016
*MAI ƊAKI...!*
Fitattubiyar
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 16*
Hankalin Rukayya duk ya tashi bata tab'a ganin mata da miji suna fad'a gaban ta ba jikin ta har rawa yake yi hankalin ta ya kai k’arshe wajan tashi sai bin su take da kallo tana dana sanin ma zuwa gidan , a zabure tabi bayan Fiddausi zuwa d'aki ta same ta a tsaye tana mita cikin masifa kamar a gaban sa take.
"Haba Fiddausi!, Haba Fiddausi, mijin ki kike yiwa wannan rashin kunyar har haka? Kuma ko kunya bakya ji a gaban idanuna?."
Fiddausi ta kalle ta tace, "Ke din bak’uwa ta ce? Ko kuma akwai abinda zan b'oye miki ne?. Kinga na gaji da zama da mutumin nan wallahi saki na nake so yayi ko yana so ko baya so, zaman shekara biyar d'in da nayi dashi Allah ya amfana nayi k’okari iyakar iyawata, tura takai bango a wannan lokacin bazan iya ba wallahi." Rukayya mamakin ta kawai take dan bata san rashin hankalin Fiddausi har ya kai haka ba tace, "Wai kina cikin hankalin ki kuwa? Kin samu miji mai sonki da qaunar ki da burin kyautata miki shine kike neman yiwa kanki salalan tsiya?, ne ya shiga kanki ne? Ina ilimin addinin da na sanki dashi?. Kowa a unguwa kwatance yake da mijin ki yana fatan y’arsa ta samu kamar sa amma shine kike fad’ar haka?.”
Fiddausi tace, "kee har ilimi in talauci yayi yawa fecewa yake, ki adana wa'azin ki wallahi bazan raga masa ba daman kiris nake jira, bai isa yayi min na kyale ba, solar kuma dole na saka tunda kudina ne."
"A Ina kika samu kudin ke?."
"Wannan kuma sırrı ne bai dame ku ba, Kun San dai ba sata zanyi ba." Girgiza kai Rukayya tayi tace, "Wallahi kin bani mamaki, kin bani kunya, ban tab’a zaton hakan daga gare ki ba. Mijin ki na aure, mijin ki na sunna kike yiwa wannan tijarar a gaban idon b'akuwar ki kuma hakan bai dame ki ba. Mijin ki uban d'anki wanda kika haifa Keda shi kike yiwa wannan wulaqancin kawai sabida wani abun ya rufe miki ido. Kiyi gaggawar neman yafiyar sa in ba haka ba zaki kuskuren da baki tab'a yi ba a rayuwar ki."
Dariya Fiddausi tayi ta tafa tace, "Ai kuskuren nake so nayi Rukayya, indai wannan fak'irin zan bawa hakuri kice za'a tashi kiyama kenan, kuma wallahi bai isa ya hanani abinda nayi niya ba Tunda shi bashi da kud'in da zaiyi min. D'ana kuma dole a dawo min dashi gabana na gaji da zaman gidan nan baya kusa dani." Rukayya da take kallon ta mamaki sai ya hana ta sake cewa komai sai kallo kawai kafin ta bud’e baki tace, "in ma wani yake zuga ki, in ma aljanu ne a akanki Ina baki shawarar kiyi gaggawar neman mafita dan zasu kai ki su baro kine, suna so ki aikata kuskuren da har abada baza ki goge shi ba. Mijin ki ba talaka bane domin ya tsare miki dukkan haqiin ki da yake wuyan sa, ke kinfi matar wani mai kudin Kyan gani sabida kulawar da yake baki. Talaka shine wanda bashi da cin yau bare na gobe ke kuwa kin fin k’arfin abinci” ta sassauta murya kana ta cigaba da cewa,
"Kin samu miji Allah ya rufa miki asiri meyasa kike son tonawa kanki asiri kina d'aga murya maqota suna jinki? Mu da bamu da mijin nema muke meyasa kike wulaqanta naki Fiddausi?. Ina ilimin da ake baki kyauta a kansa lokacin da Muna islamiyya? Ina duk suka tafi?, ya akayi kika bari shaid......" saurin dakatar da Rukayya tayi tace, "Ke bani da wani aljan ko shad’ai ko zuwan bil adama kamar ni da zaiyi tasiri a kaina, duk wannan soki burutsun da kike ba tasiri zaiyi a kaina ba. Zancen miji da nake dashi baki dashi me zai hana bazaki auri ibrahim d’in ba? Daman ai naga ke talaka kike nema ko? To Gashi kin samu ki aura ki shigo ki zauna ni kuma na fita domin banga abin kishi a wajan sa ba. Ke ko ina gidan nan ma ki shigo, banga abinda zanyi kishi a wajan sa balle ni ficewa zanyi wallahi bazan zauna ba.”
