24
by @faddabanan
Tunda naga ya fara murmushi alama ce ta ya huce, nasan kuma yanzu zai fara tsokana ta don haka na shammace na tashi tare da guduwa cikin gida, ina jiyo shi yana kirana amma na ƙi tsayawa.
*****************
Yanzu bai fi wata ɗaya ya yi masa saura ya kammala bautar ƙasa ba, don washegarin da aka yi wannan dabdalar ne ya koma inda ya fito. Ita kuma Anty Aysha an tsayar da maganar bikin su akan da zarar ta kammala jarabawar second semester na aji biyun jami'a, idan ya so sai ta aji uku a ɗakinta. Mu kuma muna zangon ƙarshe don mun kusa fara jarabawa ma.
***************
Watanni kamar kwanaki, Ya Buhari ya kammala bautar ƙasa ya dawo gida. Ya kuma fara shirye-shiryen fara digiri na biyu domin ya ce gara yayi sauri ya kammala tun yanzu kawai tunda ya san dole sai yayi, kuma rage lokacin ne a wurin shi, don ya ce lokacin da zai kammala zzzai rage mun lokaci ƙanƙani na kammala sakandare.
Tunda ya dawo ya zama busy, ko dai su yi tare da Daddy idan yana gari, ko kuma ya kula da wasu abubuwan a Kano a bayan idon Daddy. Domin ma ginin kamfanin da ake yi, shine idon Daddy a wurin, koyaushe yana can. Kuma yana yawan tafiya zuwa jahohi maƙotanmu (ba mamaki har a can ɗin ma suna gina wasu kamfanonin, idan na tuna maganar da na ji rannan).
Yawon mi da Rufaida ba mu fasa ba, ba ma kamar idan Ya Buhari baya gari. Haka kuma duk ranar da muka je Hangout idan har zama muka fara yi kafin mu yi oda na abinda muke so, to kuwa sai dai mu ga an kawo mana kaya kala-kala, duk da zuwa yanzu masu wurin suna kiyaye abinda muka fiya siya saboda yawan zuwan mu. Ranar farko da aka fara kawo mana, na tambaye shi ko nawa kuɗin amma sai ya ce wai kawai umarni aka ba shi ya kawo mana an riga an biya.
Ire-iren kuɗaɗen da Daddy, Mommy ko Yaya suke ba mu nake tattarawa na kaiwa Innarmu, tara su nake a wata ƙaramar jaka a ɗakina, da zarar sun taro sai na raba biyu na kai mata rabi na ɓoye rabin kasancewar ba ni da matsala ta kuɗi.
*****************
Wani abu da na lura da shi tun farkon komawar mu makaranta a zangon farko na aji uku, watau ita Rufaida yanzu tana ajin ƙarshe, shi ne wata cika ta musamman da jiki ya fara, na yi bul-bul na yi kyau. Tun bana lura har na fara, to ko Mommy da ba ta cika magana ba sai da rannan ta ce "Wai me yarinyar nan tawa take ci ne haka ta ke ta zuba kyau."
Ranar da Ya Buhari ya zo (ya kwana biyu baya Kano a lokacin), mun ɗane saman motar gida wurin parking ni da Rufaida, Anty Aysha muke jira ta fito don fita za mu yi. A ka buɗe gate wata mota ta shigo compound ɗin, kasancewar ba mu san motar ba sai ya zamana ba mu wani bata hankalinmu ba, kallo ɗaya za ka yi wa motar kasan sabuwa ce gal ko don sheƙin da take yi, kawai dai nasan ko ma waye idan ya fito daga motar za mu gaishe shi.
Rufaida ce ta fara ganin shi da ya fito daga motar, kawai ihunta naji ta ambaci sunansa da ƙarfi ta kuma dira daga saman motar da nufe shi da gudu tana yi masa oyoyo (kowa a gidan yayi kewarsa, ya daɗe bai jima a wani waje ba irin wannan). Ni ma na sauko daga motar na nufe su amma a hankali nake tafiya, kuma tunda na taho yake kallona ga mamaki zayyane bisa fuskarsa. Ya buɗe baki zai yi magana sai tahowar Anty Aysha da gudu ya katse shi, ya rungume ta sannan muka ɗunguma zuwa falon Mommy kamar yanda aka saba. Sannu da zuwa kawai muka yi masa muka fito don tafiya wurin da za mu.
