Taƙaitaccen Tunani

22

by @faddabanan

Da la'asar ina zaune a ƙarƙashin bishiya ina tunanin yau ban je makaranta ba, ta bokon da ta islamiyya baki ɗaya.


Kamar daga sama na hangi Rufaida na shigowa gidanmu, ban san ma tsalle na yi da na ganta ba sai da naga na rungume ta. Cikin dariya ta ce "'yar gudun hijira, ya aka yi ne? Bari mu gaisa da Inna tukunna kafin na gaya maki saƙon da aka ce in faɗa maki." Ta wuce suka gaisa da Inna sannan ta dawo wurina.


"To, Yaya ne ya ce in zo na faɗa maki ki zo yana neman ki, idan kuma kin ƙi na saɓo masa ke a kafaɗa in kai ki." Tuni na zazzaro idanuwa, fitsari har ya fara tarar mani saboda tsabar tsoro da kaɗuwa.


Na ce "Don Allah da gaske ki ke? Yau na shiga uku ni ɗiyar Abubakar."


Cikin rashin damuwa Rufaida ta ce "sai ki tashi mu tafi ko kuma ɗaukar ki ke son nayi maki?"


Idona yayi narai-narai, nayi wa Inna sallama kamar na roƙeta ta je ta ba shi haƙuri amma sai nayi shiru. Haka ina biye da Rufaida a baya kamar wata munafuka, domin sanye nake da hijabin Inna da ta wanke tare da kayana ɗazun, har ƙasa hijabin ya kai mun. Gaba na sai faɗuwa yake yi har muka shiga gidan.


Kai tsaye falon Mommy muka dosa, dana nasan ya fi zama a can idan yana gida, da yake ba ma bin sa sashinsa sai dai ya zo namu ko mu haɗu a falon Mommy kamar yanda muka saba.


Mommy ta ɗago kanta tare da amsa sallamar mu, har gara Rufaida tayi sallamar da ƙarfi, ni kuwa a hankali nayi nawa saboda tsoro. A hankali na gaishe da Mommy tare da satar kallon falon don ganin a ina Yayan ya ke zaune. Daga Mommy ba kowa a falon sai mu da muka shigo yanzu, sai kawai na zauna sosai na ƙara ɗaga kaina don na kalli falon sosai sannan na juya na kalli Rufaida da alamar tambaya, sai a lokacin na lura dariya take yi ƙasa-ƙasa.


Na fara tunanin ko dama tsokanata take yi? Kafin nayi magana Mommy ta ce " Yau kuma yaji aka yi mana Halimatu? Idan gida ki ke son zuwa ba sai ki faɗa ba? Akwai wanda zai hana ki ne? Da safe duk kin samu cikin fargaba da aka duba ba kya nan, sai da maigadi ya ce ya ganki jiya da daddare kin shiga gidan Inna shine hankalin kowa ya kwanta. Yanzu da ban aika a kira mun ke ba, da ba za ki zo ba?"


Wani sanyi ya kwararo mun don ganewar da nayi tsokanata Rufaida kawai take yi. A hankali na faɗawa tsoron faɗan Yaya ne ya sa naje can na kwana. Cikin murmushi ta ce "Ashe dai da gaskiyar 'yan uwanki da suka ce ke farar kura ce. Tunda kuna gudun faɗa da duka ya kamata ku guji abinda zai kawo maku hakan ai. Ku tashi ku je."


Da gudu muka ƙarasa sassanmu, ban da Rufaida ta girme ni da duka zan kai mata saboda yanda ta kaɗa mun ciki. Har lokacin ba ta daina dariyar tsurewar da nayi ba da kuma na hijabin da na zulmiyo domin kaf ɗin rayuwata lokacin ne karo na farko da na taɓa saka hijabi mai tsawon wannan, don ko wanda muke sallah da shi ba ya wuce tsintsiyar hannu. Tafiyata na yi na bar ta a falon ganin ba daina dariyar za tayi ba, ɗakina ka wuce kawai.


Ina shiga na lumshe idona ina shaƙar ƙamshin ɗakin, gaskiya nayi kewar ɗakina na kwana ɗaya. Banɗaki na wuce don yin irin wankan da na saba da shi, na tara ruwa a kwamin wanka tare da zuba bath salt. Wannan wankan sai da ya kai ni kusan awa domin ji na nake yi kamar na kai sati guda ban yi wanka ba.


Muryar Anty Aysha na jiyo da alama shigowar ta kenan daga makaranta. Ina jiyo Rufaida na bata labarin abinda ta yi mun cikin ɗagawar murya, na kuma san so take na jiyo, hakan ne ma yasa nayi saurin fara shiryawa don fitowa falon na same su, su duka dariya suke yi. Kiran sallar magriba ne ya katse mun hanzari, don haka alwala na yi sannan na shirya a doguwar riga mai siraran hannuwa marar nauyi, don ta dace da yanayin.


Lokacin da na fito kuma su ma basa nan nasan sallah suka je yi, don haka kwanciya nayi a kujera na fara canza tasha a TV. Wallahi wata nutsuwa da kwanciyar hankali ne ta saukar mun, wannan ce rayuwar da na saba, jiya wallahi ko ƙwaƙƙwaran bacci kasa yi nayi, yanzu haka ruwan ɗumin da na yi wanka da shi ne ya sassauta mun yanayin haƙarƙarina.