Mamaki ya saka Rukayya ta kasa magana sai kawai ta fara hawaye ta toshe bakin ta tana girgiza kai dan bata d’auka son duniyar Fiddausi ya kai haka ba tace, "kiji tsoron Allah Fiddausi, kiyi ta’awizi ki kori shaid’an in ba haka ba wallahi yana gab da komawa gefe yayi miki dariya. Shawara nake baki matsayina na k’awar ki mai son cigaban ki, wallahi Fiddausi ki tuba kije ki bawa mijin ki hak’uri.”
“Wallahi baza ni ba, ina kuma tabbatar miki da baza ki sake dawowa ki tarar dani a gidan nan ba sai dai wani amma ba nan ba, ke ki aure shi kinga kin samu abinda kike so.”
“Allah yana kallon ki duk abinda kike yi Fiddausi” abinda ta iya fad'a kenan ta juya ta fita daga d'akin da sauri. A zaune taga Ibrahim yayi tagumi fuskar sa ta nuna alamun b’acin rai da alama duk yaji abinda suka tattauna bata iya yi masa magana ba ta fita a guje tana kuka zuciyar ta na sake tabbatar mata tabbas akwai abinda yake damun Fiddausi.
^^^^^^^
A haka Rukayya ta shiga gidan su tayi d'aki a guje kai tsaye band’aki ta shiga tayi alwala ta fito ta daure tayi sallar magriba ta zauna jugum abinda ya faru yana yi mata yawo a kanta gani take kamar a mafarki shiyasa take mamakin abun sosai. Bata tab’a ganin fad’a ba mata da miji a zahiri ba sai da a film ko a littafi, mata da mijin ma kuma wai k’awar ta Fiddausi.
"ke Rukayya!" Aka fad'a Ana shigowa ta juya ta kalli Umman ta da ta shigo tace, "Na'am Umma."
"Sai yanzu kika ga damar dawowa daga gidan Fiddausin? Bayan kin San na fad'a miki zakiyi bak'o?."
Ajiyar zuciya tayi tace, "Kiyi hak’uri Umma na manta ne wallahi." Umma ta Harare ta tace, "Ai dole ki manta tunda daman ba so kike ba, tashi kije gashi can a d'akin Baban ku saura ki dawo naji wata magana daban." Da to ta amsa ta tashi jikin ta a sanyaye ta fita zuwa falon Abban nasu da hijjabin da tayi sallah a jikin ta.
Tunda ta doshi shiga d'akin take jin warin sigari; da ta sake kusantar falon ta tabbatar a ciki take jin warin, kai ta saka ta shiga ta hango wanda akace zai zo hannun sa rik’e da sigari yana sha yana busa ta sama ganin ta shigo sai yayi saurin cillar da ita akan tiles ya saka k'afa ya take ya mik’e tsaye yana dariya da yaga shigowar ta.