Anty Aysha da sai lokacin ta lura da sabuwar mota a compound ɗin mu, ta tambayi ko motar waye, Rufaida ta amsa mata sannan ta ƙara da cewa "Anty Aysha kawai ki karɓo mana key mu ɗana." Ya bamu amma sai da ya ci mun cika yawon tsiya.
Gidan ƙawar Anty Aysha muka je za ta karɓo handout ɗin ta da ta ba ta aro, gwaji gare su gobe kuma Rahina (ƙawar ta ta) kwananta uku kenan ba taje makaranta ba. Haɗuwar mu ta farko kenan da ita amma kamar ta daɗe da sanin mu amma akwai alamar za ta yi tsegumi.
Ilai kuwa, lokacin da take rako mu zuwa wurin mota za mu tafi, sai ta dafa kafaɗar Anty Aysha ta cw "Hmmm! Aysha? Kin san wani mummunan labari da naji yana yawo? Kai mutane ba sa kyautawa sam wallahi." Mu kuma muka yi cirko-cirko muna sauraren ta. Ta ci gaba "Labari na ji wai Yusuf ɗin ki aure zai yi very soon, na ji ma an ce ƙila nan da wata ɗaya ko biyu ya rage."
Ga mamakin mu sai mu ga Anty Aysha ta dafe ƙirji kamar irin maganar ta dake ta ɗin nan, ni ban ma san ta iya acting har haka ba, ta ce "Haba don Allah? Innalillahi! Ba'a faɗa maki a ina wadda zai auran take ba? Ya salam! Kai! An shammace ni." Ta ƙarasa maganar cike da jimami.
Fuskar Rahina ta ƙara warwarewa da alama yanayin Anty Aysha daɗi ya yi mata duk da tana ƙoƙarin ɓoyewa. Ta ce "Inaaa fa! Da na jiyo a ina take ai da tuni na faɗa maki ma ba sai kim tambaya ba. Na dai ji an ce ɗiyar babban gida ce tun daga kuɗi zuwa mutunci. Yanzu haka idan kika bibiya ko ƙafar ki ba ta kamo a kyau ba, kai maza munafukai ne." Mu fara tafiya domin ƙarasawa jikin motar, ta cigaba da faɗin "Kalla rannan da ya zo makaranta har da su kuka don ki aure shi, shi ne har ya juya wurin wata...." Maganar ta katse da ta lura da motar da muka zo da ita.
Ta ce "Kar dai ki ce mun a motar nan kuka zo? Maa shaa Allah." Ta shafi jikin motar. Duk cikin mu ba wanda ya ce mata ci kan ku, ni haushin ta ma nake ji don tsaki nake ta yi a raina. Kafin mu wuce sai na ji Anty Aysha na ce mata aro aka ba mu, ba tawa ba ce.
Sai da muka hau babban titi sannan Rufaida ta ce "Gaskiya Anty Aysha ki daina kula irin waɗannan mutanen, kina ganin ta kin san akwai kwaɗayi, fadanci ga uwa uba sa ido. Allah har maula duka za ta iya." Ina dariyar maganar Rufaida na ƙarasa maganar ta da faɗin "Wallahi wannan ƙawar ta ki bata yi ba sam."
Anty Aysha ma dariyar take yi ta ce "Ku dai ban ga ranar da za ku iya zama da mutane ba. Yanzu kuna gani har ɗadi ta ji da na ce ban san batun auren Yusuf ba, zuwa lokacin da za ta katin bikinmu imma da wani manufa a ranta a ƙalla na jinkirtar da ita."
Ta rage gudun motar tare da wuce yalo fiban da ke bada hannu muka shiga kwanar da maida mu ɗayan titin sannan ta ci gaba "Na rasa me ya sa Rahina ta sa wa rayuwata ido wallahi, kullum ƙoƙarin kauce mata nake yi amma sai ƙara shigata take yi. Ranar da Yusuf da har aka yi abinda aka yi a makaranta ba fa a gaban ta ba ne, ban ma san a ina ta jiyo labarin ba shi ne ta biyo tana kyarmar ɗuwawu....." Dariyar da muka kwashe da ita ne ya katse maganar da take yi.
