MAI DAKI

013

by @nanahaleema11

*MAI ƊAKI...!*

      Fitattubiyar


          ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*

*Page 13*

      



Yadda ta firgice tana zare idanu shine ya kai hankalin sa ga hannunta da kud'in da suka zube a k'asa sun watse ya bisu da kallo yana kallon ta cikin mamaki mai yawa kafin yaga ta daidaita nutsuwar ta ta sunkuya ta tattara kud'in ta nufi inda kayan ta suke ta buɗe ta saka ta juyo suka had'a ido ta sake d'aure fuska ta wuce ta zauna a gefen gado tace, "Haka kawai a dinga shigowa mutane babu sallama."


Shigowa d'akin yayi jikin sa yayi sanyi zuciyar sa na bugawa a guje tsoro ya gama mamaye jikin sa k'araso yana kallon ta yace, "Fiddausi wannan kud'in masu yawa a na waye?." K'aramin tsaki tayi ta murguda baki tace, "Bafa kud'ina bane kud'in Mama ne ta bani na ajjiye mata, kasan dai ba wannan kudin ne dakai ba balle kace sata na fara yi maka dan bana tunanin ka tab'a rike kud'i kamar su."


Share abinda tace yayi dan so yake yaji yace, "Amma yadda kika firgita hakan ya nuna min kamar baki da gaskiya" idon sa ya kai kan iPhone 11 d'in da take hannun ta a d'azu ya k'arasa wajan wayar zai d'auka tayi zaraf ta d'auka tace, "Wai yaushe ka koma mai bincike ban sani ba?, kawai dan kaga waya baka san ta wacece ba sai ka dauka?. Na fad'a ai tawa ce ko? Zakiyya ce ta aramin nayi amfani da ita."


"Me zakiyi da ita da kika ara? Ke meyasa bakya gudun abun magana ne Fiddausi?."

"Meye abin magana a nan?, naga dai kawata ce kai ka san da hakan ko?."

"Kawar ki ai ba y'ar uwar ki bace ba."

"Kaga Abban Amir dan Allah ka kyale ni kaje ka kwanta ni na gaji bana son magana" ta kalli d'akin taja tsaki tace, "Ni wallahi na gaji da zama a duhu, tun ban shiga kabari ba na saba da zaman duhu wallahi bazai yu ba."


Numfashi ya sauke yana girgiza kai zuciyar sa tana so ta jefa masa alamar tambaya akan Fiddausi domin abubuwan da take yi ya fara k'in amincewa da lamarin taya cize bakin sa ya fita domin kuwa dole yasan abinda zaiyi. Yana fita tayi tsaki tace, "Aikin banza, ko ta tsiya kota arzuk'i sai na bar gidan nan wallahi. Ni a dawo min da d'ana ma hutun ya isa haka na gaji da zaman gidan nan babu shi."


*Washe gari.*


     Tunda Yayar Bauchi ta sanar da Amina ta taso ta daure take dan yi mata abinda zata ci dan zuciyar ta cike take da zumudin ganin yayar tata dan sun jima basu had'u ba tun wani taro da akayi suka had'u basu sake ganin juna ba. Sai a lokacin Yusuf ya sakko ya same ta a tsaye a falon tana magana da masu aikin ta ganin sa suka gaishe shi suka bar falon.


Juyowa tayi ta kalle shi suka had'a ido sai tace, "Barka da safiya." Gira ya d'age duka biyun yana kallon ta kafin ya furzar da iska daga bakin sa yace, "Barka" yana fad'a ya fita daga falon bai sake ko kallon ta ba ta bishi da kallo tayi saurin kawar da abinda yazo ranta ta koma ta cigaba da aikin ta.


Sai azahar Yayar ta ta shigo cikin gidan a lokacin ta gama yi mata komai ta shirya tana zaman jiran zuwan ta. Shigowar ta ya saka Amina tashi a guje ta fad'a jikin ta sai kawai ta fashe da kuka.


Rungume ta tayi itama tana shafa bayanta tana fadin, "Haba Amina yanzu irin tarbar da zan samu daga wajan ki kenan?." D'agowa tayi ta goge idanun ta tace, "Kiyi haƙuri Yayata, Sannu da zuwa, muje sama kiyi wanka ki huta." Hannunta ta riƙe zasu hau saman sai a sannan ta lura da babar yar Yayar tata mai sunan Maman su wacce suke kira da Amira tace, "Amira ai ban ganki ba."