Fuska ta d’aure dan bata son sakar masa fuska ma ya samu wata dama ta saka gefen Hijjabin ta ta toshe hanci tana kallon sa shima haka kafin yace, "Barka da zuwa hajiya Rukayya." Bata cire hijjabin a bakin ta ba tace, "kaine bak’on nawa?." Ya gyara tsayuwa yace, "Kwarai nine, na jima Ina sonki wallahi."
"Ni kuma bana sonka kar ka sake ka sake zuwa gidan mu, bazan aure ka" ta fad'a tana niyar barın falon taji yace, "ji mana y’an mata, ai daman ba sai kin soni ba taimaka miki nazo yi sanin kin jima a gida babu mai zuwa yace yana sonki, kizo na taimaka na aure ki na rufa miki asiri kafin a fara kad'a miki ganga ana yawo da hoton ki a masallaci.”
Takaici bai bari ta bashi amsa ba ta fita da sauri ta bar masa falon zuciyar ta na k'una hawaye sun ciko idanun ta. Shikenan da ka samu jinkirin aure ko wanne banza yazo sai a bashi dama ya ganka, Tsautsayi ya saka ka amince kuma ayi auren wani abun ya faru azo ana dana sani.
Tana shiga falon Umma zata wuce Umma ta dakatar da ita tace, "Ya kuka yi dashi naga har kin dawo?.” Ta kalli Umma a lokacin hawaye suka zubo mata tace, "Umma dan na kai wannan lokacin banyi aure ba ba hakan yana nufin zan auri dan shaye-shaye ba ko mai kama da haka, Umma taba fa yake sha a gaban idanuna ko kunya baya ji kuma sunan yazo gidan mu neman aure.”
Tsaki Umma tayi tace, "Dan yana shan taba sai me? Baban ki ma da yasha taba kafin ya girma ya daina. Kina so kice min kawai kin kore shi ko?." Ta goge idanun ta tace, "Gwara na mutu babu auren Umma da dai na amince na auri irin su, bazan iya auren sa ba dan Allah ki fahimce ni. Duk sanda na gari yazo zan amince amma banda wannan.”
Umma tace, “Yaushe zai zo? Mun jima Muna jira har yanzu bai zo ba meyasa baza ki amince da wanda yake hannu yanzu ba?.”
“Bazan iya ba wallahi Umma, kiyi hak’uri.”
Umma zatayi magana aka dakatar da ita cikin taushin murya mahaifinta yace, Rukayya kina da wanda kike so ne?." Jin muryar Baba ta ya saka ta d'ago ta girgiza kai alamun babu yace, "To haka kike so mu saka ki a gaba muna kallo babu aure Rukayya?, duk wanda yazo kice bakya so?.”
"Baba duk wanda ake kawo min bana gari bane, in na amince nice zan shiga cikin wahala, nasan inda Kaga abinda wannan da naje yake yi da kanka zaka ce bazan aure shi ba" ta fad'a murya ta rawa sabida kukan da yaci karfin ta.
Baba ya sauke numfashi yace, "Allah ya kawo na garin, tashi kije." Kamar jira take ta tashi ta shiga dak’i k’anwar Zuhra ta tabi bayan ta, Umma ta kalli Baba tace, "Na gaji da halin Rukayya wallahi, kowa yazo tace bata so to wa take so?." Abba ya kalle ta yace, "Ki cigaba da yi mata addu'a kawai, Allah ya yanke mata da gaggawa" yana fad'a ya tashi ya fita zuciyar sa duk babu dadi, inda abinda yake so bai wuce yaga Rukayya tayi aure ba kanwar ta har haihuwa tayi ga wata an kusa biki itama.
Kuka Rukky take yi sosai tunda ta shiga d’aki dan bata san me zatayi ba, Zuhra taji tausayin ta sosai tace, "Kiyi hakuri Anty komai zai wuce." Kai kawai ta girgiza tana kin kuna a zuciyar, tabbas da tasan inda zata nemo aure da taje ta nemo shi tayi kodan ta huta da abinda ake mata a cikin gidan su.