Da muka dawo gida ban ma lura da Ya Buhari da ke zaune kan fararen kujerun da ke zuɓe ɗan nesa kaɗan da wurin parking ba, har na zo na gota shi hankalina ya yi gaba. "Ke!" Ya ce. Abin ka da farar kura nan da nan jikina ya hau rawa gaba na yana faɗuwa, bacin ma ƙafafuwana sun yi sanyi da tuni na sa gudu zuwa cikin gida. Rufaida da ke baya na ce ta lura da abin da ya faru, dama ita da ƙeta manyan abokai ne, ta dinga ƙyalƙyala dariya kafin ta ce "Shegen tsoro! To Ya Buhari ne, kin gan shi yana yi maki dariya."
A daidai lokacin Anty Aysha ta ƙaraso ta kuma miƙa masa makullansa tana maganar sabuwar mota zar daɗi. Su suka wuce cikin gida suka bar ni ni kuma irin kallon da ya ke mun ne ya sa kunya ta lulluɓeni.
Na dawo kusa da shi na tsaya, na ga bai rage kallon da yake mun ba sai na zauna kan wani babban dutse kusa da kujerar shi na sanya tafukan hannayena na rufe fuska ta da su. A daidai lokacin kuma na jiyo ƙaramar dariyar shi, irin wadda yake yi idan ya ga nayi abin da a ganin shi yarinta ce kawai!
Ya ce "Baƙin cikin ganin kyan da kika ƙara ki ke mun Sadiya? Faɗa mun menene sirrin ne?"
Na daure na zame hannuna daga fuska ta kafin na ce "Haba Yaya, kai ba ka kyan da ka ƙara ba sai nawa kake hange? Nawan da idan ma na yi ba wani mai yawa ba ne?"
Ya amsa "Ikon Allah, ku fa mata haka kuke, idan an ce wani abu naku ya ƙaru ko an ce kun yi kyau, ba zaku amsa kai tsaye ba duk kunsan hakan ne, sai ku fake (ya maƙale murya yana kwaikwayon muryar mata) haba dai? A hakan? Yanzu har kyau na ƙara? Don ma ba ka ganni kwanaki ba?" Na dinga dariyar maganar da yake yi.
Cikin dariyar na amsa da "Allah ba haka ba ne, kai kam kowa ma ya shaida. Amma ta ɓangarena nasan dai na ɗan yi haskw, tsawo da ƙiba kaɗan, ban dai san ko su ka gani kake kira kyau ba."
Yana ƙaramar dariyar nan ta shi ya ce "Ƙiba? A tunanin ki ƙiba kika yi kawai?" Ya sake dariyar tare da juyar da kanshi gefe sannan ya cigaba da murmushi idonshi har ƙyalli yake yi "Cika da ƙiba abu ɗaya ne?"
Ni kuma na daure na cire kunya na ce "Eh mana, idan akwai bambanci kuma ka faɗa mun don na fara ganewa daga yanzu." Na juyo na kalle shi alamar sauraren shi nake yi.
Ya ragw girman idon shi ya ce "Ke yanzu ba ki lura da cikowar ƙirjinki ba?" Gaba na ya faɗi, ashe dai Yaya ba cikakkiyar kunya ce da shi ba? Ya ci gaba "Ko rantsuwa zan iya yi brassieres ɗin ki duka sun yi maki kaɗan, shi kuma ƙugun nan a ina kika samo shi? Ko tafiyar nan da nayi ba ki kai haka, shi dole skirt ɗin kayanki na daa imma kin buɗe ko kin yi kyauta da shi. Sannan shi kuma...." Ban ma jira ya ƙarasa faɗin abinda ya fara ba na sa gudu, kawai a falonmu na ganni tsaye ina haki tare da mayar da numfashi. Kai jama'a! Ashe Ya Buhari ba shi da kunya? Rashin ta idon har ta kai haka?