Da daddare muna zaune a falon bayan mun gama cin abinci, ni rawar larabawa nake kalla sai dai idan na ji an faɗi wani abinda zan sa baki sai na yi magana. Mun shagalta sosai, ba ma kamar ni don duk a zatona Ya Buhari ya koma ne yau domin tunda na dawo ban ji ɗuriyar shi ba. Kuma da matuƙar wahala a ci abinci dare ba tare da shi ba in dai yana gari, sai dai idan wani babban lamarine ko kuma idan fitar ya haɗa da Dad. Sallamar da yayi ne ta sanya ni daɗa nutsuwa, kamar na gudu amma sai na dake a tare dukkanmu muka yi masa sannu da zuwa. Fuskar shi babu alamar ɓacin rai amma ba wani sosai ya amsa mana ba, ƙila gajiya ce.


Ina ga Anty Aysha ma ta lura da hakan ta ce "Yaya lafiya kuwa? Ganin ka nake yi wani iri?"


Ya yi ɗan ƙaramin tsaki ya ce "Wallahi gajiya ce har ta sa mun ciwon kai. A can na baro Daddy na kasa daurewa, amma nan da awa biyu zai iya dawowa ya ce.


Kallon tausayi nayi masa saboda na tsani a ce mutum ba shi da lafiya balle shi akwai soyayya a tsakanin mu. Yana zaune kan couch ya jingina kanshi a saman kujerar hakanan dafe yake da kanshi da hannun hagunsa na damar kuma yana kan kujera kamar ba shi da lakka.


Rufaida sannu ta yi mashi kamar yanda Mommy da Anty Aysha suka yi masa, amma ban ce komai domin ma ga zatona ina ganin har ma da yunwa a tare da shi.


Ban ce komai ba na miƙe naje kicin. Sanin baya son abu mai nauyi da daddare ya sanya ni duba firij ko akwai abu marar nauyi na ɗumama masa kuma cikin sa'a na iske farfesun kifi na ɗauko na sa a microwave, sai kuma na ɗora masa shayi.


Ganin da kifi zai ci nasan ba zai sa madara ba, don haka da sauri na garzaya gidan Inna na karɓo citta, kanunfari da kayan ƙamshi na dafa shayi, na kuma dawo da gudu. Ban ɓata lokaci ba na ɗora shayin. Sai kuma na soya ƙwai guda biyu na yi masa sandwich ƙwara uku sannan na haɗe su gabaɗaya a babban tire na kawo gabansa a falo na ajiye a gaban sa na ce "Yaya ga abinci, bari na nemo maka magani." Mommy ce kaɗai yanzu ba ta falon, kamar waya na jiyo tana yi.


Na ƙarasa wurin dinning table na ɗauko mug, cokali da plate na dawo gabansa na ajiye, kafin na wuce wurin da ake ajiye magani na ɗauko masa maganin ciwon kai. Na dawo na sake iske shi a yanda na bar shi.


Centre table na daɗa matso masa da shi sannan na jere duka kayan da na kawo tare da zuba shayin zuwa cikin mug ɗin daga flask ɗin, ina ɗora mug ɗin Mommy na shigowa ta yi murmushi ta ce "To ai kai ga 'yar jinya nan ka samu, irin wannan abinci kala-kala haka?"


Hakan ne ya sanya shi ɗagowa ya kalli kayan ya kalle ni sai kuma yayi murmushin dauriyya.


Rufaida ta ce "Yanzu duka wannan Yaya kawai kika yi wa? Ina laifi ma ki yi shayi da sandwich ɗin da ni? Yanzu dai babu ladan ganin ido ko? Cikin dariya ta yi maganar.


Da naga kuma ya fara cin abincin sai na koma kicin na haɗo fruit salad a babban bowl, sannan na kwaso ƙananan bowl ɗin da kowa zai zuba na shi a ciki.


Ina shiga falon, Mommy ta ce "Gaskiya Sadiya kin kyauta wallahi, tun ɗazu nske sha'awar na sha fruit salad kuma na kasa faɗa ma bare a yi mun, sai ka ce me karantar zuciyar mutane. Sannun ki, an gode, Allah ya yi albarka."


Ba mu kwanta ba har sai da Yaya ya kammala cin abincinsa tare da shan maganin sannan Rufaida ta taya ni kwashe komai bayan ta ci abinda ya rage. Shayin da yake a babban flask na juye har Mommy ma sai da ta sha. Muna shirin barin falon Daddy na shigowa, sannu da zuwa muka yi masa muka wuce ɓangaren mu.


Washegari kuma kafin mu tafi makaranta Daddy ya tara mu zai sallame mu domin a ranar zai yi tafiya. Ya kuma yi mana sallama nai kyau ƙwarai da gaske. Kuɗaɗe ya ba mu bayan ya tambaya ya ji ko akwai mai matsala? Ko akwai wani abun da ya ƙare da muke buƙata? Duk mun ce a'a, sannan muka yi godiya da kuma addu'ar Allah ya kai shi lafiya ya dawo mana da shi lafiya.


A makaranta ma ranar 'yan ajinmu kowa sai tambaya ta ake lafiya jiya nayi fashi, don abu ne da ban saba ba. Ruƙayya kawai na faɗawa gaskiyar me ya faru, cikin tsananin mamaki ta ce "Wai dakata mana Halima, me ki ke nufi ne? Kina nufin ki ce mun ba gidan ku ɗaya da su Rufaida ba? Ina nufin ba ku haɗa uwa ko uba ba? This is unbelievable!"