^^^^^^
"Ai ya fad'a min wallahi da ni ya samu bazai k'ara aure ba, matar na tasa fa yace kawai hakuri yake da ita ba wani jin dadin ta yake ba" Asiya ta fad'a tana kallon kawar ta Safina cikin murmushi wanda yake nuni da farin cikin abinda yake furtawa.
Safina ta bata hannu suka tafa tace, "kice zaki walwala a gidan ita kuma zata zama yar kallo." Dariya tayi tace, "Bari kawai, shiyasa tun yanzu nake cika nake batsewa dan bana son ya samu wani nak'asu a jikina da uwar gidan sa zata zarce ni."
"Kin yi min daidai tawan, Gashi an cafarko wuyan dan banza" ta fad'a tana kama tsintsinyar hannun ta suka sake kwashewa da dariya.
Anty Fauziyya ce ta shigo tana fad’in, "ke in kuma tare da Safina bakya ji bakya gani, to iyayen Yusuf sunzo har sun koma." Ido ta zaro ta dafe kirji tace, "Dan girman Allah da gaske Anty?." Ta Harare ta tace, "Da gaske mana."
"Ya akayi to? An tsayar da lokacin?." Anty tayi dariya tace, "Ga Baban can yana neman kwafsa miki wai yace suje zai neme su."
Tsaye ta mik’e tace,"Kamar ya kenan?."
"Kamar yadda kika ji, Gashi can suna maganar da Umma" ta fad'a Tana fita sai kuwa Asiya tabi bayan ta a guje.
A kofar d’akin Umma ta tsaya taji muryar Umma na cewa, "Ban gane kace zaka neme su ba, akan me ba'a tsayar da ranar auren ba?." Baba yace, "Ina so nayi bincike a kan yaron ne sosai bana so a sake maimaita abinda akayi a lokacin auren Maimuna." Umma tace, "binciken me za'ayi to? Waye bai San iyayen yaron ba?."
Baba yace, "Maganar yaron ake bata iyayen sa ba, shi muke so mu san waye shi ba iyayen sa ba. An kawo min wani labari duk da ban tabbatar ba ance min yaron yana...." Umma tyi saurin dakatar dashi tace, "Yana me? Me akace yana yi, neman mata ko?. Kai Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ban San me na yiwa dangin ka ba da inda suka ga alkhairi ya tunkaro ni sai sun saka k'afa sun hamb'arar dashi. Daga ji yaron zai auri Asiya har an fara lallab’owa ana fad’a maka magana Mara dadi a Kansa kawai dan a raba su ko?."
Baba ya girgiza kai yace, "Wanda ya fad’a min bashi da alaqa da dangina, kuma bazai min ‘karya dan son ransa ba."
"To wallahi tallahi ko yankan kai akace Yusuf yana yi babu abinda zai hana Asiya auren sa sai dai d'an bakin ciki ya mutu wallahi, babu damar aga arzuki yana kallona sai an samu wanda zai nuna min bak'in cikin sa k'arara dan kawai an tsane ni an tsani y'ay'ana?. Ka toshe kunen ka kome za'a zo a fad'a maka auren nan babu fashi wallahi."
Kallon ta kawai Baba yake har ta kai k’arshe sannan yace, "Baki ma tsaya kinji me akace min din a Kansa ba kina ta wannan kunfar bakin."
"Bana so naji, bana so wallahi. Kuma ba wani bincike da za'a tsaya yi yadda suka zo da kud’in aure da saka rana nan da sati takwas kayi musu waya kawai kace ka amince, akan wanne dalili zaka ce sai anyi wani bincike bayan kasan komai akan yaron. Bana son haka wallahi gwara ayi a gama a wuce wajan."