Tayi dariya tace, "Taya zaki ganni Anty Amina kina murnar ganin Mama?." Dariya tayi tace, "Bari kedai kawai, Yaya nake gani kuma Mama nake gani a fuska guda d'aya." Dariya Amira tayi kawai suka hau saman gabad'aya tana jin kewar mahaifiyarta na sake zagawa jikin ta.


Dak'i suka shiga wanda yake kusa dana Amina ta kalli Yayar tace, "Yaya kiyi wanka bara na kawo muku abinci" ta fad'a tana niyar fita. Hannun ta Yaya ta rik'o tace, "Ba wanka ko hutawa ne ya kawo ni ba Amina, nazo ne akan abinda yake damun ki har kikayi wannan ramar." Kallon Yayan tayi jin yadda take magana da rauni tana kallon ta alamun abin na damun ta sai tayi murmushi tace, "Ku fara hutawa tukkuna Yaya, Amira shiga kiyi wanka zaki ji dadi. Ina zuwa" ta fad'a tana fita duk suka bita da kallo ganin yanayin tafiyar tama kana kallo kasan bata da cikakkiyar lafiya.


Sai da ta tabbatar sunyi wankan sannan ta dawo saman da manyan flakas masu kyau ta ajjiye a falon sannan ta shiga d'akin ta same su har sun canja kaya tace, "Yaya ga abinci a falo kuzo muci" bata jira amsa ba ta juya ta fita dan bata son su fara maganar sai Yayan ta huta. A tare suka fito suka zauna suka fara cin abincin sai babu wanda yake magana a cikin su burin Yaya bai wuce taji damuwar tilon kanwar tata b shiyasa ta kasa sukuni tayi shiru dan kar ma wata hirar tazo.


Ameena tace, "Ina aka baro Hidaya da Abban mu?." Yaya tace, "Suna gidan kakar su daman sun je Hutu."

"Aka musu wayo aka tawo babu su."


Bata ce komai ba Yayan bata ci sosai ba ta ajjiye ta kalle ta tace, "Amina ba cin abinci ne ya kawo ni abinda yake damun ki nake so naji. Me yake faruwa a cikin gidan nan haka?." Shiru tayi ganin hakan ya saka Yaya ta kalli Amira tace, "Amira dauki abincin kije daki kici." Ba musu ta tashi ta dauki plate din abincin ta shiga d'aki ita kuma ta fuskance ta tace, "Ke nake saurare."


Ameena ta sauke numfashi tace, "Yaya aure Yusuf zaiyi."

"Nasan wannan kin fad'a min tun a waya, dalilin zai k'ara aure ne kika koma haka Ameena?." Kai ta girgiza alamun A'a hawaye ya sakko daga idon ta ta share tace, "Ba aure ne yake d'aga min hankali ba Yaya, canjawar da yayi shine abinda yake bani tsoro. Yaya yanzu Yusuf bai San damuwata ba ko kallo ban ishe shi ba, zaman gidan nan gabadaya ya gama gundura ta, barin sa kawai nake fata."


Yaya ta dawo kusa da ita ta dafa kafadarta tace, "Auren sa kar ya dame ki Ameena tun farkon auren ku nasan babu lallai ya rayu dake ke kad'ai a gidan nan, canjawar sa kuma zan iya cewa a cikin kaso d'ari na mazan hausawa in zasu k'ara aure kashi tamanin sai sun canjawa matan su. Kar wannan ya dame ki kalli yadda kika koma dan Allah kamar ba ke ba, na tabbata babu lallai ya samu macen da ta fiki Ameena, ki kwantar da hankalin ki. Yanzu da kika saka damuwa kika rame akwai abinda ya fasa daga hidimar gaban sa?" Ta tambaya tana kallon ta.



Girgiza kai tayi alamu A'a Yaya ta kuma cewa, "to meye na saka damuwar? Kinga tabbacin duk abinda ya same ki wannan ke kika jawowa kanki koda mutuwa kika yi bazai fasa auren sa ba. Nasan da ciwo amma ki daure ki kawar daga zuciyar ki wata rana sai labari." Idanun ta sun jiqe sa hawaye tace, "Amma Yaya ban dauk'a zai min kishiya da sauri haka ba, kwata-kwata kwanan mu nawa da auren har zai kawo mata?. Na tambaye shi ko akwai inda na gaza har yake k'ok'arin d'auko wata yak'i ya fada min. Yaya ya canja fiye da tunanin ki dan yayi kwana biyu bai waiwaye ni ba abu mai sauki ne a wajan sa Yaya, dole na damu kin San ina son sa tun ba yanzu ba zuciyata ji nake kamar zata fashe".


