwanaki sha biyar kenan?! Haba Halimatus Sadiya, ai ko daga daji ka fito ya kamata ka martaba gidanku."


Cikin matsanancin ɓacin rai na ce "To Inna, gobe sai ki je ko kuma ki aika a kwaso mun kayana tunda ba kya son zamana a can." Na kwanta ina ƙunƙuni na juya mata baya.


Ganin na yi fushi, cikin sigar lallashi ta ce "A'a, ni ba haka nake nufi ba. Ni kawai nufi na duk rintsi kar ki yi kwana biyu ba ki leƙo gida ba. Haba Halimatus Sadiya mene na fushi? Haba Halimatu na, Hali dubu ta Innarta da Babanta. Daga yau ba zan ƙara saurarar su ba kin ji? Ai sai na ji maganar ne hankali na zai tashi ko? Yi haƙuri manaaa, ai na ce daga yau shikenan." Daga kwancen na ɗaga kaina alamar na ji amma ban ƙara magana ba.


Da safe da muka tashi babu yanda Inna bata yi da ni naci ɗumame ba amma na ce in dai shine karin safen to ni dai na haƙura. Ganin muna ta ja-in-ja da Inna sai Baba ya fiddo kuɗi (da gani kudin wani abun ne) aka siya kayan shayi, biredi da ƙwai.


Ganin yanda na sarrafa ƙwan har Inna na mamakin ashe har girki muke koya a gidan. Na amsa da "Eh mana, duk ranar Alhamis da juma'a da yamma a kitchen muke yin su, Mommy ce take tura mu wajen kukunsu ya koya mana girke-girke. Haka ranar Lahadi da safe tare muka girki da kukun."


Har azahar ina gidanmu ga shi na daure nayi wanka amma babu kayan da zan sa duka suna can, kuma ba zan iya maimaita wanda na zo da su a jikina jiya daddare ba saboda mun yi sabo da rashin maimaita kaya. To wanka ma dauriya nayi kawai, saboda kasan ya daɗa faffashewa, wani wurin sumunti wani wuri ƙasa sai na dinga jin kaman ban fita ba. Da na fito daga wanka kam na wanke ƙafa ta har ban san sau nawa ba. Da nazo zan shafa mai ne na ga ashe Inna fa Vaseline take amfani da shi, ni rabon da na gan shi ma har na manta, subhanallahi! Mu a can gidan kowa da saitin kayan shafarta, haka kuma koma na waye ya fara ƙarewa za'a ba shi kuɗi ya siyo ba wai sai an jira na ragowan ya ƙare ba. Kai ko sabo ne ka fara amfani da shi ka ce bai karɓe ka ba ma ana iya siya maka wani a take.


Zuwa yanzu kam duk dauriya ta ta zaman gidan Inna ya ƙare, rana ta ɗaga ga shi babu wuta bare a zo maganar AC. Kuma ko ma da wutar ba su da TV bare a zo maganar satellite bare har nayi kalle-kallen da na saba. Kai ni fa kar girman gidan ban da ƙwayayen fitila ba su da komai na na'urar wuta, au! Sai fa wata fankar tsaye irin ta da ɗin nan. Ita ma ogan su Baba ne ya ba shi lokacin yana aikin kamfanin mutumin (kamfanin yanzu kam ya daɗe da rugujewa), lokacin ma ina ƙarama ne ƙwarau da gaske. Idan fankar na busa iska sai ma ka rasa wacce irin iska ce saboda zallar zafi da take busowa. Da ka ji iskar fankar nan gara ka zauna a tsakar gidanmu a ƙarƙashin bishiya don sai ka fi samun sanyayar iska.


Tun a lokacin na fara tausayin Innarmu, saboda kwata-kwata har yanzu daga ita har Baba ba su ɗanɗani daɗin rayuwa ba. Irin kayan da nake sawa masu tsada ne, na kuma san kala guda na kaya na zai iya siyan na Inna guda goma, saboda super print take sawa, lokacin basa wuce ɗari biyar zuwa ɗari shida kowacce ɗaya. Masu daraja a kayan na ta basu wuce ƙaramar ingila da kuma atamfofin da ba su wuce dubu ɗaya ba zuwa dubu ɗaya da ɗari biyu. Na ƙarshen adakarta sune 'yan dubu da dari biyar zuwa dubu biyu.


Mu kuwa irin kayan da ake siyo mana daga waje, sai ka samu doguwar riga ita kaɗai ta dubu goma. Mommy ba ta cika yi wa Inna kyautar kayan sawa ba, sai lokaci zuwa lokaci, ta kan yawaita ba ta kuɗi ne don Inna ta sarrafasu ta yanda ranta ya ke so.


A take a wajen na ƙuduri aniyar fara tallafa masu. Waɗannan kuɗaɗen da ake ba muda bamu komai da su, su zan fara tarawa, sai sun tarun sannan zan san me zan yi masu da kuɗin. In shaa Allah sai Innarmu ta ji daɗi ta dalilina bi'izinillah.


Ita kuma Inna ganin na ƙi maimaita kayan ina ta zama da ɗaurin ƙirji sai kawai ta zauna ta wanke mun su tare da kayan baccin da na zo da shi.