Baba yace, "In kuma abinda aka fad'a ya tabbata fa?." Umma tace, "Bazai ma tabbata ba, Kaga malam in baza ka Shege gaba akan auren nan ba wallahi sai naje na samu y’an uwana suyi komai a gama. Sai kece kana yiwa y'arka bak’in ciki….?, bayan in ta shiga gidan arzuki kaine ka shiga yawo da k'afar nan da kake watarana sai ka ganka da mota amma ka dinga fad’ar wannan maganar." Baba ya sauke numfashi yace, "Kwanciyar hankali nake so ta samu ba kud’i ba."
"To akwai kwanciyar hankalin da ya wuce kudi? Kai kanka da kana da kud'in ai baza ka tsaya ja in ja ba."
"To naji, amma wata biyu yayi kusa a barshi wata biyar kafin nan an samu abubuwan da za'a yi na kai mata d'aki."
Wata harara tayi masa tace, "Kai kake musu daman?, Ina ga ko pad baka tab’a bata ta siya ba komai ni nake mata ko?, to na shirya zan iya yi mata kayan gado koda guda goma ne, babu ruwan ka kawai a tsayar da ranar." Zuciyar Baba sam babu dad'i ,d'aci yake ji a zuciyar sa hakan ya saka shi yayi shiru baice komai ba. Umma ta kuma cewa, "Ka kira mahaifin nasa ka fada masa magana kayi jugum, ‘karya na fad’a ne ko me?."
Baba yace, "Zan kira sai da safe yanzu dare ya riga yayi. Amma kafin nan inaso ki san duk abinda ya biyo baya a auren Asiya babu ruwana, Allah ya sani nayi abinda zan iya matsayina na mahaifinta." Umma tace, "babu abinda zai biyo baya ma sai alkhairi, a daina mana fata in sha allah sai dai y’an bak'in ciki su mutu."
Baba bai iya cewa komai ba ya tashi ya fita yana fita Asiya da Fauziyya suka shigo Asiya tace, "Umma me baban yace?."
"Ke rabu dashi, munafukai har sun fara zuga shi wai ayi bincike, babu abinda za'a bincika waye bai San uban yusuf ba?." Fauziyya tace, "Kinga Kawu D’anlami..?; Sam baya so yaga min cigaba a gidan nan, Kullum cikin tsine mana suke mune y'an duniya nasa kuma masu tarbiyya."
Umma tace, "Barni dasu ai nafi k’arfin su wallahi, daidai nake da k’ugun kowa a cikin su." Asiya tace, "Yanzu Umma an gama komai?." Umma tace, "Gobe zai kıra su ya sanar dasu nan da sati takwas za'ayi auren daman da haka suka zo. Sai ki fara shiri dan ko kwana daya bana so a k'ara." Fauziyya tace, "Umma babar Yusuf na samu labarin tana son uwar gidan sa fa sosai, kar ta bamu matsala nan gaba."
Umma taja tsaki tace, "dukkan su a tafin hannuna suke, dashi Yusuf din, da matar sa, da uwar sa, da kowa nasa sai nayi maganin su akan Asiya. Asiya bazata tab'a zama bora a gidan ba wallahi sai dai mowa, in muka ga uwar gidan zata kawo mana matsala cillata waje zamuyi. Ke bazan d'auki rainin da aka yi wa Maimuna bafa, wannan Karon shiri zanyi Asiya badai ta bar gidan Yusuf ba sai dai ita matar tasa ta bari."
Dariya sukayi dükkan su Fauziyya tace, "Allah ya bar mana Hajiiya Umma. Daman kuma ba wani son matar tasa yake sosai ba, kinga sai muyi amfani da wannan damar mu dama."
"Sakina tace yana son matar sa amma hakan bazai hana mu nasara a kan su ba, kudai ku zuba ido ai sai Asiya ta zamar musu ciwon ido, badai babar sa bata son auren nan.....hmm muje zuwa" ta fad'a tana tashi ta fita Asiya dad'i yayi mata yawa ta fita da sauri zuwa d'akin su dan tayi waya da habibin ta.
#Share
#vote
#Nana haleema
#F5