A kafadarta ta kwantar da ita tana shafa kanta cikin rarrashi tace, "Nasan kina son Yusuf Ameena nafii kowa sanin hakan, shima yana sonki wannan canjin na d'an lokaci ne duk zai zo ya wuce ya zama labari."

"Allah Yaya asiri yarinyar tayi masa dan baki ga yadda ya gigice ya daina kula ni kawai yana tunanin nice nake zuga Amma tak'i ya aure ta".

Yaya tayi karamar dariya tace, "Hmmm ba wani asiri Amina, kawai in namiji yaso k'arin aure hankalin sa kamar barin jikin sa yake sai yayi yake dawowa daidai, kar ki damu komai zai wuce In sha Allah."


Shiru sukayi dukkan su babu wanda yayi magana kafin Amina ta dago daga jikin Yayan ta goge idanun ta Yaya tace, "Kiyi hakuri ki daina saka damuwa a zuciyar ki ke hakan zai cutar ba wani ba. Ni banga abinda zai saka ki rama haka a cikin abinda kika fad'a ba, Anya iya abinda yake damun ki kenan?." Ameena tace, "Shikenan Yaya bayan wannan babu komai." 

"To aure akan ki aka fara da zaki tayar da hankalin ki haka? Nasan babu dad'i amma ai komai zai wuce, ki jira yayi auren ki gani zai koma yadda kika san shi a baya, kawai ki ta addu'a Allah ya had'a ki da abokiyar zaman ta garı." Kai ta girgiza alamun gamsuwa tana Jin nutsuwa na shiga zuciyarta ko babu komai ta samu rarrashin data jima bata samu ba.


    Sallar la'asar ce ta tashe su daga wajan sukayi sallah Yaya ta tilasta mata taci abinci nan da nan ta sake tana hira da Yayarta kamar ba ita ba. Bayan sun idar ne Yaya tace, "Badan na gaji ba dana lek'a gidajen su Sumayya wallahi." Ameena tace, "Sai kije gobe."

"Kai da wuri nake so na wuce gobe gaskiya, da dai Yaya Adam yana Kano a can ai zan kwana bazan yi abin kunyar kwana a gidan k'anwa ba." 


Ameena tayi dariya tace, "ai tafiya ce mai nisa kika yi ba wani abun bane ba." Yaya tace, "Kedai kawai baki san yadda nake jina a d'aure ba wallahi." Dariya kawai tayi suka cigaba da hira. Kamar yadda ta saba bayan sallar magriba tayi girki tayi wanka ta shirya duk da batayi kwalliya ba amma dai tayi kyau tana zaune wajan su Yaya suna ta hira har Yusuf ya dawo bata sani ba. Fitowa tayi da niyar dauk'ar lemo a fridge nan tayi karo da leda a kan stool har zata wuce sai ta k'arasa ta bud'e taga cake ne k'anana masu kyau a ciki ta kalli saman sa dan dai tasan ita ba ma'abociyar yin cake bace Tunda mai gidan baya ci sai dai ya siyo taci ta bayar dan yasan tana so.


"Ya dawo kenan?" Ta tambayi kanta tana sake kallon sama kafin ta k'arasa wajan varanda ta bud'e nan ta hangi motar sa a ajjiye alamun ya dawo, baya ta dawo ta kulle varandar ta d'auki d'aya a cikin cake din ta fara ci dan a tunanin ta ita ya tawowa dashi kamar lokacin baya. A daidai nan ya sakko ya bita da kallo itama shi yake kallo a fusace ya k'araso ya kwace ledar hannun ta yace, "waye ya baki damar tab'a min cake? Dan kawai kinga abu sai ki d'auka kici naki ne ko kuma ajiya kika bani ko aike na kikayi?."


Ganin yadda yake fad'a sosai sai ta zuba masa idanu tana kallon sa ganin hannun sa da takardar cake din da alama yaci kenan, mamaki take yi dan baya ci Tana kuma mamakin abinda ya saka shi fad'a haka. ganin tayi shiru sai binsa sa da take da kallo ya saka shi yin tsaki ya kwace ledar daga hannun ta yace, "karki sake kuskuren tab'a min abu indai bani na baki ba, bana son bincike."


Gabad'aya daina Jin taste din cake din tayi hakan ya saka ta had'd'iyewa dakyar tace, "Kayi hakuri na saba d'auka ne in kazo dashi sanin ni din kake kawowa kai ba ci kake ba." A sanyaye tayi magana hakan ya saka shi sakar mata harara yace, "to yanzu Ina ci, kar ki sake wannan gangancin na fada miki, in naki ne in na shigo zan baki." Kai ta girgiza kai ya saka yin tsaki ya juya zai hau sama tace, "ina zan kawo maka abincin?."

"Ki barshi bana ci kar kuma ki dame ni bana son takura" ya fad'a yana hawa sama ya barta a tsaye Tana kallon sa har ta daina ganin sa sai sautin kulle k'ofa da taji.


K'asa ta sauka ta shiga kitchen ta kulle kanta ta fashe da kukan da ya zamar mata abokin hira, sai da tayi mai isar ta sannan ta fito bayan ta wanke fuskar ta ta koma saman d'akin dasu Yayan Kaduna take. Hira ta samu sunayi da Amira sama-sama ta shiga da sallama ta zauna Yaya ta bita da kallo tace, "Na dauk'a kin tafi wajan mijin ki sai da safe kuma?." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ganin hakan sai Yaya tace, "Ba nisanta kanki zakiyi dashi ba a wannan lokacin samu zakiyi ki kusanta kanki dashi fiye da baya, wannan baya-bayan da kike dashi bazai haifar miki d'a mai ido ba."


Numfashi ta sauke sannan tace, "To Yaya zanje yanzu, ban sanar dashi zuwan ki bama da yazo kun gaisa."

"Ma gaisa da safe in Allah ya Muna mana, yanzu tashi kije ga Zaitun nan har tayi bacci."

Amira tace, "Anty ki bar min zaitun din a nan in baza tayi kuka ba." Amina ta kalli Zaitun tace, "Baza tayi kuka ba, bara na kawo miki maganin tarin ta ki tashe ta ki bata tasha."


Yaya tace, "Ya kamata kuwa dan naji tun d'azu take tari." Amina bata ce komai ba ta tashi ta fita zuwa dakin ta. Bata ga maganin ba hakan ga bata tabbacin yana saman Yusuf ta kama k'ugu tana kallon sama tare da furzar da iska dan bata son zuwa inda yake. Bata da mafitar da ta wuce dole ta fita zuwa saman nasa duk jikin ta a sanyaye.

Hannu ta d'ora da niyar murd'a handle d'in d'akin sa sai ta fasa ganin ta a bud'e ma zata tura taji yana fad'in, "Ke yayi dad'i my love ban tab'a cin sa ba sai wannan da kika bani."


Dariya taji yayi yace, "Bari kawai kedai burina bai wuce na ganki a cikin gidan nan matsayin matata ba, gabad'aya bana jin sha'awar ko wacce mace sai ke kawai." Shiru yayi alamun Ana bashi amsa kafin taji ya sake cewa, "Hmmm! Bari kedai kawai waye yake ta waccan Kullum abu ba canji? Ke nifa da ke na samu bazan sake yin aure a rayuwata ba, ta ko ina kin had'u baki da abin kushewa ko kad'an, ni na tabbatar zan samu abinda nake so a wajan ki shiyasa bani da fargabar komai. Kya had'a data gidan nan da ko......." Sai kuma taji yace, "Hmmm a dai yi shiru kawai."


K'irjin tane yake duka sosai bata san ta bud'e dakin ba sai had'a ido da sukayi dashi ta haddiye abinda yazo mata wuya tayi k'ok'arin mayar da hawayen idanunta ta shiga ciki kai tsaye inda ta hango maganin tayi ta d'auka ta fita ba tare da ta sake kallon sa ba. 

Jikin sa ne yayi sanyi dan ya tabbatar taji me yace yasan kuma k'arya yake yi abinda yake fad'a ba gaskiya bane kawai dan waccan taji dad'in kalaman sa ne, ya d'an cize bakin sa kamar ya tashi ya biyo ta sai kuma ya fasa ya cigaba da waya da masoyiyar sa.


      A guje ta fad'a kan gado tana kuka kalaman da ya fad'a suna mata amsa kuwa a kunnen ta ta saka hannu ta toshe kunnen ta zuciyarta na bugawa sosai, bata d'auka abin nasa ya kai haka ba shiyasa jin kalamin sa ya tayar mata da hankali. tashi tayi zaune Tana goge idanun ta amma wani hawayen ne yake sake sauka ta tashi da son kawar da tunanin ta shiga wanka. A haka ta shirya ta fita ta kaiwa Amira maganin ta dawo dak'in ta kwanta badan tana jin bacci ba sai dan kawai bata so Yaya tasan tana dakin ta ba dakin sa ba.



_An fara Payment na MAI DAKI book 2&3 akan naira 500 kacal duka biyun, akwai ajin VIP shi kuma naira 1k ne. Domin yin payment neme ni a wannan number 0930398006 but only on WhatsApp pls._



#Share

#Vote

#Comments

#Book1

#Nana Haleema